Sashe 8
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D'aga novel d'in yayi yana jefa mata mugun kallo kafin yace "Me kike yi da wannan bayan kina jarabawa.?"
Shiru bata iya amsa sa ba, sai k'walla dake neman ciko idanunta don kuwa tasan halin mahaifin nata idan ransa ya b'aci, duk wasa da dariyar da yake masu akwaisa da tsayarwa musamman akan karatu..... Muryarsa ya kuma dakan dodon kunnen ta.
"Answer me! Me kike da wannan..."
Shema'u ta dubi Sajida dake faman zuban hawaye da sauri ta k'arasa gaban AT tana wani yauk'i da murmushi kafin tace "Oh that's mine, ni na barshi wajen, don tare muke zaune d'azun, ba nata bane don't scold her pls."
Kallo ya bisu dashi ba tareda ya furta komai ba ya ajiye novel d'in ya nufi stirs. Suka bisa da kallo har ya shige kafin Shema'u ta k'araso tayi hugging Sajida.
Sajida na murmushi take fad'in "Aunty yau kin cece ni, wayyo thank you Aunty na, da Daddy yasan nawa ne yau da na yaba wa aya zak'i, thank you Aunty Shemah.... "
Murmushi Shema'u ta sakar mata kafin tace "Anything for you sweetheart, yanzu ki sai ki kiyaye kinji kar ya kuma gani. " Da sauri Sajida ta gyad'a mata kai suna masu sakar ma juna murmushi. Wani sabon dad'i ya kuma mamaye Momma.
****************
Har wajajen 8:am su Sajida basu zo sun d'auketa ba, gashi 9:00am zasu shiga jarabawar. Takwas d'inma har ta gauta da 'yan dak'ik'ai..
"Hajiya kawai zan shiga adaidaita." ta fad'i tana rufe littafin hannun ta.
"Maryama yaushe kika fita, yaushe kika sami adaidaita, ai zakiyi latti, bari dai na kira Attahirun naji dalilin da yasa su Sajidan basu zo ba." Hajiya ta fad'i sanda take ciro wayar ta a bakin zani. Mik'a ma Maryama wayar tayi kana tace maza nemo min shi.
Maryama ta d'an turo baki kafin tace "Kai Hajiya yanzu fah Uncle yana wajen aiki, haka kurum a kira sa, ya bar aikin sa kenan ko me, aidai gwara na shiga adaidaita, k'ila sun mance ne."
"Ke bana son iyayi fah tam, kaiki makarantar ba aiki bane, idan bazaki kira sa ba, bani kiga na kai ma Ilu ya kira min shi."
Girgiza kai kurum Maryama tayi kafin tayi dialing lambar AT ta mik'a ma Hajiya baki a ture.
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘
07
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Fatan Alkhairi a gareku masoya littafin Shak'uwa😍🤝*
Yana tafe bisa kwalta hanyar TH ya nufa, domin akanyi booking nasa a TH ya kalli patients. Yau Surgeries daban daban ma yake dasu a TH d'in.... Wayar Hajiya ce ya shigo masa, Saida ya rage speed kafin ya d'aga wayar da hannu guda, hannu guda naga steering wheel.
Gaisawa sukayi nan Hajiya ta sanar dashi buk'atar ta... Sosai AT yaji mamakin rashin d'aukan Maryama da basuyi ba, koda yake Shema'u ce ta kaisu ba lallai idan yaran sun fad'a mata ba, shima shaf ya mance bai fad'awa Shema'u zasubi gidan Hajiya su d'au Maryam ba.
Dole AT ya d'auki hanyar gidan Hajiya don ko kusa baiso Maryam tayi missing exams d'in ta. Yana ida waya da Hajiya wata wayar ta kuma shigowa. Dr Ashfaq ne wanda suke ganin mutane tare a TH.
"Dr ya muka jika shiru ne, hope all is well?.. Komai ya zama ready, the room and everything, so kai muke jira a shiga da patient d'in." Cewar Dr Ashfaq daga d'aya b'angaren.
Cike da miskilanci ya soma maganar domin kuwa d'abi'ar sa ce, bada raini ko wulak'anci yake yin hakan ba, hasalima duk wanda ya sanshi toh kuwa yasan wannan d'abi'ar nasa "Em lafiya Ashfaq, ka gane just go ahead with the preparations, get the first patient ready I'll be there in a bit,... Okay, yauwa na gode Dr." Ya k'arashe wayar had'i da d'an fuzar da iska.... Yana shiga kwanar Janbulo wata wayar ta kuma shigo masa, daga can asibitin sa ake kiran sa.. Nan aka kuma sanar dashi jikin wani patient ya tashi.. Sosai hankalin AT ya tashi don shi akwai son kula da marassa lafiya. Cikin sauri ya shiga neman layin Hisham don yasan Hisham da lattin fita office.
Hisham na kwance saman gado Shema'u na gefensa suna aikata masha'a wayar AT ya shigo masa... Kaman bazai d'aga ba sai kuma Shema'un ta tirsasa masa d'agawa.
Murya irin ta mai barci ya soma magana. "Hello Doc.." Ya fad'i yana wani matse idanu tamkar mai barci.
Daga d'aya b'angaren gajeren tsaki AT yayi kafin yace "I knew it, nasan baka tashi ba, bayan kasan yau kaine a clinic ni zan tafi TH... Hisham don Allah ka tashi ka tafi, patients na buk'atan ka.
"Relax Doc, idan kabi na mutane tas sai sun k'arar maka da k'arfin ka, sam AT baka huta ma rayuwar ka, kullum cikin aiki... Yanzu kana can TH d'in ne.?" Ya k'arashe yana kallon Shema'u data kafe sa da idanu.
D'an tsaki ya kumayi kafin yace " Naje zan ajiye Maryam a school amma daga can TH d'in zan wuce.... Wai ma Me amfanin karatun daka jima kana yi idan bazaka dedicating lokutan ka ma Al'umma suma su anfana ba... Pls Hisham no time for jokes, ka tashi ka shirya pls.... Sai munyi magana." Daga haka ya kashe wayar daidai sanda yake horn a gate d'in gidan Hajiya.
A gurguje suka gaisa da Hajiya, sauri sauri suka fice shida Maryama Hajiya na masu addu'an Allah Ya tsare.
Sai faman satan kallon sa take da wutsiyar idanu, shikam kullum k'uriciyar sa dad'a fitowa take ta rufe tsufar sa, sam bazakace ya aifi d'iya kaman Sajida ba. Yana sanye da Jampa ruwan k'asa kansa babu hula, sajen nan nasa a kwace luf, ta kai dubanta ga hannayen sa dake rik'e da steering kaman ka tab'a jini ya fito, so fresh, ga agogon Rolex dake d'aure a hannun nasa, kai gaskiya Uncle d'an gayun k'arshe ne, shi k'anshin sa ma daban ne, ko yaushe cikin k'anshi da gayu yake, duk yanda ya zauna toh k'amshin sa yakan rinjaye wajen, tabbas shida Aunty Aysha sun dace da juna, dukansu 'yan gayun k'arshe ne, Allah sarki mutuwa mai raba tsakani, tausayin sa ya kuma ratsa zuciyarta..... Gabanta ne yayi mugun fad'uwa, ta shiga tambayar kanta. Anya lafiyanta kuwa , meyasa take jin tana tsintar kanta wani irin yanayin duk sanda suka keb'e da Uncle, sannan meyasa take yawan tunanin sa har tayi k'ok'arin wuce gona da iri..? Tabbas ita kanta zuciyarta da take faman shek'o mata wad'annan tambayoyi bata da amsar su, abu guda da tasani shine SHAK'UWA CE sosai a tsakanin su ..... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar sa yana fad'in "Wani exam zakuyi yau.?"
A d'an tak'aice ta amsa masa da "Chemistry practical."
Jinjina kai yayi kafin yace "Har yanzu baku gama practicals d'in ba.?"
"Eh ni idan nayi yau ahikenan su Sajida ne masu yin Food and nutrition su kuma sai Thursday." ta kuma yin maganar duk ba'a sake ba, sam bata saba da wannan canzawar da yayi ba, ta sani tuntuni miskili ne dukda SHAK'UWAR dake tsakanin su amma yanzu abin ya kuma yawa, k'ila rashin matar sa ne.
AT ya kuma jinjina kai kafin yace "Meyasa ke bakiyin Food and Nut d'in, ko Hajiya ta koya maki girkin ne?" Yayi tambayar teasingly.
D'an murmushi tayi tana mai kallon 'yan yatsun ta kafin tace "Ai Hajiya bata barina nayi girki."
D'an karkato da fuskar sa yayi ya dubeta kafin yayi murmushi ya maida fuskar sa ga kwalta sannan yace "Ai kinyi k'arama ma yin girki ne shiyasa, saidai irin ta makaranta banda na gida."
D'an ware idanunta tayi kafin tace "Laa Uncle fah masu shekaruna ma suna girki."
Ya juyo ya dubeta yanda tayi maganar cike da yarinta kafin yace "Nawa ne ma shekarun naki.?" Still idanunsa naga kwalta yayi tambayar.
"18 fah zan cika Decembern nan."
Murmusawa kurum AT yayi yarintar ta na burge sa kafin yace "Au ashema kin d'an fi Sajida, toh ke kin kusa fara gwada girkin amma sai kin cika 18 d'in."
Bata kuma cewa komai ba sai murmushin da tayi kanta a k'asa lokaci guda kuma taji wani iri, don harga Allah sosai yanzu take jin nauyin sa.
K'arfe 8:45am daidai suka iso makarantar. Ta bud'e marfin mota tana fad'in "Na gode Uncle."
Kallon ta Ya d'an yi kafin yace "I hope babu dukan latti."
Murmushi tayi kafin ta girgiza masa kai tace "No ba'a tare 'yan SS3."
Gyad'a kai yayi kafin yace "Allah bada sa'a koh." Ta amsa da ameen kafin ta shige. Saida yaga shigewar ta kafin yaja motar ya bar wajen.
***********
"That imbecile is always bossing me around. Nunawa yake kaman yafi kowa iya aiki da son taimaka ma mutane, I'm sick of him already, kaman na shak'esa na huta haka nake ji." Hisham ya fad'i sanda yake had'a boturan rigar sa.
'Yan kunnayen ta take sakawa kafin tace "You watch your mouth Hisham, ina gargad'in ka don't mess with my AT...." ta k'arashe tana yawo da d'an yatsar ta saman fuskar sa.
Murmushi Hisham yayi kafin yasa hannu ya kamo k'ugunta ya had'e da nasa waje guda, dab da fuskarta yake magana cikin sigan rad'a "Kiyi a hankali my Ally dukda nasan baki fed'e min sirrinki gaba d'aya ba amma ki sani Hisham ya wuce tunanin ki."
Murmushi ta d'anyi kafin ta sauk'e masa light kiss a lips d'insa tace "Dangantakar wancan bak'ar yarinyar da AT zaka fad'a min, dukda nasan AT ya ninka ajin wannan yarinyar sau babu adadi I still need to take precautions, don irin wad'annan munafukan yaran sunfi manya iya makirci."
Hisham ya murmusa kafin yace "Next time zan fad'a maki, kinga yanzu fita zanyi.