← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 63

Sashe 35

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa gaba d'aya da zata gane data k'yalesa domin kuwa gaba d'aya jinsa yake wani iri tamkar bashid'in ba... Hannunsa ta kamo ta d'aura saman waist d'inta yanda ke mata ciwo a k'aryarta. Gyara zamansa yayi k'irjinsa na bugawa sanda ta yaye masa d'an b'ingilan d'in rigar tata wanda da kad'an ya wuce kanpai dama, wani ikon Allah duk wani sha'awarta ya addabesa a baya sai ya nema ya rasa, harga Allah k'yamarta ya soma ji ba tareda sanin dalili ba, ba don yaso ba ya soma shafa mata man a wajen tsikar jikinsa sai tashi yake, baisan dalilin da ya haifar masa k'yank'yaninta lokaci guda ba. Shema'u kuwa sai faman lumshe idanu take taji lallausan hannu irin wanda bata tab'a jiba a jikinta, ba irin nasu Alh Aminu ba, gaba d'aya lokaci guda ta wani susuce, yana yunk'urin tashi ta d'ale jikinsa gaba d'aya ta soma masa wasu salo, tun yana k'ok'arin k'watan kansa har ya kasa, gaba d'aya shi k'aik'ayi ma jikinsa ya soma masa dama haka yake something small can irritate him, kuma duk k'ank'antan abu idan yayi irritating d'insa take zai soma developing allergy, lokaci guda skin d'insa yakan turning red yayi ruhu-ruhu tamkar mai borin jini. So yake ya k'wata kansa daga irin mayen sunbatan da take masa ya kasa ga d'an banzan k'aik'ayi da jikinsa ke masa, kan kace me amai yaji na yunk'urin yi, wani irin mik'ewa yayi ya nufi bathroom a tamanin.....

Shema'u ta mik'e tana rarraba idanu tana tambayar kanta lafiya, meke damunsa... Cikin sauri ta nufi bathroom d'in yanda ta gansa sai k'waza amai yake ga skin d'insa yayi jazur yayi ruhu-ruhu tamkar borin jini, murya na rawa ta k'araso ta dafasa tana masa sannu...

Taimaka masa tayi ya kintsa kansa kafin ta rik'oshi zata dawo dashi cikin d'akin yace mata zai iya... Kallo ta bisa dashi har ya fice daga bathroom d'in yana mai goge fuskar sa da k'aramar towel...

"Bantan ubancan!! " ta furta a hankali, ciwo bai tashi zuwa masa ba sai daren amarcin su, haushi ya taru ya turnuk'e Shema'u, ga wani kafiran buk'atar sa da take ji na kuma taso mata, gyara bathroom d'in tayi ta nufo d'aki ta tarar baya d'aki, a parlor ta hangesa yana waya..

"Hello ka shiga gida ne..?"

Daga d'aya b'angaren Hisham yace "Ango kasha k'amshi, hope komai normal, ai ban zaci zaka iya kirana ba kana can kana kwasan gara mutumina..." ya k'arashe teasingly.

Gajeren tsaki AT yayi kafin yace "Kaga calamine lotion da Antibiotic zaka kawo min pls..."

Hisham ya had'iyi dariyar da yake kafin yace "Badai amarya bace babu lafiya koh.."

"Kaikam ka kawo min yanzu pls, sai na jika.." daga haka katse wayar yayi. Nan Hisham ya soma tunanin AT yanada Allergy wanda duk abinda ya gani ya d'aga masa hankali ya basa k'yank'yani toh fah yana tashi, a fili ya furta "Allah sa shegiyar nan ba k'azamin salon karuwanta ta tashi nuna masa ba.." cikin sauri ya zari car keys d'insa ya fice....

Fitowa Shema'u tayi duk jikinta yayi sanyi kaman ta cinyesa haka takeji, ta k'araso yanda yake cikin salo na tafiya, zama tayi gefensa tanai masa sannu, nan taga gaba d'aya fatar sa tayi jazir...

K'ak'aro murmushi AT yayi don shi harga Allah tausayi ta basa baisan dalilin da ya haifar masa k'yank'yanin ta ba duk da cewa ita d'in 'yar gayu ce ta ajin k'arshe, a zahiri baijin k'yank'yanin ta amma kusantar ta da ya tasamma yi shi haifar masa da k'yank'yanin..

"My Dr kana son wani abu ne..?" ta tambaya tana kashe murya.

D'an girgiza kai yayi kafin yace "No babu komai kije ki kwanta akwai gajjiya a tattareda ke, sannan kema bakida lafiyan, ko wajen ya daina maki ciwon ne?"

Murmushin yak'e tayi kana tace "Eh ya daina, kaine patient yanzu, amma dama kanada allergy ne Dr, kodai kaci wani abinda baka saba ci bane a garinmu or maybe you're allergic to it baka sani ba...?" tayi tambayar cikeda nuna damuwa.

D'an murmusawa kurum yayi kana yace "Kar ki damu zai daina wani sa'in haka yake min, Hisham zai kawo min magani yanzu, na duba first aid d'ina babu, kije ki kwanta kinji I'll be fine.."

Marairaice fuska tayi tana wani babbank'arewa uwa gashashhiyar kaza kana tace "My AT wllhi bazan iya bacci kana cikin wannan hali ba pls let me take care of you..."

AT ya d'anyi jim kafin ya sakar mata murmushi cikeda tausayinta, kai shi wannan k'yank'yani nashi shi kansa na damunsa shiyasa ba ko ina yake iya cin abincin ba sabida yasan kansa, ko abincin restaurant ba ko wanne yake ci ba don wani jik'on yana cin abincin da bai kwanta masa ba allergy d'insa zai tashi, gashi yanzu abin yayi tsamari har kan matar sa.... Suna nan zaune wayar Hisham ya shigo masa, mik'ewa yayi ya fice ya karb'o magaungunan, Hisham yasha mamaki ganin yanda jikin AT yayi, tabbas jikinsa ya basa yanzu haka Shema'u ce tayi irritating nasa don yasan waye AT d'in....

Ba don yaso ba Shema'u ta shafe masa maganin uwa zata had'iyesa, dukda maganin dake shafe a jikinsa bai hana Shema'u shigewa cikin jikinsa ba a haka bacci ya d'auketa AT kam sam babu bacci a idanunsa, a hankali ya zare jikinsa yana k'are mata kallo, ikon Allah ga Mace har Mace amma wllhi ji yake bazai iya kusantar ta ba, wato da can da sha'awarta ya addabesa sharrin shed'an ne, shi ya ringa k'awata masa ita ko zai nemeta da alfasha sai kuma Allah yasa shid'in baya daga cikin mazinata, sai gashi da ya aureta ya nemi sha'awar ya rasa saima akasin haka. Sauk'e nannauyan ajiyar zuciya yayi kafin ya koma saman couch yayi kwanciyar sa....

Da asuba koda ya tasheta tayi sallan asuba komawa tayi taci gaba da baccinta don dama sallan ba wai ya dameta bane, koda ya dawo a zatonsa tayi sallah k'arshe ma a parlor ya k'araci kwanciyar sa gari na soma haske ya tsala wankar sa ya shirya tsaf cikin lallausar yadi ruwan k'asa da b'akar hula, kumburin jikin nasa sun b'ace sai rod'i-rod'in ja da skin d'in nasa yayi....

*********

Tun daga veranda yake jiyo muryar Hajiya tanai ma Maryama fad'an ta tashi taje ta cire abinda ta d'aure k'irjinta dashi, taci gaba da fad'in "Inyi banda taurin kai irin naki, sarai kin sani muddin kina al'ada k'irjinki kumburi suke suyita maki ciwo ai sai ki sarara ma kanki koh, banda felek'e kin matse kanki kin tak'ure ba dole suke maki ciwo ba , haba wannan tak'ura kai har ina, idan ba fita zakiyi ba sai ki kwab'e rigar maman kisha iska ai tunda a cikin gida kike inyi..." Sallaman AT ne ya katse Hajiya...

Duba d'aya Hajiya ta masa ta tab'e baki had'i da d'auke kai gefe, Maryama kuwa kamar ta nitse a k'asa haka taji, takaicin Hajiya ya turnuk'eta , kai Allah yasa Uncle bai jiyo maganganun da Hajiya take ba...

Waje ya nema ya zauna yana satan kallon Maryama yake gaida Hajiya.

Hajiya ta wani foze sai amsa masa take a dake, ta jawo ledar goron bikin 'yar mak'otansu da aka kawo mata ta wangale ledar gaba d'aya don AT ya gani yaji haushi... Da k'yar Maryama ta gaida shi sabida ciwo da k'irjinta suke mata...

Kaiii! Karkatowa Hajiya tayi tana duban Attahiru don d'azu a fige ta kalle sa gaba d'aya bataga sauyin da fatar tasa tayi ba... Baki sake ta bisa da kallo..

Tafe hannaye ta shigayi tana sallalalmi wanda yasa daga AT har Maryama suka bita da kallo suna jira suji abinda ya sata jero salati

"Attahiru yanzu kaima duk hasken fatar taka bata isheka ba saida kod'add'iyar can ta shafe ka da man bilicha (bleaching) d'in kaima, na shiga uku ni Fad'ime kaima ka koma roba-roba fuska uwa kakin soji, Oh Allah dai ya yaye maka mugun k'ullin da suka maka..." ta k'arashe tana rik'e hab'a

Ba AT kawai ba harta Maryama dake faman cije-cijen labb'a saida ta k'unshi dariyar ta..

AT ya d'an shafi k'eyarsa baice komai ba. Domin baima san me zai soma ce mata ba, sai lokacin Maryama ta d'ago tana dubansa suka kuwa had'a idanu, saurin sadda nata kan k'asa tayi don ba komai ta tuna ba illa Uncle fah yanzu mijin Aunty Shema'u ne...

"Kai nake saurare Attahiru ko salon naka asirin da su Kulun suka maka kenan iyi..?"

"A'a Hajiya kin mance tun ina k'arami ai inayin ciwo makacin haka, me zai had'ani da bleaching kuma Hajiya.." ya bata amsa still yana satan kallon Maryama da keta tamke idanu alamun zogi.

Ganin hankalin su ya karkata kan zancen da suke yasata mik'ewa a sulale ta wuce uwar d'aka...

"A'ah yo dole nace haka tunda ka zama shanyayye sai yanda Kulu da d'iyarta sukayi da kai, an tofa maka a ruwa ka sha..."

AT ya d'an shafi goshin sa yanaso ya kawar da zancen, mik'ewa yayi ya isa gaban flask d'in ruwan zafi dake gefe tareda kayan kari ya shiga k'ok'arin bud'e flask d'in.

"Meye haka, ko ajiya kayi ne a ciki, inyi.." ta fad'i tana watsa masa kallo.

Komawa yayi ya zauna baice komai ba, uwa maraya.

Ta mik'e tana ci gaba da sababi tana fad'in "Banda bak'in gulma da munafunci ka baro amaryar taka kazo kana neman abin kari a nan,
ai sai kaje amaryar ta dafa maka ruwan shayin wannan kam k'walelen ka ehe.."

Tagumi ya rapka uwa wanda akai ma mutuwa.

*************
Chapter 35 · 0% Book details