← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 63

Sashe 53

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ya tabbata basa hangosa kafin ya shige cikin sand'a.

A hankali ya tura k'ofar d'akin ya hangeta tana nan kwance ga mug na tea a gefenta.... Suna had'a idanu gabanta ya yanke ya fad'i..

Ya k'arasa shigowa cikin d'akin kafin ya maida k'ofar ya rufe a hankali.

Kanta a k'asa ta kasa furta koda kalma guda....

Saida ya d'an fuzar da iska kafin ya d'aga mug d'in yaga bata wani sha abin kirki ba..

Bata ankara ba sai gani tayi ya zauna dab da ita, bugun zuciyarta ya k'aru, sarai ya gane ya haifar mata da tsoro amma hakan baisa ya canza position d'in zaman nasa ba.

Fuskar sa babu yabo babu fallasa yace da ita yaya jikin naki.?"

Cikeda tsoro ta d'an matsa gefe kad'an, da k'yar ta lalumo kalamai saman harshenta tace "Da sauk'i..." kana jin yanda tayi maganar zaka gane a razane take...

AT ya kai lallausar hannunsa saman goshinta.... Take ta lumshe idanunta abubuwa da dama suka ziyarceta lokaci guda. Shid'inma hakan ce ta kasance dashi..... Nan yaji zafin jikin nata ya ragu,

B'alle magunguna ya shiga yi yana mik'a mata yace "Oya karb'a ki sha and make sure kin shanye wannan tea d'in..."

Idanun Maryama yayi rau-rau domin idan akwai abinda ta tsana shan magani ne uwa uba allura....

AT ya tsareta da idanu domin yasan halinta wajen k'in magani. D'an gyaran murya yayi ya kaikaito yana dubanta sosai kafin yace "Idan baki sha magani saidai a maki allura... Kina son allura..?" Yanda yayi maganar tamkar da Ni'ima yake magana, yanda ake ma yara idan ana so susha magani...

Baki a ture tana goge hawayenta ta girgiza masa kai alamun a'a.

Yayi nodding kansa kafin yace "Oya toh karb'a kisha idan baki so na maki allura..."

Ganin ta kasa amsar maganin yasa sakin wani numfashi kafin yace "Barin koya maki logic d'in shan magani, just close your eyes and open your mouth..." ita kanta Maryama saida ta d'ago ta dubesa domin gaba d'aya da sigan yara yake mata maganar...

Manyan idanuwan sa ya d'an ware kafin yace "Oya do as I said..."

Runtse idanunta tayi sosai kaman wacce za'a caka ma allura kafin ta bud'e bakinta... AT ya bita da kallo yanda take shivering, harga Allah ta burgesa sosai wanda hakan har saida yasa saki wata silent smile...

A hankali ya jefa mata maganin a baki kafin ya kwara mata da Tea d'in cikin wata irin kasaltecciyar murya yake fad'in "There you go... Good...."

Har saida ya gama bata maganin kafin yace "Oya bud'e idanunki toh an gama....."

Sanda ta bud'e idanunta akan fuskar AT ta bud'e su tsaf, wani irin charisma taga ya kuma mata, cikin sauri ta sadda idanunta k'asa.

Shi d'inma d'an jim yayi kafin yayi gyaran murya yace "Allah baki lafiya koh...." bata iya basa amsa ba saidai ta amsa cikin zuciyarta.

Saida ya kuma kwasan wasu mintoci kafin ta jiyo muryar sa ya soma fad'in "Maryam, I'm sorry about what happened, da ace nasan abunda Ashfaq or whatever zai maki kenan da banyi trusting d'inshi ba from the very beginning, kiyi hak'uri kinji koh, na sani it's not easy to overcome this na sani.... But na maki alk'awari ni Ahmad bazan barki ke kad'ai a dai-dai wannan lokacin ba, together we will go through this... Allah yasa haka shine alkhairi..." Shiru yayi ya kasa ci gaba da maganar yakai dubansa ga Maryama yaga kaman share hawaye take... Bazai iya juran ganinta cikin wannan yanayi ba, baisan yaya akayi ba baisan lokacin da ya janyota ya rungume cikin k'irjinsa ba...

Hankalin Maryama gaba d'aya ya tashi gaba d'aya ta kuma daburcewa, ai tuni ta kuma fashe masa da wani sabon kuka...

AT ya kuma matseta yana fad'in "It's okay, I'm here.." cikin wani irin sigan da baisan ya iya ba... Gaba d'aya ya mance kukan Maryama ta yuyu sabida aurensa takeyi yafi bada zaton sabida abinda Ashfaq ya mata take kukan...

Wani irin sanyi da nutsuwa ne yaji sun dabaibayesa yau Maryam d'insa ce cikin k'irjinsa, a koda yaushe idan yaga tana kuka yakanso rungumarta ya rage mata pain d'in gashi yau Allah Ya basa wannan damar tabbas Allah buwayi ne gagara misali... A hankali ta ringa sakin ajiyan zuciya tana nan rungume cikin k'irjinsa, itama d'in samun kanta tayi k'uncin dake cikin zuciyarta ya ragu sai wani sanyi da ya mamaye zuciyar nata...

Hajiya dake tsaye bakin k'ofa kasa shiga tayi ganin yanayin data gansu a ciki, gaba d'aya jikinta ya mace, a hankali ta Saki labulen ta dawo parlor ta zauna had'i da rapka tagumi,

"Oh d'an yau sai Allah" ta furta a hankali...

A haka Ni'ima ta shigo ta tadda Hajiya bata bi takan Hajiya ba sai kutsawa cikin d'akin Hajiya da tayi tana k'walla ma Adda Maryama kira...

Cikin sauri Maryama ta soma kiciniyar k'wace kanta daga rik'on da AT yayi mata, bai saketa ba har saida yaji Ni'ima na share masa hawayen idanunsa tana fad'in "Daddy kuka kuke yi, Daddy kuma kar ku mutu, Aunty Shema'u tace duk wanda ya mutu zai dawo Monster......" shiru yarinyar tayi ta kasa ci gaba da magana sabida tuno fuskar Shema'u datayi tana fad'in saita yankata da knife idan ta fad'i...

Daga AT har Maryama kallon Ni'ima sukayi cikin rashin gane ina zancen nata ya dosa, saurin rik'ota yayi domin ba komai ya tuna ba illa matarsa Aysha a lokacin da ya rungumi Maryama cikin k'irjinsa...

Jin maganar Hajiya a parlor yasa sa saurin mik'ewa ya rik'o hannun Ni'ima suka nufo parlor don baiso Hajiya ta shigo ta same sa..

Zama yayi kujera mai kallon na Hajiya kafin ya shafi kan Ni'ima yace "Princess oya jekice ma Baaba Delu ta shirya maku kayan ku zamu tafi gida koh, gobe akwai school.." Da sauri yarinyar ta gyad'a kai had'i da ficewa...

AT ya d'an d'ago ya dubi Hajiya yana sosa k'eya ga k'irjinsa dake bugun tara-tara, kaman mai shirin koyon magana haka ya soma k'ak'aro kalamai...

Hajiya ta dakatar dashi ta hanyar d'aga hannu kafin taci gaba da fad'in "Attahiru tun kafin ta kaimu ga ja'inja ka wareware wannan auren wasan yaran da kayi da Maryama kana jina koh, rubuta mata rasidi yanzu ka bani don dama na fad'a maka asaran sadaki kayi."

Da k'yar ya had'o kalamai ya soma fad'in "Haba Hajiya, a ina kika tab'a jin anyi auren wasa, auren Maryama da nayi da gaske nayi, Hajiya Maryama amana ce a hannun mu bai kamata mu dank'ata hannun wanda bazai iya rik'e amanar nan ba, Hajiya ki duba lamarin, kiga dai irin abinda Ashfaq ya mana shima da muka yarda dashi kenan balle kuma wani daban.... Hajiya don Allah ki taimaka min na k'arasa rik'on amanar da Allah Ya dank'a min har i zuwa lokacin da zan bar numfashi... Don Allah Hajiya..." yanda ya k'arashe maganar kaman zaiyi kuka...

"Yo sai na zuba ma roba-robar matarka idanu ta karku gaba d'aya don wannan ban yarda batada cutan zamani ba ehe...."

Yanda tayi maganar yaso bawa AT dariya, sai yanzu ya d'ago nufin Hajiya, Allah sarki har yau batasan Shema'u bane sam da bazata na mata irin zato ba... Banda Hajiya ma da nata tunanin yaushe auratayya zai shiga tsakanin sa da Maryam a halin yanzu, ai tayi k'arama sosai a ganinsa, kawai dai so yake ya koyar da ita soyayyar sa a halin yanzu..

Magiya yaci gaba da mata yana rok'onta har saida Hajiya ta gano tsan-tsan soyayyar Maryama cikin idanunsa kafin ta jinjina kai tace "Shikenan Attahiru naji, bazan tilasta maka sakinta yanzu ba, amma ka sani Maryam babu yanda zataje, tana nan zaune da ni a gidan nan, idan kaga Maryama ta tafi gidanka a matsayin mata toh kuwa babu shakka rasidi ka kawo min na gwajin jinin matarka tabbacin bata d'auke da wata cuta ehe...."

AT ya k'unshe dariyar sa don gaba d'aya yasan characteristics of old age ne ke d'awainiya da Hajiya...

Akan wannan sharad'i Hajiya ta janye maganar sakin Maryama, sannan ta k'arada sai taji daga bakin Maryama idan bata son sa dole ya saketa, AT ya amince da hakan domin shima tsantsan soyayyar sa yake ganowa cikin idanun Maryam tun ba yau ba LOKACI NE dai bai basu damar ba sai yanzu, domin wannan karan kam sam bazaiyi wasa da Damar sa ba, zai nuna mata shi d'in mai k'aunarta ne..

Kafin ya kwashi yaransa su wuce gida saida ya kuma lek'a Maryama, ya samu idanunta a lumshe tamkar mai bacci, a hankali ya sad'ad'a ya sauk'e mata light kiss saman chick d'inta wanda tajishi har cikin zuciyar kafin ya furta "Allah baki lafiya Maryam..." cikin wani irin siga yayi maganar.

Cikin zuciyarta ta sami kanta da amsa masa da _Ameen Uncle_ gaba d'aya jinta take wani iri ta kasa yarda da al'amarin, wai yau ita Maryama da Uncle a matsayin miji da mata... Da gudu ta duro daga saman gado kaman ba itace maras Lafiya ba ta k'arasa gaban dressing mirror tana ganin yanda ya sunbata tana shafa wajen a hankali k'irjinta naci gaba da bugawa... Lokaci guda k'irjinta ya tsinke sakamakon tuno maganar Ni'ima da tayi cewa Shema'u tace duk wanda ya mutu yana dawowa monster, toh Me wannan maganar take nufi??? Zama tayi dirshan bisa gado tana tunanin lamarin.....

Yau gaba d'aya jinsa yake cikin farin ciki, harta Shema'u saida ta fahimci hakan, wani babban abinda ya kuma masa dad'i shine Sajida ta basa hak'uri akan abinda tayi, sannan ta amince masa ya kawo matarsa cikin gidan ko sa'a Ni'ima ce zata zauna da ita kuma zata darajata insha Allah...

Ta kuma sadda kanta k'asa tana saman gwiwoyinta kafin tace "Daddy I'm sorry, kayi hak'uri kaji...."

AT yana murmushi ya mik'e ya d'agota kafin yayi hugging d'inta yace "Thanks for understanding me sweetheart, Allah maki albarka kinji koh..."

Tayi murmushi ta d'an rik'e hannunsa kafin tace "Ameen Daddy" ta juyo ta dubi Shema'u tace "Aunty na gode da kyawawan shawarwarin ki a gareni, Allah Ya barmu tare gaba d'aya."

Shema'u ta murmusa kafin ta k'araso tayi hugging Sajida tace "Anything for you sweetheart, burina shine family d'in nan ta dauwama cikin farin ciki mai d'orewa..."
Chapter 53 · 0% Book details