← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 48

Sashe 47

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh an saka ranar sa, kuma wata huWu aka saka." Girgiza kai yake yi lallai Manal ta shammace shi, shi a tunanin sa tunda bata da wani ilimi mai zurfi ba wani wayo ne da ita ba, kasancewar ba wata babba bace zata yi sauri yarda da abinda zai ce sai gashi tayi watsi da abinda yace mata. Nan da nan ransa ya Saci, Bebi bai isa ya cigaba da yin nasara yana barin sa ba, ya zama dole yayi nasara a kansa ya cusa masa ba™in ciki da takaici kamar yadda yake ji a zuciyar sa.

"Tunanin me kake yi?." Kallon Lubna Win yayi yace, "ina tunanin yadda baya qauna ta ne, ina so na samo mana mafitar da zai amince dani." Tayi shiru cikin damuwa ya kuma yace, "Ko Abba na samu da maganar bazai kawo mana mafita ba?." Tace, "Abba sai ya kira Bebi ya faWa masa kuma bazai amince ba tunda baya son ka."

Ya kalle ta sosai cikin taushin murya yace, "Sweetheart!." Ta kalle shi itama yace, "Kina sona?."

Ta kalle shi tace, "Wannan wacce irin tambaya ce?."

"Ki amsa min kawai." Ta girgiza kai tace, "ina son ka." Yayi ajiyar zuciya yace, "kin amince bazan cutar dake ba?."

Tana kallon sa cikin soyayya da shau™in da yake gani a idanun ta tace, "na amince baza ka cuce ni ba." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "Alhamdulillah! Sweetheart bazan cutar dake ba saboda ina son ki, mafita nake nemar mana da zamu kasance a inuwa Waya matsayin ma'aurata."

Ya gyara sosai yana kallon ta yace, "shawara zan kawo ko nace mafita, ban sani ba ko zaki amince ko baza ki amimce ba, sannan ban san da wacce fuska zaki kalle ta ba." Ta kalle shi a raunane tace, "na amince ka faWi ko meye zan amince da kai, na tabbatar baza ka cutar dani ba."

Ya sauke numfashi yayi shiru yana kallon ta kamar ba zai magana ba kafin yace, "ban san ta ya zaki Wauki abun ba, amma dai ina so na taimaki junan mu ne dan na tabbatar in muka rasa junan mu zamu faWa wani hali."

Lubna tace, "ka faWa kawai, ni na amince da kai nasan baza ka taSa cutar dani ba." Ya girgiza kai cikin gamsuwa a zuciyar sa kuwa tausayin ta yake ji amma ya zaiyi bazai bari tausayi ya rinjaye shi akan fansar sa ba, saboda fansar sa yake komai har soyayyar da yake nuna mata duk ta ™arya ce. yace, "ina so ki bani dama ki amince dani har zuciyar ki, ki yarda bazan cuce ki ba, ina so mu kusanci junan mu...." Kafin ya kai ™arshe ta kalle shi da sauri, sai ya tari numfashin ta yace, "ki jira na gama faWar abinda yake bakina kafin ki yanke min hukunci please."

Kallon sa take yi hakan ya saka yace, "so nake hakan ya faru,in ya faru babu wanda zai hana ni auren ki. Wallahi Lubna zamu yi hakan ne saboda a bani ke na aura ba dan wani abun ba Allah ya sani kema kin sani. Amma in kina ganin hakan bai dace ba shikenan sai mu ha™ura da junan mu tunda Bebi bazai bari mu auri juna ba."

Shiru tayi alamun tunani, shi kuma yana sake karyar da murya yana yi mata bayanin yadda abin zai kasance har yaga ta fara aminta da maganar sa ta kalle shi tace, "in na amince baza ka guje ni ba? Baza ka manta dani ba in hakan ta kasance?. Kaga ni ba ´ar iska bace ba, wallahi ko hugging wani namiji ban taSa yi ba har yanzu, zan amince da abinda kace ne saboda ina sonka, na amince da kai baza ka cutar dani ba domin kana sona kuma kamar ™anwar ka nake. Kayi min alqawarin baza ka guje ni ba?."

Kalaman ta sun saka yaji wani iri a zuciyar sa ya sauke numfashi yace, "bazan guje ki ba Lubna, ina son ki bazan taSa abinda zai cutar da ke ko rayuwar ki ba." Ta sauke numfashi tace, "Allah yana kallon ka in ka cutar dani, Allah bazai bar ka ba domin kaci amanar ™aunar da nake maka."

"Lubna ina wannan abun ne dan neman mafita ba dan ina so na kasance dake ba, inda ni mutumin banza ne da yanzu kin fi kowa fahimtar hakan Lubna." Ta girgiza kai cikin amincewa da maganar sa tace, "nima ban ce kai na banza bane, kawai ina so ka ri™e min al™awari ne kar ka guje ni bayan ka raba ni da abinda nake dashi." Mujahid yace, "indai al™awari ne nayi miki."

"Shikenan, na amince da abinda kace" tana faWa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa daga idon ta. sai jikin sa yayi bala'in sanyi ya kalle ta murya a raunane yace, "meye na kukan?."

Murya na rawa tace, "Daga zuciyata yake zuwa, ban san dalilin zuwan sa ba." Yayi murmushi yace, "kar ki damu, zan nema mana wata mafitar in bamu samu ba sai muyi amfani da wannan Win. Hakan yafi miki ko?."

Ta sauke Ajiyar zuciya ta Waga kai tace, "to." Ya kalle ta yace, "to ki yi murmushi mana, haba Sweetheart." Murmushi tayi shima yayi yana kallon ta kafin yaja motar su tafi zuciyar sa nayi masa sa™a da warwara akan lamarin Lubna, Anya yayi mata adalci? Anya in yayi hakan bai cuce ta ba?. Amma Itace hanyar da yake da ita wacce zai sakawa Bebi ba™in ciki a zuciyar sa, babu yadda zaiyi dole yaci amanar qaunar da take masa.

Nana Haleema.>ØBÝd'þ

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

     ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

*BOOK 1*

*Page 30*

Abban su Bebi lokacin da ya shiga gida Mama ya kira a waya yace tazo da yake yamma tayi sai ta tafi da abinci ta kai masa ta ajjiye ta zauna kamar yadda yake a zaune shi da Mamy tace, "sannu da zuwa."

"Yauwa sannu, ya gida?."

"Lafiya lau."

"Ayyuka sun mana yawa shiyasa kwana biyu komai ya sake lalacewa, ku yi ha™uri komai zai wuce da zarar komai ya dawo daidai."

Mamy tace, "Allah Sarki."  Abba yace, "nasan bana kyautawa amma ayi ha™uri, cikin kwanakin nan zan jima a gidan nan in sha Allah." Mamy tace, "hakan yayi kyau, Allah ya daWa gyara komai."

Ya amsa da amin Mamy ta mi™e tace, "ina da ba™i zan je na sallame su, in kuma ban dawo ba sai da safe" ta faWa tana fita. Mama ya kalla ganin wani wajan take kallo yace, "ran ku nasan a Sace yake dani, ayi ha™uri kawai."

Mama tayi murmushi tace, "Sai yanzu zaka ce ayi ha™uri?. Kudin ´ar ka ta cikin ka aka kawo aka saka rana baka san anyi ba, aka kai kuWin Bebi aka saka rana shima baka sani ba. Wanne irin uba ne kai?, Hakan yana nufin kana sauke ha™™in da yake kan ka wanda Allah ya rayata ya maka kenan?. Yanzu da babu ´an uwan naka haka yaran zasu zauna basu da wanda zai shige musu gaba a lamuran su?."

Ya sauke ajiyar zuciya yace, "duk na Wauki laifin, kuma za a gyara in sha Allah." Tayi murmushi na takaici tace, "sai da lokaci ya ™ure za'a gyara kenan?. To ina so ka tunda duk abinda ka ke yi mana sai an yiwa yaran ka wallahi, mu ma ´a´an ne kamar yadda naka suke ´a´a mu ma haifar mu akayi. Ko me ka ke aikatawa a waje wallahi sai an yiwa yaran ka a suke cikin gida koda kuwa ka saka ™arafuna kayi musu katanga ne, wallahi sai an samu wani ya Salle wannan katangar ko da kuwa mai gadin gidan nan ne."

Kallon ta yayi hakan ya saka ta sake yin murmushi tace, "´an matan ka na waje, in soyayya ka ke dasu ba don ka aure su ba kana da ´an mata a gidan nan ai, in ma lalata su ka ke dasu kaima kana da ´an...."

"Hauwa wacce irin magana ki ke yi haka? Kina cikin hankalin ki kuwa?" Ya faWa yana kallon ta a fusace.

Mama tayi Murmushin takaici tace, "Da hankalina nake maganar kamar yadda ka fahimci abinda nake nufi. Mu matan ka mun zama banza saboda kana da wasu a waje shiyasa ka raina mu kana ganin kamar mu Win ba komai bane face wanda suka tsufa, kana da sabon jini a waje wacce tsiyar zamu yi maka?. Kar Ka ga dai ina da jikoki a gidan nan ko?, to hakan bazai hana na bar gidan nan ba walalhi, tura ta fara kaiwa bango ™iris nake jira, lokaci kaWan kawai" tana gama faWar hakan ta mi™e ta fita ya bita da kallo hankalin sa ya tashi sosai. Kenan duk sun fahimci yana da ´an mata a waje ko me? Kenan da gaske maganar ta zata tabbata na wani zai nemi ya lalata masa yara?.  Ya firgita sosai da abinda tace hakan ya saka shi saurin kawar da tunanin amma zuciyar sa bugawa take matu™a.

          **** Maryam kuwa tun bayan abinda ya faru tsakanin ta da Kamal ta shiga damuwa sosai ko wayar sa bata Wauka, babban tashin hankalin ta bai wuce abinda ya wakana tsakanin su ba in ta tuna hankalin ta tashi yake yi sosai. Yana kiran ta bata Wauka, yayi message bata reply domin kuwa bata ga amfanin cigaba da kula shi ba, tayi nadamar abinda tayi sosai haushin kanta take ji.

A ranar yayi mata message sama da goma tayi banza bata bada amsa ba, kawai taga an turo mata hoto a ™asan hoton an rubuta, _Ko dan saboda wannan ki amsa wayata Maryam._ gaban ta yayi mugun haWuwa ganin hoton ta babu suttura irin wanda take tura masa a lokacin da take gidan sa matsayin soyayya.

Jikin ta rawa yake sosai, hankalin ta ya kai ™arshe wajan tashi kallon hotun take yi cikin kiWima da nadama mara amfani. yana kiran wayar hannu na rawa ta Wauka daga can Sangaren yace, "har ni ina miki waya ki daina Wauka? Na baki ha™uri meyasa baza ki ha™ura ba Maryam?." Maryam tace, "Kamal kace min ka goge hotunan nan."

"Akan me za'a goge bayan gashi yayi min amfani yanzu?."

"Kamal ya kamata ace ka goge shi saboda ni ba matar ka bace ba. Barin tsairicina a wayar ka haram ne."
Chapter 47 · 0% Book details