← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 63

Sashe 48

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka mik'a ma Ashfaq hannu yayi sukayi sallama ya shige gida ya bar Ashfaq a nan yana zullumin yanda zai had'a AT da Daddy suyi magana, yasan komai ka iya rushewa all his plans...

AT yana shigowa gida Shema'u ta kalallame sa tana tambayar sa abinda ke faruwa. Bai sami zarafin mata bayani iyakacin abinda ya fad'i mata shine Ashfaq yana neman auren Maryam...

Kasa b'oye farin cikinta tayi, lallai plan d'inta went perfect, gaba d'aya har wani nishad'i takeji, finally zata rabu da Maryama kuma Ashfaq zai fita daga rayuwar su ta cimma burinta kan iyalan Aysha, tabbas tasan AT bazai juri ganin Ashfaq na aiki a k'ark'ashinsa ba, dole ya ringa tunawa cewa Maryama fah matar Ashfaq ce, duk wanda ya fahimci AT kaman yanda tayi zai hangi tsan-tsan soyayyar Maryama a idanunsa....

Wasa-wasa maganar aure ya kankama, Baffah Yawale da wasu abokansa Dattawa su suka zo nema ma Ashfaq auren Maryam.

Gaba d'aya AT ko maganar ya kasa yi da Maryama, kullum da Hajiya suke zancen, Mummy tayi waya da Hajiya har kusan sau biyu saidai bata sami zarafin gaisawa da Maryamar ba. Sajida babu wanda ya kaita farin cikin kasancewar hakan, Shema'u kuwa duk wasu shirye-shiryen biki na sayan kaya ma Amarya ita keyinsu, AT har Katsina yaje bai samu mummunar shaida akan Ashfaq ba, Baffa Yawale shi yayi komai ya toshe duk wani kafa da zai fito da asalin wanene Ashfaq....

A b'angaren Maryama kuwa kullum ta k'ule a d'aki bata komai tunanin Uncle, takanyi murmushi idan ta tuna kalan SHAK'UWAR dake tsakanin su, koda shike tunda ta soma girma ma Shak'uwar tasu ta ragu, aure shine mafi mata sauk'i akan ta zauna jiran abinda ko a mafarkima ba kasancewa zaiyi ba, Allah yaga zuciyarta da sannu zai koyar da ita soyayyar Ashfaq..

Su Sajida abin nema ya samu ba'a sama ba'a k'asa, dama akwaita da son hidima balle bikin 'yaruwarta Maryama, k'awayen Amarya su Fadila Talba su Aysha cool su Anmunah kullum cikin sintiri suke dukda amaryar tasu sam bata d'auki wani damuwa ta d'aura ma ranta ba, idanma sun dameta saidai tace masu ita simple wedding kawai take so tunda shima Ashfaq d'in abinda yake so kenan.

Ana sauran sati guda Hajiya ta d'auko mai gyara mata amarya, a satin su Aunty Deenah da kuma Aunty Faty suka zo daga Abuja manyan k'awayen Mummy 'yangayu wanda kana ganinsu basai ance maka hamshak'ai bane dukda sun zo a matsayin average people...

Hajiya ma da mutanen ta daga Rano da kuma mutanenta na unguwa su suka shirya karb'an kayan.

Sosai hankalin Buzu ya tashi shi gani yake tamkar anci amanar sa ne, hakan yasa sam Hajiyar sa batazo amsar kayan ba dukda Hajiyar AT ta tura mata gayyata, Hajiya fah babu sauk'i kullum cikin cakarewa take kaman itace amaryar, _Ina ruwan su Hajiya za'a aurar da d'iya... Lol_

***********

Idanunsa sunyi jazir yake dailing lambar Shema'u..

Saida ta yastina kafin ta d'aga da k'yar..

Daga d'aya b'angaren Buzu yace "You'll pay for what you did, Maryama tawace, ki sani from this very moment na daina maki aiki, you're nothing but a trader...."

Dariya tayi kafin tace yaro dai yaro ne, you're so stupid, toh waye zai yarda da maganar da zakayi, bazan gushe ba ina warning naka, ka ci gaba da yimin biyya domin wllhi I can destroy you within a second without being pathetic, you've no idea what I'm capable of..... Wllhi nasha gabanka a iya bariki nayi da wa'enda suka damaka basu nasara ba balle kai, kai kasan farkon had'uwarmu da kai yanda aka kawo min kai, kaji yanda na baka details akan ka, so be careful boy, kar ka soma yak'in da bazaka iya k'arasawa ba, idan akan Maryama kake wannan kumfar bakin kar ka damu at the end zaka sameta bayan buk'atata ta biya...." Daga haka d'iff ta kashe wayan ba tareda ta kuma cewa komai ba..

VP ya kalli orderly d'in matar sa Hajiya Maryam a karo na biyu kafin yace "I asked you to spy on her ba shiririta na saki ki min ba, I know my wife, I perfectly well know her, nasan she's hiding something bata so na sani, and tabbas nasan bazai wuce akan Haidar ba, ina so ki kawo min komai in details within 24hrs kin fahimta..."

Saurin gyad'a kanta tayi kana ta sara masa tace "Yes Sir consider it done.." daga haka ya bata izini ta fice...

Shi kad'ai yake juya glass cup d'in hannunsa yana tunanin kalan hukuncin da ya kamaci Haidar, wllhi sai ya shayar da yaron nan mamaki sai ya nuna masa shid'in k'aramin yaro ne, har yanzu bai gama sanin duniya ba.

******************

Yau asabar tayi daidai da ranar da ake saka ran d'aurin auren Maryama da angonta Ashfaq....

AT gaba d'aya yama kasa tashi daga saman gadonsa, Shema'u ta shigo cikin shiga ta alfarma tana k'ok'arin bud'e manya-manyan cottons 'yan k'asar Turkey da aka k'awata windows dasu take fad'in "My AT you still on bed, haba Bride's Father ai kai ya kamata ku isa ku amshi bak'i ga wayarka nan Hisham sai faman kiranka yake.." ta k'arashe tana k'arasawa bedside yanda wayar AT d'in ke ajjiye, juyowa tayi taga gaba d'aya hankalinsa baya wajen...

Murmushi ta d'anyi kafin ta k'araso tayi hugging d'insa ta baya tace "Muje na maka wankan..."

Gajeren Murmushi yayi da gefen bakinsa kana yace "Kar ki damu zan iya yi, just get my clothes rady..." daga haka ya nufi closet ya d'auki bathrobe sannan ya shige bathroom d'in, Shema'u ta bisa da mayen kallo tana wani fari da idanu. A kullum taga AT Sha'awarsa k'aruwa mata yake.

Tana ficewa daga d'akin waya tayi da Allied d'inta Hisham.

Su Sajida su Ni'ima gaba d'aya suna gidan Hajiya, hidima babu kama k'afan yaro, Amara Maryama kuwa gaba d'aya sukuku take jinta tamkar maras lafiya.

*******

Tsaf ya gama shiryawa cikin wata d'anyar boyel fara k'al wanda ya d'inka zai saka a aurensu da Shema'u bai saka ba sai yau a auren Maryama da Ashfaq ya saka, AT yayi kyau har ya gaji idan ka kallesa dole ka kuma sake kallonsa, shi kansa ya jima cikin closet yana k'are ma kansa kallo a full length mirror kafin ya fito, wani daddad'an k'amshi kawai yake bulawa duk yanda ya wuce..

Shema'u bata ko ji fitowarsa ba tana nan a kitchen tana had'a masa break sai ficewar motar sa data jiyo, tamkar ta Kumar ihu haka fuskar ta ya koma.

Yana shigowa gidan Hajiya kaji yanda mutane ke gaidashi, ita kanta Hajiya yaukam sosai take shiri da Attahiru bai watsa mata k'asa a idanu ba. Yaransa su Jamal da Ni'ima suka ringa zuwa suna hayewa jikinsa.

"Daddy kaima kazo auren Adda Maryama ne? Daddy kayi kyau kayi kama da amarya..." cewar Ni'ima dake rik'e da piece d'in masa a hannunta.

Gaba d'aya mutanen wajen saida sukayi dariya wasu na tausayin AT da yaransa don sunga Shema'u da aka soma hidimar biki haka Hajiya ta ringa fad'in ga roba-robar matar Attahiru ko a jikinta, da gani sun gane Shema'u ba mace ta gari bace, abinka da manyan mata wad'anda sukayi huld'a daemutane daban-daban.

Murmushi shima AT d'in yayi kafin ya dafa kan Jamal yace "Champ kira min Addar ku Sajida ko." babu musu Jamal ya shige yana d'an tsalle.. AT kuwa rik'o hannun Ni'ima guda suka nufi babban parlor wanda ba'a bud'esa sai taro.

Bayan Sajida ta shigo ta gaishesa ta kawo masa abin kari text ya tura ma Maryama kaman haka.

_Ki sameni a parlorn bak'i..... Uncle_

Gaban Maryama ya yanke ya fad'i domin kuwa rabonta da suyi wani k'wakk'waran magana itada Uncle tun kafin a tsaida aurensu da ya Ashfaq...

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*40*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Ta karanta sak'on yafi sau abinda yafi, ita batama san Uncle nada layinta ba domin kuwa dududu wayar bata wuce sati guda a hannunta ba, angonta Ashfaq ne ya sai mata sabida su sami sauk'in yin magana da juna. A hakama da k'yar ta amsa saida ya nuna mata su d'in sun zama abu guda.

Juyawa tayi ta dubi friends d'inta da hankalinsu yafi karkata wajen mai zana masu k'unshi sai faman hayaniyar su suke, ciki harda Sajida wacce itace bisa layi ita akema k'unshin domin kuwa jiya bata samu zama an mata ba sai yau.

Mik'ewa tayi ta fice ba tareda sun lura ba, kai tsaye parlorn Hajiya ta nufa yanda mutane 'yan biki sai zolayarta suke, itako sai sunne kanta cikin mayafi take.

A uwar d'aki ta sami Hajiya nan ta sanar da ita Uncle na kiranta.

Hajiya data cakare cikin wata jan leshi mai duwatsu harda d'aurin ture kaga tsiya tayi, ta murmusa kafin tace "Allah sarki Attahiru nasan nasiha zai maki, shakka babu zaiyi kewarki sosai ni kaina nasan tsan-tsan SHAK'UWA CE a tsakanin ku,..." ta kuma murmusawa tana k'ok'arin maida k'wallanta kana tace "Duk tsiyan da kuka min a baya na yafe ku, b'oye ledar goro na, yau kuce da tsutsa gobe kuce ta rub'e duk don kar naci...." I zuwa lokacin idanun Maryama ma ya soma rau-rau, itama ta tuna wad'ancan lokutan.... Allah sarki Hajiya da Uncle zatayi kewansu domin kuwa ko Umminta bata shak'u da ita ba kaman yanda ta shak'u da Hajiya da Uncle.

Albarka Hajiya ta kuma saka mata, tasa hannu ta goge k'wallan da suka zubo ma Maryama kafin tace "Maza tashi kije ki koh nasan yana jiranki tunda lokacin d'aurin auren ya kusa."

Jiki babu laka ta mik'e ta nufi parlorn bak'i daga Maryama har Hajiya saida suka bawa mutane tausayi...

Tsaye ta hangesa ya bada baya yana fuskantar window, hannayen sa zagaye da bayansa, gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa domin kuwa tunda take uncle bai tab'a mata kyau kaman na yau ba, kayan ya amshe sa ga wani golden brown hula zanna bukar da ya zauna akansa tamkar akan nasa aka k'era, kwantattun sumarsa wanda suke gauraye bak'i da furfura kad'an sai dai bak'in yafi yawa sun d'an fito ta bayan hular tasa, gaba d'aya k'amshinsa da k'warjininsa sun cika wajen.
Chapter 48 · 0% Book details