← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 63

Sashe 58

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AT yana shigowa yayi karo da ita a bakin k'ofa uwa birin wasan tashe... Wani sabon k'yank'yanin ta yaji ya taso masa haka kurum..

A b'angaren Shema'u kuwa haka kurum taji gabanta ya fad'i domin yanayin datagan sa ciki yayi bala'in firgitata.. Murmushi ta soma masa tana sosa gashin kanta kafin tace "Gyara nake maka my AT, daga ina kake...?"

Kai tsaye ya sami kansa da bata amsa "daga gidan Hajiya nake..."

Gaban Shema'u ya kuma bugawa, baki sake take dubansa kafin tace "Gidan Hajiya kuma, gidan Hajiya fah, kaida kace ka tafi office kofah karyawa bakayi ba, toh me kaje yi gidan Hajiya..?"

Tambayar nata ya basa mamaki, shi take tambaya me yaje yi gidan mahaifiyar sa, bai amsata ba sabida zuciyarsa da yaji yana k'una lokaci guda, zai wuce Shema'u tasha gabansa uwa mahaukaciyar gaske tana fad'in "Wllhi sai ka fad'a min me kaje yi gidan Hajiya, wllhi sai ka fad'a min..."

A tunanin sa haukan nata ne ya motsa, d'an matsar da ita gefe yayi kafin yace "Barin yi wanka koh sai nazo na fad'a maki...."

"Wanka!!" ta nanata da k'arfi... Kuka ta fashe masa dashi tana fad'in "Wllhi wllhi baka isa ba, wankan me zakayi bayan wanda kayi d'azu, wllhi sai ka fad'a min idan amanata kake ci da wancan shegiyar yarinyar, wllhi bazan yarda ba tunda kaga banida lafiya shine kuke cin amanata kaida uwarka da wancan tsinanniyar yarinyar...." bata kai aya ba taji ya d'auketa da wata mahaukaciyar mari.... Yana huci yana dubanta cikeda mamaki, idan za'a ce masa Shema'u zata fad'i maganganu makamancin haka zai musa, sai gashi akan idanunsa tana fad'i, ko kad'an yak'i ba wa zuciyarsa haukan ne yasata fad'in haka..

Yana huci yake nunata da yatsa kafin yaci gaba da fad'in "Idan kina hauka kar ki kuskura ki kuma sako magaifiyata ciki, sannan Maryama matata ce banci amanarki da ita ba, tun ba yau ba na fad'a maki na sawwak'e maki idan zamana dake zai kasance akwai cutarwa kikak'i amincewa kika ce kinji kin gani zaki zauna dani haka... And yess wankan sunnah zanyi da matata na kwanta Mallaki na ba da karuwa ba don haka ki iya bakin ki... Daga haka ya finciketa ta fad'i k'asa tana kallonsa cikeda mamaki, ruhinta da zuciyarta suna barazanar tarwatsewa...

Wani irin ihu ta kurma tana birgima take fad'in "Na shiga uku na mutu na lalace, wllhi AT Allah bazai barka ba, sai ya saka min, watanni na nawa a gidanka da aurenka ka kasa sauk'e min hakki na shine zakaje ka kwanta da k'aramar yarinya 'yar cikin ka wllhi wllhi duk sai kunyi nadama.." AT kam baima san tanayi ba don tuni ya shige cikin cubicle ya sakar ma kansa shower yana tuno abar k'aunarsa da kalan soyayyar su abin birgewa....

A stirs ta had'u da Sajida don ta jiyo ihun Shema'u su Momma da iya kande suna can kitchen d'in waje basu jiyo Shema'u ba, Allah yaso su Jamal da Ni'ima sun tafi school...

A razane Sajida ta k'araso don a zaton ta ciwon Shema'u ne ya tashi.... Tun kan ta soma magana Shema'u cikin kuka take fad'in "Sajida Daddyn ku yaci amanata, Sajida AT ya zalunce ni, tunda nake aurensa a gidan nan babu abinda ya tab'a shiga tsakanin mu sabida gani nake kaman idan wani abu ya shiga tsakanin mu naci amanar 'yar uwata Aysha Mummyn ku, shine daga auren wancan k'aramar karuwar har tayi seducing d'insa sun kwanta tare... Wllhi Sajida yanzu mahaifin ku bashida sauran kima a idanun Maryama tunda taga girmansa balle ku yaransa... Wayyo ni Shema'u AT ya gama da ni..."

Girgiza kai Sajida keyi cikin rashin yarda da kalaman Shema'u, zuciyarta ya shiga mata zogi, kenan duk plans d'insu sun wargaje, duk iya k'ok'arinta not gani ta raba mahaifinta da Maryama saida suka kasance tare.... Tamkar wacce aka zabura haka ta fice daga gidan hawaye na bin k'uncinta...

Shema'u tabi bayanta da kallo had'i da yin wata munafukan murmushi..

Kallo tabi k'ofan d'akin AT dashi kafin ta shige nata d'akin had'i da banko k'ofa, bata damu ba Hisham ya banka ma asibitin wuta idan AT ya tafi Prison Maryama za'a bari da k'uncin rayuwa tana 'yar k'aramarta, sannan yaransa kuma gaba d'aya saita d'aid'aita su...

*********

Tana kwance saman doguwar kujera har lokacin hawaye basu daina bin k'uncinta ba, Hajiya ta gama kintsa ta ta koma tana kintsa d'akin suka ji an banko k'ofa an shigo....

Zunbur Maryama ta mik'e ta zauna dukda ciwon da take ji daga k'asanta... Ganin Sajida a wannan yanyi ba k'aramin tsoro ya haifar mata ba...

Kan kace me Sajida ta d'auketa da wani wawan mari ta shiga kai mata duka ta ko ina tana fad'in "You hypocrite na tsane ki, na tsane ki Maryama, kin cuce ni.... You should be ashamed of your self, wllhi kinji kunya tunda kika bari abu ya shiga tsakanin ki da mutumin da ya raine ki tamkar d'iya...."

Maryama dai bata iya cewa komai ba sai hawaye dake kwarara mata babu k'kk'autawa... Hajiya tayi tsaye bakin k'ofa tana sauraren Sajida.. Zuciyar Hajiya kaman ya fito waje sabida takaici...

A fusace Hajiya ta fito parlorn tana huci, daga Maryamar har Sajidan basu ankara ba sai jin k'aran gark'ame k'ofa da Hajiya tayi....

B'allo igiyan jikin decoder Hajiya tayi ta shiga laptar Sajida dashi tamkar wacce aka aiko.... Sajida na ihu Maryama na kuka tana k'ok'arin rik'o wayan Hajiya ta dubeta sanda ta kuma mak'uro hannun Sajida tace da Maryama idan baki matsa min a nan ba wllhi sai na had'a dake..." laptan Sajida Hajiya keyi da iya k'arfinta tana huci take fad'in "Don ubanki ko uban naki bai isa yazo har gidana yayi sakarci na k'yalesa ba, mahaukaciyar k'anwar uwar taki da take koya maki bariki itama tayi kad'an, shashasha kawai maras hankali, Attahiru ya auri Maryama ki had'iyi zuciya kuma wllhi tunda iskancin da kika tsira kenan da k'afata zan kaita har d'akinta, roba robar uwar taki ta kuma kitsa maki wani abin doluwa kawai, tashi, tashi ki fice min a gida....." ta k'arashe tana kuma zuba mata waya a gadon baya...

Jikin Sajida rud'u-rud'u abinka da farar fata, tana kuka haka ta finciki k'ofa ta fita a guje mayafi a Hannu...

Buzu da bai jima da shigowa unguwar ba don tunda AT ya auri Maryama Buzu ya k'aurace ma zaman unguwar, nan ya hangi wata kaman Sajida ta fice a guje, cikin sauri yabi bayanta...

Bagazam-bagazam Sajida ke jefa k'afafunta a kwalta tana kuka tana goge hawayen ta da mayafinta, Buzu yayi parking gefen Kwalta ya biyo bayanta gudu-gudu yana kiranta. "Baby! Miss Beauriful !! Miss Beauriful Pls ki tsaya, Ni ne Haris d'inki ne..."

Jin muryar Buzu ya sakata tsayuwa cak still mayafi a hannu tana goge hawaye... Kallo d'aya Buzu y mata zuciyarsa ta yanke ganin kalan tabon da jikin Sajida yayi, gaba d'aya yayi jazir tako ina. Shaye da mamaki yake fad'in "Beauriful wa ya maki haka... Bata iya cewa komai ba sai kukan da ta kuma fashe masa dashi, Kallo yake binta dashi ga mutane masu wucewa jefi-jefi sai kallon su suke, d'an sassauta murya yayi kafin ya soma fad'in "Baby, Beautiful pls ki daina kukan nan oya zo muje, ya janyo hannunta suka shige mota...

Hannu yasa ya ringa share mata hawayen ba tareda tayi yunk'urin hanasa ba, tsanan Mahifinta Maryama da Hajiya shi ya taru ya cika zuciyar Sajida, Buzu ya ringa lallashinta yana bata baki yana nuna mata Sam ba'a kyauta mata ba, anci amanar ta... Sajida ta kuma d'alewa dokin fushi, ji take tana dai-dai da kowa cikinsu gaba d'ayansu sai ta shayar dasu mamaki...

Buzu yace bari ya kaita gida ta mak'e masa kafad'a tace bazata koma wannan gidan ba, bai tak'urata ba yaja mota suka d'auki wani hanyar a zuciyar sa yake furta _It's payback time Dr AT yanda Mallake min abin k'aunata zan fansa a wajen d'iyarka koda dark'arfi ne...._ ya k'arashe yana sakin wata kafiran murmushi..

*******

Bai wuce asibiti ba sai gidan Hajiya da ya kuma nufowa, don ko Hajiya zata sillesa dole yazo yaga halin da ya bar Maryam a ciki..

A parlor ya sami Hajiya sai faman huci take tana kad'a kai....

Kallo d'aya ta watsa masa ya zube saman carpet... Baki na rawa yake k'ok'arin gaidata don shi duk a zaton sa fushi take dashi sabida abinda ya shiga tsakanin sa da Maryama.... A hasale Hajiya ta dakatar dashi cikin d'aga hannu..

"Yimin shiru nace kafin na sassab'a maka yanzun nan, banda sakarci baki ka bud'e ka fad'a ma d'iyarka abinda ya shiga tsakanin ka da matarka ko me, ko kai ka turota tazo tayima d'iyata cin kashi a nan iyi..?"

Gabansa ya yanke ya fad'i bai fahimci me Hajiya ke nufi ba... Girgiza kai ya soma a hankali kafin yace "Hajiya ban fahimci me kike nufi ba..."

Ta kuma harzuk'a tace "Ina kuwa zaka fahimta, ka koma tamkar lusari a cikin gidanka ka d'auko tantiriya ka dank'a mata tarbiyan yaranka..." Gaba d'aya abinda Sajida tazo gidan tayi Hajiya ta sanar dashi tana mai cika gaba da bambami ta yanda take shiga bata nan take fita ba...

Hankalin AT idan yayi dubu ya tashi, zuciyarsa ta shiga tafarfasa, gashin jikinsa suka mimmik'e idanunsa suka kad'a sukayi jazir cikin sauri ya mik'e ya lek'a d'akin Hajiya nan ya hangi Maryama na kwance uwa marainiya da alama ta gama jiyo maganganun da Hajiya ke fad'a masa, cikin sauri ya saki labulen zuciyarsa na ci gaba da tafarfasa ya nufi motar sa, suna jiyo yanda ya finciki motar ya fice daga gidan...

Da k'yar Sajida ta amince Buzu ya maidata gida bayan ya gama lallashin ta, tana shiga gida d'aki ta wuce ta kulle kanta ciki...

Hisham ya kuma kallon gallons d'in petur dake gabansa a store d'in magunguna kafin ya danna layin Shema'u yace "Kin tabbata zamu sami kud'ad'en..."

Shema'u ta murmusa tana kallon Alh Aminu dake shirin tafiya meeting da VP kafin tace "Kasha kurumin ka my Ally na shirya mu tarwatsa Tahir kuma wllhi sai mun tarwasta sa dashi da iyalansa, kawai ka cika aikin ka ka banka ma asibitin wuta...."
Chapter 58 · 0% Book details