← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 48

Sashe 15

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Komai ma kice." Tayi murmushi kawai bata sake magana ba har akazo ™ofar gidan su Bily.

Ta kalle shi tace, "zan shiga gida kar Daddy yayi min faWa. ˜are mata kallo yake irin kallon ´an bariki yake mata har ta tsargu da irin kallon da yake mata ta gyara zama kaWan ganin haka sai yace, kike so?." Jin abinda yace sai tace, "waya nake so a canja min."

"Iphone ko android?."

"Iphone." Kai ya girgiza yace, "gobe zaki ga sabuwar waya Baby, in kina so muje yanzu ki zaSi wacce kike so." Mubeena tace, "A'a, Allah ya kaimu gobe Win."

"Amin Baby. Sai sauri kike ki gudu ki barni ko? Bayan ni kewar ki nake ji kamar na jawo ki jikina haka nake ji."

Ganin babba dashi yana wani abu kamar yaro sai ya bata dariya tayi murmushi shima sai yayi y shafa fuskar ta yace, "kina da kyau Baby" ya faWa yana matsowa kusa da fuskar ta.

Ta saka hannun ta akan masa ta cire hannun sa a fuskar ta yace, "ya kike haka Baby? Wannan fa ba komai bane soyayya ce, kar ki zama wanda basu waye ba mana, ina kallon ki wayayyiya meyasa zaki bayar da kan ki baya?."

"Ina sauri ne kawai."

"Okay, hug me before you leave." Ta kalle shi zata yi magana ya riga ta yace, "please baby" kafin tayi magana ma ya rungume ta, sai taji wani iri domin duk rawar kanta wannan shine karo na farko da aka rungume ta, har gwara dai ri™e hannu amma ruguma bata taSa yi ba.

Kam ya ri™e ta sosai ga turaren da ta saka mai ™arfi da sanyi yana sake tasiri wajan sake ri™e ta sai lumshe ido yake da™yar ta iya janye jikin ta tace, "sai da safe." Muryar a sar™r yace, "okay Baby." Tana faWa ta fita ta shiga gidan jikin ta yayi sanyi shima ya ja motar ya tafi.

Bebi yana tsaye daga baya yana kallon mace ta shiga motar Abban nasa amma bai ga wacece ba, yaga dai an shiga dan lokacin ya karya kwana yaje ya siyawa Mama wani zabo gashashe da take so shigar macen ya gani da kuma wucewar motar dan yasan lambar motar mahaifin sa. Zuciyar sa sai bugawa take yi ji yake kamar yabi bayan sa amma zuciyar sa na hana shi hakan dole yaja motar ya tafi yana hana zuciyar sa tunanin da yake kai kawo a zuciyar sa akan Abba.

A haka ya shiga gida ya shiga wajan Mama ya same ta zaune ta ajjiye abinda ya kawo mata ya kalli Kausar da take zaune ya bata leda Waya yace, "kaiwa Mamy wannan. ba musu ta karSa ta fita ya zauna yayi shiru zuciyar sa dai harbawa take.

Mama tace, "Zabon ne? Allah yayi albarka. Amma lafiya kake?."

"Babu komai Mummy, na gaji ne."

"Ga abinci nan in zaka ci."

"Me aka dafa?."

"Fried rice ce" Mimi ta bashi amsa tana zaune. Ya sauke numfashi yace, "bani kaWan naci." Mimi ta tashi ta zubo masa ya karSa yana ci amma hankalin sa baya tare dasu gabaWaya.

Mama tace, "Sumayya tazo, tana ta zancen ka sai jiran ka take baka dawo ba. Ban Wauka ma a gida zaka kwana ba yau. Yace, "zan je na gaishe ta in sha Allah."

"Da ka kyauta, daman ina so kaje gidsan kodan ku tsayar da lokacin auren ku da Rumana."

Ya kalli Mama ta san kallon na meye sai tace, "haka za'ayi da Bebi, kana sonta tana sonka meyasa kake son zillewa ne?." Ajjiye bowl Win abincin yayi ya tashi yace, "na ™oshi, sai da safe" ya faWa zai fita Mama tace, don nayi maka maganar Rumana shine ka bar abincin? Da yake ga wacce ka tsana ko?.

Bebi yace, A a ba haka bane, na tuna ina da aiki anjima ne shiyasa zan je na kwanta ya faWa yana fita. Yana fita Mimi da Kausar ma suka shige Waki dan basa son zancen Rumana nan amma Mama qaunar abin take yi.

Misalin ™arfe Waya na dare Mam ta farka tana jan numfashi da™yar idanun ta sun fito waje sai wani Waga ™irjin ta sama take da alama ya dame ta da ciwo. Motsin da yake yi ne ya tashi Manal ta kalle ta da sauri ta isa wajan tana faWin, "Mama! Mama!!" Sai ta fashe da kuka ta fita a guje isa zuwa reception ta sanar da nurse suka tawo a guje zuwa kan Mama amma ina abin yafi ™arfin su dole sai Bebi yazo.

Iya abinda zasu iya suka yiwa Maman kafin su fita su biyun suka kira Bebi a lokacin kwanciyar sa kenan. Ganin kiran daga asibiti ya saka shi ya Wauka yana sakawa a kunne akace, "Sir it's ugently emergency." Ya furzar da iska baice komai ba ya yanke wayar ya tashi ya saka riga doguwa ya Wauki makulin mota ya fita.

Tun daga ™ofar Wakin da ya nufa yake jin kukan Manal mai sauti, ya shiga da sauri Nurses maza biyu suna biye dashi a baya, ganin yadda lamarin Maman yake ya saka yace a canja mata Waki da sauri aka ja gadon aka fita dashi zuwa wani Waki daban Manal tana bayan su dole ta tsaya a bakin Waki tana kuka kamar ranta zai fita.

Sun jima sosai a ciki kamar bazu fito ba, tana zaune a kasan tiles tana kuka mai ratsa zuciya ya fito tana jin an buWe ™ofa ta zabura tana kallon sa ta zube guiwa biyu yace, "ka ceci ran mahaifiyata, ita kaWai nake da ita bani da mahaifi bani da yaya namiji, itace kawai gatana a duniya, Allah ne gatana Mama itace gatana, ka taimaka min kar Mama ta mutuuuuu!. In Mama mutu nima mutuwa zan yi.

Sosai ta bashi matu™at tausayi ya bita da kallo kafin yace, "ki nutsu babu abinda zai same ta in sha Allah, ki daina kuka zata samu Lafiya ki mata addu a. Biyu biyu take gani itama kanta ciwo yake yi sosai, yanayin ta ya canja lokaci Waya tayi baya kawai ta kwanta tana dafe kanta.

Nurses biyu ya kira aka Wauke ta aka shiga da ita Waki itama aka kwantar yana tsaye a kanta. tunawa yayi Huzaifa ya ce masa tana da diabetes ya kalli nurses din yace, "ku bani glucometer da sauri."

Da sauri suka bashi ya ri™e hannun ta ya samu sabon syring ya fasa yatsan ta ya jini ya fito ya auna. Abin daya gani ya saka shi wata ido yace, "Subahanallahi, yayi ™asa sosai!." Jin abinda yace suka gane mai yake nufi da gaggawa aka kawo ruwa kala biyu lokaci Waya, da kansa ya saka mata cannula ya fara zuba mata ruwan a jikin ta dan a samu sugar Win jikin ta ta dawo daidai dan yayi ™asa sosai.

Suna Wura mata ruwan ma tayi bacci ya kalle ta ya kalle su yace, "take care of her, duk abinda ya faru a sanar dani. Suka amsa da okay Dr ya fita dan shi yaji daWi ma da take a kwance, dan bai san taya zai faWa mata halin da Maman ta yake ciki ba.

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

                  ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

*Page 011*

Da safe kasancewar monday ce da wuri ya tashi ya shirya bai shiga wajan Mummy bama ya hau mota ya fita. Kai tsaye asibitin ya wuce sanin yana da appointment da wasu patients Win yana zuwa kuwa ya tarar da mutane da yawa suna jiran zuwan sa. Zaman sa babu jimawa ya fara duba mutane wasu ya basu magani wasu ya basu test, wsu a kawo masa kafin wani lokaci ya gama dasu sai ya shiga Wakin da ya ajjiye Mama jiya.

Kallon ta yayi yana sake kallon bugawar zuciyar a na'ura sai kuma ya Wauki abin gwada bugun zuciya dan so yake yaji da kansa ya auna bugun zuciyar ta ba laifi ta dawo daidai amma ba wani sosai ba, allura ya sake mata sannan ya fita zuwa inda Manal din take.

Tana zaune ta dafe kanta idanun ta biyu tana zubar da hawaye ya shiga da sallama ta Wago ta kalle shi, yadda fuskar ta tayi ja abin ya bashi mamaki sosai tace, "ina kwana Dr, ya jikin Mama? Tun Wazu nake so na ganta ance sai kazo dan Allah ka nuna min Mamana" tana faWa tana hawaye.

Matu™ar tausayi ta bashi ya tausasa murya yace, "Maman ki tana nan lafiya."

"Ina so na ganta don Allah." Numfashi ya sauke a yanayin da maman ta take ciki bazai so ta ganta ba sai yace, "zaki ganta." Abinda yace kenan ya juya zai fita tace, "don Allah ka taimaka min naga Mama."

Baice komai ba ya fita dan bai san abinda zaice mata ba. Da nurses ya haWu yana musu tambaya akan Manal yace, "an mata Fbs?."

"A'a ba'a yi ba." Da mamaki yace, "meyasa?." Wanda yake tambaya yayi shiru sai yayi tsaki ya koma inda Manal ya take yaga ta kwanta har lokacin kuka take.

Ganin yanayin ta sai yace, "zo." Abinda yace kenan a ta™aice ta kalle shi fuskar sa tana nan kamar kullum babu annuri ita kuma hakan ne yake bata tsoro dan kana ganin sa take wanda bashi da mutunci. A tsorace ta tashi zaune ganin zai fita sai itama ta tashi tsaye kanta na ciwo sosai amma saboda kar ciwon ya hana ta ganin Mama sai ta biyo shi duk da jiri take ji sosai. Šakin da ya shiga ta shiga itama ta hango Mama a kwance an saka mata ruwa ga oxgen a hancin ta da wani abu a yatsan hannun ta.

Da sauri ta ™arasa wajan Mama tana kallon ta tana hawaye amma bata ce komai ba ta ri™e hannun Maman amma ta kasa magana yadda kanta yake ciwo bata tunanin zata iya magana a wannan lokacin. Kallon ta kawai yake yi tausayin ta yake ji a ransa, yadda take yi ya tabbatar masa da tana qaunar Mamn ta sosai sai yake ji ko shine Mummy take wannan yanayin bai san  ya zai yi ba.
Chapter 15 · 0% Book details