← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 48

Sashe 32

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh amma sai goma na dare ai, in banje ba bazan samu nutsuwar yin aikin yadda ya kamata ba, so nake naji an tabbatar min babu maganar aure a kanta."

Hamza yace, "to maza ka shirya kaje yanzu mutumina, Allah ya bada sa'a." Kamar mai jiran umarni sai kuwa ya mi™e ya shiga Waki. Hamza da Huzaifa suka ™yal™yale da dariya har suna tafawa. Sun ji daWin yadda Allah ya kama shi tun ba a je ko ina ba, cika baki akan soyayya ya ™are tunda ya samu wacce yake yiwa son da bai yi zato ba.

Nana Haleema>ØBÝ>ØöÞ<Øûß

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

                 ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu. https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.

*BOOK 1*

*Page 020*

Adnan dariyar su ya jiyo daga Waki sai ya fasa abinda yayi niya ya fito yana kallon su Huzaifa ya kalle shi yace, "ka fasa tafiyar ne Wan soyayya?." Sai shima ya samu kansa da yin murmushi ya kama ™ugu yace, "abin mamaki ko? Wai ni Adnan da son wata mace bayan soyayyyar yarinta." Hamza yace, "ba abin amma ki bane ba, ka kai kayi Win ne. Ka koma ka shirya ka ™yale wannan yana da wacce zai aura a hannun sa."

Huzaifa ya tashi yace, "tafiya zanyi ma ni." Hamza yace, "jira ni" ya kalli Bebi bayan ya tashi tsaye yace, "kar kayi wasa mutumina, kaje da zafi-zafi ake dukan ™arfe, Allah ya daidai ku. Na san baza ka zaSo ta banza, duk yadda aka yu tarbiyya da kyau ka gano, dan na san ka akwai son abu mai kyau."

Bayan su ya biyo zuwa harabar gidan suna hira, lokacin sallah yayi Adnan yace, "amin, in ma da biyu ka yi addu'ar in sha Allah zamu daidaita." Suna dariya su biyun shi kuma yana tsakiyar su.

Suna nan tsaye Mimi ta fito cikin riga da siket ´an kanti sun kama ta musamman rigar, ita da ™awar ta suka fito suna hira sai da suka zo kusa dasu Bebi suka gaisa suka wuce, ta raka ta har bakin gate ta fita sannan ta juya ta koma ciki.

A lokacin su Huzaifa suka hau mota suka tafi shi kuma ya wuce ciki rai a Sace saboda abinda Mimi tayi. Yana shiga yace, "Ke Kausar ina Mimi?." Mimi ta fito da plate a hannu tace, "Gani."

"Wanne irin rashin hankali ne zaki dinga fita waje a haka? Kalli kayan jikin ki, don baki da hankali a haka kike yawo daman?." Ta kalli kanta ta kalle shi tace, "Yaya a cikin gida nake fa."

"Zan tsinke ki da mari in kika sake min magana, kin fini sanin a cikin gidan ki ke?. Wannan wanne irin hauka da shirme ne da kuma rashin hankali?. Kin fito ko mayafi babu kina ganina da Saki maimakon ki dawo ki saka mayafi sai kika wuce ke ga ´ar gayu ko?." Tayi shiru tana kallon wani wajan Mama ta fito daga Waki taji duk abinda yake faWa tace, "Mimi jeki ki sauke min naman can a kan gas." Hakan ya saka ta wuce Kausar ta tashi ta bita dan wallahi Bebi haushi yake basu wani lokacin dan babu yadda zasu yi dashi ne.

Mama ta kalle sji tace, "Bebi yanzu dan ta fita harabar nan a haka meye laifi don Allah da zaka zo kana mata wannan faWan?, Ka dinga sassautawa yaran nan wani lokacin takurar tana yawa sosai."

Bebi yace, "Mummy tana ganina da ba™i fa, ai sai ta dawo ta saka mayafi sannan taje su gaisa. Sun kasa gane bana son abinda suke yi ne kwata-kwata."

"Sai kayi ha™uri, aure zasu yi su bar maka gidan." Ya juya ya fita bai ce komai.

       Sallah yaje yayi ya dawo yana tunanin abinda zai yi saboda da ya keSe kansa tunanin Manal ke zuwa zuciyar sa. Kamar an bashi umarni sai ya tashi shiga Waki ya shirya cikin manyan kaya da suka yi kyau sosai harda hula, kallon kansa yake a madubi yana jin ™arfin guiwar zuwan, zuciyar sa na sake bashi shawarar Tafiya gidan su Manal. Ya sauke numfashi ya fita ya hau mota ya tafi gidan su Manal kai tsaye.

Sai da ya tsaya a ™ofar gidan sai kuma ya rasa abinda zai yi, yana zaune a mota yana kallon gidan kasancewar akwai haske a layin dan da wutar nepa ko ina da haske har ™ofar gidan su. Baba ne zai shiga gidan suna tsaye da Haroun suna magana a ™ofar gidan, ganin hakan sai Bebi ya fito daga motar ya ™aarasa inda suke yana zuwa yayi sallama Baba ya amsa masa sai ya saki murmushi yace, "A'a dr Adnan, barka da zuwa."

Adnan yayi murmushi yace, "barka da dare Baba."

"Barka dai likita, ya aiki?."

"Alhamdulillah, ya masu jiki?."

"Da sau™i sosai duk sun samu lafiya. Haruna wannan shine likitan da suka taimaka lokacin da su Manal basu da lafiya, shine wanda na baka labari ko naira biyar basu ™arba ba." Suka gaisa da Haroun yace, "Allah ya saka da alkhairi, Wazu ma Manal tayi min wannann zancen, taji daWi sosai, Allah ya biya."  Ya amsa da amin. Baba yace, "ya kamata ka shiga ku gaisa in da damar hakan."

Bebi yace, "babu damuwa Baba, daman wajan ka nazo Baba." Baba yace, "wajena kuma? To mu shiga ciki" ya faWa yana shiga cikin gidan Adnan ya biyo bayan sa yana mamakin kansa wai shine yazo tambayar izinin neman wata yarinya.

Tun daga soron gidan yake jiyo muryar ta tana bada labari tana dariya da alamun tana cikin nishaWi, sai daga baya yaji muryar Mama tana cewa, "Manali Allah ya shirye ki, kice kin yi samari duk babu labari sai yanzu da Allah ya matsa bakin ki." Sai tayi dariya tace, "Amin Mama. Sosai ma kuwa, kawai bana faWa miki ne, amma yanzu zaki sani." Sallamar Baba ya saka suka yi shiru suka kalli Baban sai Baba ya juya yaga Adnan bai shigo ba yace, "Dr shigo mana."

Dr Adnan ya shigo da sallama yana kallon tsakar gidan, kai tsaye suka haWa ido da Manal da take zaune da doguwar riga a jikin ta ta saka huta a kanta wacce ta ja ta baya gashin ta ya Wan fito ta gaba.

Suna haWa ido abinda yazo mata kawai wula™ancin da yayi mata amma sai bata nuna ba dan ya taimaki Mama hakan ya saka tace, "Dr! Sannu da zuwa." Ta kalli Mama tace, "Mama Dr da ya kula dake ne fa."

Mama tayi murmushi tace, "ai daga jin sallamar na gane Wauki murya, kuma naji kin ce Dr. Sannu da zuwa." Sai yayi murmushi ya kalli Manal sai yaga ta wara idanu waje tana kallon sa dan ita mamaki take daman yana sakin fuskar har a ga ha™orin sa?.

Har kan tabarmar da suke kai ya ™arasa ya gaida Mama ta amsa da fara'a tace, "Ya aiki?."

"Alhamdulillah, ya jikin?."

"Jiki da sau™i, Wazu nake cewa Manal kinga ina jin sau™in Idon nan da alama dai abinda ka faWa zai tabbata." Yace, "indai za'a dinga shan maganin ana ganin likita babu abinda zai faru sai alkhairi."

"Allah yasa, sai dai ga Manal nan bata shan nata maganin da aka bata wallahi." Manal da take gefe ta turo baki tace, Allah Mama ina sha, maganin ne daWi fa."

Kallon ta yayi yana jin wata irin kewa a zuciyar sa kamar baya tare da ita, Allah ya saka masa son ta farar Waya a lokacin da bai shiryawa hakan ba. Wani abu yake ji yana jan sa zuwa gare ta musamman yanzu da take magana, hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallo har sai da yaji Mama tace, "™arya kike Manal, bakya sha ni nasan halin ki fa, kuma magani ai ba dan daWi ake sha ba." Manal ta kalle shi suka haWa ido sai ya janye idon sa tace, "ina sha, kawai Mama ce take cewa bana sha."

Baba yace, "kun barshi a dur™ushe sai magana kuke yi, Dr taso mu shiga ciki." Adnan baiyi musu ba ya tashi suka shiga falon Baban yana jiyo maganar Manal cikin shagwaSa Maman na sake gwale ta kamar dai kawaye baza kace uwa da ´a bane ba.

Baba ya zauna Adnan ya zauna a ™asa Baba yace, "Haba Dr, tashi ka dawo sama don Allah." Adnan yace, "Babu komai Baba, nan ma yayi." Baba yace, "Allah yasa Lafiya."

"Lafiya lau Baba."

"To ina jin ka." Bebi yayi shiru yana tunanin ta ina zai fara kafin ya aro jarumta yace, "Baba nazo ne akan maganar Manal."

Baba yace, "To wani abun ne ya faru? Ko a kan ciwon nata ne?." Bebi ya girgiza kai yace, "Ba akan ciwon ta bane Baba."

"To ina jin ka."

"Baba nazo ne daman akan in ba'a yi mata miji ba ina so a bani dama da izinin magana da ita."
Chapter 32 · 0% Book details