← Book details Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 48

Sashe 19

Baya Da Kura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take fuskar da ta koma yadda take yayi shiru Hajiya tace, "da gaske? Kai amma nayi murna wallahi sosai, na jima ina burin hakan ya faru tsakanin yaran ku. ina son auren zumunci dan kar ace na takura ne yasaka nake yin shiru amma da hakan ya faru naji daWi. Ni in tani ne yaran nan mata da maza babu wanda zai fita waje yayi aure, nafi so kowa ya zaSa cikin ´an uwan sa. Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

Mama ce kawai ta amsa Hajiya ta kalle shi tace, "shugaban masu Waure fuska, ka dinga dariya don Allah Adnanu wannan rashin fara'ar taka yayi yawa wani lokacin.

Baice komai ba akayi sallama duk suka amsa suka kalli mai shigowa sai ga Rumana ta shigo da kwano a hannun ta Hajiya tace, "ga amarya, ga kuma angon a zaune." Ganin su Adnan sai zuciyar Rumana tayi fari karr ta ™araso ta zauna kusa dashi tace, "Hajiya Ina wuni."

"Lafiya lau Rumana, ya Umman taki?."

"Lafiya lau. Mummy ina wuni?." Mummy ta masa tana murmushi ta kalli Adnan da yayi kamar bai ganta batace, "Beb ina wuni."

Kamar abinda yake jira tace kenan sai yayi sauri ya mi™e bayan ya amsa yace, "Mama in kin gama ina mota" ya saka hannu aljihu ya Wauko kuWi ya baya Hajiya yana cewa, "duk da nasan kuWi ne dake, amma a saka mana albarka." Tayi dariya ta karSa tana godiya tare da addu a ya fita.

Rumana ta mi™awa Hajiya kwanon tace, "Hajiya gashi inji Ammi." Hajiya ta karSa ta buWe tace, "dambun kaza muka samu, kai Allah yayi albarka. Ga so yayyen nama ma Hauwa u ta kawo." Rumana ta kalli Mama tace, "Mama ke zan bi a can zan kwana, bara na faWawa mai kuWi ya wuce gida kawai" ta faWa tana Waukar waya ta faWawa wanda ya kawo ta . Hajiya tace, banda abin babar ki ma ai bai kamata ta Wauke ki ba, ga wacce ta ri™e ki tun kina shekara biyu har kika girma, amma da tgaa kin zama mutum sai ta ™wace ki. Suka yi dariya suka yi sallama da Hajiya suka tafi.

     Rumana ce ta shiga gaban motar Adnan yana zaune yana danna wayar sa Mama da Mimi suka shiga baya yaja motar suka tafi. Tsaki Mama taji yayi sai tayi dariya tace, "Ke Rumana ban san me yake damun ki ba, har yanzu kin kasa gane Adnan baya son turare mai ™arfi, amma ke duk sanda zaku haWu sai hakan ta faru, wannan tsakin da yake na turaren ki ne."

Rumana tace, "to ni Mama ban san ya yake so nayi masa ba, shi ace baya so a saka turare haka zaka zauna babu turare?" Ta faWa tana kallon sa, bai kalle ta ba bai kuma ce komai ba tu™a motar kawai yake yi.

Har suka je gida baice komai ba yana faka motar duk suka fita shima ya fita ya shiga ciki kai tsaye banWaku ya wuce ya jima ciki sannan ya fito bayan yayi wanka ya saka doguwar riga ya fito ya zauna a lokacin Rumana ta shigo da abinci a hannun ta ta ajjiye masa tace, "Gashi inji Mama."

Baice komai ba ya ja abincin ya fara ci ta zauna kusa dashi ya tsayar da cin abincin yace, "in kina son zaman lafiya ki daina zuwa inda nake da irin wannan turaren, bana son oil perfume."

Rumana ta jingina da kujera tace, "nasan wannan tun a baya Beb, amma ni mamaki kake bani har yanzu meyasa baka son turare?. Da na Wauka zaka daina zuwa yanzu sai gashi yanzu abin yafi na baya ma, kuma kai ai ana jin ™hamshin a jikin ka.

Bai bata amsa ba ya cigaba da cin abincin sa tace, "Ko dai yana saka ka cikin feeling Win mace ne?." Kallon ta yayi sai ta rufe baki tana kallon sa baice mata komai ba ya cigaba da cin abincin ta tashi zaune tace, "ni ina son turare kai ma ka sani, tun a wancan lokacin na faWa maka amma in mun yi aure zan rage."

Ta sake cewa, "Beb wa na gani Wazu a motar ka? Na ganka kai da mace wacece ita?." Cikin salon tura mata haushi kai tsaye yace, "Wacce zan aura ce." Tayi dariyar rainin hankali tace, "ai kasan baka da matar da ta wuce ni a duniya."

"A aya aka faWa ko a hadisi?."

"Babu Waya, amma dole ya tabbata." Ta sake yin dariya tace, "gwara ka faWa mata tun wuri ta nemi mijin aure wannan mijin na Rumana ne kawai."

Ya ajjiye abincin ya sha ruwa ya kalle ta sosai yace, "kina ji, ni banza auri ragowar wani namijin ba, komai nawa sabo nake amfani dashi ko meye kuwa. You have to know that, I'm not your type. Banyi kama  da wanda zai auri ragowar wani banza ba kin gane?. Ya kamata ki daina hauka a kaina Ruman, na riga na rufe shafin rayuwar ki bazan sake buWe shi ba har abada. Mummy baza tayi min dole ba dan nasan duk wani hope din ki akan Mummy yake, nobody can force into married you, ki daina wannan rawar kanAdnan na sabuwar mace ne ba na wacce aka rage ba" ya faWa yan kallon ta ido cikin ido, ya lura maganar ta kashe ta dan tunda auren ta ya mutu ta dawo tana wannan rawar kan bai taSa faWa mata magana kamar haka ba.

Murya a sanyaye tace, "Adnan ni ka ke cewa ragowar wani?." Ya jingina da kujera yace, "to meye in ba ragowar wani ba? Ke ba ragowar bace?. Kuma wacce ke da bazan faWa miki haka ba Ruman?." Ta girgiza kai tace, "ni Ruman wacce ka ke so."

"Point of correction! Ruman wacce Adnan yaso a duniyar yarinta ba wacce Adnan yake so ba. Adnan mace Waya yake so yanzu tak a duniya itace wacce kika gan mu tare, ya kamata ki ™yale mata mijin ta ki daina wahalar da kanki akan abinda baza ki samu ba.

Adnan har yanzu kana sona." Yayi Murmushin da yake masa kyau a duk sanda ya bayyana a tare dashi yace, "this is your failure Ruman, kina tunanin har yanzu Adnan yana son ki wannan shine abinda yake cutar dake, Baki san Adnan ya manta da wata mace mai suna Ruman a duniyar soyayya ba. Yana mata kallon ´ar uwa ne kawai kuma wacce suka tashi tare bayan nan babu wani abu. Inda zaki kwantar da hankalin ki ke ´ar uwata ce, kina da wannan matsayin a wajena amma batun soyayya babu ya faWa yana wara idanun sa yana girgiza mata kai.

Ta kasa magana sai kallon sa da take yi, ya lura da ya kulle mata baki shi kuma yana sane ya mata haka dan ta san bata isa ta barshi taje tayi aure ba bayan ta fito kuma tace sai ya aure ta ba, beside shi babu soyayyar ta a zuciyar sa Allah ya sani. Ana cewa ba a mantawa da first love shi kam ya mata da ita.

Ya sake kallon ta yace, "Kina ji, na farko turaren ki ya dame ni, na biyu bana son magana dake ki tashi ki bani waje."

Kai take girgizawa cikin Sacin rai tace, "wallahi sai ka aure ni Bebi, ko sama da ™asa zata haWe sai na zama matar ka." Ya taSe baki ya tashi yace, "babu abinda zai saka sama da ™asa ta haWe a kan ki Ruman, aure ne bazan yi dake ba tunda ba a dole you have to give me some space please, kina ta insisting akan abinda bazai faru ba."

Tashi tayi tsaye tana kallon sa tace, "dole ya faru ko bak so. Ko dan wannan cika bakin naka sai na tabbatar da ka zama mallakina, wallahi sai ka aure ni, a ranar zan mayar maka da martanin ba ko yaushe ake samun abu sabo ba, ni da ka ke kira ragowar wani sai an kira ni da suna matar Bebi.

"Okay! we shall see" ya faWa yana kallon ta ta fita ya bita da kallo sannan yayi tsaki. A bayyane yace, "na gode Allah da ya cire min son wannan yarinyar da ban san ya zanyi ba, ina ni ina auren ta? Ga rashin kunya sannan gata bazawara?. A baya ma tsautsayi ne da ™uruciya ya kai ni ya faWa yana tashi ya shiga Waki.

*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025

©þNana Haleema.

Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

Book one

Page 013

A fusace Rumana ta fita kalaman sa sun mata ciwo sosai ta nufi wajan Mama dan abinda ta faWa masa so take ya tabbata taga ya zai yi. tana shiga Wakin Mama ta wuce ta same ta a zaune da ´an matam tace, "Mama meyasa yanzu Bebi baya sona? Meyasa yake wula™anta ni dan Allah ya Wora min ™aunar sa?. Na san nayi kuskure a baya da na auri wani bashi ba, wannan dalilin ne ya saka yake min haka? Kuma na gane nayi kuskure kuma na nemi yafiyar sa meyasa bazai sake bani dama ba?." Mama da take kallon ta tace, "me ya faru kike kuma haka? Zauna ki faWa min ne Bebin yayi miki kuma?."

Rumana ta zauna tace, "Mama ni yake kallo yana cewa ragowar wani ce bazai aure ni ba, Mama in wani zai ce min haka bai kamata shi yace ba, amma shine yau yake cemin bazawara wai yafi ™arfina.  Kuma Mama ko babu komai ni ™anwar sa ce tare dashi muka tashi a gidan nan, ko dan wannan ala™a Win bai kamata yace min haka ba, auren nan da nayi ™addara ce ta kaini tunda ko shekara ban yi ba na dawo. Wallahi Mama ina son Bebi in na rasa shi zan iya mutuwa."

"˜aryar banza" Kausar ta faWa tana daga gefe Mama ta harare ta ta dawo da kallon ta ga Rumana tace, "Haba uwata, na faWa miki baki da wani miji na gaba a duniya in ba Adnan ba, meyasa kike son zubar da hawayen kina banza a wofi?."

Ta share hawaye tace, "Mama bai yana faWa min magana kamar yau ba, har cewa yake nice na nace amma shi yanzu baya sona, ni kuma ina son sa Mama."
Chapter 19 · 0% Book details