← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 63

Sashe 5

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shema'u ma ta murmusa kafin tace "I love you too sweetheart, oya tashi muje mu had'a ice-cream gaba d'aya tareda su Jamal, I know it'll be fun..." Suka mik'e a tare fuskokin su cike da fari'a...

Tsaye suka hangi AT na k'ok'arin barin wajen.. Sajida ta k'arasa da gudu tayi hugging nasa kafin tace "Daddy zamu had'a ice-cream will you join us..?"

D'an d'ago kai yayi yana duban Shema'u da murmushi ya wanzu saman fuskar ta kafin ya dawo da dubansa ga Sajida yace "Baby.... Em.... " 'yan kame kame ya soma yi dai.

Sajida ta rik'o hannunsa tace pls Daddy don't say no, ka tuna tare fah mukeyi da kai da Momy gaba d'aya family... Daddy pls kar ka canza mana don Momy bata nan..." Ta k'arashe cikin rawar murya alamun zatayi kuka.

Kasa ce mata komai yayi sai kallon da yake binta dashi..

Shema'u kuwa ganin haka yasata saurin k'arasowa tana murmushi kafin ta rik'o hannun Sajida, tana mai duban AT take fad'in "Sweetheart karki damu pls understand your Daddy, he still needs some space to recover.... why not muje muyi, since I'm here... " Ko kuma mu fita mu sayo a waje, ni ke da kuma su Jamal, what do you see."

Sajida ta gyad'a kai kafin tace "Eh Aunty Shemah, hakan ma yafi, dama gidan nan is kind of boring... " Shemah ta d'an dara tana rik'o hannun Sajida tana duban AT take fad'in "Dr pls anyi mana izini..?"

D'an gajeren murmushi yayi had'i da gyad'a Kai kafin yace " Yeah... Yeah sure zaku iya zuwa..." Yasa hannu a aljihu yana k'ok'arin zaro kud'i Shema'u ta wani murmusa kafin tace " Em don't worry Dr I can take care of everything, burina shine naga yarana cikin farin ciki...." Daga haka ta dubi Sajida dake kan kallon ta tana murmushi sannan tace "Oya muje mu shirya su Ni'ima suna wajen Momma...." Haka suka jera ita da Sajida suna mak'ale da kafad'un juna suka nufi downstairs suna hira gwanin sha'awa.

AT ya bisu da kallo har suka b'ace ma ganin sa, tabbas har ransa yaji dad'in abinda Shema'u tayi. For the first time da yayi murmushi mai tsawo tun bayan mutuwar matar sa... Sauk'e deep breath yayi kafin yaci gaba da taka matakalan.

**************

"Hajiya fah zanyi latti." Ta fad'i baki a ture.

Tab'e baki Hajiya tayi kafin tace "Aiko babu yanda zakije sai kin kamo min arewa tonti po (Arewa 24), Yo shi wannan malamin naku baisan kin girma bane, k'irji sur nono yace zai na dukan zagada zagadan 'yanmata haka inyi...."

"K'wafa Maryama tayi kafin ta kuma turo baki tace "Nikam wllhi Hajiya ki daina irin wannan maganganun don Allah kar watarana bakin ki ya sub'uce kiyi a gaban Uncle."

Hajiya ta sake baki da hanci tana duban ta kafin tace "Tooh, auho wato gaskiyar ce bakiso a fad'i inyi, toh ai sai kuje yayita lallasa maku duka zagada zagadan 'yammata daku, inji Ma'awuya ne d'an gidan Laminde, me wuya uwa Mark'en lema, ni Fatsuma banma san sanda yaron yayi karatu ba wai har ya zama Malami, imm abun babu wuya, girman d'an mutum..." Ta k'arashe tana goga aswakin ta a hak'waran ta..."

Marayama dai bata kuma tanka ta ba har saida ta gama had'a mata talabijin d'in kafin ta mik'e ta d'au jakar makarantar ta saman kujera... Ko sallama batai ma Hajiya ba ta nufi k'ofa.

Hajiya ta bud'e murya tace "Bakya amshi kud'in istira'in ba, ko fushi ne kikayi... Haba Maryamu Daso, haba ta gaban goshin Hajiya... Yaki abinki, ungo zo ki amsa..." Ta shiga sunce bakin zaninta tana k'ok'arin zaro kud'i.

Fozewa kurum Maryama tayi a wajen still bakin nan a ture, kaman bazata dawo ba sai kuma ta dawo cikin parlorn, tasan idan bata tsaya ta karb'a ma ba k'aramin aikin Hajiya bane ta bita har makarantar ta kai mata tunda a unguwar ne.

"Yauwa Maryama d'iyar albarka, bak'a mai farin zuciya, fitilan gidan Hajiya.... Amshi abinki.. " Saida Hajiya tasa Maryama ta dara, idan tana mata wannan kirarin dole takan yi dariya, ba ita kad'ai bama, harta AT yakanyi dariyan draman Maryama da Hajiya.. Musamman idan Maryama ta dage da fad'in ita ba bak'a bace wankan tarwad'a ne... AT yakance babu wankan tarwad'a a kaloli, daga bak'i ne sai fari... Idan Maryama tayi fushi toh haka Hajiya zata salle AT tass dukda ita Hajiyan ita ta kawo zancen... Yakanyi murmushi yace " Maryama ta Hajiya, ba'a shiga tsakanin ku.

Sauri sauri take tafiyar nata don kuwa already tayi latti kam gashi Malam Mu'awuya nada karb'an hadda, gashi nata Ya taru don tunda akayi rasuwar nan bata samu ta bayar ba. Kaman daga sama tajiyo horn kaman za'a had'e da ita a markad'e. Gajeren tsaki tayi gamida matsawa gefe.. Nan fah taji horn d'in ya kuma biyo ta... A hasale ta juya zatayi masifah ganin mak'ocin su ne yasata fasa masifar, ta sakar masa murmushi a tak'aice kafin tace " Amma Buzu wllhi ka d'auki hakki na, yau kuwa da kasha masifah don wllhi a k'ule nake.

Buzu, matashin sauri irin k'wara d'in Kanon nan dake zaune cikin motar sa k'irar Camry Anaconda yayi murmushi kafin yace " 'Yar kunama ba, ai ta nan kukafi kauri, masifa ba... Yanzu dai shigo na kaiki islamiyan don wllhi yau kam kinyi latti, yanzu na wuce gate d'in islamiyar naku naga sai jibgan 'yan latti ake."

Idanun Maryama sukayi rau rau kafin tace "Buzu don Allah da gaske kake, wayyo Hajiyata wayyo Ummita, wai da gaske kake har an tsare latti.."

"Kindai san haka kurum bazan sharara maki k'arya ba.." Ya fad'i yana taje sumar sa da k'aramar cumb wanda dama d'abi'ar sa ce....

Toh kodai ta shiga Buzu ya sakata ne, tunda ko wani minti ya shud'e yawar dukan ka ne ke k'aruwa. ... Buzu kuwa ganin ta tsaya tayi jigum tana tunani yasa sa mik'a hannu ya bud'e mata front seat...

Hancin motar sa tana karyo kwanan ya hangeta tana k'ok'arin shiga wata mota... K'irjinsa ya yanke ya fad'i, baisan sanda ya k'ara wuta wa motar nasa ba ya shigo layin cikin sauri.

*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘

05

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Cak ta tsaya sai faman muzurai take ganin AT na zuge glass d'in motar sa.

Fuska babu walwala yake duban su, itakam Maryama tunda Aunty Aysha ta rasu tayi noticing wannan canzawan da Uncle yayi, sam duk SHAK'UWAR dake tsakanin su a baya yanzu babu ita, kai gaba d'aya ya canza ya kuma zama miskili na k'arshe, magana ma ba kasafai yake yinta ba har sai ta zame masa dole.

"Emm barka da yammaci Dr." Cewar Buzu had'i da d'an sunkuyar da kansa.

Tsaf AT ya gane Buzu, yaron layin ne wanda yake tunanin courting Maryama yake, domin so tari yakan gansa har gidan Hajiya yana shiga ya gaishe ta. Saida ya d'anyi still kaman bazai amsa ba sai kuma yace "Barkan ka." A tak'aice.

Maryama kam k'irjinta ne keta faman lugude. A hankali ta bud'e murya tace "Uncle sannu da zuwa."

D'an dubanta yayi kafin yace "Ya baki tafi islamiyan ba kika tsaya a nan."

Maryama ta kuma rungume K'ur'anin ta dake rik'e hannun ta kafin tace "Uncle dama latti nayi shine Haris yace bari ya saka ni." _Haris shine asalin sunan Buzu._

Kallon Buzu AT yayi kafin yace "Kana iya tafiyar ka ko, zan kaita."

Buzu ya d'an murmusa had'i da sadda kai kafin yace "Toh Dr babu matsala, Allah Ya taimaka." Maryama sai k'yafta masa idanu take kan yayi ta'aziya ma AT.

Har ta zaga mazaunin mai zaman banza zata shige ta jiyo muryan Buzu yanai ma AT ta'aziya... Still babu walwala saman fuskar sa haka ya amsa wa Buzu.

Kai tsaye Buzu gidan su ya gangara yayinda AT da Maryama suka d'au hanyar islamiya.

Cikin tsanaki yake driving d'in idanun sa naga bisa kwalta. Gaba d'aya sai ji tayi she's not comfortable, ta fi saba da wasa da dariyar da suke a baya, sam bata jin dad'in wannan changes d'in nashi, tausayin sa na rashin matar sa kuma uwar 'ya'yan sa ya kuma rufe ta. Muryar sa ne ya katse ta sanda yake fad'in "Maryam ba na hanaki shiga motar saurayi ba ko wani iri ne?"

Maryama tayi shiru tama rasa masar da zata basa.... Jin ta soma 'yan kame kame yasa shi ci gaba da fad'in "Kar ki sake attempting shiga motar kowa idan dai bana gida ba kinji, komin rashin nisar wajen da zaku je."

Gyad'a masa kai tayi kafin tace "Bazan k'ara ba Uncle insha Allah, dama yanzun ma tsoron duka nake shiyasa zan shiga ya rage min hanya."

AT ya d'an juyo ya dubeta yanda tayi maganar cike da tsoro, shakka babu tsoron dukan take ji. Bai kuma fad'in komai ba har suka iso k'ofar Makarantar. Yana gama parking ta bud'e k'ofar ta sauk'o cike da tsoro, ga wasu Malamai kuwa sai tsaron latti suke.

Ga mamakin ta sai ganin AT tayi ya sauk'o ya nufi Malaman, bayan sun gaisa bata jiyo maganar da ya masu ba, kawai dai ta hangi fuskokin su sai murmushi suke suna girgiza kai alamun babu komai.

Juyowa yayi yanda ya barta nan tsaye, itama shi take duba.... Tana jiyo muryar Malam Kabiru yana fad'in "Maryama kizo ki shige ai ke baki latti sai ta b'aci."

Da murmushin ta take kallon AT dake k'ok'arin bud'e marfin motar sa tace "Na gode Uncle."

Murmushi kawai shima ya mata kafin yace "Allah bada sa'a koh." Daga haka Ya shige motar sa ya bar wajen.

***************

Gidan da yaga Haris ya shige nan ya k'arasa yayi parking motar sa a k'ofar gidan, kafin ya bud'e motar sa ya fito.. Kaman daga sama saiko ga Buzu ya turo gate ya fito.

AT ya tsaya yana karantar yanayin yaron sosai da yanayin dressing d'in sa..

Buzu ya fad'ad'a murmushin sa yana mai k'arasowa wajen AT dukda Charsman AT ya cika masa idanu.

AT ya d'an Saki fuska kafin ya mik'a ma Buzu hannu sukai masabaha. Kaman babu mai cewa komai sai kuma AT ya katse shirun da fad'in "Malam Haris ko."

Buzu ya gyad'a kai yana murmushi alamun eh haka.
Chapter 5 · 0% Book details