← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 63

Sashe 13

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga d'aya b'angaren Hisham ya fashe da wata irin muguwar dariya kafin yace "Shema'u annoba, wani improvement d'in kika samu don nasan haka kawai bazaki kirani ba, saidai kin sami wani ci gaba ko kuma you're planning for something."

K'asaitaceccen murmushi tayi kafin tace "Kaida ka sani, komai yana tafiya yanda nake so, I'm pretty sure yanzu AT zai amince gidansa baza'a tab'a zaman lafia ba muddin babu ni. Nasan wannan Uwar tasa itace zata zame min matsala, but I have my way to get rid of her. ..." Cikin sauri Hisham ya katse ta da fad'in "No Shema'u, don't hurt Hajiya, ko kinsan AT yana son mahaifiyar sa fiye da komai a duniyar nan,? ...wait what's wrong with you ne kam, You said you love him, but meyasa kike cutar da mutanen da yake so, first kin rabasa da matar sa uwar 'ya'yan sa, kina k'ok'arin rusa tarbiyar da ya bawa d'iyar sa, and now his Mother..? Shema'u are you human.? "...... Katse sa tayi da fad'in "Hisham don't tell me you're backing down, toh idan ma ka hak'ura da k'udirin ka ne, ni zanfi kowa farin ciki coz bana so kayi hurting AT, abu guda da nake gargad'in ka dashi shine, don't you dare think of betraying me.. Wllhi Hisham kayi tunanin turning back d'inka on me I won't go down alone, tare da kai zamu tafi k'asa... "

Tunstirewa da dariya yayi kafin yace "Stop being so sensitive, haba my Ally kema kinsan hakan bazata tab'a kasancewa ba.. Ban janye k'udiri na ba kuma bazan janye k'udiri na ba. Yanzu me kike so kika kirani.

Murmushi tayi kafin tace "Yanzu naji bayani, akwai wani yaro a nan Janbulo, Haris Buzu, ina son ka taimaka min nasan komai a gameda shi, I want to work with him.. " Ta k'arashe tana murmushi.

Murmushi Hisham yayi ya shafi kansa da yasha aski low-cut kafin yace "What can I have in return..?"

Murmushi ta kuma yi kafin tace "Nasan matsalar ka, gani nan zuwa apartment d'inka, dama inaso na d'an b'oye masu, su nemeni su rasa nasan Sajida zata d'aga masu hankali har sai na dawo gidan..."

Hisham ya murmusa had'i da kashe wayar kafin a hankali ya soma furta, "AT I'll ruin you completely..."

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*10*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*_REMINDER..!_*

_(This book is a work of fiction. All names, Characters, locations and incidents are products of the author's imagination or have been used fictitious. Any resemblance to the actual persons living or dead, locales or events is entirely coincidental.)_

Tsareta da idanu AT yayi yanda ta tak'ure waje guda sai faman shan zuciya take alamun taci kuka. Cike da masifa yaci gaba da fad'in "Answer me! Kinyi hauka ne huh..!" Kafad'unta ya rik'e yana jijjgata yana ci gaba da mata fad'a, gaba d'aya fuskar sa tayi jazir sabida b'acin rai, jijiyoyin goshin sa sunyi rud'u rud'u.

Girgiza masa kai Sajida take still tana hawaye, ba tareda ta iya fad'in komai ba sai kuka da take.

D'an dafe kansa yayi had'i da fuzar da iska, gani yake kaman he's going to far... A hankali ya durk'usa a gabanta yana kallonta, tausayin su gaba d'aya ya rufesa, yana tsananin son yaransa musamman yanzu da suka rasa mahaifiyar su.

Hannu yasa ya kamo hannayen ta kafin yace "Sweetheart, what you did out there was crazy, haba Sajida, da girman ki.... If to say Jamal ne ko Ni'ima sukayi abinda kika yi zan masu uzuri nace su yara ne, but you at your age, haba Sajida, have you forgotten what this family had been through lately.. Huh? Or do you want the same tragedy to repeat it self huh..? Har kin manta Sajida, if your Momy was here, do you think she will be proud of you, no sweetheart, bazataji dad'i ba... " Sajida dai hawaye ne kawai ke kwaranya a idanunta... AT ya kuma kamo hannayen ta kafin yaci gaba da fad'in "Sajida my family are my first priority, bazan tab'a yafewa kaina ba idan na bari wani abu ya same ku da ganganci, but I can't do this alone, kece babba kece zaki taimaka min na kula daku da k'anenn ki, pls sweetheart kar ki sake irin wannan tunanin kinji." Ya k'arashe maganar fuskar sa dab da nata mai zuban hawaye.

Gyad'a masa kai tayi kafin tace "Daddy kayi hak'uri, bazan sake ba insha Allah... But pls Daddy ka min alk'awari zaka rok'i Aunty Shemah ta zauna damu a nan for good, pls Daddy kar ka bari ta tafi kaji Daddy..."

Dummm! Haka k'irjin AT ya buga, yama rasa me zaice ma Sajida, tattaro naman goshin sa yayi had'i da d'an fuzar da iska kafin yace "Sajida Auntin ku tanada tsarin rayuwar da tayi ma kanta, and she can't be here for good, sabida mace ce ita, sooner or later zata soma tunanin gina nata family d'in itama, sannan ta baro aikinta a can gida which is ya kamata da tuni ta koma bakin aikinta, she also need to prioritise her own happiness.. Sajida.... " Bai kai aya ba ta soma ci gaba da wani sabon kuka ta rik'e hannayen sa tana fad'in "Daddy pls this is all I'm asking of you, Daddy don Allah kar ka bari ta tafi, wllhi Aunty Shemah tana sonmu tana son zama damu, pls Daddy kar ka bari Hajiya ta koreta, do this for us please." Ta k'arashe cikin rawar murya.

Sauk'e deepbreath AT yayi kafin ya gyad'a mata kai yana murmushi kana yace "Okay, I'll see what I can do, I'll talk to your Aunt, hakan yayi maki.?"

Saurin gyad'a kai tayi cike da murna tace "Daddy na gode, Allah saka da alkhairi."

Bai iya amsa mata ba sai ficewa da yayi daga d'akin jiki babu laka. Yana fita Maama Juu ta shigo Sajida ta tafi da sauri tayi hugging nata. Rik'eta Maama Juu tayi suka k'araso suka zauna saman gado. Kafin ta soma tambayar ta abinda ke faruwa. Sosai tayi fad'a ma Sajida jin rashin hankalin da tayi..

"Inyi, haba yaya ma zakiyi haka Sajida, baki tausayin mahaifin ku ne, da wanne zaiji, da rashin mahaifiyar ku, ko kuma da fitinar da kike neman b'ullo masa...Haba, haba Sajida wannan aiki ko Jamal bazaiyi ba balle ke...."

Jikin Staircase Shema'u ta mak'ale tana sauraren su tana murmusawa ita kad'ai, Har Momma shigowa tayi tana salle Sajida akan abinda tayi, gaba d'aya sai fad'a suke mata. Jin Sajida ta soma masu kuka tana fad'in ba da gangan tayi hakan ba yasa Shema'u saurin shigowa d'akin ta k'arasa cikin tashin hankali tana fad'in "What's going on here, Momma meke faruwa.? " Da sauri Sajida ta tafi ya rungume Shema'u tana fad'in "Aunty Shemah pls tell them to stop scolding me.."

Rungumeta Shema'u tayi kafin tace "Oh Sajee na, yi shiru abin ki, kema ba son ranki bane kikayi hakan, bedsides thank goodness I was there, and I was able to save you.... " Maama Juu dai ficewa tayi cike da shakku gameda Shema'u. Momma kuwa surfa masu masifa taci gaba da yi daga Shema'un har Sajidar.

Shema'u sai faman k'yafta idanu take wa Momma inaa Momma tak'i yin shiru. Nan ta soma fad'in "Haba Momma yarinya ce dai, sann mu duka 'yan Adam ne muna kuskure, for crying out loud give her break Momma..."

Cikin kuka Sajida take fad'in "Aunty yanzu na gane keda Daddy ne kawai masu sona, Hajiya ta mare ni, Momma ma ta min masifa, har Maama Juu ma masifa take min..."

Shema'u ta kwantar da kan Sajida cikin jikinta tana lallashi, lokaci guda tana aika ma Momma kallon kin k'i saurare na, kin ga abinda nake ji maki.

*************

Da yamma lis ya nufi gidan Hajiya yana sanye cikin k'anan kaya da shike lokaci ne na zafi. Red Armani shirt da bak'ar jeans, sosai kyaun sa da k'uruciyar sa suka fito.

Sanye take cikin purple top kanta babu d'an kwali, gashinta mai cika wanda bai faye tsawo ba amma ba guntu bane tupke cikin ribbon, zani ne d'aure a jikinta tayi rigingine saman tabarma ta bararraje sai faman karatu take, sam bataji sallamar sa ba.

Haka kurum ya tsinci kansa da fad'uwan gaba hangota a haka da yayi.... Still yayi a wajen ya kasa ci gaba da tafiya.... Kaman daga sama ya jiyo muryar Ilu Mai gadi ya nufosa cikin sauri yana basa sak'o....Cikin sauri Maryama ta mik'e zaune zumbur tana kallon su daga can k'asar bishiyar Hajiya da suke tsaye...

AT kuwa cike da takaicin shigowar da Ilu yayi har cikin harabar gidan ya soma masa fad'a... Sosai Ilu ya shiga basa hak'uri yana basa sak'on... _Wato ma Ilu ya saba shigowa haka kenan_ AT ya fad'i haka cikin zuciyar sa ... Gajeren tsaki kawai yayi, don kuwa sam Ilu bashida nitsuwa, irin mutanen nan ne masu barkwanci sosai. Hajiya kuwa bazata tab'a bari a sallame sa ba don tasu tazo d'aya.

Zuru tayi tana kallon yanda AT ke sille Ilu, gaba d'aya kasa tashi ma tayi har saida ya iso yanda take. A d'an daburce ta soma gaishe sa.

A tak'aice ya amsa kafin yace "Ina d'ankwalin ki, ba hanaki zama babu d'ankwali ba..."

Mik'ewa tayi zunbur cike da kunya ta nufi palorn Hajiya ta d'auko hijabi ta saka.

Fitowa tayi ta same sa yana nan zaune saman faran kujera. K'ara gaishe sa tayi kafin ta zauna a mazaunin ta, haka kurum ta sami kanta da jin nauyin sa mussaman ganinta a haka da Uncle yayi.

"Hajiya bata nan ne.?" ya tambaya sanda yake ciro waya a aljihun sa sakamakon k'arar shigowar sak'o da yaji.

"Eh ta tafi dubiya gidan Baaba Dije nan mak'ota jikarta ta karye."

Idonsa naga wayarsa yana karanta sak'on da ya shigo masa yake gyad'a mata kai kafin yace "Allah bata lafiya."

Sajida ta amsa da "Ameen."

"Ya karatun, hope kina yi.?"

Gyad'a masa kai tayi ba tareda ta iya furta komai ba.

Saida ya d'an gyara zaman sa, ya had'e yatsun hannun sa waje guda, hannayen sa na d'aure saman laps d'insa kafin ya d'an yi gyaran murya yace "Maryam."

D'ago kai tayi tana dubansa lokaci guda k'irjinta ya kuma yankewa ya fad'i, cikin sauri ta sadda nata kan k'asa.
Chapter 13 · 0% Book details