← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 48

Sashe 25

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.

*BOOK 1*

*Page 016*

A nan yayi sallar la'asar yana idawar Kamal yana zuwa, tare suka koma ciki dashi da shugaban da kuma Kamal dWin. Kamal sai kallon Bebi yake domin ya tabbatar shine ya kawo ™arar sa baice masa ba shima baice ba a haka suka shiga ciki suka zauna, aka gaisa da Kamal da Malam kafin yace, "Kaine Kamal?." Kamal yace, "™warai ni ne."

"Kasan wannan?" Ya faWa yana nuna masa Bebi ya kalli Bebi yace, "na san shi, ™anin tsohuwar matata ne."

Yace, "kaima kace tsohuwar matar ka amma yace kana bibiyar ta, kana so ka mayar da ita ne?." Kamal ya sauke numfashi cikin takaici yace, "A'a babu wannan a zuciyata. Saboda saki uku ne a tsakanina da ita."

Malam yace, "to meyasa ka ke bibiyar ta?." Kamal yace, "in dai naje wajan ta saboda yaran ta ne, wani lokacin maganar makarantar su ce, wani lokacin maganar rashin lafiya ko abinda yayi kama da haka. bayan wannan babu komai."

"Yara zaka iya haWa su da ita koda a waya ne, sannan zaka iya kai mata su ba lallai sai kun haWu ba. HaWuwar ma inda ba ko yaushe bace dan an haWu an gaisa ba komai tunda akwai zuri'a a tsakani, amma ko yaushe ba daidai bane, shaiWan zai iya shiga tsakanin ku a aikata abinda za'a yi dana sani." Kamal yayi shiru Malam yace, "Gashi da kan ka kace baka da ra'ayin mayar da ita, to meyasa kuma ka kasa rabuwa da ita?."

Kamal yace, "kamar yadda na faWa da farko maganar yara ce take kaini wajan ta."

"In maganar yara ce kaje har cikin gidan su a gaban kowa kayi mata maganar yaran ta wannan ba wani abun bane, ko ka kira ta a waya ko ka kira wani nata kamar shi Adnan Win. KeSewar ku ku biyu illa ce a gare ku, zaku dinga tuna rayuwar ku ya baya ne daga wannan lokaci kuma shaiWan zai ratso ta tsakiya sai wani abun kuma ya afku, ga saSon Allah ga dana sani."

Kamal yace, "za'a gyara in sha Allah." Adnan ya tari numfashi Malam  da yake niyar magana yace, "Malam ayi musu tsakani da ita, tunda babu aure a tsakani to ya jira in akwai rabon zata dawo wajan sa zata koma, ya daina bibiyar ta." Malam yayi murmushi tace, "kar ka damu, duk da itama naso ace tana wajan nan dan itace babbar mai laifi, da bata bada fuskar hakan ba da bai faru ba."

"In bai je inda take ba bazata saurare shi ba" Bebi ya faWa yana kallon Manal.

Malam yace, "A kiyaye Kamal, kodan saboda gujewa aikin dana sani." Kamal yace, "Gaskiya ne, na gode zan iya tafiya?." Ya amsa masa ya tashi ya fita shi kam Adnan godiya yayi masa sannan ya tashi ya fito.

Yana zuwa gaban motar sa yana niyar shiga yaji Kamal yace, "Wai kai me ka Wauki kan ka ne? Mahaifin Maryam?." Bebi ya juyo yana kallon sa yace, "zaka iya kira na da hakan ba laifi bane."

"Kana ganin wai hakan da ka yi  shikenan ka raba ni da Maryam?."

"Ai hukuma gaba take da kowa, in kana ganin kai kana gaba da ita ne ka sake maimaita abinda kayi. Wallahi nan gaba sojoji zan saka su yi maka dukan da zaka kasa tashi."

Kamal yayi murmushi yace, "ni ka wula™anta Bebi har ka kawo ™arata wajan nan. Ka jira abinda zai faru sai na tartarsa maka zuciya wallahi, badan kai mai kishin ´an uwan ka ba? Na tabbatar Maryam zata baka kunya wacce baka yi tunanin jin ta nan kusa ba. Kuma ina so ka sani bazan nemi wata hanyar da zan gyara auren mu da ita ba, kuma bazan rabu da ita ba kayi abinda zaka yi."

Adnan yace, "zaka ga abinda zan yi kuwa, domin ba'a shiga gona ta a zauna lafiya, abinda nake so shi nake aikatawa kuma shi nake aiwatarwa akan kowa koda shi baya so. Nafi ™arfin ka tarwatsa min zuciya Kamal, sai dai ni na tsarwata taka. Rashin ilimin addini ne yake sakawa namiji ya bibiyi wacce ba matar  sa ba, ina baka shawara ka koma islamiyya domin ya™i da jahilci domin yana damun ka sosai. Shine ya ke saka ka aikata hakan kan ganin hakan daidai ne, baka san tsabar jahilici da rashin sanin addini ne ya saka ka ke aikata hakan ba" ya faWa yana nuna shi da key na mota kafin ya juya ya buWe motar ya shiga yana ya fita daga cikin wajan.

Da kallo Kamal ya bishi zuciyar sa na zafin kiran sa jahili da yayi, yayi ™wafa shima ya shiga mota lokaci yayi da zai tabbatarwa da Bebi shi zai tarwatsa masa zuciya, zai ga aikin jahilai kuwa, zai yi dana sanin kiran sa jahili da ya yi.

Mubeena ce ta fito daga banWaki Bily ta kalle ta taga ta zauna tana cigaba da danna waya tans murmushi  Bily tace, "Wai da wa kike chart da kika kasa tashi kiyi sallah?." Ta kalle ta tace, "my future husband mana." Ta faWa tana Waga wayar ta yiwa kanta hoto ta kalli hoton tayi murmushi ta cigaba da danna wayar.

Bily tace, "yanzu kuma kin fara jin daWin zancen banzan da yake miki kema kenan?."

"Na fahimci soyayya ce hakan, yanzu ma hoton sa ya tura min babu riga amma view once ne" ta faWa  tana dariya alamun abin bai dame ta ba. Bily tayi dariya tace, "Mubeena ki kiyayi wannan tashon fa, wallahi zai iya saka ki dana sani."

Mubeena  ta kalle ta da mamaki tace, "na rasa yaushe kika canja Bily, Wai duk meye wannan Win? Bafa wani abun yake min ba kawai chart ne, kuma kin san wayewa ce ba wani abun ba."

"Sexy chart din ne wayewa?."

"Ya akayi kika san sexy chart ne?."

"Saboda naga abinda ya rubuto miki a notifications yanzu, shi ko kunya baya ji da ´a´an sa da jikokin sa ya tsaya yana wannan shirmen dom Allah?."

Mubeena tace, "kinga Bily don Allah ya isa haka." Bily tace, "bai isa ba Mubeena, sai na faWa miki gaskiya. Dan ina biye miki ina cewa baki dace da haihuwar gidan ku ba hakan yana nufin na biye miki ki fara iskanci ba." Da sauri ta kalle ta tace, "ni kike ceawa ´ar iska Bily?."

"Ita kike ™o™arin komawa ai Mubeena." Mubeena tunawa a gidan su Bily take sai tayi sanyi tace, "kinga ki ™yale ni kawai ni yunwa ma nake ji" ta faWa tana fita ta bar mata Wakin, Bily ta bita da kallo tana tunanin lokaci yayi da zata raba garo da Mubeena domin tafi ™'arfin ta a yanzu.

Bebi yana komawa asibiti baban Yayan su yayi masa yace in ya tashi daga aiki yazo gida ya same shi ya amsa ya kashe wayar ya ajjiye ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa ne ya masa waya ya Wauka ya saka a speaker yace, "ina ji."

"Nayi discharging Maman Manal suna so su ganka su yi maka godiya abubuwan da suka faru, ka dawo ne?."

"Godiyar me za'a yi min? Me nayi kuma?."

"Kaga Bebi don Allah ka nutsu, Wai kai Sacin ranka kowa sai ya shafa? Meye haka ne wai?."

"Mtsww! To me nayi musu ne? Naga aikina ne ko? Dan na yi aikina sai an yi min godiya?. Bana son takura suj je kawai ai nasan sun gode." Huzaifa yace, "sun ce baza su tafi ba sai sun ganka, sannan akwai maganin da kace min zaka rubuta musu, meyasa kake haka ne wai?." Ya sake jin takaici a fusace yace, "indai magani ne zan turo maka yanzu kaje ka siya musu. Bana son magana ka sani in raina yana a Sace,

domin duk abinda yazo baki na zan faWa musu ne, don Allah ka ™yale ni kawai bana son haWuwa da kowa."

Knocking ake yi hakan ya saka shi datse kiran yace, "yes." Aka buWe ™ofar aka shiga ya hango Manal ta shigo ya dauke kai daga kallon dan ji yayi kan sa ya sara haka kawai bai san dalili ba, ta kalle shi a nutse tace, "Dr zamu tafi, Allah ya saka da alkhairi Mun gode."

"Amin" ya amsa a ta™aice ya cigaba da abinda yake yi. A tsorace take itama tace, "Dr Huzaifa yace zaka bani takardar magani...." A fusace ya katse ta yace, "kije ki same shi zai naki, bana son magana bana son takura kije kawai!" Ya faWa yana nuna mata hanyar fita.

Sai da ta tsorata jin irin tsawar da yayi mata tayi baya tana kallon sa tace, "Allah ya baka ha™uri, baza mu iya tafiya bane ban maka godiya ba ka ceci ran mahaifiyarta wacce bani da kamar ta, koda dukana zaka yi bazan tafi ba sai na tabbatar na gode maka."

Shiru yayi baice mata komai ba, amma ji yake kamar ya tashi ya tsinke ta da marin da zata daina gani, ya lura shegiyar maganar ta inda waje Waya suke zai iya sakawa ya mata dukan tsiya, ta juya tana tafiya ido ya ciko da hawaye. Da wata likita mace suka haWu  tana fitowa tana shiga ita kuma ta wuce wajan Dr Huzaifa ta shiga da sallama ya amsa yana murmushi domin nutsuwar ta na burge shi sosai yace, "Manal zaku tafi ko?." Ta goge idon ta  zata yi magana yace, "ya dai? Ko jikin Maman ne?."

"A'a babu komai."

"FaWa min mana, me ya faru kike goge hawaye?."
Chapter 25 · 0% Book details