← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 63

Sashe 61

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

VP ya shak'o wuyan Alh Aminu yana huci yake fad'in "Laifinka ne, duk laifinka ne, matar nan bamu santa ba haka kurum ka jona mu da ita yanzu ga abinda hakan ya haifar mana wllhi ina mai tabbatar maka idan 'yansandan nan mu suke farauta zaka bar tafiyar mu, tun wuri kasan yanda za'ayi ka tsare matar nan from coming to this place, just do whatever you can to stop her... I can't lose my carrier.." ya k'arashe yana huci kafin ya doka kira ma Chief security d'insa yace ya dubo masa Haidar a penthouse d'insa...

Alh Aminu da ransa ya gama b'aci da hidiman Shema'u, layin d'aya daga cikin 'yan dabansa na garin yayi kafin ya sanar dashi aikin da yake so yayi masa, kalan motar Shema'u ya fad'a masa sannan ya sanar dashi zasu ganta da yara... Take Cuna yace "An gama mai gida...."

Cuna ya dubi yaransa yayi masu pito had'i da masu alama da kai cewa su ware ta samu... Cikin sauri suka d'auki kayan aikinsu suka fice daga uncompleted building d'in...

**********

Masu tsaron gate firfir suka hana Hajiya shiga domin su kansu yanayin matar ya basu tsoro...... Mai napep ma harda shi a magiya amma sun hanasu shiga, Hajiya data cika tayi fam sai aunasu kawai take da idanu... Basu ankara ba sai hangota sukayi tayi tsalle ta cab'e k'arafunan gate tana k'ok'arin haurawa ga wayan wuta a sama....

Ai a tamanin d'ayan yayi jifa da kulkin dake hannunsa ya durk'usa saman gwiwoyin sa yana rok'onta Allah Annabi ta sauk'o don idan wayan wuta Ya ja ta ta mutu shi za'a Kama..

D'ayan inyamurin kame kansa yayi yana ambato Chineke...

Bahaushen kuwa yaci gaba da fad'in "Iya kiyiwa Allah ki sauk'o..."

Hajiya tana cab'e da gate take fad'in " Bani sauk'owa don uwarka sai ka k'yaleni na shiga nan na fito da jikata..."

Mai napep me zaiyi banda dariya fad'i yake "Baaba wllhi kar kika sauk'o sai sun bud'e maki...."

Ganin draman Hajiya bazai k'are ba yasanya inyamurin nan saurin bud'e mata k'aramar k'ofa jikinsa har k'yarma yake don baison biafara ta maimaita kanta...

Sai sannan Hajiya ta sauk'o ta shige cikin hotel d'in tana fad'in "Dama baku bud'e min ba kuga yanda ake d'ale katanga, masu taimakawa ma yad'a fasadi kawai....."

Mai napep daga chan yana dafe da napep d'insa yake fad'in "Yauwa Hajjaju Baaba shiga ki fito ina nan ina jiranki...."

******

Jini sai faman d'iga a hannunsa yake kaman daga sama sai ganin KB yayi ya paka mashin d'insa Kimko a gefe kana yace "Dr dan Allah ka hau muje zaka iya fad'i kaga jini na ta zuba, pls ka hau muje...."

AT baima fahimci me KB ke cewa ba shidai kawai yasan ya d'ale mashin d'in, bai fad'a destination ba bai iya fad'in komai ba don already sama ta soma juya masa k'asa... KB kuwa bai yi wata-wata ba ya koma dashi asibiti don yasan ogan nasa na buk'atan taimakon gaggawa....

********

Gudu Shema'u kema shararawa a kwalta, ganin Jamal ya kusa bud'e k'ofa yasata yin parking a gefen hanya don wajen babu mutane sosai, wani igiya ta rarumo a gefen kwalbati uwa zararriya tana niyyan d'aure yaran kaman daga sama taji saukan itace a gefen fuskar ta saida jini ya tsarto... Lokaci guda ta saki wani jahilin ihu.... Daidai lokacin da taxi d'in su Maryama ya iso...

Haidar da mai taxi suka fito a guje suka nufo wajensu Shema'u.... Oga Cuna kuwa ganin mutane sun nufosu yasa sa saurin ciro ruwan acid d'in dake aljihun sa ya watsa ma Shema'u sai gefen kunnenta da wani b'angare na jikinta..... Wani wawan ihu Shema'u ta kurma ta shiga fiffincike jikinta tana rawan alanta uwa wacce tayi wanka da ruwan k'arara... Ihu take tana dafe kunnenta ga fuskanta gaba d'aya halittan ta canza sabida sauk'e mata itace dasu Cuna sukayi....

Jamal da Ni'ima sai ihu suke suna kuka yayinda su Cuna tuni sun cika ma rigarsu iska a guje...

Maryama da k'yar take takawa sabida itama lafiya bai isheta ba, ta k'araso wajen motar da sauri ta bud'e su Ni'ima suna ganinta suka rungumeta suna kuka itama kukan take... Haidar da mai tasi kuwa sunbi bayan su Cuna saidai basu cimmasu ba...

Duban Shema'u dake birgima a gefen titi sukayi lokaci guda wayan ASP ya shigo ma Haidar nan ya sanar dashi abinda ke faruwa...

ASP ya sanar dashi zasu turo masu cover-up cikin gaggawa.....

*******

Gaba d'aya Buzu ya canza mata lokaci guda, bai b'oye mata ko abu guda ba na shirin da suke akanta shida Shema'u, sannan ya sanar da ita fansan abinda mahaifinsa ya masa na auren Maryama zai d'auka akanta...

Sajida ta shiga jada baya tana hawaye... fyad'e yake shirin mata da k'arfin da Allah Ya masa, Sajida ta kuma dubansa idanu na zuban hawaye kafin tace "Haris na d'auka kace kana sona...."

Dariya Buzu ya fashe dashi kafin ya soma fad'in "Da shike ke doluwar k'arshe ce ba, koda yake tunda evil Aunt dinki ta iya manipulating d'inki kowa ma zai iya, you such a daft... Bari kiji na kuma fad'a maki Maryama is the love of my life.... Kuma wllhi kinji na rantse sai na rama abinda munafukin ubanki ya min akanki ya hanani aurenta ya aura ma kansa sabida son zuciya irin nasa... Sai na maki kaca-kaca ta yanda idan yaga illa da na maki sai zuciyar sa ya buga tunda shi likita ne...."

Sajida tana huci hawaye na bin k'uncinta take fad'in "Kar ka kuskura ka kuma zagin mahaifina da wannan la'anannen bakin naka, kuma Maryama ba ajinka bace bari kaji, matar manya yace, baka cancanceta ba, Daddy shi kad'ai ya cancanci ya mallake ta...." Bata kai aya ba Buzu ya d'auketa da wani wawan mari...

Cikeda tsoro ta nufi k'ofa a guje tana kuka.... Nan taji k'ofa a gark'ame... Ya fashe da wata dariya kafin ya fincikota ya jefa ta saman gado yana k'ok'arin zuge belt d'in wandon sa....

Tsalle ta kuma yi ta nufi jikin window tana bubbuga glass d'in tana neman d'auki nan ta hangi Hajiya a k'asa sai bin tapka tapkan benayen take da kallo....

Kuka Sajida take don babu mai jiyota already ya kunna TV ga k'ofofi da winduna a gark'ame...

Hajiya ta warware bakin zaninta lokacin da wani dabara ya fad'o mata kafin tayi addu'a ta nufi wani k'ofa, akako yi sa'a reception ta nufa, nan ta danna wayarta hoton Sajida ya bayyana ta shiga nuna masu tana tambayar su, matse hawaye take yi tana rok'onsu su taimaka jikarta ce tanada matsalan k'wak'alwa sato ta saurayin yayi...

Receptionists d'in wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wannan, Hajiya ta basu tausayi ganin tana neman zuba gwiwoyinta a k'asa..

D'ayan yace Baaba zamuje dake mu duba idan abinda kika fad'i ba haka bane ki kuka da abinda zamu maki domin yin hakan na nufin rasa aikin mu ne idan Oga ya sani..

Hajiya ta gyad'a kai tace ta yarda...

D'aya ya zaro key a shell kafin suka nufi bene...

Aiko suna zuwa wajen d'akin sukaji hayaniya sosai gana TV gashi kaman harda kukan mace...

Hajiya ta zare idanu had'i da d'aura hannu a k'irji tace "Na shiga uku ni Fad'ime! Bud'e min don uwarka nace.." ta k'arashe tana had'e kan receptionist d'in da jikin k'ofa wanda keta faman manna kunnensa a jikin k'ofar yana son jiyo meke faruwa cikin d'akin...

Jiki har na rawa yake gyara hulan security d'in dake kansa wanda tuni ya zame sabida had'e kansa da k'ofa da Hajiya tayi, tuni ya shiga zura Key nan k'ofa ta bud'e...

Hajiya hango Buzu tayi yana kokawan raba Sajida da suturanta ya danneta gaba d'aya...

Saida ta kwararo wani ashar kafin ta waiga gefe da gefe tana neman abin lapta masa nan ta hangi irin dogon flower vase d'in nan aiko shi ta rarumo tana fad'in "Zakaci gwafar ubanka yau ka gama bariki....

Gadon bayansa ta samu wanda yake jazir sai shek'e yake kafin ta sauk'e masa Vase d'in nan lokaci guda ya tale had'i da sake k'aran azaba....

*Saminah Aliyu Mrs💖*

💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*50*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*_FINALE_*

Jikin Sajida har na rawa ta mik'e tana goge hawaye tayi bayan Hajiya data shak'o Buzu da iya k'arfinta tana k'ok'arin ka dashi, bil hakk'i da gaskiya kokawa Hajiya ke shirin yi dashi saida securities suka k'araso suka k'waci Buzu domin kuwa da k'yar idan k'ashin bayansa bai karye ba...

Sai Huci take tana gyara d'aurin kwalinta da zaninta take nuna sa tana fad'in "Kaji jiki munafuki algungumi mai fuska biyu.... Allah Ya tsaremu da mugaye irinka watsetstse kawai.... Ke kuma wuce ki daina mun kuka ai kinga irin abinda nake fad'a maki kink'i yin hankali wauwata da sokanci sun taru sun maki yawa wuce nace...!!!" ta k'arashe tana daka tsawa ma Sajida dake cazgan kuka....

Bata iya tafiya ba sai rungume Hajiya da tayi cikin muryar kuka take fad'in "Hajiya ki yafe min, wllhi na yarda nayi dolanci amma ki yafe min dan Allah duk abinda nayi bada son raina bane kuma na yarda mutum bai wuce k'addaransa, ki yafe min pls Hajiya tah...." Hajiya jikinta yayi sanyi d'an rungumar Sajida itama tayi tausayinta fal zuciyarta kafin tace "Na yafe ki takwarata Allah Ya k'ara tsare min ku....."

Ta dubi Buzu dake nishi da k'yar hannun securities kafin tace "Yan sanda zaku kira min wannan barin su a gari masifah ne...."

D'aya security d'in ya gyad'a kai kafin yace "K'warai Hajiya already ma suna nan tafe amma wannan kin illatasa sai an kaisa asibiti....."

Hajiya ta tab'e baki kana tace "Sakamakon irinsu kenan nidai bana barin nan sai naga 'yansanda sun kame sa....." Bata kai aya ba wayarta ya shiga ruri tana dubawa taga bak'uwar lamba abinda aka fad'a mata a wayar shi yayi mugun d'aga mata hankali.... Cikin sauri ta shiga janyo hannun Sajida suka fice hawaye na gangaro mata take fad'in "Sajida Mahaifin ki, mahaifinki ne muje.... Muje kar mu rasa shi..."

Sajida na kuka take girgiza kai tana fad'in "Hajiya Aunty Shema'u fuska biyu gareta ki fad'a min me tayi wa Mahaifina... Ina Daddy na...?"
Chapter 61 · 0% Book details