← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 48

Sashe 14

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban Manal faWuwa yake sosai ta kalle shi suka haWa ido, haka kawai gaban sa ua faWi dan tayi yanayi kaWan da wata da ya sani a baya tace, "na gode ka ri™e kayan ka, bana so na amince a kama ni Win indai sai ka ri™e ni ne. Kuma Allah sai ya saka min abinda kayi min, Allah bazai barka ba, indai haka ne taimakon Allah ya wadaran sa wallahi. kuma abinda ka yiwa Wan wani sai an yiwa naka Wan ko yanzu ko nan gaba ta faWa tayi tsaki ta fita a guje tana hawaye da dana sani, tashin hankali, rawar jikin duk sun tarar mata. Lokacin da taje fita an buWe gate mota zata shigo sai ta sake kwasa da gudu ta fice tana kuka sosai.

Babu nisa sosai daga gidan zuwa asibitin tana kuka sosai ta isa asibitin, a ™asa lokacin har duhu yayi tana shiga ta zauna inda take zama ta dafe kai tana kuka sosai, jikin ta har lokacin rawa yake saboda gani take kamar zai biyo ta. Sai kalle-kalle take yi saboda tsoro da tashin hankali, hakan bai taSa faruwa da ita ba sai yanzu, hakan ya saka ta firgita sosai bata Wauka ita wannan halin bazayen mazan zai zo kan ta ba.

Babban tashin hankalin ta bai wuce yanzu abinda ya kamata tayi ba akan kuWin asibitin da kuma kuWin allurar da akace ana so da gagawa, gaban ta ya tsananta faWuwa kana kallon ta zaka hango tashin hankali ™arara akan fuskar ta. _yanzu ya zakayi Manal? Da wanne kuWin zaki biya kuWin asibitin nan da a ™alla ya kai dubu dari biyu? Ga kuWin allurar da akace za'a yiwa Mama, ya zanyi ni Manal me zanyi na samu wannan kuWin?._

Hawaye take yi sosai cikin zullumi da tsoro, ™irjin ta sai bugawa yake yi sosai hankalin ta ya tashi saboda tsoro da tashin hankali. "Ashe daman amfani aka yi da rashin lafiyar Mama dan a keta min haddi? Innalillahi wa inna ilaihir raji un! yanzu ba a taimakon mace sai dai ayi amfani da ita?. Babban ba™in cikin ma babbba dashi, ya kusa jika dani amma ba kunya ba tsoron Allah. Duk laifina ne, nice na jawowa kaina ta faWa tana kuka sosai.

"Manal! Huzaifa ya faWa yana zuwa inda take ganin tana kuka sosai sai ya tsorata yace, "jikin Maman ne ya tashi?" Ya fadWa le™a Maman yaga bacci take ya dawo yana kallon ta yace, "Meya faru kike wannan kukan? Me ya faru? Wani ne ya rasu a gida?.

Manal kukan take yi sosai muryar ta har sar™ewa take, so take tayi magaar amma ta kasa. Ganin hakan sai yace, nutsu, nutsu ki faWa min abinda yake faruwa..

Manal tace, "Bani da kuWin da zan biya kuWin asibitin nan, ni zan Wauke Mama mu tafi gida kawai. Tsoro nake ji, tafiya zamu yi.

"Me kike cewa haka? Ina shi Yayan naki da kika ce ya kawo ki nan?."

Ta girgiza kai tana hawaye wani yana bin wani tace, "Ba Yayana bane, wallahi ban sa shi ba, kawai yayi amfani da ciwon Mama da ruWewar da nayi ne a can babban asibiti ya kawo mu nan. Nidai tafiya zamu yi, baza mu zauna ba. Daidai a lokacin Bebi yazo wajan yana kallon su Huzaifa yace, "to yanzu yana ina? Ina allurar da likita ya baki yace a kawo kafin dare?."

"Tana hannun sa" sai ta sake fashewa da kuka mai cin rai tana rufe fuska da hannun ta duka biyun. Ya kalli Bebi da yake tsaye ya sake kallon Manal yace, "yana ina shi? Ki yi bayani lokacin allurar yana yi.

Sai da ta tsagaita kukan yace, "ban sani ba, nidai na bashi sai yace sai mun je na yiwa wanda ya saka aka kawo ni nan godiya& ..! Sai muryar ta tsay tana kuka kafin tace, Nidai a can na barsu na gudo nan bazan iya abinda suke so ba, wallahi tsoro nake ji sunce za'a kama ni tunda bani da kuWin biyan asibitin nan, Nidai ka taimaka min Mama ta samu lafiya koda za'a kama ni Win, na yarda naje prison indai har Mama zata warke na tabbata zata dinga min addu'a. Amma bazan iya abinda suke so ba, wallahi bazan iya ba ta faWa tana kuka sosai.

Huzaifa ya kalli Bebi da suka fahimci maganar ta, yadda take maganar ya nuna musu kenan dai sai ta bayar da kanta za a taimaka mata shine abinda take cewa baza ta iya ba. Huzaifa ya sauke Ajiyar zuciya yace, ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai kama ki, kuma kuWin asibiti dana magani duk kar ki damu za'a yi Mama komai in sha Allah. Kin amince bazan cuce ki ba?.

Ta Waga kai alamun eh yace, to ki daina kuka, za a yiwa Mama komai har sai ta samu lafiya in sha Allah Ya kalli Bebi yace, "don Allah ka sake bani allurar sai naje a samo ayi mata, lokaci na tafiya kace kafin dare.

TaSe baki Bebi yayi yace, Done! yana faWa ya bar wajan shima yabi bayan sa.

Office ya koma yana tattara kayan sa zai tafi gida Huzaifa yace, "ka duba rashin imani irin na mutanen mu, baza'a taimake ta ba kenan sai ta bada kanta?. Anyi amfani da rashin wayo da kuma ruWewar da tayi ana neman lalata mata rayuwa. Na tsani irin wannan mutanen wallahi. Yarinyar nan yadda take son Maman ta abin a taimaka mata ce, amma mutanen mu an lalace ba a taimako tsakani da Allah.

Bebi baice komai ba amma har zuciyar sa ta bashi tausayi ya sauke numfashi ya Wauki wayar sa yana kallon huzaifa kana yace, "haka duniyar ta koma, itama kuma bata da hankali ne. Tun farko ma bai kamata a barta a wajan nan ba, ina Baban ta? Ina ´an uwanta?, duk baza su zo ba sai a barta ita kaWai yau kwana biyu?. Tun farko meyasa ma ta amince dashi har aka kawo ya nan? da ace komai ma ya faru da ita tace ta jawowa kanta."

"Bebi yarinya ce fa, kuma tana cikin ruWewa in ka duba. A yadda na san yarinyar nan akan Maman ta wallahi zata iya yin komai, in akace yau diabeties Win Maman ta yyai high yadda hankalin ta yake tashi ko Maman nata baya tashi, tsaf za a cuce ta akan Maman ta.

Bebi ya taSe baki yace, wa™ila ma ™arya take, daman bata da abin biya tazo na, wannan duk cikin plan ne.

Na faWa maka na san ta, baza ta yi haka ba wallahi.

"Shikenan shugaban masu sanin mutane, Allah yayi tana daga cikin wanda za'a yiwa komai for free, ta huta. Ni gida zan wuce" yana faWa ya wuce shi shima ya fita ya samu ta koma ciki wajan Mama amma har lokacin kuka take. Da™yar ya lallaSa ta ta daina kuka ta kuma amince baza'a kamata ba sannan ya tafi shima.

Sai a sannan Manal ta Wauki wayar ta wacce Surayya ta kawo mata ta kunna ta kira lambar Baba amma a kashe ake cewa ta ajjiye wayar kawai tayi tagumi tana kallon Mama har lokacin zuciyar ta rawa yake saboda tsoro.

"Da yake baki da mutunci ki ko ki kira ni ki faWa min Mama babu lafiya" Mubeena ta faWa tana shigowa cikin Wakin. Ganin ta sai Manal taji daWi sosai ta tashi da sauri ta rungume ta sai kuwa ta janye ta tace, "ke bana son sabon salon iskanci, da yake kina so a dinga yi dani a baki a unguwa ana cewa ban damu da uwata ba sai kika ™i faWa min kina nan, Sai Surayya muka haWu da ita takr cemin ai kuna wanna asibitin. A ta™aice ma ubanwa ya baki kuWin asibitin nan?."

Manal kallon ta kawai take yi ta kasa magans, ita kuma ta isa wajan Mama da take bacci ta sake kallon Manal tace, "ni zan koma bacci nake ji sosai gaskiya, waye ya kawo ku nan?." Manal kallon ta kawai take yi bata ce komai ba ta Wauki apple guda Waya a wacce take ajjiye tace, "ashe daWi ma kike ci, ni na wuce" ta faWa tana hanyar fita Manal tace, "Yaya tun jiya Mama take tambayar ki, ki dakata ta farka ta ganki don Allah."

"Manal na faWa miki bacci nake ji, ina so na huta sosai zan dawo da safe."

"Hutun yafi zama a wajan Maman ne?."

"Ke bana son iyayi, baga ki nan ba ai dani dake duka Waya ne ko?." Wayar tace tayi ™ara sai bata sake magana ba kawai ta fita Manal ta bita da kallo.

Tafiya take tana waya har ta Wan yi tafiya mai nisa kafin taga motar wanda take nema ya sauke ba™in glass Win sa, ganin hakan sai ta shiga tace, "meyasa baka je bakin gate Win ba ka barni Ina takawa a ™asa?."

"Sorry Baby, akwai wanda bana son haWuwa dasu ne shiyasa." Cikin shagwaSa tace, "to ba sai ka turo a Wauko ni ba, ni duk ™afana ya gaji."

Murmushi yayi yace, "sorry na tuba, in kina so zan iya miki tausa." Ya faWa yana jan motar suka tafi. Tayi dariya bata ce komai ba yace, "Tunanin ki kawai nake yi sai naga kina waya, in ba ke ba babu wanda zai saka ni na fito daga gida yanzu, sai ke Win kawai."

Tayi farrr da ido cikin jin daWi kafin tayi magana yace, "amma wa kika zo dubawa a nan?."

"Wata course mate Wina ce."

"Kin taSa zuwa asibitin ne?."

"Ban taSa zuwa ba sai yau. Yana da kyau a ido gaskiya. Yayi murmushi yace, "akwai kyau a ido amma ba wani aiki suka iya ba, kar ki sake zuwa ma saboda kar ki Wauko ciwo."

Tayi dariyar jin daWi tace, "an gama Baby." Yayi murmushi sai ya kai hannun sa cinyar ta inda hannun ta yake ajjiye ya ri™e bai kalle ta ba yaga dai ta kalle shi reaction Win ta ya canja amma bata nuna ba yace, "ina sonki Baby, in muna tare Ina kasa ri™e kaina sai na rasa nutsuwa ta gabaWaya Baby."

Murmushi tayi har lokacin hannun sa yana kan nata ya ri™e yana matsawa a hankali yace, "Baki ce komai ba Baby."

"Me zance?."
Chapter 14 · 0% Book details