← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 48

Sashe 17

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna cikin tafiya drivern ya kalle ta ta madubi yace, "ranki ya daWe akwai sa™on da Alhaji ya bayar yace na baki" ya faWa yana nuna mata wata leda a kusa da ita. Ledar ta Wauka ta buWe, kwalin iPhone ne a ciki da hanzari ta buWe taga wayar sabuwa dal a ciki, ta duba takardar jiki taga an rubuta iPhone 16 pro max. Farin ciki taji yana mamaye mata zuciya ta cigaba da juya wayar bayan ta kunna tana ji kamar tayi ihu saboda murna.

Wayar tace tayi ™ara ganin Babyn tane sai ta Wauka cikin yanga da shagwaba tace, "Baby!." Daga can Sangaren yace, "Babyna, an baki sa™on ki?."

"An bani Baby, na gode sosai."

"Kar ki damu Baby, kin cancanci fiye da hakan a wajan. Anjima kaWan jirgina zai tashi zuwa lagos ina so na ganki." Mubeena tace, "to ai kaine baka zo Waukana ba."

"Ina da ba™i ne Baby, amma yanzu in kina so ya kawo ki nan inda nake daga nan sai ku wuce gida, minti biyu kawai ganin ki zanyi ki koma."

Mubeena tace, "Kar Mummy tayi min faWa fa Baby."

"Baza tayi miki faWa ba, baza ki jima ba ai."

"To gamu nan."

"Thanks you Baby, sai kun zo" ya faWa tana yanke wayar ta faWawa driver suka wuce gidan alhaji Mu'azzam.

Har gidan aka shiga da ita a motar ya fito aka nuna mata inda zata bi ta shiga cikin gidan ta same shi a zaune akan kujera yana danna waya ganin t sai ya mi™e cikin nuna farin ciki yace, "Welcome my Baby."

Murmushi yayi ganin harda buWe mata hannu alamun runguma sai ta basar ta nuna kamar ba gani ba yayi murmushi yace, "Zauna Baby, ya school?."

"Alhamdulillah." Kallon ido cikin ido yake mata yace, "a kawo miki ruwa?." Kai ta girgiza alamun A'a kafin tace, "Ashe ma baka shirya tafiyar ba kasa nazo" ta faWa da shagwaSa wacce ta shige shi lokaci Waya ya kwance ya kasa gane kansa. Da™yar ya danne abinda yake ji yace, "Yanzu zan fita ke kawai na tsaya na gani."

Bata ce komai ba y sake cewa, "Dama zaki raka ni da nayi farin ciki." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta mi™e tace, "zan koma gida Baby, sai ka dawo a kawo min tsarabar lagos." Ya mi™e tsaye yace, "kar ki damu, in ma lagos Win kike so a Wauko miki zan kawo miki" ya faWa yana matsowa kusa da ita kafin yace, "in na tafi zanyi kwana biyu ban ganki ba, baby please ki bani hug guda Waya wanda zan tuna dashi in bana nan." Jin abinda yace sai ta kalle shi kamar wani yaro har marairaicewa yake sai tayi murmushi dan wallahi dariya yake bata tace, "A'a ni dai."

"Yanzu bazan samu ba kenan? Ni ki bani dama to." ˜afa take bugawa cikin son sake burge shi tace, "A'a nidai." Hakan da tayi bai san lokacin da ya jawo ta jikin sa ya rungume ba yana furta, "ina sonki Baby." Sacanni bai wuce goma ba ta janye jikin ta tana turo masa baki gaba wanda yake jin wani abun na fizagar sa akan bakin tace, "to zan tafi." Cikin taushin murya yace, "bana so ki tafi, ki tsaya a nan kin ji baby" ya faWa yana ri™e hannun ta.

Bata ™wace hannun ba tace, "A'a ni dai tafiya zanyi." Ya sauke numfashi yace, "shikenan Baby tunda bakya son kasancewa dani." Bata ce komai ba bai saki hannun ta ba ya Wauki wayar sa yana dannawa da hannu Waya kafin ya kalle ta yace, "na tura miki kuWin shan ice cream." Murmushi tayi tace, "thanks you Baby."

"I love you Baby."

"I love you so much" ta faWa da wata murya mai Waukar hankali.

Šakyar yake iya ri™e kansa, amma ji yake kamar ya fizgo ta ya kama bakin ta ya tsotse shi ya haWe kirjin sa da mata  yana jin buguwar zuciyar shine abinda yake bu™ata a wannan lokacin, amma baya son yi mata shigar sauri dan sabuwa ce shiyasa yake bin ta a hankali, ya san lagon mata irin ta sababbi. Har ™ofar falon ya tako ta kafin ya koma ciki ta shiga mota su Wauki hanyar gidan su Bily.

Shima gidan ya shirya ya bari ya tafi gidan sa ya ajjiye motar sa ya shiga Sangaren sa kai tsaye. Mama daman jiran zuwan sa take tunda ta san yana garin, tana ganin ya dawo ta nufi Sangaren nasa ta same shi a tsaye a falon yana amsa waya yana murmushi a lokacin da yake cewa, "zanyi kewar ki sosai Baby, kamar na fasa tafiyar nan." Taji abinda yake cewa sai bata nuna ta ji ba ta shiga da sallama ya amsa yana yanke wayar bai kalle ta ba tace, "sannu d zuwa." Sai da ya kalle ta sannan ya cigaba da abinda yake yi yace, "Yauwa."

Mama tace, "ina so zanje na gaida Hajiya an jima." Fuskar sa a Waure matu™a yace, "sai kin dawo." Ta juya zata tafi yace, "zanyi tafiya zuwa lagos yau, ki faWawa  ´ar uwar ki." Mama ta kalle shi tace, "ai mu ko yaushe a baka nan muke Waukar ka a gidan nan, ko baka faWa mana ba, hakan ba sabon abu bane a wajan mu Alhaji."

Kallon ta yayi kamar zai magana sai ya fasa tayi dariyar takaici tace, "Su baby sune suke ganin ka ko yaushe, amma matan gidan ka sune basa ganin ka sai lokacin da ka so, sai lokacin da su Baby suka sallame ka ka ke zuwar mana." Ya kalle ta yace, "me kike nufi?." Kai tsaye tace, "´an matan ka nake nufi, sune suke ganin ka ko yaushe available amma matan ka na gida ko yaushe baka nan a wajan su, Allah ya kiyaye hanya. Sannan ina yawan faWa maka ka dinga sara kana duban bakin gatari, kar ka bar baya da ™ura" tana faWa ta fice ya bita da kallo sai ya share dan kar maganar tayi tasiri a zuciyar sa. Abinda yazo Wauka kawai ya Wauka ya fito y sake gida mota driver ya ja suka fita.

Zuwa yamma Manal taji faWin jikin ta sosai, wanka take so tayi ya canja kaya gashi Surayya ta tafi. Tashi tayi ta fita zuwa Wakin da Mama take tana kallo duk da bata ganin ta a wajan ta kallon Wakin ma kawai hankalin ta kwanciya yake yi. Tana zaune tayi tagumi tana hawaye Bebi ya fito daga Wakin ya kalle ta dan bata ji fitowar sa ba.

Wucewa sa ta gani ta gaban ta ta kalle shi taga dai shine sai taji tsoron tambayar sa halin da Mama take ciki dan babu wannan fuskar a tare dashi. Mi™ewa tayi kawai tabi bayan sa duk da bata jin dadi amma haka ta tashi ta bishi zuwa office Win da ya shiga, ™wan™wasawa tayi ya amsa daga ciki ta shiga da sallama ta same shi a tsaye shan ruwa, ya kalle ta ta kalle shi ya sauke jarkar ruwan daga bakin sa ya amsa sallamar sannan tace, "Likita don Allah ya jikin Mamana?."

Kallon ya yayi yaga kamar jiri take a tsayen sai yace, "zauna" ya faWa yana nuna mata wajan zama ta zauna ya ajjiye ruwan ya ™arasa inda take ya zauna akan kujerar da yake zama ko yaushe yace, "jikin ta da sau™i zata samu lafiya." Ta goge idanun ta tace, "yaushe zata tashi?."

"Nan kusa!" Ya bata amsa a ta™aice.

Kafin tayi magana yace, "meye sunan ki?." Murya na rawa tace, "Manal."

Ya maimaita sunan a zuciyar sa kafin yace, "Ina Baban ku?."

"Baya nan yayi tafiya ina ta kiran wayar sa a kashe take."

"Baki da Yaya namiji?." Ta girgiza kai tace, "bani dashi, sai dai Wan Baban mu kuma baya ™asar nan yna Qatar."

Yayi shiru kafin yace, "yaushe Mama ku ta samu ciwon rashin gani?." Manal tace, "ba'a fi shekara uku ba, kuma da tana gani da rana da daddare ne ganin yake raguwa sosai."

Ya girgiza kai kafin yace, "zuciyar fa?."

"Ta riga samun zuciya akan idanun, ciwon baiyi yawa bane sai yanzu." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "zata samu lafiya in sha Allah. Kar ki damu, kwantar da hankalin ki."

"Allah yasa" ta faWa a raunane hawaye na zubo mata. Sosai yaji ta burge shi da alama tana son Mama ta sosai, shi kuma duk wanda yasan darajar iyayen sa yana samun matsayi babba a wajan sa yace, "zaki din shan wannan magani kema shine  zai dinga daidaita sugar jikin ki, but na iya lokaci kawai ba ko yaushe ba" ya faWa yana tura mata maganin gaban ta yace, "ki buWe yanzu ki sha kafin ki tashi."

Da to ta amsa ta buWe  maganin ta ri™e a hannu tana kallon inda taga yasha ruwa, tana niyar tashi ya dakatar da ita ya Wauko mata ya ajjiye tayi murmushi tace, "Na gode." Maganin ta sha ya kalle ta yace, "zaki iya tafiya."

Manal tace, "don Allah zan iya zuwa gida na dawo? Har na dawo Mama bata farka ba?." Ya Waga  mata kai ta tashi ta fita ya sauke numfashi yayi shiru cikin tunani. ganin macen da yayi a motar mahaifin sa yana sake dawo masa cikin zuciyar sa da idanun sa.

Manal daga nan Wakin da take kwance ya koma ta saka takalmi ta fito zuwa bakin titi. Titin kamar anyi shara babu abin hawa ko kaWan  shiru, kasancewar asibitin a cikin gra ne ba'a samun mota sosai a hanyar sai kayi sa'a. Tana nan tsaye sai taji tsayuwar baza ta yu ba sai ya zauna akan wani ™aramin dutse da yake gefen wajan.

Wanda ya kai ta wajan Alhaji Mu'azzam ta gani gaban ta yayi mugun faWuwa ta tashi tsaye tana kallon sa, ganin kamar ita yake nufowa tana ja da baya bata san ta shiga kan titi ba ga mota ta tawo sai jin ta tayi a ™asa tayi ™ara.

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

Page 012
Chapter 17 · 0% Book details