← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 48

Sashe 35

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

angaren Bebi haka ya kwana ya yini cikin karsashi  da farin ciki da annushuwa, koda yaje asibiti sun lura da yadda yake komai da kazar-kazar kai da ka ganshi kasan akwai wani abu mai daWi da ya same shi.

Lokacin da yake asibitin su na getting better babu wani conjunction na marasa lafiya in ma akwai ba Sangaren da bane da yawa Sangaren su Hamza ne da ´an team Win sa, hakan ya saka shi zama kawai yana tunanin Manal da abinda zaice mata in yaje wajan ta a ranar.

Bai jima sosai ba ya tashi zai tafi sai a sannan suka haWu da mutanen nasa Hamza ya kalle shi yace, "Ahha Bebi wannan yanayin da na ganka a ciki duk soyayyar ce?." Šaure fuska yayi gudun kar su jawo masa raini ganin basu kaWai bane a wajan, hararar su yayi yace, "ku kuka sani" yana faWa  yayi gaba suka yi dariya suka cigaba da abinda suke yi shi kuma yayi gida.

Yana shiga gidan Maryam tana shigowa itama ya bita da kallo, gabaWaya baya amincewa da yawan fitar da yake gani suna yi ita da Lubna su kaWai,  amma da yake idanun sa basa ganin abinda baya so a tare dasu bai wani damu ba.

Ciki ya wuce ya shiga wajan Mama ya samu Yayar sa Farida a zaune ita kaWai tana danna waya. Ya zauna yace, "saukar yaushe?."

"Na jima a nan, ya aikin?."

"Alhamdulillah. Ina Mummy?."

"Tana ciki. Ya batun Rumana ne?, Mama ta matsa a kai fa, yanzu ma kafin ta tashi maganar take yi min, maganar ta taso da gaske ne?." Ya kalli hanyar da Mama zata Sillo yaga bata nan yace, "zan zo gida mu tattauna a kai."

"Ya dai kamata, ni sam-sam bana so yanzu wallahi, da dai naso ka aure ta amma yanzu abin ya fita a kaina haka kawai."

"Hmm! Kema dai kya faWa."

Mama ce ta fito tana cewa, "A'a Bebi an dawo?." Yayi murmushi yace, "eh Mummy, na dawo" ta ™araso ta zauna tana kallon sa tace, "to Sannun ka."

"Ina su Mimi?."

"Sun je gidan Yayan ku."

"Me ake yi?."

Mama ta kalle shi da mamaki tace, "Sai ana wani abun zasu je gidan Yayan su? Meyasa ka ke haka ne wai?."

Baice komai ba yayi shiru ya tashi ya shiga kitchen sai gashi da abinci yana yamutsa fuska san baya son macaroni amma gashi an dafa kuma jellop duk tayi sanyi ba yadda yake so ba.

Mama ta kalle shi yana ci yana taSa baki yace, "Bana son wannan abar Mummy."

"Sai ka ajjiye ai." Baice da yawa ba kuwa ya ajjiye ya kalli Farida yace, "dama zaki min girki da naji daWi." Hararar sa tayi tace, "ashe zaka kwana baka ci ba wallahi." Ya taSe baki Mama tayi dariya tace,

"Kema dai , ai da sai kice ya jira ki zaki dafa masa, in kana son girki na kira Rumana nace ta kawo maka."

Ya girgiza kai yace, "A'a Mummy ™yale ta, zan san abinda zan ci" ya faWa yana tashi ya fita. Mama tayi dariya bayan ya fita tace, "duk zilliyar ka sai ka auri Rumana Adnan." Farida bata ce komai ba dan itama ba so take yi ba.

Sai bayan sallar magriba sannan yayi wanka yayi kyau cikin manyan kaya kamar jiya, yana ta ™hamshi mai sanyi dan shi baya ™hamshi mai Waukar hankali, baya son turare mai ™arfi kowa ya san da wannan indai kuna tare. Falon ya shiga ya tarar da Mama da Farida dasu Mimi duk sun na nan ganin sa sai suka tsaya kallon sa dan ya yi musu kyau sosai.

Farida tace, "Sai ina?." Mimi ™asa-™asa tace, "Kamar dai mai zuwa zance" ta faWa tana kulle bakin ta tana dariya.

Mama ta kalle shi tace, "ma sha Allah Bebin Mummy, kayi kyau sosai, ina zaka je haka?." Yayi murmushi Yace, "zanje wani waje mai mahimmaci Mummy, kiyi min fatan samun nasara" ya faWa yana ™arasowa inda take ya cire hular kansa ya tsiguna a gaban ta Wora hannun ta a kana tace, "Allah ya bada nasara, ko ina kaje kai ne mai nasara ai Adnan."

Ya mayar da hular ya tashi ya kalli Farida da suke gulmar sa ita da su Kausar yace, "me kuke cewa?."

"Cewa nayi yanzu wata™ila dan wata kayi wannan kwaliyyar ko?, Ko da yake Kausar tace ko wacece bata san wanda zata Wauko bane shiyasa".

Yayi ´ar ™aramar dariya yana kallon su yace, "munafukai." Ganin har dar1ya yayi sai suka suka yi  dariya suka samu ™arfin guiwa Mimi tace, "wallahi kayi kyau Yaya, kuma yau naji kana khamshi kuma naga baka son turaren."

"Na gode. ™aryata ni ki keso kiyi kice daman dai ina sakawa ko?." Ta girgiza kai tace, "A'a, kawai dai nayi mamaki ne da na ji ™hamshin yanzu, ban taSa jin khamshin mai yawa haka a jikin ka ba, nasan ana ji amma sai anzo inda ka ke sosai."

"Ke dai munafuka ce, to dan kin ji turare a jikina sai ki cigaba da sakawa kizo inda nake" sai ya faWa cikin wasa suka yi dariya. Mama dai kallon sa take tace, "wannan kwaliyyar kamata yayi ace ta Rumana ce, ina zaka je haka ne?."

"Zan sanar dake Mummy sai na dawo" yana faWa ya fice suka cigaba da gulmar sa suna dariya.

Nana Haleema>ØöÞ<Øûß>ØBÝ

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

  ©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu. https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.

*BOOK 1*

*Page 022*

Bebi sai da yayi sallar i'sha sannan ya ™arasa ™ofar gidan su Manal, Baba ya gani ya fito daga masallacin da yake farkon layin yana shigowa a ™asa yana jan charbi, ganin sa sai ya fito daga motar Baba da ya hango shi sai yayi murmushi ya ™araso yace, "Adnan ka ™araso?."

"E Baba, barka da dare" ya faWa yana du™awa ya amsa yana cewa, "barka dai likita, ya aikin naku?."

"Alhamdulillah."

"To ma sha Allah. Muje ciki" Baba yayi gaba yana bin sa a baya.

Sai da suka shiga soron gidan su Manal Win sannan yace, "anyi sa'a ma yau ma da wuta, kasan da yake ni ban amince da wani taWi a soro ko a mota ba gaskiya, nafi gane a shigo har cikin gida in ta kama a tsakar gida ma a zauna hakan yafi min kwanciyar hankali." Bebi ya girgiza kai cikin jin daWi da gamsuwa yace, "haka ne Baba." Tare suka shiga gidan babu kowa a tsakar gidan a share tiles Win yayi tass sai ganyen bishiya da ya faWo ™asa, gidan shiru kamar babu kowa.

˜aramin falon da suka shiga jiya nan suka sake shiga an gyara shi sai khamshi yake kaWan kaWn Baba yace, "ka zauna a nan zan turo maka ita yanzu nan." Bebi yayi godiya ya zauna Baba ya fita dan ya kiran Manal.

Yana zaune yana danna wayar sa yaji sallamar ta ya amsa yana Wago kai ya ganta cikin ba™in hijjabin da ya ganta a asibiti, shine lokacin da ya kasa mantawa ko yaushe tunawa fuskar ta yake a wannan lokacin. Shaf ya manta kallon ta yake yi, yaso yayi controlling emotion Win sa a kanta amma ya kasa ashe har ta ™araso ta zauna daga gefe a kan carpet Win da yake falon sai ji yayi tace, "ina yini."

A lokacin ya dawo hankalin sa ya dake kamar bashi ba dan ya shagala da kallon ta shi kansa ya sani yace, "kin yini Lafiya? Ya jikin ki?, I hope kin samu Lafiya sosai?."

Jin tambaya har uku da yayi mata lokaci Waya sai ta kalle shi suka haWa ido ta shagwaSe fuska tace, "to wacce zan fara amsawa?. Na yini Lafiya, naji sau™i, eh sosai a samu Lafiya." Jin ta amsa masa duka a tare yadda ya tambaya sai yayi murmushi sosai yana jin wani nishaW a zuciyar sa, ya gama lura shagwaSa a jinin ta take kowa ma yi amsa take yi.

Ganin yana murmushi abin ya bata mamaki tana kallon sa a ranta tana ayyana daman ya iya murmushi yake kullum fuska a Waure fuska.

Ya girgiza kai yace, "Adnan Mu'azzam shine sunana, nasan kin san aikina ni likitan zuciya ne." Ta girgiza kai bata ce komai ba ya kalle ta yace, "Baba ya sanar dake dalilin zuwana nasan da hakan, haka kawai Allah ya saka min ke a zuciyata na kasa mantawa dake har sai da nazo gidan nan jiya na samu Lafiya."

Bata ce komai ba yace, "Manal bana son ™arya, duk wani abu da kika sani ya shafe ki ki sanar dani kar ki yi min ™arya kat ki Soye min wani abu. Manal ™arya tana sakawa naji mutum ya fita daga raina lokaci Waya, dan haka kar ki Soye min komai a kan ki. Bazan ce lallai sai kin so ni ba, in kina da ra'ayina daman haka nake fata, in bakya yi haka Allah yayi daman." Yayi shiru yana kallon ta dan yaga yanayin ta amma bai fahimci komai ba yadda take haka take yace, "meye a zuciyar ki?."

Ta girgiza kai tace, "babu komai. Amma ni masu aikin ku basa burge ni, likita bai taSa burge ni ba, so bana tunanin...." Sai tayi shiru bata ™arasa ba.
Chapter 35 · 0% Book details