← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 48

Sashe 40

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin sa sai Baba ya mi™e tsaye Bebi ya ™araso yace, "Baba ya jikin nata? Ina aka kai ta?." Baba yace, "Dr Huzaifa ne ya karSe ta." Da sauri ya juya suka haWu da Huzaifa ya nuna masa Wakin ya shiga don ganim abinda ya kamata ayi.

Nan da nan ta samu bacci ciwon ya lafa, ya fito daga Wakin ya koma reception ya tarar dasu har lokacin suna zaune sai dai ta daina kukan sai jan numfashi da take yi. Ya kalli yace, "Baba muje ciki."

Ba musu Baba ya taso suka tafi cikin har Manal Win ya zaunar dasu a wani personal room. Sai a sannan yace, "Baba bamu gaisa ba." Baba yayi dariya yace, "Manal ta ruWa ni, ta ruWa kowa taya zamu iya gaisawa?."

"Barka da rana."

"Barka dai Adnan, ya aikin?."

"Alhamdulillah. Jikin nata da sau™i, akwai damuwa ko Sacin ran da ya haifar da ciwon, amma yanzu zai daina mata ciwon in sha Allah."

Baba ya girgiza kai yace, "Ban san me yake damun Fatima haka ba da zata dinga saka damuwa a ranta bayan tasan ba lafiyar kirki ce da ita ba." Baba ya sake cewa yace, "zamu iya zuwa mu ganta?." Adnan yace, "sosai, muje na raka ka" tare suka fita aka bar Manal a zaune bata dawo daidai ba har lokacin tayi shiru kawai.

Sai bayan sun fita tabi bayan su zuwa Wakin Mama na kwance tana bacci Manal ta tsaya kusa da ita Baba yace, "Hankalin ki ya kwanta ko Manal? Ga Mama nan ta samu lafiya, to sai ki nutsu don Allah." Bata iya cewa komai ba sai daga baya murya a sar™e tace, "Baba kaje ka baro kasuwar babu kowa zan zauna da ita a nan."

Baba yace, "A'a bazan barki a nan babu kowa ba, mu zauna duka ai yamma ta kusa daman."

"Yaya Haroun zai zo, kaje kawai Baba."

"To bara yazo Win na tafi." Adnan yace, "babu damuwa Baba zaka iya tafiya duk muna nan tare." Jin haka sai Baba ya amsa gudun kar ya gwale shi yaji babu daWi ya fita bayan sun yi sallama.

Kallon ta yayi amma ita Mama take kallo yace, "ki barta ta huta a nan, muje ko?." Gaba tayi tana tafiya a hankali kamar bata so suka fita. "Manal jikin nata yayi sau™i ko?." Kai ta Wagawa Huzaifa da yake tsaye a bakin ™ofar. Yayi dariya yace, "Tunda naga kin daina kuka nasan jiki Alhamdulillah, ki shiga wannan W'akin ki zauna ki huta kema." Šakin da ya nuna mata da hannun ta kalla taga wanda suka zauna da Baba ne, ta nufi Wakin shi kuma ya kalli Huzaifa yace, "Ya akayi suka zo nan?."

"Kirana tayi hankali a tashe, da yake ina kusa da gidan na su sai naje kawai muka taho nan." Gaban Adnan yayi mugun faWuwa cikin fargaba da kishi mai tsanani yace, "kana da number ta kenan, kuma har ka san gidan su ma?." Yayi dariya yace, "eh mana, kasan da yake yanzu da ita za'ayi na fasa da waccan" ya faWa cikin wasa ba tare da yasan ala™ar su da Adnan ba ya tafi ya barshi a wajan kamar an dasa shi a tsaye shi kuma bai lura da yanayin sa ba.

Gaban sa ne yake faWuwa sosai tashin hankali ya dabaibaye shi, zuciyar sa na bugawa da ™arfin gaske saboda kishi. kallon inda Huzaifa ya shiga yayi ya kalli inda Manal ta shiga nan da nan ransa ya kai ™arshe wajan Saci, yayi ™o™arin sarrafa kishin sa da Sacin ran ya huce zuwa office bai ma sake waiwayar ta ba.

"Amma na faWa mata bana son ™arya meyasa bata sanar dani wannan ba?, Meyasa bata ce min Huzaifa yana son ta ba?" Ya faWa shi kaWai yana dukan kujera yana jin zuciyar sa har wuya ya tsaya gabaWaya ya rasa ma abinda ya kamata yayi.

Ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zagaye yake daga nan yaje nan, da™yar dai ya samu ya zauna yayi shiru baice komai ba ya zubawa waje Waya idanu zuciyar sa na bugawa a guje. Kishi ne yake addabar sa, baya so a Soye masa komai shiyasa ya faWa mata tun farko, meyasa bata faWa masa Huzaifa ya san ta har haka ba?.

Huzaifan ne ya shigo da sallama yace, "Bebi ya ka yiwa Abba maganar machine Win nan?." Lumshe ido yayi ya haWWiye yawu ya buWe idanun nasa ya kalli Huzaifa da shima shi yake kallo tace, "lafiya kake idon ka yayi ja haka?, Meyasa cikin kwanakin nan baka zama daidai ne?. Idanun ka sunyi ja, akwai wani abu ne?" Ya faWa dan shi ya manta da katoSarar da ya aikata.

"Huzaifa kasan bana son Soye-Soye, bana son ™arya kuma, meyasa baka faWa min kuma soyayya da Manal ba?." Huzaifa mamaki ya dabaibaiye zuciyar sa yace, "ikon Allah, meya kawo wannan maganar kuma?. Ban da abin ka in ma ina soyayya da ita ai kamar ba sai na faWa maka ba ko?, kai ma baka faWa mana da wa ka ke soyayya ba, dan na Soye maka ai ban yi laifi ba."

Baice komai ba amma ya zuba masa idanu yana kallon sa Huzaifa yace, "wannan shine silar Sacin ran naka?, To meye na Sacin ran? Akwai aibu a ciki in ma son nata nake?. Kai ko Lubna ce nake soyayya da ita ai bana tunanin ranka zai Saci haka balle ita da baka da ala™a da ita. Ba kai ka ke cewa daman sonta nake ba?, meye na damuwa kuma?."

"Ya isa! Ya isa Huzaifa!. Don girman Allah bani waje bana son magana ma dakai gabaWaya." Mamakin sa Huzaifa yake yi yayi shiru ya tafi tunani na wani lokaci kafin ya sake kallon sa baice komai ba sai ya fice.

Wajan Hamza yaje ya jawo hannun sa suka fito daga Wakin da yake cewa, "Meya faru?." Huzaifa yace, "Adnan ya faWa maka akwai ala™a tsananin sa da Manal ne?."

"Wace ma Manal?."

"Wata yarinya kwanaki da suka kwanta a nan da Maman ta?. Duk suna da ciwon sugar ka gane ta?."

"Ohh na gane, bai faWa min ba meye ya faru?." Huzaifa yace, "Wasa nayi masa nace yanzu da ita za'ayi na fasa auren waccan kaga yadda ya canja?, da naje na same shi a office ya tsare ni da ido yana cemin baya son Soye-Soye na faWa masa yaushe na fara son ta."

Hamza yayi dariya yana kama baki da mamaki yace, "kar dai itace yarinyar da yake faWa mana?." Huzaifa yace, "nima nayi wannan tunanin, kai kaga yadda ya tashin hankalin sa sosai? Fuskar sa ta kaza Soye abinda yake zuciyar sa, kai da ka gani kasan akwai kishi a lamarin." Hamza yayi dariya harda tafa hannu yace, "Shege Bebi yana son mata masu kyau. yanzu dai naga kuna mutunci sosai da ita, muje ka tambayar mana, ka san gulma akwai daWi." Huzaifa yayi dariya shima yace, "jira ni ina zuwa" ya faWa yana wucewa ya bar Hamza yana dariya kafin ya cigaba da abinda yake yi.

Wajan Manal Win yayi niyar zuwa amma sai ya fasa tunawa da aikin da ya bari an office amma yaso yaje yaji kwakwaf dan ya ™ure Adnan.

Bebi bai sake ganin Manal ba itama bata kuma ganin sa bar bayan la'asar, a lokacin Maman ta farka kuma ance shi zata sanarwa, sai a sannan ta ™wan™wansa office Win ya amsa daga ciki ta shiga da sallama ya amsa bayan ya Waure fuska sosai tace, "Dr Mamana ta farka."

Ba tare da ya kalle ta ba yace, "reception ake zuwa a faWa."

jin abinda yace ta kalle shi sai tace, "Okay, thanks." Ta faWa zata fita sai taji yace, "wait." Ta kalle shi yace, "ina zuwa." Bata sake magana ba ta juya tana mamakin hali irin nasa, gabaWaya ya canja kamar ba shi ne suke hira a waya da zahiri ba. Takun sa taji a bayan ta kafin ta shiga Wakin ma ya riga ta ya saamu Mama ta farka tana kwance ya ™arasa yace, "Sannu Mama." Mama tace, "Adnan ne?."

"Shine Mama, ya jikin?."

"A asibiti muke kenan. Da sau™i, ciwon yayi sau™i sai kaWan da nake ji."

Adnan yace, "Zaki daina shima in sha Allah, damuwa ce ta miki yawa shine ya haifar da wannan ciwon. Sai Ana ha™uri ana kawar dakai a kan dukkan lamura, ina ance komai sai an damu a kansa zuciyata baza ta zauna lafiya ba. Kuma shi wannan ciwo ko ya Sacin rai yake baya iya Suya sai ya bayyana."

Mama ta girgiza kai tace, "Haka ne Adnan, na gode. Ina Manali?."

"Gani Mama" ta faWa murya na rawa. Mama tace, "Manal meye na kukan gashi ai na tashi ko? Kina ina?" Ta faWa tana mi™a mata hannu Manal ta ™araso ta ri™e hannun Maman tana kuka.

Mama tace, "meye na kukan kuma Manal? Ai naji sau™i yanzu ciwon kaWan nake ji."

"Mama Wazu ko magana bakya yi, hankalina ya tashi na rasa ya zanyi."

"To ki yi ha™uri na samu sau™i, ki gode Allah da ya haWa mu da su Adnan." Murmushi yake yana kallon su suna burge shi sosai domin akwai soyayya da sha™uwa a tsakanin su sai ya fita dan yaga sun manta ma dashi.

Bai jima da komawa office ba ta sake dawowa da sallama ya amsa a lokacin yana zaune da laptop yana dannawa ya kalle ta bayan ta shigo tace, "sorry na kuma dawowa, Mama tace zamu iya tafiya gida?." Kallon ta yake yi kafin yace, "zauna." Bata musu ta zauna ya tashi ya Wauki ruwa da kansa ya bata yace, "sha." Ta karSa tasha kaWan ta ajjiye yace, "ki dawo nutsuwar ki."

Manal tace, "a nutse nake."

"Mama ta samu lafiya kar ki damu, ki dinga ™o™arin ganin bata shiga damuwa ba ko tunani, duk abinda kika san zai saka ta a damuwa ko tunani kiyi ™o™arin ki ga bai faru ba kina ji?." Ta Waga kai alamun eh yace, "anytime, anywhere wani abun ya faru just call me, in banyi picking ba ki ta kira na har sai kin tabbatar na Wauka, kin gane?." Ta Waga kai alamun eh.
Chapter 40 · 0% Book details