← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 48

Sashe 37

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaka aure ta mana, kaima ai baza yi mata ™arya ba?." Ya girgiza kai yace, "wai kasan yadda na tsani batun aure akan yarinyar nan?." Hamza yace, '"mafita kake nema, zancen ka tsana duk bai tashi ba ai Bebi. Dan Mama zaka yi ba don ita ba." Ya sauke numfashi yayi shiru baice komai ba dan bai san abinda zaiyi din ba.

Mujahid yana tsaye a bayan su yana jin duk abinda suke faWa,yazo ya yi masa albishir akan yayi nasarar fara soyayya da ™anwar sa sai yaji abinda yafi soyayya da ™anwar sa ma dadi, yana tsaye yana girgiza kai a zuciyar sa tana faWa masa ba mutuncin ™anwar sa ya kamata ya taSa ba, wacce yake so ya kamata ya fara da ita domin shima abinda yake so ya raba shi dashi. Murmushi yayi daga bayan su yace, "Ina da Shawara...." Duk a tare suka juya suna kallon sa cike da mamaki.

Nana Haleema>ØBÝ>ØöÞ<Øûß

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

                ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

*Page 023*

HaWa idanu suka yi da Mujahid yana tsaye yana aiko musu murmushin da ya saba na yaudara yace, "Ya naga dukkan ku kuna kallona?, Kun manta Mujahid abokin ku ne?." Hamza  ya kalle shi yace, "Yaushe ka shigo nan?."

"Ban wani jima ba, daman wajan Bebi nazo."

Ya tako ya ™araso zuwa inda suke ya kalli Bebi da shima shi yake kallo tace, "Yayan mu barka da dare, nasan da cewa Yayan mu bai san da cewa soyayya ta da Lubna tayi nisa ba ko?." Sai yayi dariya yace, "kai a ganin ka wai zaka iya raba mu da Lubna ne? Ai na riga na shiga zuciyar Lubna mai raba mu a wannan lokacin babu shi, in kaga Lubna ta bar ni tabbas lokacin hakan ne ya yi a wajena."

Huzaifa yace, "Mujahid ka faWi abinda ya kawo ka bama son maganar banza da wofi." Yayi ´ar dariya yana kallon hotunan Adnan da suke manne a bangon office Win wanda ya samu awards a ™asar india da saudia da sauran wurare, ya kalli hoton su su huWu ranar da aka buWe asibitin yayi murmushi yace, "cardiologist Adnan, ya kamata ka duba zuciyar ™anwar ka tunda aikin ka ne zaka cire mata Mujahid in ka isa. Kana ganin kamar kwana biyu bama haWuwa saboda baka ganina ko?" Ya faWa yana Wauko wayar sa ya nuna masa yace, "to kalli wannan Kaga Yaya."

Kallon fuskar wayar Adnan yayi yaga hoton su ne da kayan da ya ganta ta ta shigo gidan ya kalle shi yayi dariya yace, "Lubna na sona, ko yanzu nace Lubna tazo g1dana ta same ni zata zo zan kuma zan iya yin duk abinda nake so da ita baka isa ka hanani ba, sai naga bayan license Wina me zaka sake a karSa. But I found something important better than this, so maybe I'll get it twice, nayi al™awarin sai na saka ka rasa farin cikin ka kamar yadda ka saka na rasa nawa."

Bebi ya kalle shi yace, "Baka isa kayi nasara a kaina ba Mujahid, na fika ™arfin ikon samun nasara a ko yaushe saboda zuciyata a tsarkake take, baka isa ka yiwa Lubna komai ba in kuma ka iya kayi Win." Ya ™yal™yale da dariya yana kallon su yace, "kun ji abinda yace ko?" Ya kalli Bebi yace, "Wallahil azim sai nayi nasara a kan ka Bebi, ko yanzu ko nan gaba sai na saka maka ™una a zuciyar ka kamar yadda ka saka min."

Bebi ya gyara tsayawa yace, "go ahead." Huzaifa ya kalle shi yace, "babu nasarar da zaka iya yi Mujahid, domin kuwa komai ya faru kaine ka jawowa kanka ba wani ba, kuma ko yaushe gaskiya ce take nasara ba ™arya ba."

Mujahid ya girgiza kai yace, "mu zuba dai mu gani" yana faWa ya juya ya fice suka bishi da kallo har ya Sace. Bebi ya kalle su yace, "Kun gani ko? Yarinyar nan Lubna daman nasan baza ta rabu da Mujahid ba, sun yi min shiru suna ganin kamar bana kula da komai amma nasan suna haWuwa har ita Maryam suna haWuwa da Kamal, so suke su kashe ni su huta kawai."

Hamza ya sauke ajiyar zuciya yace, "Kayi ha™uri Bebi, babu abinda zai faru in sha Allah. Amma laifi na Maryam ne wallahi, ita Lubna ka ture maganar ta yarinya ce dole zai yi galaba akan zuciyar ta, ka sani na sani ko da muna karatu Mujahid ya iya tsara ´an mata, lokaci Waya yake yake galaba a kansu, amma Maryam fa?. Miji ya sake ki kuna da yara biyu shi bai mayar dake ba kuma ya dinga bibiyar ki kina biye masa?. Ko me ya faru ita ta jawo."

Ya sauke ajiyar zuciya yace, "haka wasu matan suke yanzu ai, miji zai sake ki amma rashin hankali da sanin ciwon kai sai ya saka ya dinga bibiyar ki kuma kina sauraren sa, nida Kamal a office Win hisba yace ko da akwai ragowar igiya bazai mayar da ita ba, amma da yake bata san abinda take yi take zuwa inda yake wai da sunan tattaunawa akan batun yara."

Huzaifa yace, "Abba ne zai maganin lamarin Maryam fa, kai tana ganin ™anin tane baka isa ka hana ta ta hanu ba." Ya kalle shi cikin ™unar rai yace, "Abba! Hmm." Abinda yace kawai kenan.

Knocking ™ofar aka yi aka shigo wata nurse tace, "Dr akwai wanda aka kawo yanzu ™arfe ya soke shi a zuciyar sa, "it's emergency."

"Bebi yace, "They come with police?."

"Yes sir."

"Okay I'm coming" ya faWa ya kalle su yace, "Zamu ™arasa maganar, ina zuwa." Dukkan su fita suka yi ya ™arasa wajan mara lafiyaa, a nan yaga ™arfe ne dogo aka soka masa dan a sume ma yake,  ya kalle shi yana karanta yanayin shigar ™arfen sukayi handling case Win da police ya kalli wanda ya kawo shi yace, "garin ya hakan ta kasance?" ya faWa a lokacin ana Waukar sa aka shiga dashi theatre room.

"Matar sace ta soke shi." Bebi da mamaki yace, "matar shi?."

"Eh wallahi likita." Ya girgiza kai kawai ya wuce zuwa Wakin, nan da nan aka shiga aikin cire masa ™arfin Allah ya taimaka ma a gefen zuciyar ne da a tsakiya ne da yanzu ba labarin ake ba.

Kusan mintina arba'in aka kwashe a ciki kafin ya fito zuwa lokacin ´an uwan sa sun ™aru a wajan ya kalle su yace, "kar ku damu zai samu Lafiya." Suka amsa a tare ya wuce su ya zauna akan kujera yayi shiru.

Raba dare yayi ranar a babban asibiti yana aiki yaso tafiya g1da ma sai ya fasa kawai ya kwana a ciki, da asuba  ya koma gida a nan ya samu yayi bacci sosai sai azahar ya farka. Da ya shiga wajan Mama bata nan ya fita suka gaisa da Mamy ya koma ya zauna.

Wayar sa ya Wauka yana kallon lambar Manal da ta bashi jiya yana tunanin ya kira ko kuma kar ya kira, "in na kira nace mata meye?." Ya kifa wayar bai san ya kira Win ba yana can yana kallon wani wajan yaji ance, "Hello." Da sauri ya kalli wayar yaga seconds suna tafiya alamun ya kira har an Wauka yace, "Hello."

Manal daga can Sangaren ta gane maganar sa amma sai taso raina masa hankali sai tace, "ina ji, da wa nake magana?." Shiru yayi bai bata amsa ba jin wai da take magana ta raina masa hankali Manal tace, "na kashe kenan?."

"Kina so kice baki gane mai magana ba?."

"Inda na gane bazan tambaya ba." Yayi murmushi domin haka nan yaji a jikin sa ™arya take yi yace, "okay, basai kin san waye ba zaki iya cewa Mama ina gaishe ta."

"Sai nace Mama wani ya kira ban san shi ba yace yana gaishe ki?."

"Yeah you can." Murmushi yaji tayi yasan daman ta gane shi rainin hankali ne kawai sai yace, "Adnan ke magana, duk da na san kin sani." Yayi murmushi tace, "ina yini."

"Lafiya lau, ya jikin?."

"Alhadulillah, na samu lafiya."

Bebi yace, "Allah ya ™ara lafiya." Ta amsa da amin yace, "kina cin cucumber Win?." Manal tace, "eh." "Ki daure zai daidai miki blood sugar Win." Bata amsa ba yace, "meye real name Win ki?."

"Fatima."

"A ina kika tsaya a karatu?."

"Secondary school."

"Baki da burin cigaba da karatun?."

"Ina so, amma nafi son culinary school."

Shiru ya biyo baya daman ya jima da fahimtar tana da magana sosai sai yace, "You're so good in kitchen?." Yaji tayi murmushi tace, "i think so." DaWin waya da ita yake ji sosai komai tana bashi amsa in ya tambaya kamar kar su daina sai yaji waya na zuwa ya kalla ganin daga asibiti ne sai yace mata, "Kashe kiran it's emergency." Datse kiran tayi ya Wauki waccan yayi shiru ana faWa masa kafin ya tashi ya fita.

Cikin kwanaki biyu Manal da Adnan sun saba sosai duk da babu wani kalaman soyayya da yake yi mata in ya kira ta, hira ce akan abinda ya shafe ta sai yanayin jikin ta dana Mama bayan wannan babu wani abun da yake ce mata. Shi a wajan sa kalaman soyayya kamar sai yara, shi kawai sai ya tsaya yana wani tsara kalamai, ai tunda yaje gidan su da niyar aure zancen soyayya ya ™are. Tunda yaje zuwan farko bai sake zuwa ba sai dai suna waya sun saba har tana mamakin dama yana magana kuma yana da kirki haka.

       A ranar litinin yayi nufin zuwa gidan nasu bayan sallar i'sha kamar wancan lokacin yaje ya haWu da Haroun a waje  suka gaisa ya raka shi har inda suka zauna a wancan lokacin.

Bai jima sosai da zama ba ta shigo Wakin da haske wutar solar amma ba sosai ba kasancewar babu wuta ta zauna bayan tayi sallama tace, "ina yini." Khamshin turaren ta yayi masa yawa sosai hakan ya saka shi kulle ido ya buWe, ya dafe kansa da lokaci Waya ya harbawa. Shiru yayi na wani lokaci kafin ya kalle ta yace, "Manal i forgot to tell you that bana son khamshin turare da yawa, wannan turaren na ki yayi min yawa sosai, yana bani ciwon kai sometimes it cause dizziness."
Chapter 37 · 0% Book details