← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 48

Sashe 36

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi murmushi yace, "Kina da wanda kike so?." Ta kalle shi ya Waga mata kai yace, "na faWa miki bana son ™arya ko Soye-Soye, ina son magana kai tsaye."

Tayi ´ar dariya tace, "™arya ba halina bane, bazan kuma fara daga yau ba."

"Okay Answer me."

"Ni bana dashi, dan bani da wannan lokacin, kula da Mamana shi na saka a gaba."  Ya girgiza kai cikin jin daWin hakan yace, "Zaki iya saka Adnan zuciyar ki?."

"Sai na duba naga yuwar hakan" ta faWa bata kalle shi ba. Yayi murmushi yace, "haka ne, amma nasan you most love him." Sai tayi dariya tace, "really? For what reason?."

"Saboda na yarda da kaina." Tayi murmushi bata sake magana ba yana kallon ta, Allah ya sani yana sonta matu™ar so, daga lokacin da ya fara sonta soyayyar ta tayi masa kamu sosai musamman yanzu da take gashi gata tana kuma murmushi tare da magana mai sanyi cikin muryar ta mai za™i.

HaWa ido suka yi sai yace, "Ki bani phone number ki." Ta kalle shi ido cikin ido kamar zata yi magana sai ta fasa ya mi™a mata waya ta karSa tana saaka number kira yana shigowa taga an rubuta Rumana.

Mi™a masa wayar tayi ya karSa ganin wace take kiran sai ya ajjiye bai Wauka ba suka yi shiru babu mai magana a cikin su. Kallon ta yake yi yana ji farin ciki sosai a zuciyar sa, Allah ya sani yana son Manal so mai yawa. ˜ara wayar ta yi ganin mai kiran sai ta Wauka tace, "Yaya."

Bai ji me akace mata ba sai yaji tace, "subscription din ya ™are." Cikin shagwaSa yaji ta kuma cewa, "nidai Yaya kawai ka shigo yanzu, in kace sai gobe ni bana so na kai gobe ban gama ba" ta faWa kamar zatayi kuka. Sai yaga tayi murmushi tace, "to ina jira." Ta yanke wayar ta ajjiye tana murmushi yana kallon ta sai suka haWa ido ta sake faWaWa murmushin tace, "na tafi?."

Wani irin abu yake ji a zuciyar sa na tasowa yana game ilahirin jikin sa, ko ba'a faWa ba yasan kishi ne hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallon ta. Allah ya sani yana da kishi shi kansa ya sani. Ya sauke numfashi domin ya san kishin Manal sosai, zuciyar sa zafi take yi jin tana waya da wani.

Ya sauke numfashi yace, "Manal you have to be careful ba komai nake iya controlling a kai ba lokacin. Kina waya a gabana hakan zai bai min daWi ba."

Manal ita mamaki ma yake bata daga zuwa zance zuwan farko sai a dinga kafa mata sharaWi kamar mijin ta?. Sai magana yake yi dan ita bata Wauka ma yana da magana haka ba, wai ba komai yake controlling ba kamar wanda yake auren ta. Ta kalle tace, "Yayana ne." Bai bata amsa ba sai kallon ta da yake yi tana kallon sa kafin ya janye Idon sa yace, "Ban san kina da Yaya ba."

"Ynzu na sanar da kai." Ya kalli gefe ya kulle ido ya buWe, in ba soyayya ba taya wannan yarinyar zata zauna a gaban sa yana faWa tana faWa?. Ya tabbatar ko Mimi zata iya girmar ta, amma itace yana faWa tana mayar masa inda sune da yanzu zanen yatsun sa sun bayyana a fuskar su.

Sake kallon ta yayi ta sauke kai ™asa tana wasa da wayar ta yace, "sai da safe."

"Allah ya tashe mu Lafiya" ya faWa tana tashi itama ya ajjiye kuWi a inda ya tashi baice komai ba ya fita ta bishi da kallo, ita dariya ma ya bata wallahi da mamaki, daga zuwa zance sai a fara mata zancen bana son kaza ba'a son kaza.

A haka ta koma cikin gidan Mama tace, "Manal ina fatan kin amince dashi?."

"Wanne irin na amince Mama? Kina ji yana kafa min sharaWi daga zuwan farko?, shi baya son ™arya kuma yana da kishi kamar wanda ya haife ni ko yake aurena."

Mama tayi dariya tasan halin Manal Win ta bata son rainin hankali sannan akwai faWa duk da kuma akwai surutu kamar aku tace, "ai ya faWa miki gaskiya ne Manal, gwara ku saba tun yanzu."

"Yaya Haroun ne fa kawai yayi min waya dan na Wauka muna waya shine ya dinga kallona irin zai zane Win nan fa Mama, shine aka fara cemin ana da kishi" ta faWa tana dariya.

Mama ma dariyar tayi tace, "kema da laifin ki meye na Waukar waya a gaban sa?."

"To Mama Yaya Haroun ne fa?."

"Na sani ai, amma ai ba™o ne dake sai ki bari ai kin fito sai ku gaisa."

Manal tayi dariya Mama tace, "kina jin a zuciyar ki zaki iya amincewa dashi?." Manal tace, "gashi nan dai Mama, bashi da fara'a ko kusa ni sai jiya da yau naga dariya, sannan yana da shariya da faWa."

Mama tayi dariya sosai tace, "Manali ta kenan, Nidai ina miki sha'awar aure sa duk da bana ganin rashin fara'ar tasa." Tayi dariya itama tace, "to Mama zamu gani dai" ta faWa tana tashi ta shiga Wakin su ita da Mubeena tana dariya dan bata Soyewa Mama komai.

Shi kuwa farin ciki farin ciki, Sacin rai Sacin rai haka ya koma gida, bai yi niyar shiga wajan Mama bama ta window ta gano shi ta kira shi ya shiga ta bi shi da kallon tuhuma tace, "zance kaje ne Bebi?."

Ya kalli Maman alamun bashi da gaskiya zaiyi magana tace, "in ma can kaje na faWa maka kayi ganganci, kana Satawa ko wacece lokaci ne domin kuwa kai mallakin Rumana ne, ya kamata ka san da wannan tun ba yanzu ba, babu wata mace da zata zama mallakin ta matu™ar Rumana tana da rai. Sannan gobe ba jibi, kaje ka samu Yayan mahaifin ka aje gidan su Rumana a nemo maka auren ta, kar kayi min bayani akan wata mace na riga na faWa maka tun ba yau ba. Indai ina raye baka da mata sai Rumana ka jingine ko wacece a gefe, in kuma ban isa da kai ba dai zan gani" tana gama faWa masa haka ta koma ciki. jikin sa yayi sanyi sosai, gashi soyayyar Manal tayi masa kamun da bazai iya ha™ura da ita ba, gashi kuma dole yayi abinda Mama take so, to ya zai yi?.

Yana shiga Waki zama yayi a kan kujera ya zubawa waje Waya ido cikin rashin sanin abinda zai yi, tashi yayi ya shiga Waki ya canja kaya zuwa ™ananu ya fito ya hau mota ya wuce asibiti.

Yana shiga da Dr Hadiza suka haWu zata fita tace, "barka da zuwa Dr." kai ya Waga mata kawai ya wuce ciki a reception ya tarar da Huzaifa yana niyar tafiya ganin ya wuce shi sai yabi bayan sa daman akwai abinda zai faWa masa.

HaWuwa suka yi da Hamza ya fito daga maternity yace, "Ga Bebi Win can yazo, muje muyi masa zancen ko?." Ya amsa suka wuce suka same shi a tsaye ya juya baya ya harWe hannayen sa a ™irji Hamza yace, "Yauwa Bebi kana ji, akwai machine Win nan da aka siyo to custom sun kama shi a jirgin ruwa, don Allah ka yiwa Abba magana bazai rasa sanin wani ba a sake su don Allah. In machine Win nan yazo mune asibitin farko da muka fara mallakar sa a kaf nigeria." Huzaifa yace, "Akwai sabbin ma'aikata da muke tunanin Wauka this year, shima yana da kyau ka nutsu mu duba cv Win su mu gani, ni nan da wasu kwanaki zan je Qatar Daddy yana son ganina, kaima kace min akwai contract Win ku da india."

Sai a sannan Bebi ya juyo ya kalle su yace, "kuyi abinda ya dace kawai, zan samu Abba na sanar dashi zancen machine Win. Amma batun wani members kawai ku yi." Huzaifa ya kalle shi yace, "akwai damuwa ne?."

Kamar jira yake yace, "Na rasa ya zanyi, Mummy tana cewa in ma akwai wacce nake so na ajjiye ta a gefe indai tana raye bani da mata kamar Rumana. Na shiga tashin hankali sosai, na farko bazan iya tsallake maganar ta ba, na biyu bana son Rumana a yanzu, na uku yarinyar da nake faWa muku Allah ya Wora min ™aunar ta fiye da tunanin ku. GabaWaya komai baya min daWi."

Hamza yace, "to kayi ha™uri ka aure su duka su biyun." Ya kalle shi yace, "wallahi bana son Rumana, in na aure ta kamar tayi nasara a kaina ne, kullum gadarar ta sai na aure ta ko bana so."

"Haka zaka yi ha™uri kayi na dan ita na dan saboda Mama, ita kuma waccan Win ka ha™ura da ita in da hali." Ya girgiza kai yace, "bazan iya ba wallahi, baku san abinda nake ji a kanta ba shiyasa ku ke cewa haka. Ban taSa son wani abu lokaci Waya kamar yadda nake son ta ba, bana so na rasa ta. Bana son Satawa Mummy rai, in akwai mai son farin cikin Mummy ni ne, amma....!" Sai bai ™arasa ba yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya.

Sun lura yayi rauni sosai, da alama abin ya taSa shi har zuciyar sa yake maganar. Huzaifa yace, "Ka cigaba da addu'a kawai, kar ka daina sauraren ita sabuwar saboda kana sonta, in duka matan kane sai ka aure su. Ni a shawara ta in Mama ta matsa ka samu kuyi magana kace mata zaka auri Rumana amma ta bari ka fara auren ita wacce ka ke so Win daga baya sai ka aure ta, zata iya amincewa saboda tasan baka yi mata ™arya sannan kuma itama Rumana an bata dama ta farko har ta auri wani bakai ba, duk da lokacin kana sonta ba'a matsa mata ba aka bari ta auri wani ba kai ba, kaima ya kamata a baka wannan damar."

"Anya Mummy zata amince kuwa? Bata da burin da ya wuce na auri Rumana."

"Zata iya amincewa mana ai ba ™in auren nata kayi ba ka fahimta?."

Ya kalli Huzaifa yace, "to ™arya nayi mata kenan ko da gasken zan aure ta Win?."
Chapter 36 · 0% Book details