← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 48

Sashe 42

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ka fahimta kuma kake tambaya ta? Kasan dai babu inda zan iya zuwa ko?." Huzaifa yayi dariya yace, "lallai soyayya tana wahalar da kai." Baice komai ba ya fita ya barshi ya shiga inda su Manal Win suke a lokacin ma Baba yazo suka gaisa ya bawa Baba glasses Win yace, "Wannan zata dinga amfani dashi, zai taimaka mata wajan gani in sha Allah."

Baba yace, "mun gode sosai Adnan, Allah yayi albarka." Yayi murmushi kaWan ya kalli Manal a lokacin ta kalle shi sai tayi masa murmushi ya Wauke kansa yace, "zan wuce gida yanzu, akwai wanda zai kai ku gida in kun gama shiryawa zai zo ku tafi." Mama tace, "ai mun gama ma mu tafi kawai." Adnan ya girgiza kai ya fita. Jim kaWan sai gashi tare da wani suka fita gabaWaya suka shiga mota ya tafi kai su shima ya hau mota ya tafi gida dan bacci yake ji matu™a.

Koda ya koma gida ko wajan Mama bai iya zuwa ba kai tsaye Waki ya wuce ya cire kayan jikin sa ya kwanta nan da nan bacci ya Wauke shi. Sha biyu na rana wayar sa ta tashe shi ya kalla yaga daga asibiti ne, kamar bazai Wauka ba sai kuma ya Wauke abinda akace masa ya saka shi sauke wayar ya mi™e da™yar ya shiga wanka.

Da sauri da sauri yake shiryawa ya gama ya fita ya gaisa da Mamy ya shiga wajan Mama Mimi tace bata nan ya hau mota ya koma asibitin, kansa har ciwo yake saboda bai samu bacci ba.

      Mama tayi wanka taji daWin jikin ta sosai suna zaune da Manal Maman su Surayya ta fita a lokacin Mubeena tazo ta zauna tace, "Mama ya jikin?." Mama tace, "da sau™i."

"Allah ya ™ara lafiya." Ta amsa da amin kafin Mama ta kalli Manal tace, "Baki faWa min ya kike ji a zuciyar ki akan maganar Adnan ba, har yanzu baki yanke hukunci ba?." Manal tayi shiru jin shirun Mama tace, "Ni dai ina miki sha'awar auren sa, duk ke zaki yanke abinda kike ganin daidai dake ne, amma ni kam ina so ki aure shi. Duk da ban san ya kammanin sa suke ba, amma yanayin maganar sa zai baka tabbacin nustuwar sa a zahirance."

Manal tayi murmushi a zuciyar ta tana ayyana daman ai shi zan aura in sha Allah, a zahiri sai tace, "Na yanke hukuncin ai Mama." Mama tace, "faWa min to mana."

Manal tayi dariya tana Soye fuska tace, "To Mama ki gane abinda nake nufi mana." Mama tayi dariya dan ta fahimta tace, "to na gane, Allah yasa shine mijin ki, Allah ya sa ya zamar miki na gari Manal. Burina daman ki samu mijin da zai kula min dake kuma na tabbatar kin samu." Tayi murmushi tana jin daWi a zuciyar ta.

Manal tace, "Mama bara naje wajan Surayya kin ji Mama tace bata da lafiya." Mama tace, "to yi sauri, duk da nasan zaki je ki bata labarin Adnan ne." Tayi dariya ta saka mayafi da takalmi ta fita. Gidan su Surayya Win ta shiga ta samu Mama zata aike ta farkon layi kawai suka fito tare suka jera suna hira.

A hanyar su ta dawowa da yake rana ce babu mutane sosai suna ta hira Manal taji an kira sunan ta daga baya, ta juya ta kalli wanda ya kira ta dan bata san shi ba hakan ya saka ta mamakin a ina ya santa. Ya ™araso yace, "Barkan ki, nasan baki sanni ba ko?." Bata yi magana ba yace, "Abokin Adnan ne ni, sunana Mujahid."

"To sai akayi me?" Ta faWa tana kallon sa. Yayi murmushi yana kallon ta yana kuma yaba kyaun ta yace, "in kina tantama zan nuna miki shaida" ya faWa yana Wauko wayar sa ya nuna mata hoton su ta kalli screen Win wayar yace, "abokin sa ne ni sosai, in kika tambaye shi zai faWa miki.."

Manal ta Waga ™afa zata tafi yace, "Nazo na sanar dake wata gaskiya akan Adnan. Manal Tsakani da Allah ba wai yana son ki bane, Adnan ´ar masu kuWi yake burin aure daidai shi, yana amafani dake ne saboda kina da kyau daga zarar ya samu abinda yake so shikenan zai mama gaban sa. Zan iya cewa kece mace ta goma da Adnan zai yaudara domin wannan halin sane, kar kiyi mamaki ko tunani akan wani abu kiyi tunani akan rayuwar ki."

Ya sake cewa, "na zaSi na sanar dake ne saboda naga ke marainiya ce mai kula da mahaifiyar ta, kiyi baya da Adnan kar ki amince da duk wani daWin bakin sa in ba haka ba nan gaba kaWan zaki dana sani" yana gama faWar hakan ya shiga mota ya tafi ya bar Manal tana kallon motar.

Kallon Surayya tayi Surayya itama ita take kallo tace, "kar wannan yayi tasiri a zuciyar ji, irin mutanen nan ne masu so lallai sai sun raba mutum da wanda yake so. Ni ban Wauka ana korarwa maza wacce suke so ba, na zata mata ake yiwa suma kuma daga na jikin ka yake faruwa. Don Allah ki share kawai mu wuce, da ganin wannan bana kirki bane, in haka halin Adnan Win yake da yanzu Baba ya raba ku."

Manal ta share maganar a lokacin suka tafi suna sake tattaunawa akan maganar Mujahid Win har suka je gida ta shiga g1da itama ta shiga gida zuciyar ta cike da sa™e sa™e.

Tana shiga Mama tace, "har kin dawo?."

"Eh Mama na dawo." Mama tace, "Yanzun Baba ya fita nake sanar dashi kin amince da auren Adnan ayi musu magana manya su shiga maganar." Manal ta yi shiru jin hakan sai Mama tace, "Lafiya kike?."

"Lafiya lau Mama, bacci nake ji" ta faWa tana tashi ta wuce ciki Mama ta girgiza kai kawai dan tasan akwai abinda yake damun ta.

Manal duniyar tunani ta tafi a wannan lokacin, in hakan da gaske ne ya zata yi kenan? In hakan da gaske ne kenan yazo ya lalata mata rayuwa ne ya gudu?. Dafe kanta tayi ta bayyane tace, "da gaske fa nayi mamaki, meyasa kaf matan garin nan ´an gayu masu wayewa da ilimi bai nemo wata ba sai ni?. Kuma tabbas a office Win sa akwai hoton su da wannan mutumin, kenan da gaske abokin sa ne?."

Shiru ta sake yi a lokacin Mubeena tazo ta zauna a inda take ta kalle ta dan tana bu™atar a bata shawara amma ba daga Mubeena ba, gabaWaya haushin Mubeena take ji hakan ya saka ta tashi ta bata waje ta koma da™in Mama ta kwanta ba dan tana jin baccin ba.

Tashi zaune tayi ta Wauki waya tana tunanin ko ta tambayi Huzaifa ne?. Shiru tayi ta ajjiye wayar ta koma ta kwanta ba tare da ta nemowa kanta mafita ba kuma bata kira Huzaifa ba.

      Bebi bai dawo gida ba sai magriba yana tsayawa yaga motar Kamal ta wuce sai kawai ya fasa shiga gidan ya karkata motar kai tsaye ya Wauki hanyar gidan iyayen su Kamal Win dan abin nasa yaga ya fara yawa.

A ™ofar gidan ya tsaya kasancewar gidan ba gate bane ya rasa yadda zaiyi ayi masa magana da mai gidan. Yaro ya gani zai wuce ya tsayar dashi ya aika gidan jim kaWan sai ga mahaifin nasa ya fito Adnan ya ™araa suka gaisa da girmamawa sannan yace, "Alhaji nasan baka sanni ba, sunana Adnan ni ™ani ne ga tsohuwar matar Kamal Maryam."

Sai fuskar sa ta washe yace, "to na gane ka yanzu, kana magana sai naga kama da Alhaji Mu'azzam Alhassan. Ya mahaifin naka da masu gidan?."

"Alhamdulillah."

"Mu shiga ciki." Adnan yace, "A'a nan ma yayi, ™orafi na kawo akan Kamal." Mahaifin sa yace, "wani abu ya faru ne?."

"Yana faruwa ma Alhaji, Kamal yana cigaba da bibiyar Maryam bayan babu aure a tsakanin su. Nasan itace ta bada fuska ita ya kamata na fara yiwa magana, nayi mata wanda suke gaba da ita ma sunyi,  shima Kanal Win na same shi nace indai akan yara ne babu damuwa duk sanda take son ganin yaran zan je na Wauko su shima in yana sona dawo dasu zan dawo masa dasu. Abin yayi yawa Alhaji, har maganar na kai gaban babban malamin hukumar hisba amma Kamal bai ji ba."

Adnan ya sake cewa, "Shiyasa nazo da maganar gaban ka, tunda babu aure babu amfanin bibiyar da suke yiwa juna, in Allah ya rubuta zai sake zama da ita matsayin mata zai sake nan gaba in muna da rai, amma bibiyar bata da amfani wani ma sai yayi musu fasssarar da bata kamata ba. Wannan tambari da nake guje musu zai bibiye su har yaran su."

Girgiza kai yake yi cike da gamsuwa da maganar Adnan a bayyane yace, "Na jima ina ji ana labarina kawai yaron da yafi babba hankali da hangen nesa da iya kalamai ban amince ba sai yanzu, gaskiya kayi tunani mai kyau da kuma hangen da mu iyaye a mu yi ba. Tunda babu aure a tsakani babu amfanin bibiyar ta da yake yi kamar yadda yace. Zan yiwa tufkar hanci in sha Allah, na kuma gode sosai da ka same ni da maganar kai tsaye dan wannan gyaran babbar Sarna ce." Jin ya fahimce shi sai yayi murmushi yayi godiya shima ya gode suka yi sallama ya hau mota ya tafi gida.

Nana Haleemad'þ>ØBÝ

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

                ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

*Page 027.*

Sai da yayi sallar i'sha sannan ya shiga gida, yunwa yake ji matu™a domin tun da yaci abinci da safe a office bai sake ci ba. Yana shiga wajan Mama ya same ta a zaune ranta a Sace matu™a amma bai kula da yanayin ta ba ya wuce kitchen yana cewa, "Mummy yau bamu gaisa ba, na dawo kuna bacci zan fita bakya nan sai yanzu."

Jin tayi masa banza yasan akwai wani abun ya dawo da abinci a hannun sa ya zauna yace, "Barka da dare Mummy." Bata amsa ba bata kuma kalle shi ba,  sai ya kalli Mimi ta masa magana da ido ya kalli kausar itama ta masa alama nan ya fahimci akwai damuwa.
Chapter 42 · 0% Book details