← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 63

Sashe 14

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryan AT ta jiyo yana fad'in "Regarding what happened earlier, kiyi hak'uri kinji."

Saurin girgiza kai tayi kafin tace "Uncle ni ce mai laifi, ni ya kamata na apologizing, dan Allah kayi hak'uri uncle, I know you still having a hard time..... Kayi hak'uri kaji Uncle."

Baice komai ba sai tsareta da idanu da yayi, abubuwa da dama ne suke yawo a kwanyar sa wanda bazai ce ga ma'anar su ba... Muryar Maryama ya jiyo tana fad'in "Uncle barin kawo maka ruwa."

Bai sami zarafin amsa ta ba, sai mik'ewa da yayi ya d'an matsa gefe yana amsa wayar Dr Ashfaq, matashin likitan da yake so ya sami gurbin aiki a asibitin AT. AT ya yarda da qualification d'in Ashfaq tunda sukanyi aiki tare a TH, duk matashi ne da bazai wuce 32 ba amma yanada k'wazo da sanin aikin sa, shiyasa samun aiki bazai masa wahala ba a ko ina, shi kansa AT yaji mamakin yanda Ashfaq ya nace saida shi zaiyi aiki, koda yake ta yuyu hakan nada alak'a da sabon da sukayi na yin yawancin ayyuka tare a Teaching Hospital.

Shigowar Hajiya yayi dai-dai da ida wayar sa. A tare suka jera suna shigowa da Hajiya, sai faman hura hanci take, tana a'a'amsa shi a ciki-ciki, ita a dole fushi take dashi, don Hajiya tak'i jinin d'abi'ar AT na sakalta yara da yake, a cewar ta d'abi'ar yahudu ne.

A verandan suka yada zngo, ta kwab'e hijabinta tana fifita dashi lokaci guda tana rangad'a kira ma Maryama.

K'arasowa Maryama tayi had'i da ajiye trayn ruwa gaban AT dake faman gaida Hajiya tana amsa masa a ciki.

"Uncle ga ruwan." Ta fad'i sanda take ajiyewa.

Murmushi ya d'an sakar mata kafin yace "Sannu Maryam, na gode ko."

Maryama na murmushi ta juya tanai ma Hajiya sannu da dawowa. Hajiya ta amsa kafin ta warware k'ullin bakin zaninta ta ciro k'ullin goro a leda ta mik'a wa Maryama tace "Ungo wanko min su yanzun nan." Tayi maganar fuskar nan tamau, a tare AT da Maryama suka kalli juna, sarai sunsan don AT yaji haushi Hajiya tayi haka. Ko ta kansu Hajiya bata bi ba ta ciro karan aswakin ta ta soma goga hak'waran ta.

AT ya gane kallon da Maryama take masa na tambaya ne, don dama sun saba 'yar haka, watarana yakan k'yafta mata idanu, ko yabi bayanta yace ta fad'awa Hajiya goron dakwai tsutsa. Amma yau kam sam babu fuskar wasa a tattare da Hajiya, don haka gyad'a ma Maryama kai yayi alamun ta wanko goron. Saida suka sakar ma juna murmushi kafin ta wuce.

Maryama tana wucewa AT ya tattaro nutsuwar sa ya maida su ga mahaifiyar sa.

Da 'yan kame-kame ya soma yana mai bata hak'urin abinda ya faru safiyar yau.

Shek'ek'e ta kalle sa kafin tace "D'an boko mai hak'waran ABCD, naji ai na hak'ura tunda ba yau ka saba irin hakan ba. Toh nidai ka jini da kyau, bazan zauna inaji ina gani su susutaka ba, su gurb'ata maka tarbiyan yara, don Kulu da wannan d'iyar tata, mai fuska kaman an bad'a wa agwagwa toka ba tarbiya bane dasu, dama zakkan kenan Aisha kuma ta tafi abinta. Don haka dole su tattara su tafi, don wllhi basuda muhalli a gidan ka." Ta k'arashe dai-dai sanda Maryama ta aje mata plate d'in goro kafin ta kwashi books d'inta ta shige ciki.

Saida AT ya sauk'e deep breath kafin yace "Hajiya, kiyi hak'uri don Allah, ki duba halin da yaran suke ciki, sannan kiga yanda Sajida tayi reacting d'azu, idan na kuma zuwa masu da wannan maganar Allah kid'ai yasan abinda zatayi. Hajiya zaman Shema'u a gidan sosai yake taimaka wa yaran... Dama so nake idan abin ya bar jikkunan su, da wai sai su koma, but for now Hajiya ki d'an yi hak'uri don Allah. Ki mana nida yarana, Don Allah Hajiya..." Ya k'arashe cikin sanyin murya.

"Attahiru bazan zuba ido Kulu da d'iyarta su d'aid'aita min ku ba kaida yaran ka.. Idan kaga na d'aga maka k'afa toh fah Uwa ta gari ka kawo wa yaran nan cikin gidan su, ma'ana Aure kayi."

Kaman sauk'an aradu haka yaji maganar Hajiya, shi take ma zancen aure Matar sa ko wata biyu batayi da rasuwa ba...... Tamkar gunki haka ya d'ago yana duban Hajiya.

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘

*11*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Bakinsa har na rawa yake furta "Hajiya Aure.... Aure fah Hajiya.? Haba, haba Hajiya, Aysha ko wata biyu, kai ko wata guda ma bata cika da rasuwa ba kina min maganar aure.? Hajiya idan wani ne daban yayi maganar nan ba ke ba sai yafi min sauk'i.... Kiyi hak'uri Hajiya amma harga Allah bazan iya aure ba, mace guda nake so gidan duniyar nan kuma ta tafi ta barni ina fatan na had'u da ita a rayuwar da zamuyi gaba... Hajiya don Allah kiyi hak'uri kiyi maganar komai amma don Allah bada aure kiji tausayi na dan Allah kinji." Tamkar k'aramin yaro haka ya k'arashe maganar.

Jikin Hajiya ya d'anyi sanyi, kuma sai yanzu take ganin tamkar ta masa hanzari sosai, amma kam sam bata son zaman Kulu da d'iyarta a gidan Attahiru. Saida ta d'an muskuta kafin tace "Shikenan Attahiru naji bazakayi aure yanzu ba, amma kasa a ranka bazaka tabbata a haka ba, dole wata rana zakayi aure ko don inganta rayuwar iyalanka.. Sannan magana ta gaba shine sam ban yarda wannan zabon ta ringa kai Maryama makaranta ba, idan dreban nasu bai dawo bakin aiki ba ka nemi wani ko kuma kake zuwa da kanka kana kaita. Ka fahimce ni."

Gyad'a kai AT yayi kafin yace "Insha Allahu ma gobe drivern nasu zai dawo, za'a kiyaye insha Allah."

Saida ta jinjina kai kafin tace "Yayi, Allah shi maka albarka."

AT ya amsa da "Ameen Hajiyata, Hajiyar Maryama." Har ransa yake jin dad'in albarkan da Hajiya ke saka masa dukda wani sa'in tanada wuyan sha'ani.

Murmushi Hajiya ma tayi don kuwa sosai take son d'an nata, tunda shi kad'ai Allah Ya mallaka mata.

***************

Washe gari Sajida sam bata wani sake da Maryama ba, sai faman tattamke fuska take. Har aka fito exams Maryama kuwa bata daina bata hak'uri ba.

Fuska a d'aure Sajida tace "Maryama wllhi idan Aunty Shemah ta tafi bazan tab'a yafe maki ba, don kece sila.

Maryama ta murmusa kafin tace "Sajida insha Allah Aunty Shema'u bazata tafi ba, zata zauna tareda ke.. Na kula SHAK'UWA CE mai k'arfi a tsakanin ku.".

D'an tab'e baki Sajida tayi kafin tace "K'warai kuwa, SHAK'UWA CE mai k'arfi a tsakanin mu wanda babu wanda ya isa ya tsinka ta."

Sauk'e ajiyan zuciya Maryama tayi kafin tace "Sajida no matter what happens ki sani I'll always be your friend kuma 'yar uwarki, don Allah kar ki tab'a mance wannan."

D'an kallon ta Sajida tayi don kuwa tabbas akwai Shak'uwa da soyayyan juna tsakanin ta Maryama, basu da shirgin k'awaye sai su biyun su tun tasowar su, saiko wad'anda ba'a rasawa. Tunawa tayi she needs Maryama now more than ever, ta tuna abinda Aunty Shemah ta fad'i mata cewa ta tambayi Maryama ta had'ata da Buzu. Cikin sauri tayi murmushi kafin ta kamo hannun Maryama tace "Hakane 'yar uwa. Nima kiyi hak'uri pls."

Murmushi Maryama tayi kafin tace "Mu k'arasa mazaunin mu..." A tare suka jera suna tafiya kaman babu wani abu da ya shiga tsakanin su, nan suka hangi k'awarsu Fadila Talba ta nufi motar su anzo d'aukar ta, sai faman d'aga masu hannu take alamun sai gobe, suma waving d'in suka mata Sajida ta bud'e murya tace "Fadee don't forget to study hard."

Daga can Fadila tace "Wannan saidai ki gaya ma Maryama allazi boko, tunda bokon ba do or die bane..." Gaba d'aya sukayi dariya don haka nan Fadila take sam babu ruwanta da b'oyo.

Bayan sun zauna a mazaunin su Sajida ta dubi Maryama kafin tace "Maryama waini ya labarin Buzu ne.?"

"Yana nan mana, ko shekaran jiya ma nasha kin gansa sanda kuka ajiye ni. Meyasa kika tambaya. ?"

Shek'eke Sajida ta kalleta kafin tace "Ban gane meyasa na tambaya ba, kaman baki san dalilin da yasa nayita nacin kuke gaisawa da mutunci dashi ba."

Tsaf Maryama ta gane ina Sajida ta dosa, gyara zamanta tayi kafin ta soma fad'in "Sajida wai har yanzu baki mance da zancen Buzu ba, wllhi da na d'auka tsaban k'uruciya ce dai kawai yasa kike son sa."

Murmushi Sajida tayi kafin tace "Lallai da alama har yanzu bakisan menen soyayya ba.

Maryama ta murmusa kafin tace "Aah gaskiya ban san soyayya ba kam amma nasan SHAK'UWA."

"Kinga Maryama joke aside pls, muyi magana ta gaskiya , yanzu yaya za'ayi na ringa had'uwa dashi ba tareda sanin Daddy ba."

"Ban gane ba tareda sanin Uncle ba, since when kika soma b'oye masa abubuwa.. Sajida we're writing our final Exams kiyi hak'uri mu kammala before ki fara ire-iren wad'an nan tunanin, sannan had'uwarki da Buzu a b'oye bashida wani alfanu, idanma auren kike so ai kin kai auren... Na tabbata idan kin gama secondary d'inki Uncle will listen to you, and he'll understand you, na sani mahaifin ki d'an boko ne kuma yana valuing karatu fiye da komai, tunda shi irin iyayyen nan ne da sam basu da matsala, kiga yanda yake daku yaransa very friendly, kai bama ku ba harta nima, pls Sajida karki betraying that trust da yake dashi akanki...."

Gajeren tsaki Sajida tayi kafin tace "Kinsan burin da Daddy yaci min na karatun likitanci, kinsan ban isa na je masa da maganar wani saurayi yanzu ba ko... Toh wai ma aure nace maki zanyi yanzun, kawai dai son shi nake, kinga ai gwara yasan dani tun yanzu gujema kar ya fad'a ma soyayyar wata."

Sauk'e ajiyan zuciya Maryama tayi kafin tace "Amma nidai a ganina ki bari namiji ya fara furta maki kalman so kaman zaifi akan ke ki fara, dukda dai bansan meye so d'inba.

Tsaki Sajida tayi kafin ta mik'a don already anzo d'aukan su, saida ta watsa ma Maryama mugun kallo kana tace "Ke ai naga irin SHAK'UWAR da kikayi dashi, Maryama wai son Buzu kike ne.?" tayi tambayar tana tsareta da idanu.
Chapter 14 · 0% Book details