← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 63

Sashe 55

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AT ya kuma jawota ya d'aura saman laps d'insa kafin yace "Kar ki damu saura kad'an, nama gano maganin da zan baki, yanzu fad'a min yaushe zaki fara sallah domin sai kin fara sallah kisha maganin I mean sai an gama period ake shan maganin daga nan bazai kuma maki ciwo ba..."

Jim ta d'anyi kaman mai tunani don tsoro take ji sosai kar ace za'a yanke mata breasts d'inta, cikin sanyin murya tace "Saura kwana 4..."

AT ya murmusa kafin yace "Allah Ya kaimu, da zaran na baki maganin kin daina ciwon kinji koh..."

"Da gaske Uncle..? " ta fad'i tana duban sa, gyad'a mata kai yayi kafin yace "Amma zaki bari mu k'arasa mammography d'in sabida na tabbatar da maganin..."

Jiki a sanyaye ta runtse idanunta tana jin sanda ya kwanto da ita saman k'irjinsa....

Murmushi AT yayi yarintar ta yana kashe sa, banda yarinta yaushe zata wani biyesa wai mammography yake mata, iyakaci yasan aurene zai sawwak'a mata ciwon da take fama dashi lokacin al'ada.....

Lumshe idanunsa yayi yaci gaba da koya mata salon soyayyar sa.

*********

A tamanin su Sajida suka shigo d'akin suka tarar Shema'u tayi kaca-kaca da komai, Jamal da Ni'ima tsoro ya cika su, domin Jamal kanma bacci yake ya jiyo k'aran fashe-fashe ya fito a razane, waje guda suka tak'ure shida Ni'ima yayinda Sajida ta nufi wajen Shema'u dake durk'ushe tana kuka, ta dafata a d'an tsorace kafin tace "Aunty lafiya, meke faruwa, meke damunki...."

Shema'u tayi saurin rungume Sajida tana mai ci gaba da kuka take fad'in "Sweetheart I'm scared, I'm so scared banaso ta rabamu, zata rabani da Daddynk ku, kinga time gashi har yanzu bai dawo ba, nasan wajenta ya tafi, Sajee ki kiramin Daddyn ku pls kinji sweetheart...."

Yanda take maganan kaman wata tab'ebb'iya, cikin sauri Sajida ta rik'eta sosai tana girgiza mata kai take fad'in "Aunty haka bazai tab'a kasancewa ba, bazamu tab'a rabuwa ba, nayi yanda kikace and Maryama nasan zatayi abinda na umarceta pls ki kwantar da hankalin ki..."

Shema'u taci gaba da k'walalo idanu tana girgiza kai take fad'in "Sajee pls just call him, I'm scared I'm so scared..."

Sajida da tuni hawaye sun soma ciko idanunta ta shiga girgiza kai tana fad'in "Aunty you're scaring us too, pls ki daina kuka.... Ai kafin Sajida ta rufe baki Ni'ima ta soma kuka tana fad'in "Aunty pls kar ki mutu kema kar ki zamo monster kaman yanda Mummy da Maama Juu suka zama, pls Aunty kar ki mutu kinji...."

Kallon mamaki Sajida tabi Ni'ima dashi tana nanata abinda ta fad'i a zuciyarta...

Ganin Sajida tayima Ni'ima k'uri yasa Shema'u saurin k'arasawa ta rungume Ni'ima tana mai ci gaba da kuka da iya k'arfinta..

Saurin jawo wayar Shema'u Sajida tayi kafin ta shiga dialing layin AT...

Daga shi har Maryama saida suka razana da kiran...

Ta cikin wayar yake jiyo sautin kukan Shema'u da Ni'ima ga Sajida tana masa magana a birkice...

Cikin sauri yace da ita gashi nan zuwa...

Ya dubi Maryama da tayi tsaye tuk'wik'une da hijabinta tana dubansa, itama d'in hawaye ta soma murya na rawa take tambayar sa lafiya.. Don gaba d'aya mutuwar Ummin ta ne ya dawo mata sabo..

Kafad'unta ya dafa ya zaunar da ita saman sofa kafin ya shiga calming nata, yana sanar da ita babu komai insha Allah zaije yanzu ya duba su..... saida ya tabbata ta sami nutsuwa ya rakata har k'ofan d'akin Hajiya kafin ya mata sallama harda manna mata kiss a kumatun ta na hagu bayan ya saci idanunta...

Tausayin su daga ita har Uncle ya dabaibaye mata zuciya, wani sabon k'aunarsa takeji na ratsa zuciyarta idan ta tuna yanayin da suka kasance ciki, lokaci guda kuma kunyar sa sai ya dabaibayeta... Lumshe idanu tayi kafin a hankali ta furta "Allah Ya tsareka da iyalanka Uncle..."

**********

Sajida tana ganin mahaifin nata ya shigo ta janye 'yan k'anneta suka rab'a ta gefensa kafin tace "Daddy is Aunty Shemah, she's not well..." kaman mai rad'a haka tayi maganar...

AT ya jinjina mata kai yana duban Shema'u da tayi durk'ushe a wajen tana kuka, ga d'akin ta wargaje shi gaba d'aya....

*Saminah Aliyu Mrs💖*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*45*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

_Maryam T Baliya_
_Zee Virus_
_Anty Hajir Minjibir_
_Hafsat winner_
_Surayya_
_Maman Safiyya_

_Wannan shafi tukwici ne a gareku, na gode da nuna k'auna da kulawa ❤🤝_

A hankali ya tako yana bin d'akin da kallo kafin ya kamota ya d'agota, suna had'a idanu ta kuma fashewa da wani kukan had'i da shigewa cikin jikin sa, jiki a sanyaye AT ya rungumeta cikin jikinsa..

Cikin muryar kuka Shema'u take fad'in "Tahir kar ka rabu dani pls, ko me zai faru kamin alk'awarin bazaka rabu dani ba.... Tahir ina sonka ina son yaranka don Allah kar ka rabu damu kaji pls my AT....." ta kasa ci gaba da maganar sabida kuka da yaci k'arfinta...

AT ya masu masauk'i saman armchair dake gefe kafin ya d'ago fuskar ta yana dubanta kana yace "Shema'u meyasaki fad'in all those things, bazan tab'a rabuwa daku ba daga ke har yarana, we are family akwai strong bond a tsakanin mu bazai yuwu na rabu daku ba...."

Shema'u ta kuma dafe face d'insa tanai masa wani irin kallo lokaci guda tana tunowa da Hisham kafin ta soma girgiza kai tana fad'in "My AT mafarki nayi wai Maryama zata rabamu gaba d'aya, pls kar ka bari ta rabamu kaji pls pls...."

D'an murmushi AT yayi kafin ya kwantar da kanta cikin k'irjinsa murya a taushashe ya soma fad'in "Maryama ba haka take ba Shema'u, mafarki ne kawai ba gaskiya ba kinji koh, ki kwantar da hankalinki, ni Tahir bazan tab'a rabuwa daku ba....."

Shema'u dai ta jisa ne kawai amma kalaman Hisham ba k'aramin d'aga mata hankali sukayi ba, idan ya k'ona asibitin AT ya d'aura masa blame ta rasa AT har abada, idan ta bata kai masa takardun ba zai iya fallasa ta wajen AT.... Take wani tunani ya fad'o mata... Ai Hisham bashida wani prove da zai tabbatar ita ta kashe Aysha don haka babu mai yarda dashi sabida abune da sam hankali bazai kama ba, saidai ma AT ya masa wani zargin daban.... Da wannan tunani ta samu hankalinta ya d'an kwanta dukda sam bata sami nutsuwa ba..

Shema'u na kwance cikin jikin AT ya kasa bacci shi kad'ai sai murmusawa yake yana tuno moment d'in da suka kasance shida Maryama, abubuwa da dama suka cika masa zuciya, shi kad'ai sai nishad'i yake ji.... A b'angaren Shema'u kuwa zuciyarta turnuk'e take da bak'in ciki, ita kad'ai sai k'ulle-k'ullen da neman hanyar b'ullowa ma rayuwarta take.... Ita ko Maryama yanda ya kasance da AT hakan ne ta kasance a gareta, data lumshe idanu kyakkyawar fuskar mijinta take gani, ita kad'ai sai faman murmushi take tana tuno lokutan da suka kasance ciki, lokaci guda sai ta saka tafukan hannunta ta rufe idanunta... Kuma wani ikon Allah ta nemi ciwon da take ji ta rasa.... Kewar mijinta ya cika mata zuciya, _Shin SHAK'UWA CE ko kuwa SOYAYYA CE tsakanin su da Uncle_ tambayan da ya haifar mata da fad'uwan gaba domin kuwa gani take tausayi da SHAK'UWA su suka saka Uncle aurenta ba soyayya bace... Jikinta yayi sanyi ta janyo pillow a hankali ta shige ciki cikeda tausyin kanta......

*************

Abu kaman wasa Shema'u tana bacci tana ihu, hankalin AT gaba d'aya ya tashi, zaune yayi dirshan saman gado yana mata addu'a

Fad'i take "Wayyo kar ku kashe ni, don Allah kar ku kasheni..... Wayooooo....." ihun da tayi na k'arshe ta mik'e ta had'a gumi gaba d'aya jikinta sai kyarma yake dukda sanyin AC da ya gauraye d'akin.

AT ya rik'eta sosai yana fad'i mata tayi addu'a....

Kallonsa tayi lokaci guda kuma ta shiga bin bangon d'akin da kallo kana ta rungume shi tana fad'in "I'm scared Tahir..... I'm so scared..."

AT ya rungume ta k'irjinsa na bugawa da sauri da sauri, gaba d'aya ya kasa gane meke faruwa... A wannan dare kusan kwana zaune sukayi da Shema'u, data kwanta zata mik'e tana ihu... Hankalin AT gaba d'aya ya tashi abu kaman wasa yana neman zama babban abu..

Washe gari ya kira Hisham yana sanar dashi..

Hisham yayi wata kafiran murmushi kana yace a ransa _Baki haukace ba ma sai kinga abinda nake shirin maki Shema'u_

A fili kuwa cewa yayi, "Okay ba damuwa zanzo na dubata insha Allah.."

AT yayi masa godiya kafin sukyi sallama,.

Shema'u tana ganin yanda ko k'ofa bai fita ba yana nan tareda ita, tayi wata kafiran murmushi kafin tace a ranta _Ai kuwa na sami abun fakewa, da wannan zan hanaka zuwa ganin Maryama..._

Lokaci zuwa lokaci AT ke duba agogon hannunsa, yana kallon Shema'u datayi lamo cikin jikinsa, Sajida ta kawo abinci , AT ya soma bata a baki, har lokacin bata daina matsan hawaye ba .... Da ya yunk'ura zai tashi zata kuma cukwikuyesa tana fad'in "Zasu kasheta...."

Haka dole ya hak'ura da fita, ga zuciyarsa cike take da son ganin abin k'aunar sa....

Hisham na isowa AT ya rik'o Shema'u suka sauk'o parlorn k'asa... Hisham ya tsareta da idanu yanda tayi wani lamo cikin jikin AT, abin yaso basa dariya ya gimste dariyar sa yana jinjina tamtiranci da shed'anci irin Shema'u, wato ta nan ta b'ullo...

AT nama Hisham bayani, yayinda Hisham da Shema'u tuni sunyi nisa da zance ta idanunsu..

Hisham na mata alama da _Bakima fara hauka ba idan hauka kika zab'a muddin baki cika min alk'awarina ba..._

Shema'u ta kuma shigewa jikin AT tana zazzare idanu take fad'in "My AT waye wannan..."

Hisham yace a ransa _your Ally don uwarki._

AT ya dubi Hisham yace "kaga irin abinda take tun jiya..."

"Toh banda abinka AT cewa kayi mafarki tayi shiyasa take hakan, ai ni a gani na Malamai masu ruk'uya zaka d'auko mata ba likita ba, tunda ba wani had'ari tayi ba ko wani tashin hankali na musamman ne ya haifar mata da hakan.."

Jakar uba! Gaban Shema'u ya yanke ya fad'i, lallai Hisham ya cika d'an bariki wato so yake a kira malami idan ma Malam duba ne su gano cewa ita ta kashe Aysha ko zuba mata wani abin tayita fad'e-fad'en duk muggan abubuwan da tayi...
Chapter 55 · 0% Book details