Sashe 26
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunanin maganganun da sukayi da Hisham shike faman yawo a kwanyar sa, a b'angare guda kuwa tunanin halin da Maryama take ciki a halin yanzu yake, yasan tabbas yau tasha kuka har ta gaji, take yaji zuciyar sa nai masa zafi da zogi, lokaci guda yaji yana son ganinta yana son sanin halin da take ciki, cikin sauri ya karya kan motar sa ya nufi gidan Hajiya.
Isarsa ya samu har an shiga sallan Magrib a masallacin unguwar, don haka kai tsaye paka motar sa yayi ya wuce masallaci.
*************
"Miss Beauriful dukda banga kwalliyarki na liyafarki ba naji dad'in sake ganin ki, and I hope zanci gaba da ganinki har k'arshen rayuwata." Yayi maganar fuskar sa dab da nata.
Gaba d'aya jin abubuwa na tsarguwa a jikinta take, bata tab'a jin irin hakan ba, ga kyaun halittar sa na firgitata.
Gyad'a masa kai tayi cikeda kunya kafin tace "Ni zan k'arasa gida kar Daddy ya dawo nasan zai nemeni, sannan Aunty Shemah ma bata san nida kai are seeing each other ba..."
Buzu ya zaro fararen idonsa masu narkar da 'yanmata da manyan mata waje kafin yace "Haba Miss Beauriful, we ain't doing anything wrong right, gaskiya banji dad'i ba da baki sanar da Aunt d'inmu ba, at least idan ta sani yafi, this is legal banaso kina b'oye mata abu tunda babu Mummy.." Ya k'arashe in a serious tune.
Cikeda jin dad'i Sajida ta gyad'a masa kai kafin tace "Insha Allah zan sanar da ita."
Buzu ya murmursa kafin yace "Good hakan yayi, toh yanzu sai yaushe na sake ganinki Miss Beauriful.?" A shagwab'e yayi mata tambayar.
Murmushi ta kumayi cikeda jin dad'i kafin tace "Gobe babu islamiya jibi ma babu sai weekend kenan, ko kuma idan nayi magana da Aunty na tasan da zaman ka zan iya nemanka a waya sai na sanar da kai.."
Buzu ya kuma marairaice mata fuska kaman zaiyi kuka yana wani matso da jikinsa kusan seat d'inta kafin yace "Miss Beauriful bazan iya kwana biyu mai kyau ban ganki ba sai nayi ciwo, amma babu matsala ki sanar da Antyn namu things will be easier..." Ya k'arashe yana kasheta da mayen kallo..
Abunka da budurwa mai ji da tashen budurci da k'uruciya duk sai ta ringa jin wani irin feelings na fizgar ta. Gaba d'aya a tak'ure take, d'an d'ago idanu tayi ta dubesa kafin tace "Ni zan wuce gida kaga yanzu za'a fito daga sallah ina son na shige gida kafin a yi sallama nasan Daddy na masallaci."
Buzu ya gyad'a mata kai kafin ya turo hannunsa daf da k'irjinta yana k'ok'arin bud'e mata marfin mota, wani irin abu taji yanai mata yawo a jiki dukda hannun nasa bai shafi jikinta ba. Abunka da tsohon d'an bariki sai karantar ta yake, tsaf ya lura yarinyar batada wayo, she's so naive and innocent, and babban weak point d'inta shine she fell for him completely, samun kanta bazai masa wuya ba sannan yasan duk abinda ya sata da wanda ya kwab'eta zatayi....
Koda sukayi sallama bai shige ba saida yaga ta karyi kwanan layin su kafin yaja motar sa ya bar wajen...
******************
A veranda ya samesu sun sallame sallar magrib, Hajiya na gefe tana lazimi Maryama kuwa Al'Qur'ani ne k'arama a hannunta da alama shigar da Hadda take.
Jiyo sallamar sa da tayi yasata dasa aya ma karatun nata dukda dama ba da sauti takeyi ba, ta amsa masa sallamar kafin ta masa sannu da zuwa.
Dukda hasken k'wan wuta ne ya haske masa fuskar tata hakan bai hanasa gano kumburi da idanunta sukayi ba alamun taci kuka. Samun kansa yayi da fad'uwan gaba mai tsanani, gaba d'aya ji yayi tausayinta ya rufesa, gaskiya ba don Momma ita ta haifi marigaiya Aysha ba da kuman yana ganin girman tsufa da yau d'in nan sai yanda k'arfinsa ya k'are wajen karb'a wa Maryama hakkinta.
"Lafiya ka mana tsgege haka aka uwa bashi kazo amsa." Muryar Hajiya ya katse sa, gaba d'aya baisan ma yayi tsaye yana bin Maryama da kallo ba.
Saita kansa yayi kafin ya janyo k'aramar kujeran zaman kitchen dake gefe ya zauna had'i da gaida Hajiya.
A tak'aice ta amsa masa don shima a wuya take dashi.
Maryama ta gaishe shi ya amsa har lokacin idanun sa na kanta, harta Hajiya saida ta lura da kallon da yake bin Maryama dashi dukda duhu da ya soma.
Qur'an d'inta ta d'auka ta nad'e abin sallanta kafin ta shige parlour ta barsa shida Hajiya zaune a verandar.
Hajiya ta kaste masa kallon nasa da fad'in "Meye kake binta da kallon k'urilla ko kaima baka yarda da ita bane, ko sharrin satan kaima zaka k'ulla mata inyi.?" cikeda fad'a tayi maganar.
AT ya tura hular kansa baya kafin ya gyara zama yace "Hajiya don Allah kiyi hak'uri maganar nan ta wuce har abada, Momma zata tafi jibi-jibin nan insha Allah, kiyi hak'uri dan Allah."
Tab'e baki tayi kafin tace "Ai ko kotu akaje Kulu ce batada gaskiya idan Alk'ali bai d'aureta ba zaici taranta sabida sharrin data k'ulla ma Maryama ta ehe..."
Hajiya taso basa dariya jin harda batun zuwa kotu amma sai ya d'an dake don yasan dariyar sa ka iya zama wani chapter daban.
"Hajiya me ya kawo batun zuwa kotu kuma, Momma ai me tafiya ce...." Dakatar dashi Hajiya tayi ta hanyar d'aga masa hannu kana tace " Dakata Attahiru, wai naji kanata cewa Kulu ce mai tafiya, ita kuma wancan mai roba-robar fuskar fa uwar me zata zauna tayi, ko d'akin k'anwartar ne zata shige inyi.?"
Gaban AT ya yanke ya fad'i, k'ok'arin had'a kalmomi saman harshen sa ya soma yana fad'in "Amm dama Hajiya wai da zata d'an kuma zama da yaran....."
"Rufe min baki banason ji, gaka uban 'yan son 'ya'ya ko, irinku ne masu d'auko rayuwar nasara ku d'ora yaranku akai , yaro sai abinda yaga dama zaiyi, da anyi magana kace gaka d'an boko ko, toh naji yayi kyau, halan ni haka kaga na tayar da kai ko?" Ta k'arashe tana rik'e da hab'arta.
Kasa cewa komai yayi don bayaso aja maganar....
Karyar goronta tayi kafin tace "Nidai bazan daina maka addu'an Allah Ya warware asirin da Kulu da d'iyarta suka maka ba, ta kirkin cikinsu ta tafi abinta, Allah Ya tsare yaranta daga koyi da halin Kulu da d'iyarta.."
Idan Hajiya tayi maganar an masa asirin nan sosai abin yake basa dariya da mamaki, bil hakk'i da gaskiya take fad'i abinta......Idonsa ya hangi tray na abinci ta cikin parlour.
Hajiya ta bisa da kallo taga yanda idanunsa ke kalla.
"A kawo maka abincin nan ne ko kuma zaka shiga kaci."
Ta tambayesa tana mai mik'ewa tana k'ok'arin linke sallayar ta, saurin karb'an sallayar yayi ya linke mata kafin yace "Maryam ta kawo min nan, ta fito mun da darduma kawai, barin shiga na gaisa da Maama Juu."
Hajiya ta jinjina kai kafin ta bisa da kallo har ya shige, ita sam wannan sanyin hali na Attahiru na bata mamaki, saikace ba ita ta haifesa ba, kodashike mahaifinsa Alh Shattima ya biyo.. Hajiya harda d'an murmusawa gamida goge k'walla an tuno tsohon soyayya.. Lol....
Sanda ya fito daga sashen Maama Juu ya samu har ta shimfid'a darduman, zama yayi bisa had'i da cire agogon hannun sa.
Cikin tsanaki ta k'araso ta ajiye masa tray d'in sallama a saman bakinta.
Tak'aiteccen murmushi yayi had'i da amsa mata sannan yayi mata sannu, don ya lura da rashin sakewanta gaba d'aya dashi.
Zata mik'e taji ya kira sunanta da irin sigar da shi kad'ai ke kiranta dashi.
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*21*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*For my Avid Readers😍💘*
*Kufah bar Shema'u ta shana ehe lokacinta ne 🤣 irin wannan zagi ai zaku karta kafin ran mutuwarta 😹🙆🏻♀*
D'an kallonsa tayi gabanta ya yanke ya fad'i, cikin sauri ta sadda nata kan k'asa.
"Zuba min abincin." ya fad'i idanunsa naga wayarsa.
Bud'e flask d'in tayi ta d'au serving spoon da plate ta shiga serving nashi.
Kallonta yake kanyi yanda take zuba abincin tamkar wacce k'wai ya fashe ma a ciki..... Saida ta gama kafin ta mik'a masa plate d'in tuwon shinkafa da miyar taushe cikin tsanaki.
Ssannu ya mata kafin yaja plate d'in gabansa sosai.... Zata mik'e ta kuma jin ya kirawo sunanta.
Murya can k'asa ta amsa masa.
"Maryam, kiyi hak'uri kinji, nayima Momma magana insha Allah abu makamancin haka bazai kuma faruwa ba.."
Gyad'a masa kai tayi had'i da k'ak'aro murmushi tace "Babu komai Uncle ai ya wuce."
AT ya gyad'a kansa kafin yace "Me ya sameki a idonki, yana ciwo ne...?" yayi tambayar idanunsa naga plate yana juya spoon..
"Emm a'a babu komai..."
"Are you sure.. " ya fad'i yana mai tsareta da idanu.
Gyad'a masa kai ta kumayi alamun tabattarwa..... Sallaman da Ilu keyi ne ya katse su.. AT ya amsa murya a dake don sam baya wasa da Ilu.
"Datta dama bak'on da ya kawo su Hajiya d'azun da rana ke sallama yace shi abokin aikin ka ne..." Ilu ya fad'i cikeda ladab.
Kallon Maryama AT yayi kafin yace "Tashi ki shiga." ya dubi Ilu yace "Ce masa ya shigo."
Ilu ya amsa da "An gama rankashidad'e.."
Da sallama Ashfaq ya shigo hannunsa d'auke da shopping bag. AT ya amsa masa babu yabo babu fallasa kafin yace "Ah Dr bismillah, k'araso mana."
Ashfaq ya fad'ad'a murmuahin sa ya k'araso yana fad'in "Ah Ya Doctor (haka yake kiran AT wani sa'in) ashe kana nan kenan.." ya k'arashe yana mik'a ma AT hannu sukayi masabaha had'i da gaidashi.
AT ya amsa yana masa nuni da gefensa yace "Bismillah zauna mana bari a kawo maka plate..."
Ashfaq ya d'an murmusa had'i sosa k'eyarsa kana yace "A'a na gode Ya Dr a k'oshe nake."
AT ya jinjina kai sannan "Da fatan dai lafiya ko...?" ya k'arashe yana kai spoon bakinsa..... Ashfaq baikai ga basa amsa ba domin kuwa shi kansa baisan me zaice ma AT ba, Hajiya ta fito don taji kaman muryar AT da wani ne. Burki tayi tana kallonsa da kyau kafin tace "A'ah Keenafas (Kidnappers) ka kuma dawowa ne.." cewar Hajiya da ta masu tsaye aka..