← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 63

Sashe 50

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'ago rinannun idanunsa yayi yana duban Hisham kafin yace "You were right, kayi gaskiya Hisham, I shouldn't have trusted him, he made a fool out of me...." kasa ci gaba da maganar yayi yana tunanin yanda wannan abu zaiyi hurting Maryam, ace anzo aurenta ga abinda ta faru.... Lallai wannan aya Allah Ya gwada masa, Maryam amana ce a hannunsa tun daga ranar da ya tsince ta, batada kowa sai shi, tunda abu makamancin haka ya soma faruwa tabbas zaiyi wuya ya sami mai rik'e masa ita bisa gaskiya da amana, Ashfaq yaci amanar su, ya yaudare su...... Tabbas bazai tab'a yafe masa ba.... Yana cikin tunanin ya jiyo muryar liman yana fad'in "Dr Ahmad kar ka damu, lallai komai muk'addari ne daga Allah, ka sani Allah yana tareda masu hak'uri, ka gode ma Allah da yasa komai ya bayyana kafin ayi auren.... Lallai Allah yana sonka da alkhairi, kayi addu'an Allah yasa haka shine mafi alkhairi ita kuma yarinyar Allah Ya bata wanda yafi zama alkhairi a gareta, muyi addu'a sai mu watse... Domin manzon mu tsira da aminci su k'ara tabbata a gareshi ya koyar damu yin addu'a bayan ko wace zama da mukayi daga abinda ya kai mutum biyu...."

AT gaba d'aya baya gane me ake fad'i, Maryama ce cikin zuciyarsa, tunani yake yanda zataji, tunanin halin da zata kasance ciki yake idan wannan labari ya risketa, fad'i yake cikin zuciyar sa _I won't call off your wedding Maryam_, zakiyi aure insha Allah... Bai ankara ba sai gani yayi yana shafe addu'a ana mik'ewa...

Cikin sauri ya mik'e tamkar wanda aka tsinkaya kafin ya dubi Liman yace "Allah gafarta malam a tsaya akwai d'aurin auren, ina zuwa.."

Bai jira cewan Liman ba ya kutsa cikin mutane ya nufi motar sa.

Hisham dai kallon mamaki yake bin AT dashi, kafin AT ya dawo farfajiyan d'aurin auren yayi amfani da damar yayi dialing lambar Ally d'insa...

Hajiya na gefen su Sajida ta mik'a hannu tana fad'in "Maza zana mani k'unshina kiga, farar mace alkyabban mata, faran Mace lantarkin gida, na tabbata nawa k'unshin sai yafi na amaryar ma kyau..." gaba d'aya k'awayen amaryar sai shan dariyar Hajiya suke, gashi har hoda pankeke Sajida ta shafa mata, harda foundation, Maryama tana hanawa Sajida tana k'i... Hajiya ko cewa take "Shafa mani bud'a jakar naku, amma kar ki maidani roba-roba, don wannan ba irin ta zamanin mu bane..Abinka da farar fata kuwa sai tayi kyau sosai ...

Hajiya ta murmusa ta lakuci fuskarta taga jan hoda ya bayyana, foundation ya lakaci yatsanta, sai ka rantse abin arziki zata fad'i "K'ura ma yatsun nata idanu tayi yanda ta lakaci hodan kana tace "Oh ni Fad'ime Allah ka kiyasheni zama roba-roba.... Ke 'yar nan gane mani banyi zubin zabon can ba koh..." ta k'arashe tana nuni da Shema'u dake zaune can gefe tana shafa wayarta...

Gaba d'aya son k'unshe dariyar su suke sun kasa don sunsan sarai Shema'u ta jiyo Hajiya, don tunda tazo gidan Hajiya ke yab'a mata magana ko ajikinta, sai Maryama ta d'an b'ata raine ma Hajiya ke yin shiru....

Kaman daga sama suka jiyo muryar Shema'u na salati ta mik'e tsaye had'e da rik'e k'irji tana fad'in "Mun shiga uku mun mutu mun lalace....."

Hajiya kallabinta a kaikaice ta mik'e tana fad'in "Allah Ya tsari bakinki kedai kika lalace bamu ba, banma san uwar kinibibin da yasa kika d'ebo wannan sawayen naki uwa ta d'an marini sabida tsaban shafe-shafe kika zo mana bikin mu ba, muguwa mai halin tsiya wato kizo ki mana mugun kaba'iri toh Allah Ya tsari bakin ki.... Aniyarki ya biki mai mummunar fata, bamu shiga uku ba saidai muga alheri ehe...."

Mutanen Hajiya sai tausanta suke yayinda Sajida tasha kunu ta k'arasa wajen Aunt d'inta tana tambayarta meke faruwa...

Cikeda makirci Shema'u ta soma fad'in "Sajida waya aka min yanzun nan daga wajen d'aurin aure ana sanar dani taron aure ya watse an fasa auren Maryama da Ashfaq, shine na birkice gaba d'aya banma san me nake fad'i ba amma Hajiya bata saurareni ba...." Bata kai aya ba Hajiya dake kaikaita kallabinta ta d'ago tana watsa mata mugun kallo kafin tace "Me kika ce...!!! Ke ahir d'inki nayi imani da Allah kinyi kad'an kizo ki mana barikanci a nan... Aure babu fashi, saidai naki auren da Attahiru ne ya k'are....."

Maryama da juwa ya soma d'ibanta, sama-sama take jin batun su Hajiya domin kuwa tuni labari ya soma yad'uwa ta wayar salula.... Ba Shema'u kawai aka kira ba har da wasu daga cikin 'yan biki...

Kan kace me Maryama ta d'ibi jiki ta fad'i, nan hankula yayi kanta.. Sajida da k'annenta sai kuka suke... Hankalin Hajiya idan yayi dubu ya tashi, haka aka shigar da Maryama d'aki ana mata fifita still bata farfad'o ba... Hajiya sai matse hawaye take tana jero sallalami, gaba d'aya tama rasa wanne zatayi, kai da zataga Keenafas yau da ta cukumesa sun dambatu da kyau.....

Friends d'inta sun kewayeta sai mata fifita suke, kowa ya cika da al'ajabin wannan lamari.

Hajiya ma zubewa kurum tayi cikin kujera kallabi a hannu anai mata fifita, rabonta da ganin irin wannan tashin hankali tun mutuwar mijinta Alh Shattima, gani take tamkar zata rasa Maryaman ta.

Shema'u na gefe banda addu'an Allah sa zuciyar Hajiya ya buga bata komai, zuciyarta ya cika da farin cikin ganin Hajiya cikin tashin hankali, yanda take mashassharan nan da zata sami hali data k'arasata daga ita har Maryamar ta huta....
Tana cikin wannan tunani wayan Hisham ya kuma shigo mata. Mik'ewa tayi ta fice can waje kafin ta amsa wayar. ....

Hankali tashe Hisham ya soma fad'in "An d'aura auren....."

Saida ta waiga gefe taga babu mai zuwa kafin ta sauk'e ajiyan zuciya tace "Haba hakan ai yafi gwara a d'aura, amma ko banza naji dad'in mishkilan da aka samu daga farko tunda dukansu biyu zukatansu k'iris ya rage basu buga ba......"

Gajeren tsaki Hisham yayi kana yace "Ki saurareni kiji waye mijin..."

Hayaniyar Ilu data jiyo daga can veranda yasata katse kiran Hisham ta nufi wajen cikin sauri don ta jiyo muryar Hajiya.

Ilu mak'ale da hularsa a hammata irin tashi ka faye naci d'in nan yaci gaba da fad'in "Aradu Hajiya ban tab'a ganin maraimakin shugaban k'asa ido da ido ba sai yau, har jikin motar sa saida na shafa...." Hajiya dake zaune saman faran kujera ji take kaman ta tashi ta rufe Ilu da duka.... Gaba d'aya mutanen wajen sai mamaki suke jin Ashfaq wai d'an vice president ne ciki harda Shema'u wanda tabbas bata fatan Maryama ta aurin d'an mataimakin shugaban k'asa... Take kuma ta soma tambayar kanta toh ai Hisham yace an d'aura auren kuma yanzu Ilu yace VP ya tattari d'ansa ya tafi dashi.... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryan Ilu yana ci gaba da fad'in "Ai Hajiya da rabon aure dai ta gidan nan zai dawo, wllhi Dapta yayi tunani bai bari jama'a sun taru a banza ba tuni aure ya juya kansa..... Hajjaju namu ai anyi tuwona maina da Dapta......."

Kan bala'i!!!!! Bata fahimci me ake fad'a ba kaman zautacciya haka ta tako har gaban Ilu tana girgiza kai kaman wata mahaukaciya ga fuskarta uwa mage ta fad'a a talge take fad'in "Me kake cewa, mijina, Tahir d'ina ne yayi aure.....?"

Ilu ya wage baki uwa gonar auduga kana yace "Au dama kece matar da Dapta ya aura kwanaki..... Yo murna zakiyi anyo maki k'anwa ta gida, ko Hajajjun mu...." ya k'arashe yana kai dubansa ga Hajiya da tuni ta mik'e tsaye...

Kallon Ilu da kyau Hajiya ta kuma yi kafin tace "Kai Ilu banason sakarci, kana nufin Attahiru ne mijin Maryama, Maryama tawa...?"

Ilu ya kuma wage baki kafin yace "Insha Allahu Hajajjun mu.... Abu yayi kyau ai..."

Kasa furta komai Hajiya tayi lallai Attahiru hankali bai ishesa ba, yo ita ina zata bari ya kwashi Maryama ya had'a da wannan matar tasa mai suffar kafirai, wannan da ganin idanunta tsaf zata salwantar da rai, yo shi kansa fata da addu'a take ya rabu da wannan kod'edd'iyar kafin ta watsa masa cututtukan zamani shine yanzu kuma zai had'a harda Maryama yakai a karsu gaba d'aya ta yab'a masu cuta ta kashesu gaba d'aya.... Inaaa ba da ita ba.... Huci kawai take tana jiransa ya iso ya warware wannan aure da ba d'orewa zaiyi ba..... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo kukan Shema'u tana fad'in "Kai Ilu kake ko wa, wllhi wannan kuma k'arya kenan... Wllhi ni nasan Mijina bazai tab'a yin abinda kace ba......" Fitowar Sajida daga d'aki yasa Shema'u ta kuma kurma wani ihun tana jijjiga uwa tab'ebb'iya.

A tamanin Sajida tayi kanta tana tambayarta lafiya...?

Shema'u cikin kuka ta rungume Sajida tana fad'in "Sajee wai Daddyn ku shine ya auri Maryama, wayyo Allah na Sajee mutuwa zanyi....

Sajida ta d'ago idanu tana dubanta cikin rashin yarda da abinda take ji, kallon illahirin mutanen wajen take ta shiga girgiza kai tana jada baya take fad'in "No.... That's not true, wllhi wannan ba gaskiya bane, Daddy na bazaiyi abu makamancin haka ba......."

Shema'u ta rik'ota tana hawaye take fad'in "Sajee gaskiyar kenan, aure my AT yayi kuma wai Maryama for that matter.."

Tamkar wacce aka zabura haka Sajida ta fice a guje Shema'u tabi bayanta, Hajiya ta rungumo Jamal da Ni'ima ta wuce dasu d'aki.... Lokaci guda gidan biki ya tarwatse kowa na fad'in albarkacin bakinsa, wasu gani suke Tahir yayi dai-dai yayinda wasu ko suke ganin sam bai kyauta ba duba da yanayi Maryama tare suka taso da d'iyarsa Sajida. K'awayen amarya aka barsu da Al'ajabi harta Fadila k'awar fad'an Sajida saida taji tausayin Sajida yau, sam hakan bai kamata ba a cewar su dukda hakan bai sab'a ma Shari'a ba....

Duk wannan wainar da ake toyawa Maryama bata san yanda hankalinta yake ba, tana nan a kwance...

Shema'u tana ganin Sajida ta nufi kwalta ta soma addu'an Allah sa trailer tabi kanta....

Aiko mai machine ne ya kwashe Sajida nan ta zube a k'asa sumammiya Shema'u tayi kanta, mutane sukayi chaaa.... Kai tsaye aka kwashi Sajida aka wuce da ita asibiti mafi kusa Shema'u sai huci da turiri take tana tunanin kalan tuggun da zata k'ulla....
Chapter 50 · 0% Book details