← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 63

Sashe 17

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani uban tsaki Hisham ya buga yana wani huci yake buga kujera yana furta "Dammit! Damn that Bastard." a hankali ya furta "Ashfaq" yayi wata murmushi kafin yace "That imbecile bazai bari na cimma burina ba muddin yana asibitin, I really need to get rid of him." buga kujera ya kumayi yana mai ci gaba huci.

*************

"Haba giwar mata, yanzu bazaki bari na k'ara koda round guda bane. " Yayi maganar yana shafa tuleliyar tumbinsa.

A d'an yatsine Shema'u ta kallesa tana mai ci gaba da jan zip d'in rigarta take fad'in "My Alhaji kasan uzuri na, ka fahimce ni don Allah. Nai maka lak'awari gobe kafin ka tafi zan zo."

Murmushi yayi ya shafi gefen fuskar ta kafin yace "Ai na yarda dake d'ari bisa d'ari tauraruwata." yasa hannu a bedside ya ciro car keys da Check ya shafawa Shama'u a fuskarta..

Ware idanu tayi batasan sanda tayi wani tsalle ta haye kansa tana murna ba.

Kai tsaye gidan Hisham ta wuce da motar ta ajiye a can, bata sami Hisham ba don suna asibiti dasu AT suna fixing issue na magungunan.

***************

*Bayan kwana biyu*

Jinta take cikin kud'i, suna zaune itada Hisham a parlonsa aka shigo da Buzu idanunsa a rufe.

Mik'ewa Hisham yayi ya mata alama da idanu kafin ya shige d'aki.

Murmushi ta sakar masa kafin ta masa alama da idanu itama.

"Ku bud'e masa idon." Ta fad'i sanda take zama bisa sofa.

************

Ashfaq ne zaune saman sofa a 'yar k'aramar apartment d'insa, k'aramar madubi ya d'auko ya shiga cire makeup d'in da yakeyi a fuskar sa na b'atar da kamanni... Kaman daga sama yaji wayarsa na ruri.

Ganin sunan da ya bayyana jikin screen d'in yasa sa sakin murmushi kafin ya d'aga wayar yana fad'in "Assalamu'alaiki the most amazing mother on earth."

*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*13*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Shiru Ashfaq yayi yana sauraren mahaifiyar sa daga d'aya b'angaren. A hankali ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ya soma fad'in "Mummy don Allah ki daina saka ma ranki damuwa I'm very well here, yanzu ne zansan rayuwa da kuma k'alubalen da ake fuskanta a cikinta, sannan Mummy hakane kawai zaisa na sami wacce take sona tsakani da Allah ba don kud'i da muk'amin mahaifina a gwamnati ba, Mummy idan na zauna a gida I'm quite sure Daddy arrange marriage zaimin kaman yanda suka saba shida abokan siyasar sa da kasuwancin sa."

Daga d'aya b'angaren Mummy ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Haidar, kana ganin hakan shine maka mafita. Idanma asibitin kanka kake so ko ni nan zan gina maka shi but pls ka dawo gida Son, I'm afraid to lose a child again."

Shiru Ashfaq ya kuma yi zuciyar sa na tafarfasa yana mai tuna har abada k'wandala da ta fito daga wajen mahaifin sa bazai kuma anfanuwa da ita ba sabida k'azanta irin ta dukiyar, if only zai iyar sanar da mahaifiyar sa abinda ya gani da ya sanar da ita, amma bashida hali..... Muryan Mummy ta kuma katse masa tunani da fad'in "Daddyn ka yayi fushi sosai da kai tunda ka watsa masa k'asa a idanu ranar da ya kamata ace ya kasance ranar bikin ka, yace sam babu shi babu kai muddin baka dawo ka nemi yafiyar sa ba kuma ka aminta da auren Fairuza ba."

D'an murmushi yayi kafin yace "Mummy pls ki daina damuwar nan kinji, it shall all pass, zan dawo amma ba yanzu ba, na fad'a maki har sai na sami macen da take sona ba don kud'u muk'ami ko kyau na ba. Sannan ina so na tashi tsaye ma rayuwata banaso na kasance kullum dogaro da mahaifina nake."

Jinjina kai tayi tana goge k'wallan da suka zubo mata kafin tace "Shikenan Haidar, kana tare da addu'o'ina a duk yanda kake, Allah Ya maka albarka." Ashfaq ya amsa da Ameen kafin sukayi sallama.

Tagumi ya rafka idanunsa sunyi jajazir a duk lokacin da ya tuna abinda ya gani a d'akin sirrin mahaifin sa, shakka babu k'ok'on kan tilon k'anwarsa ce Nabila, shin yaya Mummy zatayi idan tasan Daddy shi yayi tsafi da Nabila, Nabila ba mutuwa tayi kawai ba tsafe ta akayi daga ita har mai rainonta, shin yaya zataji idan tasan tsafi ne yakai Daddy matsayin da yake na mataimakin shugaban k'asa a yanzu...... . Ya tuna sanda zai koma makarantar kwana k'arshen ganinsa da Nabila kenan tana 'yar k'aramar Baby. Share wasu hawayen ya kumayi kafin ya furta "Zanyi aiki ba tareda taimakon ka ba Daddy, bazan huta ba har sai na had'a kud'ad'en da nasan zasu isheni shari'a dakai."

**************

Fincika Buzu yayi yana fad'in "me kike nema a wajena, wacece ke.?"

Kafiran dariya Shema'u tayi kafin tace "Relax boy, kai baka sanni ba, amma ni nai maka farin sani. Sunan ka Haris amma anfi saninka da Buzu a layin ku, mahaifiyar ka mijinta ya mutu ya bar mata ku biyu, kaida yayar ka dake auren tsohon sanata Kamilu Ashir, tun kuna k'anana mahaifanku suka dawo k'asar nan da zama, amma asalin ku 'yan k'asar Yemen ne..... A iya sani na mijin yayar ka shike d'awainiya daku don harta motar da kake shiga shi ya saya ma mahaifiyar ka..." Ta d'an ja fasali kafin taci gaba da fad'in "Tooh gashi yanzu Kamilu Ashir ba Sanata mai ci bane, an sauk'esa shi kansa ya fad'a a kwata taimako yake buk'ata. "..... Kallonta kawai Buzu yake baki sake cike da mamakin yanda akayi tasan abubuwa da dama a gamedashi, ko da yake ba abin mamaki bane, k'ila itama d'aya ce daga cikin irin matan manyan mutane da suke neman sa ya biya masu buk'atunsu su basa kud'i, amma kuwa ai da ba sai tabi ta hakan ba tunda dama sana'ar sa ce....

Kaman tasan tunanin da yake, ta k'araso gabansa tana murmushi kafin tace "Kana mamakin nasan abubuwa da dama gameda kai ko.? Toh ba a nan ta tsaya ba, nasan kai d'in matan manya suna nemanka daga nan har Abuja, basai na lissafo maka su ba tunda kasan na sani, sannan duk club d'in garin nan babu yanda bakayi k'aurin suna ba, while on the other hand a unguwar ku kana acting innocent, kana nuna kai yaron arziki ne kuma na kowa, da wannan d'abi'a ka saye zukatan mutane da dama ciki harda Maryama da Hajiya Fatima mahaifiyar Dr Ahmad Tahir Shattima. Am I right?" ta k'arashe tana wata munafukar murmushi.

Zufa ne ya shiga keto ma Buzu ta kota ina, ina bazai bari a b'ata tsakanin su da Maryama ba ko a bak'antasa a idanunta da na Hajiya ba.. Don kuwa son Maryama yake da gaske bada wasa ba..... Cikin sauri ya soma girgiza kai baki har na rawa yake fad'in "Baiwar Allah don Allah wacece ke, sannan me kike nema a wajena, pls ki fad'a min ko meye zan maki shi amma pls don't ruin my reputation especially a idanun Maryama da Hajiya, pls kar ki b'ata min suna a idanun su." ya k'arashe yana d'aga mata hannu bibbiyu alamun rok'o.

Murmushi Shema'u tayi tana shafa fuskar Buzu tamkar tab'ebb'iya take fad'in "Are you sure Baby boy, are you zakayi duk abinda na umarce ka, I can even pay you sannan na b'oye maka sirrin ka, no one will learn about it."

Buzu dai kallonta kawai yake cike da tsoro, don kuwa duk taurin kansa bai tab'a gamuwa da macen data firgita sa ta basa tsoro irin Shema'u ba.

D'an yatsanta ta saka ta shiga gyara masa kwancecciyar sumar sa tana fad'in "Aikin me sauk'i ne Malam Buzu." Wayarta ta latsa hoton Sajida ya fito cikin screen d'in kafin tace "Ka ganta, isn't she sweet, yeah tanada kyau da k'uruciya, tafi sugar Mummies d'in da kake spending nights dasu. Ko ba haka bane.?"..... Jin yayi shiru ya kasa amsata yasata juyowa tana dubansa yanda yayi mutuwar zaune yana bin hoton Sajida da kallo.

Murmushi tayi kafin tace "Oh... I know you'll like her Boy, she's every Man's type right." Ta k'arashe tana d'aga masa gira alamun tambaya.

Girgiza kai Buzu ya soma kafin yace "Wannan ai Sajida ce, 'yar uwan Maryama ce kuma d'iyar Dr Tahir ce, I'm afraid but I can't mess with her."

Shema'u ta tuntsire da dariya kafin tace "Ashe kai k'aramin d'an iska ne kuma bakayi shirin yin bariki ba idan har akwai wanda yake baka tsoro."

Kamo fuskar Buzu tayi suna facing juna kafin tace " The girl is madly in love with you, she's the reason why you and Maryama are in good terms.... Zan baka mota da kud'i, just love her, make her feel like she's a Queen, daga farko, daga k'arshe inaso kayi ruining d'inta, ka koya mata zuwa club, if possible ka koya mata shan duk wani miyagun k'wayoyi, sannan daga k'arshe get her pregnant."

Ganin yayi sakare yana kallonta yasa ta d'auko key d'in sabuwar motar da Alh Aminu ya bata ta shiga shafawa a fuskar Buzu tana wata mayaudariyan murmushi...

**************

"Oyoyo Ummi nayi missing d'inki da yawa." Ta fad'i sanda ta tafi ta rungume Ummin nata.

Hannunta ta rik'e kafin tace "Oh wato Maryama bazaki girma da d'ale jikin mutane ba."

D'an turo baki tayi kafin tace "Ai wllhi Ummi idan dai keda Hajiya ne sam bazan daina d'ale jikin ku ba....... Tsulum Hajiya dake zaune saman Sofa tana wurga d'anwake a baki tace "Yo idan na aurar ki ai saidai ki d'ale jikin mijin."

Maama Juu dai murmushi kawai take yayinda Maryama tayi kicin-kicin da fuska tace "Waike Hajiya da anyi magana sai kice wani aure, wllhi nidai koma auren nayi tareda zamu tafi gidan mijin."

Hajiya ta dara kafin tace "Aiko ga kutiri na ga naki dole mijin ya gina mini nawa d'akin inko ba haka ba saidai ya kora mu don babu wanda ya isa ya rabamu." Gaba d'aya sukayi dariya kafin Maama Juu ta zauna tana gaida Hajiya sanda Maryama ta nufi madafi kawo ma Umminta abin tab'awa.

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*14*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
Chapter 17 · 0% Book details