← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 63

Sashe 44

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta k'araso tana goge fuskarta da yayi jazir sabida kuka kafin ta dafa kafad'an Sajida tace " Sajida kuyi hak'uri kuyi mata addu'a shine kawai gatan ta a halin yanz.... .." kasa ci gaba da maganar tayi sabida kuka da ya kuma b'alle mata. AT kam Bai iya ce mata komai ba sai kallo da ya bita dashi, yana rungume da 'yan 'ya'yansa lokaci guda tunanin Maryama da tausayin ta na ratsa zuciyarsa.

K'unshe bakinta Shema'u tayi saika rantse irin kuka ne yaci k'arfinta kafin ta haye sama ta d'au wayarta hawaye na bin k'uncinta take wata kafiran murmushi, waya suka somayi da Hisham ta sanar dashi abinda ke faruwa, sosai ya razana da hidiman Shema'u, amma mutuwan Maama Juu da Spider shine rufin asirin sa shima. Suna gama waya dashi ta soma murmushi tana tunanin kiran Hajiya ta mata breaking news d'in cikin salo na makirci da kashe jiki, tabbas idan ta kira Hajiya tana kuka k'ila ta soma saye zuciyar jarabebbiyar tsohuwar, kawar da ita a doron k'asa bayan ta saye zuciyarta sai yafi mata sauk'i.

Cikin kuka Shema'u ta kira Hajiya ta sanar da ita abinda ke faruwa, yanda take kuka harda shesshek'a saika rantse har cikin ranta iyakacin gaskiyarta kenan..

Hajiya gaba d'aya jinta take tamkar a wata duniyar, bakinta ya kasa furta komai, kwanyarta na barazanar juyewa. Meke faruwa dasu ne, Aysha bata jima da mutuwa ba, yau b'arayi sun far masu sannan GA wani tashin hankalin kuma, anya ba wani laifi sukayi ma Allah yake jarabtansu haka ba... Cikin sauri ta furta "Astagfirullah" domin kuwa ikon Allah Ya wuce gaban wasa, shi d'in kunfa yakun ne, sannan fad'insa ne _Kullu man alaiha faan_ tabbas Allah baya k'ara ma rai tsawon kwana idan lokacinta yayi d'if zata tafi koda ciwo ko babu ciwo... (Allah ka bamu k'arshe mai kyau, ameen.)

Hawaye suka shiga gangaro ma Hajiya, bata ma san me zata soma fad'i ma Maryama ba. Ta sakata gaba ta tsura mata idanu hawaye na gangaro mata...

Maryama daketa sararan mafarkai don tunda b'arayin nan suka tab'a mata jikinta bata dawo normal ba, baccinma satan ta yayi, farkawa tayi taga Hajiya ta baza tagumi tana kallonta tana hawaye..

Cikin sauri ta mik'e ta isa gaban Hajiya ta durk'usa saman gwiwoyinta tana tambayanta "Hajiya lafiya...? Hajiya sun maki wani abu ne, Hajiya meke faruwa... Don Allah ki min magana...?"

Hajiya bata iya amsata ba sai sabon kuka da ya kuma b'arke mata.

Hawaye suka soma bin k'uncin Maryama sanda taci gaba da fad'in "Hajiya don Allah ki fad'a min meke faruwa, Hajiya kukanki tashin hankali ne a gareni, wani abune ya sami su Uncle, b'arayin nan sun harbi su Uncle da Ya Ashfaq koh, Hajiya ki fad'a mun? Don Allah ki fad'a min.

Kallon tausayi Hajiya ta bita dashi kafin ta rungumeta sosai tana mai ci gaba da kuka, kaman wacce aka sinkaya kuma sai d'ago kafad'un Maryama tayi kana tace "Tashi, tashi muje... " Maryama da har lokacin kuka take ta mik'e tana zura hijabi had'i da d'auko slippers d'inta dana Hajiya wari-wari batama san ta had'a ba...

Ilu ya tsorata sosai da ganin yanayinsu, duk tambayan da yake masu babu wanda ya sami zarafin amsa sa cikin su, gaba d'aya basu san yanda suke jefa k'afafun su ba.

Ilu cikin sauri ya k'arasa gate d'in su Buzu ya shiga bugawa ganin Hajiya da Maryama sun nufi bakin kwalta suna neman abin hawa ga dare ya ja....

Mai gadinsu yana fitowa Ilu ya shaida masa halin da ake ciki.. Cikin sauri ya nufi sashen Buzu ya tada shi.

Shi kansa Buzu ya razana da lamarin, motar sa ya d'auki ya nufi yanda su Hajiya ke tsaye. Cikeda tashin hankali yake fad'in su shigo ya kaisu.

Gaba d'aya suka d'unguma cikin motar Buzu, sai basu baki yake dukda baisan musababbin abinda ya faru ba, lokaci guda zuciyarsa ta cika da firgicin abinda Shema'u ka iya yi don cimma burinta, sam Shema'u ba abin yarda bace, sosai yake tsoron kaidinta...

Hajiya rik'e da Maryama suka nufo cikin gidan, Ashfaq dake tsaye daga waje yana hangosu gabansa ya yanke ya fad'i. Su kuwa sam basuma lura dashi ba suka nufi cikin parlorn...

Abinda idanunsu ya gane masu sai yafi d'aga masu hankali, AT rungume da yaransa Jamal da Ni'ima yayinda Sajida ke rungume cikin k'irjin Shema'u gaba d'aya basu a hayyacin su, hankalin Maryama bai gama tashi ba saida ta hangi mace kwance a k'asa an lullub'e kanta.. K'irjinta yayi wani irin bugawa. Batasan sanda ta furta "Ummmiiiiii!!!!!" da k'arfin gaske.

Wanda hakan ya janyo hankalin su AT suka kai dubansu ga bakin k'ofa yanda Maryama da Hajiya suke a sandare.

A guje ta tafi kan gawan ta yaye rufin fuskar, jinin da ta gani sai ya kuma d'aga mata hankali... Take ta zube a wajen sumammiya....

A tamanin AT yayi kanta yana jijjigata yana kiran sunata inaaa bata bud'e idanu ba... Ya mik'e ya nufi saman dinning ya suri goran ruwa ya dawo ya durk'usa nan gabanta yana yayyafa mata gaba d'aya ya rikice..... Shema'u sai uwar harara kurum take watsa masa yanda ya daburce sabida Maryama.

A hankali ta soma bud'e idanunta kafin ta mik'e ta kwanta saman Maama Juu tana kuka mai tsuma zuciya.

"Umm.... Ummi, Ummi na ki tashi don Allah, kar ki tafi ki barni, Ummi kince min kowa namu sun mutu ke kad'ai kika rage min meyasa kema kika tafi kika barni, Why Ummi, why....." kuka ya kuma kufce mata..

Shema'u ta k'arasa tana k'ok'arin janye Maryama tana bata baki, Hajiya ta k'arasa kan Maama Juu tana hawaye take tuno tun farkon had'uwar su har zuwa rana mai kaman ta yau... Addu'a ta shiga jero mata hawaye na bin k'uncinta..

AT ya dubi Shema'u ya mata alama ta haura da Maryama sama. Babu musu ta gyad'a masa kai kafin tayi yanda yace..

Suna tafe take fad'i ma Maryama "Ki dinga karanto innalillahi kinji, ki daina kukan nan kinji koh..."

A wannan bak'in dare haka akayi kwanan k'unci tareda tarin alhini a gidan Dr Ahmad Tahir.... Allahu Akbar, dukkanin mai rai mamaci ne, 'Yan uwa mubi duniya a sannu.

Washe gari aka mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Hisham da Ashfaq harma da Buzu tareda su akayi komai.

Maryama da Hajiya dole suka tare gidan AT. Gaba d'aya Maryama ta zama abin tausayi, harta Sajida tausayinta take, AT kuwa shiga goma fita goma sai ya tambaya taci abinci kuwa? Kacaukam hankalinsa na kan Maryama da yaransa musamman Maryama data kasance d'iya ga Maama Juu.

A b'angaren Shema'u kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba ganin yanda AT ke ririta Maryama yana sakata a gaba taci abinci na dole, koda tace masa ya bar mata kulada Maryama a hannunta bai kula zancen nata ba. Yana ahigowa gida daga wajen 'yan karb'an gaisuwa d'akin Hajiya da Maryama yake nufowa, yaran ma gaba d'aya sun k'aura d'akin. Hankalin Shema'u ya soma tashi, dole tasan abinyi, ga Ashfaq ma kaman competition suke akan Maryama, sabida shid'in ya zama d'an gida wajen Hajiya....

AT da Hisham basu sami zarafin maganar halin da Spider ke ciki ba sai bayan kwana uku. Nan Hisham ya shaida masa aikin Was successful zai iya farkawa nan da wasu kwanaki...

AT ya jinjina kai kurum ba tareda ya furta komai ba.

Hisham sai faman karantar yanayinsa yake kafin ya gyara zama had'i da d'an gyaran murya ya soma fad'in "Tahir kai d'an uwa ne a gareni, a gaskiya bazan zauna ina ganin abubuwa suna faruwa da kai ba nayi shiru ba tareda na maka magana ba. Tahir kanada saurin yarda da mutanen wann zamani, kowa jawosa kake jikin ka, kai da niyyan taimako kake su kuma su cutar da kai, regarding abubuwan da suke faruwa da Family d'inka lately a gaskiya ka bud'e idanunka da kayu kasan waye kake jawowa jikinsa.... Ya d'an ja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Good example mu d'auki wann yaron Ashfaq, from no where yazo shi ka karb'esa hannu bibbiyu ka yarda dashi lokaci guda har ka had'asa da iyalanka... Tahir ka bud'e idanunka da kayu before it is too late...

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*37*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

D'ago idanu AT yayi yana duban Hisham ba tareda ya iya furta komai ba. Da k'yar ya k'ak'aro murmushi kana yace "Hisham kenan ni da ka ganni ban tab'a yarda wani d'an Adam zaimin abunda Allah baiyi mun ba, walau ta cutarwa ko akasin haka. Duk abunda kaga ya sami bawa a rayuwa toh fah ka tabbata Allah Ya hukunta faruwan hakan. So bazan d'aura blame d'in abinda ke faruwa dani ga wani ba. Ashfaq yanada matuk'ar mahimmanci ga rayuwata, kar ka mance a sanadin sa Allah Ya tsare Hajiya da Maryam, Ashfaq alkhairi ne a garemu. So pls ka daina irin wad'an nan maganganun saikace ba musulmi ba, ansan musulmi da yarda da k'addara a duk yanda tazo masa, iyakaci muyi addu'an Allah Ya bamu jarabawar da zamu iyaci a rayuwa."

Hisham ya k'ura ma AT ta mujiya yana mamakin k'arfin imani irin na AT. Gyara zama ya kumayi kafin yace "Tahir bank'i maka ba, amma kai baka ganin zuwan Ashfaq nada alak'a da abubuwan da suke faruwa, ka sake tunani Tahir, me ma ya kai Ashfaq gidan Hajiya da daddare idanba shi ya tsara zuwan b'arayin ba. I'm not saying kayi firing nashi a wajen aiki, but ka saka masa iyaka da iyalanka... Shawari ce..." ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa tsaye.

D'an jim AT yayi kafin yace " I'll think about it, amma ka sani zuwan Ashfaq gidan Hajiya baida alak'a da b'arayin da suka shiga gidan hasalima zuwan nasa alkhairi ne..." ya k'arashe maganar nasa yana mik'a ma Ashfaq hannu sukayi sallama. Kafin Hisham ya nufi ma'ajiyar motar sa yayinda AT ya nufi cikin gida yana mai tunanin maganganun Ashfaq.

Koda Hisham ya labarta ma Shema'u yanda sukayi da AT a waya sosai hankalinta ya tashi, kenan tabbas AT bazai rabu da tsinannen yaron nan ba? Lalallai kuwa gwara tasan abinyi tun wuri.

Abu guda da ya faranta mata rai shine, Hisham ya sanar da ita yama Spider wata allura wanda a hankali zai mace ba tareda kowa ya fahimta ba, wato slow dying zaike yi.

***************
Chapter 44 · 0% Book details