Sashe 23
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin haka yasa Maryama dake tsaye har lokacin tana mai mamakin canzawar Sajida saurin fitowa ta nufo yanda suke tsaye carko-carko. Tuni su Momma dasu Iya Kande sun nufo wajen. Maama Juu kuwa dama tana waje tareda su Jamal.
"Ke lafiya kike wannan doka salati haka.?" Momma dake kama staircase tana k'ok'arin k'arasa haurowa ta tambaya.
Shema'u cike da rud'ewa take fad'in "Momma d'akin Sis ne, Momma we've been rubbed, Momma lek'a kiga d'akin Aysha na tabbata b'arayi ne suka shigo."
Momma ta lek'a d'akin tana mai tafe hannuwa kafin ta maida dubanta ga Iya Kande tace "Kin shiga d'akin da sunan gyarawa ne..?"
Iya Kande tayi saurin girgiza kai baki a tab'e tana mai tafa hannuwa take fad'in "Hajiya, ni Haramiya, me zaikaini d'akin Marigayiya da sunan gyara idanba umartata akayi ba tunda bata nan, saidai ko ta bakin *Hajiyan sake Hannu* (Shema'u) b'arayi ne suka shigo." Ta k'arashe tana lek'e-lek'e.
Momma kuwa cikeda b'acin rai tace "Yo wani b'arawo ne zai shigo gida ko ta ina tsaro..." Cikin sauri ta shiga d'akin ta tarar k'aramar akwati 'yankunnayen Aysha a bud'e... D'aukan d'an kit tayi ta shiga tafe hannaye tana salallami.
"Toh wllhi babu mai barin wajen nan sai na caje ku gaba d'aya, tunda babu wanda suka shigo nan sai ku." Ta k'arashe tana nuni da Maryama da Iya Kande..
Girgiza Kai Maryama ta shiga yi idanunta na k'ok'arin kawo ruwa take fad'in "Wllhi Momma bani bace, yanzu shigowata kuma kai tsaye d'akin Sajida na wuce.. Pls ki yarda dani bazan yi abu makamancin haka ba.."
Tsaki Momma tayi ta fincikota ta shiga cajeta ta ko ina.... "Shema'u kuwa cikeda makirci take fad'in "Haba Momma let the girl be, bazata yi haka ba tunda tana tareda su da jimawa batayi ba.."
"Ke dalla rufe min baki, tsintacciyar mage bata 'ya'ya, kika sani ko ta jima tana shirya hakan, yanzu dama ta samu tunda babu mai d'akin... Wllhi wllhi sai an caje kowa.
Cikeda makirci Shema'u rai b'ace take duban Hajiya kana tace "Toh idan dai haka ne saidai nima ki caje ni.."
Sajida kam downstairs ta nufa ganin ran Aunty Shema'u ma ya b'aci da abinda Momma keyi, tasan tana fushi da Maryama amma tasan bazata shiga d'akin Mummyn su tayi sata ba..... Nan Shema'u tabi bayanta tana kiran sunan ta.
Momma kuwa bakin skirt d'in Maryama da bakim zanin Iya Kande ta kamo ta nufo k'asa tana fad'in "Wllhi duk wacce na sameta da tsinken Aysha cikin ku hukuma ce zata rabamu."
Tuni hawaye ya wanke idanun Maryama, tunda take a rayuwarta ba'a tan's cin zarafinta kamar yau ba, sata, Allah Ya tsareta da d'aukan kayan wani...
Babu yanda Shema'u da Sajida basuyi ba Momma ta bar maganan caje fir tak'i, k'arshe dai harda Shema'u aka caje..
Ba'a sami komai a jikin kowa ba..
Sajida ta d'an girgiza kai tace "Momma kin gani koh, ta yuwu buglers ne suka d'an hauro window..." Ta k'arashe maganar tana satan kallon Maryama dake goge hawaye ta d'auki jakarta ta rataya...
Zata fice Momma tayi saurin jawota baya tace "Aiho ashe wannan jakar ki ce, toh ko baki isa tafiya ba sai an duba jakan nan..."
AT sai sallama yake sam basu jisa ba..
Shema'u data hangi shigowar sa tayi saurin k'arasawa tana janye Maryama daga rik'on da Momma ta mata tana fad'in "Haba Momma duk fa kinyi searching d'inmu baki sami komai ba, this is not fair, pls ki k'yaleta.."
Maryama kam sai kuka take tana fad'in wllhi bata d'au komai ba.
AT ya k'arasa shigowa cikin parlorn sosai kafin ya bud'e murya yace " What's going on here..."
Shema'u ta k'arasa gabansa da sauri cikeda makirci take fad'in "Thank goodness ka iso, inaji buglers ne suka hauro window sukayi b'arna a d'akin Sis, and Momma tak'i yarda ba d'aya daga cikin mu bane ta shiga d'akin, tayi searching namu bataga komai ba still bata yarda ba..."
Katse ta Momma tayi da fad'in "Shema'u wllhi kinji na rantse sai na duba jakan yarinyar nan don ban yarda da ita ba, kuma ai ban duba jakar nata ba, da kike maganar ki dole na damu na cajeku tunda nima inada hakki a gadon d'iyata..." ta k'arashe tana huci.
Sai sannan AT ya sauk'e idanunsa kan Maryama da tayi tsaye hawaye na bin k'uncin ta... Ji yake kaman ya rungumeta ya share mata hawayen ta sabida tsananin tausayin ta da ya lullub'esa.
Tunda yake bai tab'a wani sa'insa da Momma ba amma yau kam har cikin k'ahon zuciyar sa yaji zafin abinda tayi ma Maryama. Cikeda b'acin rai yace "Momma pls ki sakar mata jakanta, babu wanda za'a k'ara cajewa.. Sakar mata jakarta ta, nasan Maryama wannan ba halinta bane... Sannan ko meye ya b'ace a d'akin Aysha zan biya, so pls banaso a sake d'aga wannan maganar."
Zuciyar Shema'u kaman ta fashe sabida takaici ganin yanda AT yake defending Maryama.
Girgiza kai Maryama tayi still tana hawaye kafin tace "Uncle pls ka bari ta duba jakan.."
Kallonta yayi kafin yace "Maryam."
Da sauri tace masa "Please."
Bai kuma cewa komai ba sai wani mugun kallon da yake watsa ma Momma, babu kunya babu tsoron Allah Momma ta bud'e jakar ta shiga zazzagewa.
Kaman daga sama sai kuwa ga sark'an zinaren Aysha ya fad'o daga cikin jakar.
Iya Kande ta soma salati tana sallalami ta d'ago sark'ar tana fad'in "Wllhi ga sark'ar Marigayiya cikin jakar, Oh ni Kande..."
Momma sai faman tafasa take tana huci fad'i take "Zan kira 'yansanda yanzun nan kuwa su rabamu dake, algunguma anammimiya b'arauniya."
Shema'u da Sajida baki sake suke kallon ta, tsanar ta ya kuma shiga zuciyar Sajida.
Maryama kam ta kasa fad'in komai sai girgiza kai kurum take da tsananin mamaki..
AT ya kasa motsawa daga yanda yake, ya tabbata wannan aikin Momma ne tunda dama ya kula bata son Maryama da Maama Juu... Har cikin b'argo da tsoka yake jin zogi da rad'ad'in abinda ya faru ga Maryama...
Maama Juu dake tsaye bakin k'ofa ta gama ganin komai, goge hawayen da suka zubo mata tayi kafin ta k'arasa shigowa.... Da sauri Maryama ta tafi ta rungume Ummin ta..... Sosai Maama Juu ta rik'eta idanunta da suka kad'a sukayi jazur k'yam akan Momma... K'arasawa tayi gabanta kafin tace "Maryama ba b'arauniya bace, Maryama bata d'auka ba, na tabbata kece kika yi hakan, domin ki cimma burinki na ganin na fita daga rayuwar yaran gidan nan, ki sani duk iya makircin ki SHAK'UWA da soyayyar dake tsakanina dasu daga Allah ne, bazasu tab'a sonki kaman yanda suke sona ba, sannan idan zaki k'ala sharrin ki mani zaki k'ala ba d'iyata ba...."
Huci Momma take tana jin zafin maganganun da Maama Juu ke watsa mata.. "Yo sai me, sata ne tayi kowa ya shaida bari ma ki gani wllhi 'yansanda zan kira su zasu rabani da wannan b'arauniyar.." Ta k'atashe tana k'ok'arin shafa wayar ta tana faman girgiza...
AT gaba d'aya kansa ya kwance yama rasa wanne zaiyi... Tsakiya ya tsaya yana fad'in "Enough pls.." Parlorn yayi tsit sai kallon kallo da ake aika ma juna....
AT yaci gaba da fad'in "Momma ki daina maganar kiran police this is family issue...." Momma tayi saurin katsesa da fad'in "Waye family d'in, Allah fidda k'wad'o daga rogo...."
AT ya dafe kansa hak'urinsa yana gab da k'arewa... Maama Jun ta rik'o hannun Maryama tace "Wuce mu tafi.."
AT yayi saurin tsaresu yana bawa Maama Juu hak'uri..
Tak'aitaccen murmushi tayi kafin tace "Dr kayi hak'uri, ina son yaranka ina k'aunar su, amma ya zama dole na bar gidan nan sabida d'iyata..." Daga haka bata kuma sauraren AT ba ta fizgi hannun Maryama suka wuce zuciyarta na tafarfasa... Sajida tayi saurin rik'o hannun Maama Juu tana fad'in "Maama Juu tafiya zakiyi ki barmu, pls don't leave, don Allah ki tsaya, wllhi bazamu iya rayuwa babu ke ba..."
Ta juyo tana watsa ma Momma mugun kallo kafin tace "Momma meyasa zakiyi haka, wllhi na tabbata kece kika saka a jakar Maryama, gashi kin jawo Maama Juu zata tafi, Kinyi searching har Aunty Shema'u hakan ya tabbatar min kece kika saka Momma just admit..."
Haba nan fah Momma ta daburce, reshe ya juye da mujiya, gaba d'aya suka mata k'uri suna jiran amsar ta.. Kallon Shema'u Momma ta juya tanayi, Shema'u ta kauda kanta had'i da rik'o hannun Sajida.
Inda-inda Momma ta soma ta rasa me zata ce.. Maama Juu kuwa girgiza kai tayi kafin tace "Kinji kunya Hajiya Kulu, daga haka janye hannun Maryama tayi suka fice cikin sauri..
Sajida ko sai bin Momma da mugun kallo take.
Juyowa AT yayi yana watsa masu mugun kallo gaba d'ayansu kafin ya nufi Upstairs zuciyar sa na masa zogi, kaman zai kifa da k'asa.
Liyafar da ba'ayiba kenan Sajida ta sallami k'awayenta.
A d'aki Shema'u ta sami Momma sai faman huci take don kuwa babu wanda yabi bayanta harta Shema'u da take tunanin ita ta k'ulla wannan k'ulelliyar..
Mik'ewa tayi tana huci take fad'in "Me kike tunanin kinyi Shema'u, meyasa kika kasa bin bayata alhali kina gani kowa ya juyan baya, meyasa kika bari laifi ya dawo kaina.?"
Murmushi Shema'u tayi kafin ta rik'o kafad'un Momma ta zaunar saman gado kafin tace "Relax Mom, and keep it down, someone might here you, abinda yasa nayi haka sabida ke kad'aice ya dace kiyi taking responsibility, nima bansan abin zai koma haka ba, amma koma an d'aura maki laifi ai kwalliya ta biya kud'in sabulu tunda buk'ata ta biya, we got rid of them... Sannan I'm only doing this ne for your grandchildren, kinga idan laifi ya dawo kaina AT da yaransa bazasu kuma aminta dani ba.... " Tayi wata murmushi kafin tace "Momma ta kar ki damu, ni ce fah I'll make it up to you... Inaji a jikina aurena da AT yazo..." Ta k'arashe maganar tana wata kafiran murmushi tana kallon Momma da tayi jigum tana sauraren d'iyar tata..