← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 63

Sashe 59

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hisham ya fashe da wata kafiran dariya kafin ya katse kiran, shi kad'ai yake fad'in "Shema'u the Devil, tabbas kin shiga tarko na, da zaran kin dank'a mani kud'ad'en nan nikuma zan cin amanarki kafin kici nawa..." ya k'arashe yana mai kuma fashewa da wata dariya, lokaci guda ya tokari galan d'in petur guda ya fad'i k'asa ya shiga zuba tamkar mai....

Kallon ta Alh Aminu yayi kafin yace "Giwan mata kenan, ai ni yanzu bani huld'a da manyan mata irinki sai dai na kaiki ma uban gidana..."

Shema'u ta fashe da dariya kafin tace "hakan ma yafi mun..."

Kai tsaye wargajejen guest house d'in VP suka nufa..

********

Ko parking bai gama ba ya shiga gidan yana doka kira ma Shema'u da Sajida, don yasan Shema'u ce ta fad'a ma Sajida abinda ke faruwa...

Daga Iya Kande har Momma saida suka fito a bikice, tambayar su yayi ina Shema'u da Sajida..

Murya na rawa Momma tace "Sajida dai tun safe ban ganta ba inaga bata sauk'o k'asa ba tana d'akinta Shema'u kuma tace min ta tafi asibiti....."

Bai gama saurarenta ba ya nufi upstairs kaman zai kifa da k'asa....

Tana kwance saman gado tana matsan hawaye taji an tokari k'ofar d'akinta, ta mik'e zunbur tana raba idanu... Bata tab'a ganin mahaifin nata cikin irin wannan yanayi ba.

Kifa mata mari ya ringa yi yafi sau abinda yafi ya shiga k'wallo da ita, .... Ihun Sajida dasu Momma suka jiyo yasa suka nufi sama a tamanin....

******

Gaban Haidar ya yanke ya fad'i ganin harda Shema'u a masu zuwa meeting wajen mahaifin sa, dukda tsaro da suke bama wajen saida yayi yasan yanda ya kutsa ya mak'ale jikin k'ofa don dama tuntuni shi bai yarda da matar ba..

VP yayi murmushi yana dubanta kafin yace "Ni a k'a'idana bana huld'a da macen data haura shekaru sha takwas bayan matata, amma tunda kin matsa kina son kud'in, kije ki nemo min Yarinya 'yar shekara biyar da kuma yaro d'an shekara goma, umarni aka bani idan nazo garin nan nayi amfani dasu burina na mallakan kujeran Shugaban k'asa zai cika, don haka idan zaki iya aikin fine zaki sami kud'ad'enki cash..."

Murmushi Shema'u tayi don ba komai ta tuna ba illa Jamal da Ni'ima, saida ta juya idanu kafin tace "An gama Your excellency..." Daga haka aka sa guards suka fice da ita...

Haidar na nan mak'ale zufa na keto masa tako ina don baisan arnancin ubansa ya kai har haka ba.... Cikin sauri ya silale jikinsa ya fice daga wajen....

*Saminah Aliyu Mrs💖*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*48*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

A tsorace Momma ta shiga tsakanin AT da Sajida wacce har shid'ewa take sabida kuka, jikinsa ya kuma yin jazir kan wanda Hajiya ta mata.... Momma na kuka Sajida na kuka... Huci kawai AT yake yana dubanta kafin ya d'ago wayar hannunsa yana nunata dashi yace "Kinji na rantse aure zan maki da duk wanda naga dama sannan ita mai koya maki rashin kunyar zata dawo gidan ta same ni... Useless kawai...." daga haka jifa yayi da bulalar yana mai ci gaba da huci ya fice daga d'akin....

Sajida ta rungume Momma tana kuka lafin tace "Momma Daddy is a big disappointment, wllhi na tsane shi, na tsane...... Saurin toshe mata baki Momma tayi ta jawota suka zauna saman gado tana goge mata hawayen da suke kan fama zubowa daga idanunta, jikin Momma gaba d'aya ya kuma yin sanyi.... Suna nan zaune suka hange AT ya fito ya nufi downstairs cikin tsananin tashin hankali waya manne a kunnen sa yake fad'in "You mean the Hospital's on fire...? Ina Hisham,... Okay pls KB kar ku bari wani abu ya sami patients..... I'll be on my, na gode...." yana katse kiran fire service ya shiga nema....

Momma hankali tashe ta mik'e tana duban Tahir da tuni ya fice cikin tsananin tashin hankali hannayenta dafe a k'irji...

Mahaifinta na fita ta jawo wayarta tayi dialing lambar Buzu.... Cikin tsananin kuka take sanar dashi yazo ya d'auketa bazata iya ci gaba da zaman gidansu ba aure Daddyn ta zai mata sabida abinda tayima Maryama...

Buzu da bai k'arasa gida ba parking motar sa yayi a daidai garun Hajiya ya fito yana amsa wayar tamkar wanda basira ta b'ace masa...... Hajiya na jikin pampon bayi ma flowers ta jiyo muryar Buzu yana amsa wayar yana ambato sunan Sajida yana lallashinta yana fad'in zaizo ya d'auketa yanzu su tafi yanda babu mai sake ganin su.....

Ai Hajiya zani a hannu tayi patali da butan da take shirin alolar azahar, mayafinta dake mak'ale saman igiya ta fincika ta rufa ko sallama batayima Maryama ta fice, Ilu sai magana yake mata inaa bata ko kulasa ba.

Tana fita ta hangi motar Buzu na shirin fita daga layin... Hannu bibbiyu Hajiya ta d'aga tana kiran mai adaidaita.....

**********

Burinsa ya cimma Shema'u baya fatan ta sato yara a lalata masu rayuwa innocent souls.... Hankalinsa yayi mugun tashi ganin bai cimmata ba dashike a motar take, Haidar ya rasa wanne zaiyi, cikin sauri ya zak'ulo wayarsa ya shiga neman layin Maryama, ga mamakin sa yau sai ya jita a kunne...

Ya kira yafi sau biyar ba'a d'aga ba, k'arshe text ya tura mata yana neman taimako, matar AT tana shirin salwantar da rayuwar k'anan yara kuma baisan wasu yara zata kawo ba, ko yaran gari ko kuwa yaran AT....

Dukda Maryama bata fahimci sak'on nasa ba saida gabanta yayi mummunar yankewa, hannunta har na rawa ta soma dialing layin Ashfaq....

***********

AT yana isowa asibiti yaga hayak'i ya turnuk'e ko ina gaba d'aya, mutane wad'anda 'yanuwansu ke cikin asibitin sai kuka suke suna hango AT wasu suka soma bore suna fad'in sam bazasu yarda ba wannan wutar kunnawa akayi ba tashi tayi haka kurum ba,...

AT cikin tsananin tashin hankali ya nufi cikin asibitin su KB da sauran Nurses d'in sai turo gadajen marassa Lafiya suke, mutane sun jirkita bana wasa ba, ga wuta dake ci fal-fal...

Dai-dai lokacin fire service suka iso aka soma mik'a taimakon gaggawa...

Hisham bai zaci abin zai zama haka ba domin gaba d'aya hayak'i ya turnuk'e store d'in sannan wani k'arfe ya kama masa gefen riga yayi yayi ya keta ya kasa, tun yanada sauran k'arfi har yaji babu k'arfi a jikinsa...

AT shiga cikin fire service d'in yayi suka dinga k'ok'arin kashe wutan, gaba d'aya idan ka gansa kasan a birkice yake k'arshe dole ya kuma komawa wajen wad'anda had'arin ya shafa yana basu kulawa shida Nurses d'insa....

**********

Dukda ciwon da take ji hakan bai hanata fitowa ta sami Ashfaq a waje ba, dubanta yayi kafin yace "Maryam bamu da time ina muka nufa, ina kike tunanin zamu samu Shema'u....?"

Maryama ta ringa recalling abubuwan da sukayita faruwa a rayuwan gidan Uncle kafin ta soma girgiza kai tace "Ya Ashfaq wllhi ta yuwu su Ni'ima zata kai, su zata sayar muguwa ce ta k'arshe,...." ta k'arashe hawaye na nema zubowa daga idanunta...

Haidar ya girgiza kai kafin yace "Idan nayi ido hud'u da ya Dr nasan kasheni ne kawai bazaiyi ba, bazan iya zuwa gidan sa ba, sannan ko na fad'a masa ba lallai ya yarda dani ba, kar mu tsaya b'ata lokaci ni yanzu zan tafi nazo da 'yan sanda ke kuma ki tafi can gidan nasa pls ki bi bayansu..."

Gyad'a kai Maryama tayi kafin tace "K'warai Aunty Shema'u makira ce ta k'arshe Uncle bazai yarda da kai ba, amma nasan makarantar su Jamal zata nufa tunda yanzu k'arfe d'aya ta wuce lokacin tashin su yayi.... Ni zan wuce makarantar nasu kai kuma ka tafi ofishin 'yan sandan kazo dasu...."

Shafe kansa yayi kafin yace inada layin orderly d'in Mr President zan kira sa yanzu , domin basu san abinda ke wakana ba zan sanar da Mr President komai domin Daddy na shed'anan sa yafi k'arfin 'yansandan garin nan, sai an turo cover-up daga Abuja..... Amma still suma zasu tsare mana Shema'u....

Gyad'a masa kai tayi cikin sauri, Haidar yayi saurin tsare mai adaidaita baima san yawan kud'in da ya damk'a ba Maryama ta shige ciki a tsorace... Yayi masu addu'an kariya kafin shima yasa hannu ma d'an acab'a ya d'ale....

*************

Napep d'in su Hajiya tana shigowa layinsu AT ta hangi Sajida sun shige motar Buzu har wani rirrik'eta yake...... Ai a tamanin taceda mai adaidaita "Yaro mubi bayansu, mubi bayansu nace, jikata ce tsinanne zai lahanta min ita..."

Cikin sauri mai adaidaita yace "Toh Baaba an gama, gaskiyarki ne kam gwara ki tsare mutuncin jikar ki, irin wad'an nan gurb'atattun samarukan lalata 'yanmata kawai suke....

Ko zarafin amsa sa Hajiya bata samu ba idanunta k'yam kan motar Buzu yanda yake kwasan gudu da jikarta Sajida cikin motar.....

**********

Da taimakom Allah suka samu wutan ya mutu, AT gaba d'aya fatarsa tayi ja, bak'in hayak'i duk ya rina masa fata... Dole aka kawo masu d'auki daga Teaching Hospital....

Kai tsaye CCTV FOOTAGE na cikin asibitin ya bud'e ya soma dubawa domin shima kansa bai yarda wutan ba kunnata akayi ba, don tafi kama da kunnata akayi... Duk abinda ya faru a asibitin tun daga safiya ya soma gani....

Har isowan Hisham saida ya gani, wani ikon Allah basiran Hisham gaba d'aya ya shafe bai yi hacking cameras d'in ba kodashike sam bai zaci asibitin bazata k'one gaba d'aya ba...

Jiri ya fara neman kada AT ganin Hisham na fito da gallons d'in petur ya nufi cikin Store dasu yana gani ya saka su a last store kafin ya fito parlorn yana fashewa da wata irin dariya.... Tashin wutan saida yayi jifa da Hisham gefe, wutan bata biyo ta parlorn yanda Hisham yake ba sai ta shige cikin asibitin cikin ward d'in majinyata... Hisham kwance a wajen sai k'ok'arin janye rigarsa data rik'e k'arfe yake ya kasa ga hayak'i ya soma gauraye wajen.....

Kasa ci gaba da kallo AT yayi sai hawaye dake kwaranyo masa, yak'i aminta ma zuciyarsa cewa Hisham ya gani, Hisham dai his very own best friend wanda ya zame masa tamkar d'an uwa.....

Cikin wani irin huci yayi jifa da computer d'in, hawaye na bin k'uncinsa ya fito ya nufi store d'in magunguna, su KB na ganinsa ya nufi wajen sukayi saurin take masa baya, sabida sun razana da ganin yanyin nasa...
Chapter 59 · 0% Book details