← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 48

Sashe 31

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kewar ta yake ji sosai, burin sa ya ganta amma ya rasa ta wacce hanya zai bi hakan ta kasance. Ranar bai ma fita ba yana gida tunani yayi masa yawa akan Manal, da ya kulle ido ita yake gani zuciyar sa na harbawa sosai alamun soyayyar da yake mata mai ™arfin gaske ce. Duk ya damu, tunanin kar yaje an mata miji gashi soyayya ta gama kama shi, hakan ya hana shi nutsuwa gabaWaya shine dalilin da ya hana shi fita.

Yana zaune yana wannan tunani Huzaifa ya kira shi ya Wauka Huzaifa yace, "Bebi baza ka fito bane har rana tayi?." Bebi ya sauke numfashi yace, "gaskiya ba zan shigo ba sai zuwa yamma."

"Amma akwai mutanen da suke jiran ka, akwai wanda aka kawo ma yanzu kuma matsalar zuciya ne. Da zaka daure da kazo Win ka san David da Yasir  suna off." Ajiyar zuciya yayi yace, "gani nan" ya faWa yana yanke wayar ya tashi daga inda yake ya saka kaya ya fito.

Ganin motar Abba tana nan sai ya shiga wajan sa ya same shi a zaune da alama bai san ya shigo ba duk da yayi sallama, Abban yana zaune yana magana shi kaWai yana cewa, "Wai me yake damun wayar yarinyar nan ne? Kwana biyu a kashe Allah yasa ba fushi tayi ba."

Girgiza kai yayi domin kuwa ya fara tabbatar da Abban su yana harka da ´an mata a waje, duk da bai san ala™ar su ba amma a yadda ya damu hakan ya nuna ya damu da yarinyar sosai.

"Asslaamu alaikum". Bebi ya sake faWa yana kallon sa, sai a sannan ya juya ya ajjiye wayar yace, "Wa'alaika salam, Bebi yau ba'a fita ba?."

Ya ™arasa ya zauna a ™asa yace, "barka da rana."

"Barka dai, ya aiki?."

"Alhamdulillah. Yanzu zan fita sai naga motar ka na shigo mu gaisa."

"Ka kyauta sosai, Allah ya taimaka." Ya sauke numfashi sannan yace, "Amin" ya mi™e yace, "a tashi lafiya" ya faWa yana fita.

Yana fitowa compound na gidan Lubna na shigowa, haka nan bai amince da ita ba duk da hankalin sa ya kwanta kwana biyu baya ganin Kamal baya ganin Mujahid amma yanayin yadda take murmushi ita kaWai kamar bata da gaskiya.

Ganin yana kallon ta sai ta tsargu ta ™araso inda yake tace, "ina wuni."

"Daga ina kike?."

"Mamy ce ta aike ni?."

"Shine sai ki fita ke kaWai?." Lubna tace, "ita tace naje." Baice komai ba ya wuce ta bishi da harara ta wuce Sangaren su itama.

Yana shiga wajan Mama bata falo ya wuce Waki ta ya samu tana Waura Wankwali ya zauna tace, "kace min yau babu inda zaka je gashi naga ka shirya." Bebi yace, "ana nema na ne a asibiti shiyasa zan tafi." Ya sake kallon ta yace, "Mummy Abba ya dawo." Mama tace, "na sani, sai me?."

"Mummy gaskiya a rashin zaman da Abba baya yi a gida nan wallahi da saka hannun ku ciki." Mama ta kalle shi tace, "Bebi akwai abinda baza ka gane bane shiyasa, mahaifi ne a wajan ka shiyasa bana son buWe bakina a gaban ka, amma in kana yi min irin haka wata ran zan faWi  kalmar da zaka kwana baka manta ba."

Bebi yace, "shikenan yanzu haka za'a zauna kenan? Kamar ba mijin ku ba don Allah?." Mama bata ce komai ba sai ta canja maganar tace, "da alama dai wannan yaron saurayin Mimi shine mijin ta, dan Yayan ku yace yaje ya samu Daddyn ku a kan maganar da." Bebi ya gigita kai yace, "Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta amsa da amin ya mi™e yace, "sauri nake Mummy sai na dawo."

"Allah ya kiyaye, dole ka gudu ai saboda kar nayi zancen Rumana, daWin ta a nan zan kwana ai." Baice komai ba ya wuce dan kuwa haka Win ne, yanzu zata masa zancen yaje ya samu Yayan mahaifin sa da suke kira Daddy da maganar Rumana shi kuma baya so.

Bebi koda ya fita sai ya samu kansa da bin unguwar su Manal, umarnin zuciyar sa kawai yake  bi a lokacin ban da son ganin ta babu abinda yake so.  a daidai layin ya faka motar yana kallon layin zuciyar sa na wani irin bugawa tana tura shi akan yaje gidan nasu amma ya kasa.

Kamar ance ya juya ya ganta ri™e da leda a hannun ta ita da Haroun tana murmushi shima haka sun jera sun shiga layin gidan.

Gaban sa ya faWi sosai saboda abubuwa biyu da suka haWar masa a lokacin wanda yake gudun faruwar sa, na farko ganin da yayi mata ya saka gaban sa ya faWi haka kawai, na biyu kuma ganin ta da Haroun ya saka zuciyar sa a ruWani, domin bai san ala™ar su da shi ba duba da murmushin da yaga tana yi masa.

Numfashi ya sauke ya kwantar da kansa a kan sitiyarin motar yace, "kaiii! Meyasa zan faWa soyayya cikin ™aramin lokaci haka? Meyasa?!." Ya jima a haka kafin ya mi™e zaune ya kunna motar ya ja ya tafi jiki a sanyaye gabaWaya bashi da kuzari. Bai je office ba sai da ya fara ganin wanda aka kawo Win tun a ™asa kafin ya wuce office yaga mutanen da suke gaban sa.

Tashi yayi ya fito suka haWu  da Dr Hadiza tace, "Dr akwai meeting yanzu." Ya kalle ta yace, "kuje ku yi bazan iya attending."

"But why?."

"Please!" Ya faWa kawai yana barin wajan a lokacin Huzaifa yazo ta kalle shi tace, "yace bazai attending meeting Win ba." Huzaifa yace, "share shi muje muyi abinda yake gaban mu kawai."

Cikin mota kawai ya koma ya zauna ya rasa abinda yake damun zuciyar sa a wannan lokacin, ji yake kamar ya fashe da kuka saboda abinda yake ji yayi masa nauyi a cikin zuciyar sa.  Ya rasa yadda zai sarrafa kansa, nauyi yake ji a ™irjin sa ya rasa inda zai saka kansa yaji daWi.

Har suka fito daga meeting Win yana cikin mota a zaune sai waya ake masa amma ya kasa kallon wayar ma balle ya Wauka dan baya cikin nutsuwar sa. Kulle motar yayi kawai ya kunna ya ja motar ya fita daga gidan. Babban asibiti ya wuce bai jima ba ya sake wucewa gida ko wajan Mummy bai shiga ba ya shiga Wakin sa yana ji kamar ya zubar da hawaye saboda kaifin soyayyar da take sukar zuciyar sa.

Bayan sallar magriba Huzaifa da Hamza suka zo gidan wajan Bebi, har wajan Mummy suka je suka gaishe ta take cewa, "mutumin naku ma da ya dawo bai shigo min ba, na lura tun Wazu kamar bashi da lafiya." Hamza yace, "Mun ga hakan, yau ko damu bai haWu ba ya dawo gida." Huzaifa yace, "bara muje wajan sa Mama." Ta amsa suka fita suka shiga wajan Bebi suka same shi a kan kujera ya harWe hannayen sa waje Waya yana kallon ™asa.

Hamza ya zauna kusa dashi yace, "Me yake faruwa ne ka koma haka Bebi?." Šago kai yayi ya kalle su ya sauke numfashi yace, "ni kaina ban sani ba, wani iri nake ji a zuciyata kamar nayi kuka. Zuciyata tayi min nauyi sosai, na rasa gane kaina nima."

Huzaifa yace, "me ya kawo hakan?."

Tsaki yayi a bayyane kafin yace, "Wata yarinya ce, haka nan na kasa daina tunanin ta." Hamza yayi dariyar sha™iyanci yace, "shine ka shiga wannan damuwar Bebi?, Kamata yayi kayi murna ai ka samu wacce kake so ko babu komai ka samu mafita akan lamarin Rumana."

Huzaifa yace, "Yanzu akan wannan ne duk ka tayar mana da hankali?, wallahi na Wauka wani babban abu ne yake shirin faruwa ko ya faru."

Bebi yace, "ni ba Waga hankalina nayi ba, na tabbatar ina sonta na amince tun ban amince ba na yarda yanzu, amma abin ne yayi min yawa a zuciyata, kwata-kwata magana sau biyar bana tunanin ta shiga tsakanina da ita, amma yadda nake ji zuciyata na bugawa soyyayar ta tayi yawa." Hamza yace, "tsakanin so Win kenan Bebi. Kuma shi so ina ruwan sa da baku yi doguwar magana ba? Daga kallo Waya ana faWawa soyayya."

Bebi a raunane yace, "tun yanzu?, Tun kafin mu saba ina jin haka a kanta ina ga nan gaba?. Wallahi bana son soyayyar da zata wahalar dani Allah ya sani, bana son soyayyar da zata hanani sukuni. Can you imagine Wazu kafin na tafi office sai da naje bakin layin su kawai ko zan ganta?. Na kuwa ganta Win, amma ita da wani namiji da ban san ala™ar su ba. Yanzu wannan soyayyar da na sakawa zuciyata in an yi mata miji fa ya zan yi?."

Huzaifa ya girgiza kai yana murmushi, Allah ne ya kama shi ko yaushe gani yake shi zai saka soyayya a zuciyar sa dan haka sai yadda yaso, Gashi Allah ya nuna masa iyakar sa, ya nuna masa shi ke saka soyayya a zuciyar bayin sa. Huzaifa yace, "Wannan ba abin damuwa bane, kayi addu'a akan lamarin ta?."

"Nayi, tunda na fara tunanin ta na fara addu'a, sai bayan nayi addu'ar nake ji tana sake shiga raina sosai." Hamza yace, "magana ta ™are kawai, kaje ka nemi izinin ganin ta wajan iyayen ta, kaga in kaje in ma da maganar auren a kan ta zaka ji."

Ya girgiza kai yana kallom su da manyan idanun sa yace, "ina niyar hakan, amma zuciyata baza ta jure ace na yi mata miji ba Hamza, a yadda nake ji in akace an yi mata miji zan...." Sai kuma yayi shiru yana girgiza kai.

Hamza yayi dariya yace, "kar ka damu khairan in sha Allah, mallakin ka ce  wannan yarinyar da izinin Allah." Huzaifa dariya yake yi sosai yana kallon Bebi kafin yace, "Bebin Mummy manya, Wai wacece yarinyar ma?." Hararar sa yayi dan kuwa bazai faWa musu ba sai ya tabbatar komai ya tabbata sannan zasu san wacece.

Hamza ma dariyar yake yi yace, "ka share batun Huzaifa, kaje gobe ka samu iyayen ta akan maganar." Bebi ya wara ido yace, "har sai gobe? Meye amfanin yau?." Hamza da mamakin gaggawar Bebi yace, "kana da theater amma kace yau ko?."
Chapter 31 · 0% Book details