← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 48

Sashe 30

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya zauna ta kalle shi tace, "Ka tashi ka Wauko abinda zaka ci babu mai yi maka jeka ka dawo bacci suke yau." Yayi dariya kaWan baice komai ba Mama tace, "Murmushi yana yi maka kyau Adnan amma gaba kake yi dashi, kai kullum fuska a haWe kamar mala'ikan mutuwa. Shiyasa ake fassara ka a mutum mara kirki, dariyar ma sai ka saba da mutum ka ke yi."

Yayi dariya yace, "to Mummy kawai sai na dinga dariya kamar wani mara hankali?."

"Lallai, mu da mu ke yi duk bamu da hankalin kenan ko?." Ya wara ido yacec "Ni na isa?."

"Sak Alhajin mu kayi, shima bashi da fara'a sai kun saba zaka ga dariyar sa, amma in baku saba ba kallo Waya zaka ce bashi da kiri. Allah ya ji™an sa." Ya amsa da amin.

Tashi yayi ya shiga kitchen Win sai gashi ya fito da kofi a hannun sa yace, "Mummy ashe anyi min kunu."

"Eh gashi nan nayi karanbani nayi maka, Allah yasa kar a sake bani kunya ace babu daWi." Ya zauna yana dariya yace, "ai yayi daWi matu™a." Tayi dariya bata ce komai ba shi kam kallon ta yake gabaWaya tausayi suke bashi saboda halin da mijin su ya saka su a ciki.

Mama ta katse masa tunani tace, "Da alama Mimi saurayin nan mata dai yayi mata Bebi." Yace, "na tura shi wajan Yaya ni maganar ya bar hannun kuma ai." Mama tayi shiru kafin tace, "ya zancen Lubna Win?." Yace, "na sanar da Yaya komai akan waye wanda take so Win ya tabbatar da bazai bari ta aure shi ba."

Mama tace, "Bebi kana da saurin fushi amma na rasa meyasa ka kasa fushi akan lamarin su Lubna." Yace, "Mummy ai ba dan su nake yi bane shiyasa" ya faWa yan ajjiye kofin ya tashi yace, "zan tafi Mummy."

"Shikenan har ka ™oshi?."

"Eh, in naje zanci abinci."

"To sai ka dawo, kofin an barni a Wauke ko?." Šaukar kofin yayi yace, "Tuba nake." Ta Harare shi tace, "yau ka saba?, a Wauko maka kuma a Wauke maka, dan gata. Shiyasa in na tura Wakin ka plate Win da na manta dashi ma zan ganshi." yana ji murmushi yayi kawai ya fita daga falon. Wajan Abba ya shiga amma bai ji motsin sa falon ba hakan ya saka shi fitowa ya hau mota ya tafi.

Nana Haleema>ØöÞ<Øûß

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

  ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.

*BOOK 1*

*Page 019*

Mubeena haka ta kwana a gida gabaWaya babu walwala, Manal na lura da ita ta share ta kawai dan haushin ta take ji sosai. Sai da safe Baba ya shigo sun gaisa ya kalle ta tana zaune da wayar a hannun ta yace, "Mubeena zo Wakina ki same ni yanzun nan." Haushi taji a zuciyar ta tana tunanin yanzu to me kuma tayi, haka ta tashi rai Sace ta shiga inda ya shiga, ba tsammani taji ya karSi wayar hannun ta gaban ta ya faWi sosai yace, "a ina kika samu kuWin wannan wayar? Waye ya siya miki ita?."

Mubeena ta fara kame-kame cikin rashin gaskiya tace, "ba tawa bace, ta ™awata Bily ce ta ara min." Yadda take maganar kana ji kasan ™arya take yi ya girgiza ki ya saka ta a aljihu tace, "to shikenan kice mata tazo ta karSa a wajena tunda ba taki bace ba, sannan daga yau Win nan kar ki sake fita baki tambaye ni ba, duk inda zaki koda bana nan ki faWawa Manal ta baki waya ki kira ni. Ko makarantar ce kar ki sake zuwa sai na sani."

Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Bab yace, "kin Sata wayon ki indai wannan hanyar da kika Wauka kike ganin itace daidai da rayuwar ki Mubeena, zaki yi dan sani a lokacin da baza tayi miki amfanin komai ba." Mubeena tace, "wallahi ni babu abinda nayi Baba."

"Waye ya sauke ki jiya da magariba a mota?." Gaban ta ya faWi sosai tayi shiru, ya sakar mata tsawar da sai da ta firgita ta kusa faWuwa daga zaune yace, "tambayar ki nake waye ya sauke ki a mota jiya?" Ya faWa da tsawar da bai taSa yi mata irin ta ba.

Tace, "Drivern gidan su ™awata ne." Baba yace, "™arya kike wallahi, ki cigaba da abinda ki ke yi, ke a ganin ki hakan shine wayewa ko? Hmmm Mubeena zaki dana sani indai wannan banzar rayuwar kika zaSarwa kan ki, kin ga ina bin ki ta lallami shine kike abinda kike so kina ganin babu mai hana ki ko?, daga yau mun saka ™afar wando Waya dake, zamu ga waye mai nasara ni ko ke." ya faWa yana tashi ya fita ta bishi da kallo babban tashin hankalin ta itace wayar ta.

Yana fitowa tsakar gidan yaga Mama a zaune da alama taji komai tace, "Wayar mai tsada ce a hannun ta ko Baban Manal? Sannan jiya waye sauke ta a mota?. Ai shikenan Mubeena sai ta kashe ni zata huta."

Baba bai so taji ba yace, "Kar ki saka wannan a zuciyar ki, ta tabbatar min da motar gidan su ™awar tace na kuma amince da haka, wayar ma ba ta ta bace ta ™awar tace." Mama tayi murmushi tace, "Ko Manal baza ta amince da abinda kace ba balle ni Baban Manal, ni fa na haife ta. Shikenan ai duk wanda yayi daidai ya sani, wanda bai yi daidai bama ya sani."

Baba yace, "bance ki saka wannan abin a zuciyar ki ba, addu'a zaki mata itace maganin komai." Mama bata ce komai ba Baba ya kalli Manal yace, "ki kula da ita kin ji."

Ta Waha kai alamun to har ta fara kuka ya fita. Mubeena ta wuce zuwa Wakin jiki a sanyaye Manal ta tashi tabi bayan ta tana shiga tace, "in wani abun ya samu Mama ta dalilin ki Allah ya isa ban yafe miki ba Yaya, sannan har abada kar ki tuna ni matsayin ´ar uwar ki daga ranar bazan sake kallon ki matsayin jinina ba, daga ranar bazan sake miki kallon ´ar uwata ba wallahi. Babu ni babu ke kamar yadda kika Wauki hakan a yanzu.  ke bakya son mahaifiyar mu ni ina sonta, in ke kin raina ta ni ina girmama ta, in ke kunya kike ji ace itace ta haife ki ni alfahari nake na nuna ta matsayin wacce ta haife ni."

Mubeena da take kallon ta tace, "ni kike faWawa wannan maganar?."

"An faWa miki, in kinga dama ki dake ni kuma wallahi sai na rama. Meye a duniyar in baka girmama mahaifiyar ka ba? Me zaka tsinka a cikin ta in baka yi biyayya ga iyayen ka ba?, Ke a ganin ki wannan wayewa ce ai ko? To kije ki tayi Allah ya bada nasara. Amma ki tuna daga lokacin da kika saka wani abun ya same ta babu ni babu ke" tana faWa mata ta fita ta barta a tsaye. Taji kunya sossi amma wayar ta kawai take ji domin ko wanne lokaci za'a iya yi mata waya.

Haka Manal ta wuni kusa da Mama, duk da Maman tayi shiru bata cewa komai kai da ka ganta kasan tana cikin damuwa sosai amma bata nunawa.

Kwanan Mubeena biyu bata fita ba saboda babu fuska wajan Mama gashi Baba ya saka mata ido ko ya ta motsa yana kallon ta ko kuma ya saka ana kallon ta gabaWaya ta damu zaman gidan ya ishe ta sosai.

Ranar laraba a safiyar Mama na zaune suna hira da Manal kamar yadda suka saba tace, "Manal kin ji yadda nake jin idona ya Waure ya daina wallahi, a hankali nake ji yana saki, da alama dai abinda likitan nan ya faWa zai tabbata." Manal cikin farin ciki tace, "Da gaske Mama?."

"Da gaske mana."

"Allah ya tabbatar Mama." Mubeena tazo ta zauna a kan tabarmar da suke tace, "Mama zanje makaranta na dawo."

Mama tayi mata banza kamar bata ji me take cewa ba tace, "kiyi ha™uri ni duk abinda ake zargina a kai ba haka bane ba wallahi." Mama tace, "in ma haka ne Mubeena rayuwar ki ce ba tawa ba, Dana sani ke zata bibiya ai bani ba domin kowa yayi daidai ya sani. Tashi ki bani waje ai ba tambaya ta kike ba in zaki fita." Mubeena tayi shiru ta kalli Manal da ba ita take kallo ba sai ta tashi ta fita.

Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena hmmm!." Abinda tace kenan bata sake magana ba Manal ma bata dawo da zancen ba ta Waukewa Mam hankali da hira dan ta kawar da batun Mubeena.

        A cikin kwana biyun Bebi ya tabbatar da son Manal yake so na gaske ba na wasa ba, duk yadda yaso ™aryata zuciyar sa ta dage akan hakan domin duk wata alama ta soyayya ta gama shiga zuciyar sa ta kuma bayyana a ganganar jikin sa.
Chapter 30 · 0% Book details