Sashe 57
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba d'aya hankalinta ya tashi wa'adin da Hisham ya d'ibar mata sun cika...
**********
Mummy ta kuma duban Haidar da ya shirya tsaf cikin sky blue shadda kansa babu hula kafin tace "Son abin ya bani mamaki ganin kai da Daddyn ka kun shirya lokaci guda har zakuyi tafiya tare..."
Haidar ya k'arashe brushing sumar sa kumatunsa d'auke da murmushi domin yau zai tafi Kano zai gano Maryamar sa, juyowa yayi yana duban Mummy kana ya dafa kafad'unta yace "Mummy naji shawarwarinki insha Allah I'll fix everything kinji I promise you...." ya k'arashe yana d'an fito da idanunsa waje..
Murmushi tayi ta mik'a hannu ta shafi kumatun sa lokaci guda ta tuno mahaifyar sa da d'iyarta Nabila wanda suka mace shekarun baya kafin tace "Allah maka albarka Haidar, Allah maka albarka....."
Hannu yasa yana d'an goge mata hawayen dake neman fitowa kafin yace "Ameen Mummy na...." rage tsayin sa yayi ya d'an bata light hug kafin yace "You take care okay, ki sha maganin ki pls kinji Mummy nah..."
Gyad'a masa kai tayi kafin tace "Insha Allah zan sha Son, I promise you Dr..."
Murmushi ya kuma yi sanda suka jiyo tawagar mahaifinsa sun fito.... Mummy ta bisa da kallo kaman mai masa kallon k'arshe, ta tuna kallon k'arshe da tayima Nabila... Da gudu ta k'arasa window tana gani Daddy da Haidar suka shige wargajejiyar jeep d'in, da shike tafiyar ta sirri ce, babu tawagar motoci, mota d'aya tak suka fita da ita....
Haidar yayima Daddy k'uri yana murmushi cikin ransa, domin yasan hakan da yayi shine daidai, amince masa da auren Fairuzah da yayi shi zaisa ya sami kusanci dashi har Allah Ya tainake shi ya karya sa kab'as, domin idan baiyi kusa dashi ba bazai tab'a iya ganin bayansa ba tunda yanada mulki da dukiya...
***********
Jinsa wani iri yake gaba d'aya, kaman kullum saida ya tsaya yayi masu sayyan kayan mak'ulashe dangin su fresh milk kafin ya nufi gidan Hajiya....
Maryama na zaune tana kallo Hajiya ta tafi islamiya... tayi kyau cikin doguwar riga na atampa d'inkin ya zauna a jikinta, lokaci zuwa lokaci gabanta ke fad'uwa ba tareda tasan dalili ba, jiyo sallaman sa da tayi yasata mik'ewa zunbur ta zauna.
Shid'inma ya jima yana binta da kallo daga bakin k'ofa kafin ya soma takowa, ta masa kyau sosai yau d'in, shi har wani girma yaga ta k'ara masa... Bai iya cewa komai ba sai rungumeta da yayi cikin jikin sa...
Sun jima a haka kafin ya masu masauk'i saman kujera, dab'as ya d'aurata saman cinyoyin sa...
Da k'yar ta iya gaidashi ganin irin kallon da yake binta dashi, ya amsa yana kwaikwayon muryar ta. Gaba d'aya sukayi dariya...
Fuskar ta Ya dafe da duka hannayen sa biyu kafin yace "Baby kinyi kyau da yawa..."
Ta d'an turo baki tace "Ai ka fini kyau, kaifa fari ne ni kuma bak'a ce..."
Murmushi ya kuma yi kafin ya lakaci hancinta yace "Inji waye, ai bak'i yafi tsan-tsan kyau na fad'aki, fari na saurin attracting mutane ne, but real beauty is black... I love you..."
Kallonsa take yanda yake maganar abin burgewa kafin ta kwantar da kanta saman k'irjin sa....
Ledar da ya shigo dashi ya soma bud'ewa, duk a tunaninta magani ne, har ta soma ya mutsa fuska, nan taga shirgin kayan k'walama ne ga tarin na jiya a fridge gashi yauma ya kuma taro wasu...
Da kansa ya shiga bata a baki, tun tana nok'ewa har ta Saki jikinta, shiru-shiru bata ga an fito da magani ba..
Dubansa tayi da mamaki kafin tace "Uncle ina maganin...?"
AT ya kamo kunkuminta suna fuskantar juna kafin yace "Zan baki kafin na tafi, promise Me bazakiyi kuka ba Baby, kinji pls..."
Abin har yaso bata dariya ganin ma ita za'a bada magani amma shine mai marairaicewa. A hankali ta gyad'a masa kai kana tace "Bazan yi ba Uncle..." Murmushi yayi kafin ya d'an ja kumatun ta yace "Ai dai kinsan ni mijin ki ne koh, sannan kinsan hakkin miji akan matar sa da kuma hakkin mata akan miji koh, anyi maku a islamiya koh..."
Gabanta ya yanke ya fad'i da jin wani sabon zance da Uncle d'in nata yazo mata dashi..
Ganin tayi jigum yasa AT yin murmushi kafin yace "Don't panic it's nothing kinji koh, tashi muje muyi sallah I'll teach you everything..." Bai jira cewarta ba ya sunkuce ta suka shige d'akin bak'i mai kallon na Hajiya...
Jikinta duk yayi sanyi dama jiya kafin ya tafi saida ya sata ta gyara masa d'akin, wllhi itakam bata kawo komai ba, sai yanzu take recalling abubuwan, sai yanzu ta gane maganin da Uncle yake nufi, Innalilhai itakam batasan yaya hakan zata soma kasancewa tsakanin su ba, tasan tana son sa kuma tana tausayin sa but ina alk'awarin su da Sajida.... Bata k'arasa tunanin nata ba taji hannun AT a goshinta yana karanto mata addu'o'i...
Saida ya mata nasiha mai ratsa zuciya wanda har saida ya sakata zuban hawaye... AT ya jawota cikin jikinsa yana lallashi, daga nan zance ya soma canzawa..
So take ta hanasa abinda yayi niyya ta kasa, so take ta dakatar dashi bazata iya ba, shin idan ta k'yale Uncle ya ida nufin sa ina matsayin alk'awarin da tayima Sajida... Wata zuciya tace toh idan kika yini kika kwana cikin tsinuwar Allah da Mala'ikun sa fah? Maryama ta rinste idanunta hawaye na gangaro mata...
A hankali yake rad'a mata "I'll be gentle..."
Tsam ya matseta cikin jikinsa yana lallashinta don yasan tayi namijin k'ok'ari, abubuwa da dama suka ziyarci zuciyar AT, tabbas yau ya bud'e amanar sa da kansa, sannan ya tuna da matarsa Aysha, ya sami nutsuwar da ya rasa tun bayan mutuwar ta...
Albarka yaci gaba da saka mata ita kuwa ta kasa yin shiru sai kuka take, jikinsa yayi sanyi gaba d'aya gani yake bai kyauta ba, gani yake she's still young, gani yake ya sab'a alk'awarin da ya d'aukar ma kansa... Shi gaba d'aya gani yake ya ji mata ciwo ne ma.... Tak'i daina kuka tak'i d'ago fuska su had'a idanu...
AT ya marairaice murya yana mai ci gaba da bata hak'uri...
Ita kuwa Maryama sam ba abinda ya sata kuka sosai kenan ba, karya alk'awarin Sajida da tayi shi ya sata kuka babu ko k'akk'autawa, laifin kanta take gani, tana tsananin son Uncle bazata iya hanasa kanta ba, gashi hakan ya jawo ta karya alk'awarin 'yar uwanta, shikenan tasan har abada Sajida bazata tab'a yafe mata ba...
Yana nan rik'e da ita yana aikin lallashi suka jiyo Hajiya ta tasaya daga gate suna magana da Ilu da alama tambayar sa take ko Attahiru ya zo gidan ne... Gaba d'ayansu saida k'irjinsu ya buga, ai sai yanzu suka tuna a yanda suke, ashe gidan Hajiya ne..."
Maryama ta kuma fashe masa da wani sabon kuka, shikenan itkam, ta mutu ta lalace, shikenan Hajiya zatace ta zama 'yar iska wayyo Allahn ta, Uncle ya shammace ta.....
Cikin sauri ya gama zura rigarsa shi sam bai kawo Hajiya zata dawo yanzu ba... Duban Maryama dake duk'unk'une cikin bedcover kafin ya sassauta murya yace "Baby let me take you to bathroom, kiyi hak'uri kinji Hajiya won't find out.."
Mak'e masa kafad'a tayi tana mai ci gaba da kuka..
Sai faman share zufan goshinsa yake bazaiso Hajiya ta shigo ta gansu a wannan yanayin ba, cikin sauri ya nufo k'ofa jin muryar ta parlour sai bin parlorn da kallo take, ga d'ankwalin Maryama saman kujera yanda suka gama ciye-ciyen su...
Turus suka kusa cin karo shida Hajiya a bakin k'ofa.... Ya kasa bata hanya ta shige ya kasa ficewa...
Kallo ta bisa dashi shek'ek'e kafin ta had'e giran sama da k'asa tace "Meye haka kai kuma inyi, sai faman muzurai kake uwa kayima sarki k'arya, bani hanya na wuce ni... Waima ina Maryama ko bataji na dawo bane..."
AT yasa hannu ya goge zufan goshin sa kafin yace "Ki k'arasa d'akinki Hajiya, dama dama tana.... tana kitchen...." Yanda yake maganar sarai zaka fahimci bashida gaskiya..
Gyara tsayuwarta Hajiya tayi don gaba d'aya bata yarda dashi ba kafin tace "Kai bafa na son sakarci, matsa min na shige nace, yo gidana ne ko ina naga daman shiga zan shiga ko iyaka zaka min..."
AT ya soma girgiza kai yana shafa k'eya ko zarafin magana bai samu ba ya kuma jiyo muryar Hajiya tana fad'in "Matsa min nace ban yarda da wannan sunne kan naka ba..."
Jiki a sanyaye ya matsa ta nufi d'akin tana ci gaba da sababi..... AT kuwa tuni ya suri car keys d'insa ya fice...
Turus Hajiya taja tayi birki ganin Maryama kwance cikin gado baka jin sautin kukan ta sai hawaye....
*Saminah Aliyu Mrs💖*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*47*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINIWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
Tafe hannaye Hajiya ta shiga yi tana sallallami.... "Eh lallai mana, haba ai biri yayi kama da mutum, ni tunda naga wannan kame-kamen da yake yi nasan za'a rina..." ta kuma duban Maryama da har lokacin sharan hawaye take kafin ta yab'e baki tace "Toh ke kuma hindiya sarkin kuka ke ba 'yar soyayya ba, ai kinga soyayya da idan ina korarsa har haushina kike ji kega Hemamalin sarauniyar soyayya koh, ai kinga soyayya dama shikam ai wayo zai maki.... Zai dawo gidan nan ya same ni ne..." ta k'arashe tana shigewa bathroom don had'a ruwan zafi wa Maryamar ta, zuciyarta ya cika da nishad'i dukda a fili fad'a take.....
************
Yana driving yana tunanin Maryamar sa, a hankali yake sakin murmushi idan ya tuna yau shida Mariam sun zama cikakkun ma'aurata, lokaci guda tausayin ta Ya cika zuciyar sa, inama suna tare shi yake jinyar kayansa, inama suna tare yayita riritata she's indeed a Queen to his heart.... Ya kuma sakin wata murmushi sanda ya tuna kalan yarintar ta...
Har ya iso gida tunanin da yake kenan, Shema'u tana cikin d'akinsa ta wargaza sai binciken neman takardun asibiti take don batayi tsammanin yanzu zai dawo ba tunda tasan sai yamma k'arfe hud'u yake dawowa daga office... Sam ko k'aran tsayuwar motar sa bataji ba don gaba d'aya Hisham ya d'aga mata hankali...
Tana cikin bincike drawer tajiyo muryarsa a bakin k'ofa yana amsa waya.... A tamanin ta Saki takardun hannunta tayi saurin warware gashin kanta kaman mai haukan gaskiya...