Sashe 32
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AT ya gyara zamansa ya d'an tattaro nutsuwar sa kafin ya soma fad'in "Malam Habu zai kaiku, idan yaso sai ki bar motar ki a nan tunda ko kin tafi da itama wahalan dawowa za'ayi da ita, sannan banaso kina long journey irin haka yanada had'ari though nasan kin k'ware a driving amma kiyayewa ne.." Ya d'anyi shiru..
Shema'u kuwa sai gyad'a kai take cikeda jin dad'i jin AT har ya soma mata umarni, wayyo komai nasa abin burgewa ne... Muryar sa ya kuma dawo da ita daga duniyar soyayyar sa data lula yanda yake fad'in "Ammm Shema'u ina so nasan more about you, dukda nasan ke 'yaruwar Aisha ce amma kinsan nidake bamusan juna sosai ba sannan bamu saba da juna ba..." ya k'arashe yana d'aura hab'ar sa saman hannayen sa.
Shema'u ta d'an murmusa kafin ta soma fad'in "Dr yanda ka ganni haka nan ni d'in kenan, saidai abu guda da baka sani ba shine na tab'a aure tun kafin Aysha tayi aure, na auri wani Alh Aminu, kishiyoyi suka hanani zaman gidan, toh shiyasa ma batun aure ya fita daga tsari na, ban kuma yin wani aure ba tun wancan lokacin don na wahala sosai hannun kishiyoyi, sai yanzu da ka zo min da maganar, sannan abinda ya k'arfafa min na amince da kai sabida yaran 'yaruwata ce, both nida kai nasan munayi ne sabida su.." ta k'arashe tana sadda kai k'asa,. AT ya d'an tausaya mata, ashe dole taji tsoron auri tunda bataji dad'in gidan aure a baya ba... Gyad'a kai yayi kafin yace "Haka ne sabida su zamuyi, and I trust you, na tabbata zaki rik'e min su amana.."
Shema'u ta murmusa kafin tace "Bakada haufi Dr, yaran nan are my life, insha Allahu bazasuyi kukan rashin uwa ba..."
AT ya jinjina kai cikeda jin dad'i kafin yace "Toh ya batun aikin ki, ko zan nema maki transfer of service ne..?"
Girgiza kai tayi cikeda kissa kafin tace "Ai a halin yanzu aikina shine kula da kai da iyalanka, wllhi sam babu batun aiki a gabana, da d'inma don banason zaman banza ne shiyasa...."
Ran AT ya kuma yin fari, murmushi yayi mai bayyan hak'wara kafin yace "Toh shikenan, naji dad'in hakan sosai, Allah ya wuce mana gaba..."
Shema'u ta rausayar da idanu kafin tace "Ameen Dr." Su Sajida ne suka shigo suna gaida su, suna fad'i ma Shema'u Momma ma ta fito, a tare suka nufo downstairs gaba d'ayan su AT na rik'eda 'yar autar sa...
Momma kanta har wani sabon hankali ne ya shigeta....
Gaba d'aya har wajen mota sukai masu rakiya harda AT da yaran...
************
Tunda suka zo Jalingo ko shi bai kirata ba sai ta kirasa, wasu kalaman girma saye zuciya da soyayya take karanto masa, Shema'u tayi nisa a iya makirci...
Momma ta kuma dubanta kafin tace "Kedai shashasha ce sam keda Aysha tamkar baku had'a jini ba, ni nasan wannan shegen gantalin naki bin maza dama kike, bacin haka meyasa zaki shera masa k'arya cewa kin tab'a aure, ke ko tsoron k'aryar ta k'are maki ba kyaji..." ta k'arashe tana watsa mata mugun kallo....
Tsaki Shema'u ta buga a karo na babu adadi kafin tace "Momma kinga ki daina min ihu akai, ai ke ban tab'a abin arziki kika yabeni ba sai Aysha, kuma da kike cewa bin maza nake lokacin da nake kawo maki kud'ad'e kin tab'a tambayata ina nake samun kud'ad'en da suka ninka salary na ?? Baki ttab'a ba, sai yanzu zakizo ki sakani gaba, sannan wannan aure fah don jikokin ki zanyi ba don kowa ba, idan kin amince wancan jarabbabbiyar tsohuwar ta aura masa ko wace iri ta zauna kan jikokin ki fine sai na fasa ba abin tashin hankali bane, tunda duk abinda nake baki gani...."
Momma ta share zufan da ya keto mata kafin ta shiga bawa Shema'u hak'uri, tabbas idan da laifin Shema'u harda nata, sannan wannan gaskiya ce kayi k'ok'ari ka samar da iyalanka ta tsaftacecciyar hanya, domin kuwa duk abinda ka shuka sai ka girbe... Ta fad'a duniyar tunanin yanda Mukhtar ya taimaketa sanda kowa ya gujeta sabida cikin Shema'u, Mukhtar shi ya share mata hawaye ya kuma jadadda mata Shema'u bazata tab'a sanin ba shine mahaifin ta ba, kaico dukda hud'ubar samari tabi a wancan lokacin abin saida ya bibiyeta,.... _Allah ka rabamu da sharrin samari masu neman yaran mu domin sharri, ameen_
*************
Ranar d'aurin aure abokansa likitoci, 'yan uwa da abokan arziki gaba d'aya sun hallara, su Goggo Asabe ma motoci na musamman Hisham ya sama masu dukda AT baiso a wani d'aukaki bikin saida mutane suka hallara, Hisham baya k'asa baya sama, sai hidima yake sai ka rantse aminin arziki ne...
Alh Aminu ya kad'a kai a karo na biyu kafin ya kwararo wata ashariya, har shine Shema'u zata masa 419 a cikin garin nan toh kuwa wllhi k'aryarta tasha k'arya, ya kirata yafi sau abinda yafi tak'i d'agawa, k'arshe text ya tura mata kaman haka.....
*Sameena Aleeyo Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*26*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
A zabure ta mik'e tana kuma karanta sak'on, ita kad'ai take girgiza kai ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Mata mai mata gyaran jiki dai kallo ta bita dashi ganin yanayin ta, a d'an kid'ime ta furta "Lafiya Amarya..?"
Shema'u ta d'an saita kanta kafin ta sakar mata murmushi tace "ba komai Dakura, ina zuwa..." Bata jira amsarta ba tayi ficewarta zuwa wani d'an store dake tsakanin corridor, tana shiga ta maida k'ofar ta rufe sai waige-waige take, Momma da fitowar ta kenan ta sallami wasu bak'i ta hangi Shema'u ta shige store, gabanta ya yanke ya fad'i, me Shema'u zatayi cikin store?.... Bata gama tunanin ba wasu 'yanuwansu suka yi sallama haka dole tayi ta kansu ta fita sabgan Shema'u amma zuciyarta sam bai kwanta ba da yanyin da taga Shema'un.
"My Alhaji pls ka tsaya ka saurare ni wllhi nima bansan su Momma na shirya wannan auren ba sai da abin ya k'arato, kaga yaran nan ne sam basu yarda da kowa ba sai ni basu SHAK'U da kowa ba sai ni ever since their mother passed away, pls ka tausaya min kar kayi....." Bata kai aya ba yace "Rufe min baki and don't take me for a fool, jiya na sanki da zaki wani kashe murya kina min k'aryar banza, dama tunda naga kin mak'ale a gidan Daktan nan nasan da abinda kike shiryawa, kin maidani ATM machine d'inki koh tun yaushe nake binki da maganar aure amma kink'i amince min da shike idanunki sun rufe da soyayyar mijin k'anwarki koh... Ko ki fasa auren nan ko kuma nazo har wajen d'aurin auren na fad'a ma mijin who you really are.."
Huci kawai Shema'u keyi ga zafin store da ya addabeta, zufa tako wani sak'o tsattsafo mata yake, take wani tunani ya fad'o mata ta Saki wata kafiran murmushi kafin ta soma fad'in "Alh Aminu don't you dare do that, I won't go down alone, tareda kai zamu ruguje idan kayi tunanin rusa min rayuwata, Shema'u nake, komai nasa a gabana sai nayi nasara, kasan inada labarin zaka tsaya takarar d'an majalisa...." ta kuma yin murmushi kafin taci gaba da fad'in "Wllhi wllhi zan maka sharri irin wanda imagination d'inka bai tab'a baka ba, zan ruguza maka rayuwarka dana iyalanka, wllhi idan kayi yunk'urin rabani da Tahir da iyalansa sai na rabaka da kowa naka, kai sai na maida kai abin kwatance, wllhi 'ya'yanka sai sunji su kashe ka da hannayen su shi yafi masu sauk'i..... So a shawarce mu ci gaba da rufawa juna asiri tunda ni nasan jikina kake so kar ka damu bazaka daina samu ba muddin zakabi dokoki na..." ta k'arashe tana kashesa da murmushi...
Tsoro ya cika Alh Aminu, tabbas baya fatan ya rasa kujeran da yake nema tunda gashi har ajiye aikinsa yayi ya shiga siyasa tuk'uru, sannan yana son 'ya'yan sa fiyeda komai a duniyar nan... Murmushi ya sakar mata kafin yace "Toh ai ke d'ince kinsan bana jure rashinki, ina jiranki a guest house d'ina tunda kin hanani fitowa..."
Tab'e baki tayi kafin tace "Ta ina zan fito bayan 'yan d'aurin aure sun cika ko ina..."
Alh Aminu ya dara kafin yace "Haba giwar mata wai dama so nake kizo kinga sai na baki nawa gudumawar sannan idan zaki min adalci ai ya kamata kizo muyi sallama,."
Ta d'an juya idanu kafin tace "Cash ne ko check.?"
"Sai wanda kika zab'a" ya bata amsa kai tsaye...
Murmushi tayi kafin tace "Ka saurare ni." daga haka ta katse wayar...
Tana cikin waige-waige tana k'ok'arin fitowa ta ji an jawota an shige d'aki da ita, ba kowa bace Momma ce, sai faman huci take tana watsa ma Shema'u mugun kallo kana tace " Jarabebbiya babu yanda zaki je, banda shegen fitina inji gidan wani za'a kaiki yau uwar me zaki fita kiyi da wani inyi.."
Shema'u ta buga tsaki kafin tace "Momma kinafa shige gona da iri, idan banje ba cewa yayi zai fallasa ma AT halina na bin maza sannan kinsan idan wannan aure ta fasu ba AT kawai ba harta su Sajida jikokin ki sai sun tsane mu daga ni har ke, don haka a shawarce ki barni na fita kuma ki rufa min asiri sabida dolenki ne..." ta k'arashe tana juya idanu hannu rik'e a k'ugu...
Idanun Momma sukayi rau-rau, kai Shema'u bala'i ce, harga Allah ita batayi wannan bin mazan ba gashi Allah Ya jarabce ta da samun 'ya haka, Kuskure d'aya tayi tak a rayuwarta, ji take kaman a fasa wannan aure amma babu yanda ta iya, jikokin ta zasu tsaneta...... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryar Shema'u tana ci gaba da fad'in "Momma duk lalacewan naka naka ne, nasan tunanin ki bai wuce kar nabawa jikokin ki wannan tarbiyar ba, kar ki damu wllhi bazan tab'a abu makamancin haka ba, ina sonsu tamkar yanda nake son 'yaruwata mahaifiyar su, hasalima zuwa wajen Alh Aminu da zanyi sabida su zanyi, and I promise you wannan shine na k'arshe bazan kuma pls Momma kifahimce ni, nasan kina sona kina son su Sajida pls kar kiyi abinda zai zame mana tarin danasani dagani har ke..." ta k'arashe tamkar zata runtuma ihu idanunta sur k'walla.