← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 63

Sashe 34

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashfaq ya d'an dake kafin yace "Pls ke 'yar gidan nan ne.?" Ya tambaya yana dubanta.

Rasa me zata ce masa tayi gashi dama tana ji da haushin abinda masoyinta Haris ya mata, wannan kuma ko waye shi oho, ya tsaya yana mata tambayar rainin sense.

Ashfaq ya d'an k'araso jikin bishiyar umbrella dake tsakiyar farfajiyan kafin yace "Kiyi hak'uri da Allah, dama Dr ne ya aiko ni da kaya so pls idan bazaki damu ba kiyi magana wa mutanen gidan su fad'i yanda za'a zuba.."

D'an jim tayi kafin tace "Menen aikan.?"

K'arasawa jikin motar sa yayi ya d'aga both kafin yace "Kin gansu.."

Sajida ta gyad'a kai kafin tace "Bara na shiga na tambaya a ina za'a zuba.." Daga haka ta barsa nan tsaye ya bita da kallo yana mamakin jin kanta...

Shiganta gida neman Maama Juu ta soma tana son tambayarta ko Daddy ya sanar da ita za'a kawo aika, bata sameta ba don suna can sashen bak'i suna shigar da warmers na taran bak'i...

Daga yanda yake tsaye yana dafe da motar sa ya hangi gefen fuskar wata mata da tayi mugun masa kama da wata, kai gaskiya yanayin matar ma yai masa kama da ya tab'a ganinta, toh a ina yasan mai kama da wannan matar..... Yana nan tsaye ya fad'a duniyar tunani sai jiyo muryar Sajida yayi tana fad'in "ka zubasu a nan kawai za'a shiga dasu later..." bata kuma jiran amsar sa ba tayi shigewar ta, murmushi yayi cikin zuciyar sa yace wannan duk yanda akayi masifar Hajiya tayo....

Yana gama sauk'e kayayyakin ya kira AT ya sanar dashi, AT ya masa godiya kafin yace "Suna hanyar Kanon suma. Ashfaq ya masu fatan sauk'a lafiya kafin ya shige motar sa ya bar gidan, tunanin yanda ya tab'a ganin mai shigen fuskar matar can yake, wata zuciya tace k'ila dai ka had'a kanninta dana wata ne, d'an tab'e baki yayi kafin ya maida hankalin sa ga driving...

************

Basu suka iso Kano ba sai wajajen isha, gaba d'aya a gajjiye suke, amarya sai k'anshi turarruka ake, an tsuma da maganin mata iri da kala, batada burin da ya wuce a barta a d'akinta daga ita sai angonta...

Ta d'aga idanu tana duban d'akin k'anwarta Aysha wanda yake a matsayin nata a yanzu, murmushi tayi mai tarin ma'ana, cikin zuciyarta take furta _Aysha inama kina gani na, yau gani nan na mallaki gidanki, mijinki da kuma yaranki, tabbas ni ce nafi cancanta da wannan rayuwar ba ke ba, da sannu Tahir zai zama nawa ni kad'ai.._ ta kuma murmusawa kafin ta haye saman gado. Babu k'awar data rako Shema'u don dama ita bata yarda da wata k'awa ba sabida ita kanta bata yarda da kanta ba, wani sa'in har tsoron kanta take sabida zata iya k'ulla sharri ma kanta, tunda Aysha tayi aure ta yaye k'awaye dama yawanci sabida kirkin Aysha suke zuwa dashike duk tare sukayi sch..

AT kuwa suna isowa gidan Hajiya ya nufa, sam bai gane kansu ba daga Hajiyar har Maryamar, sama-sama Hajiya ta masa barka fuska babu walwala kafin ta kunna radio d'inta ta shige uwar d'aka tana sauraren zab'en dare, don ya fiye mata sauraren Attahiru.

Parlorn ya rage saura shida Maryama, yana hankalce da ita yanda ta koma sukuku gaba d'aya yana son tambayarta meke damunta. D'an duba agogon hannunsa yayi kafin yace "Maryam ina so ki fad'a min gaskiya, be honest with me.."

Gabanta ya yanke ya fad'i, toh me Uncle zai tambayeta yanda yayi maganar sounds serious... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar sa na fad'in "Hajiya tayita fad'a ko, tayi fushi sosai koh..?"

Jikinta yayi sanyi don sam bata kawo abinda zai tambayeta kenan ba, d'an saita kanta tayi kafin tace "A'a batayi fad'a ba, bata ce komai ba..."

AT ya sauk'e ajiyan zuciya kafin ya shafi goshinsa yace "And you yaya baki tafi can gidan bikin ba, ko kema taya Hajiya kike ne...?"

D'an murmushi tayi gamida sadda kai kana tace "A'ah ba haka bane, kawai banjin dad'i ne.."

AT ya kafeta da idanu kafin yace "Meke damunki...?"

Nan fah ta tuna ashe fah Uncle likita ne, tasan bazai k'yaleta ba har sai ta fad'i masa abinda ke damunta... Kame-kame ta soma tama rasa me zata ce, cikin sauri tace kanta ne ke ciwo..

Ya k'ura mata idanu kafin ya soma jero mata tambayoyi gameda ciwon kai d'in "Gefe ne ke maki ko kuma gaba d'aya ne, yaushe ya soma maki, kinsha wani magani ne...?"

Gaba d'aya ma ta rasa wanne zata amsa masa cikin daburcewa tace "Eh eh na sha paracetamol, yama daina..."

Yayi shiru yana dubanta kafin yace "Idan bai daina ki sanar dani kinji koh."

Gyad'a masa kai tayi alamun toh, daga nan ya sata ta kawo masa abinci ya zauna yana ci yana jefo mata hira jefi-jefi wanda akasarin hiran gameda karatu ne,... Maryama dai um da um-um kawai take amsa masa don kuwa gaba d'aya ji take ta kasa sakewa dashi, kaman ba shine Uncle d'inta wanda suka shak'u a baya ba, wanda suke hana Hajiya cin goro tare da plans d'in su...Shi kansa AT ya lura da hakan..

Wajajen nine ya mik'e ya lek'a d'akin Hajiya zai mata sallama nan ya samu tayi barci, daga nan kuwa ba bacci Hajiya tayi ba jin lek'owar sa ne yasata lumshe idanu...

Kallon Maryama dake tattara plates d'in da yaci abinci yayi kafin yace "Muje mota ki karb'i sak'o,." amsa masa tayi da toh, bayan ya fice tabi bayansa...

Front seat ya bud'e ya ciro wani shopping bag kafin ya mik'a mata yace "here tsaraban ki, and gobe Shema'u zatayi event don't tell me kanki na ciwo, Malam Habu zaizo ya kaiki..."

K'ak'aro murmushin k'arfin hali tayi kafin ta shiga gyad'a masa kai, da k'yar ta lalumo kalmomi saman harshenta tai masa godiya..

Har ta juya ta soma tafiya ta jiyo daddad'an muryar sa ya ambato sunanta "Maryam"

Juyowa tayi suna duban Juna, hasken wutan lantarki ya haske fuskokin su, a hankali ya furta "Baki min murna ba."

Nanma k'ak'aro murmushi tayi kafin tace "Kayi hak'uri Uncle, congratulations Allah Ya bada zaman lafiya, Allah Ya kad'e fitina." Har cikin ransa yaji dad'in addu'an data masa, murmushi ya sakar mata kafin ya amsa da amin had'i da mata godiya, sallama suka kuma yi kafin ta soma tafiya cikin yanayin tafiyar ta..

Gaba d'aya sai yaji jikinsa yayi sanyi, ya jima a wajen shi kansa baisan tunanin me yake ba kafin ya shige motar sa ya tada...

Tana shiga gida ta bud'e jakan ta zaro abinda ke ciki, riga ce Navy blue mai kyau irinta larabawa wanda tasha ado da duwatsu, haka kurum ta tsinci kanta tana mai yin murmushi, rungume rigar tayi tana shak'an k'amshin turaren Uncle da tuni ya kama jakan da rigar....

Yana isowa gida saman sa ya nufa ya shiga bathroom ta sakar ma kansa shower don a gajjiye yake lib'is..

Shema'u kuwa tana jin shigowar sa ta d'aura hijabi saman rigar baccinta ta nufi nasa parlorn, bata gansa a parlor ba hakan yasata shigewa master bedroom d'insa kai tsaye irin batada shamak'i d'in nan...

Tana jin alamun tab'a k'ofa zai fito tayi saurin rarumo abin sallah ta haye kai tamkar mai sallan gaskiya...

AT da fitowar sa kenan daga bathroom towel d'aure a kunkumin sa sai d'an k'arami yana goge sumar sa har ya d'an razana da ganin mutum saman abin sallah, gabansa ya yanke ya fad'i don ba kowa ta tuno masa ba illa Aysha... Nan yayi tsaye yana kallonta, ganin tana k'ok'arin sallamewa yasa sa saurin komawa cikin closet d'insa, jallabiya fara k'al ya zura kafin ya komo cikin d'akin, zuciyar sa k'unshe da tambayoyi me ya kawota d'akinsa, b'angare na zuciyar sa tace yaya zakayi ma kanka wannan tambayar, ko ka mance matar ka ce, wata zuciyar tace toh ai ko 'yan biki basu watse a gidan ba, wata b'angare ta basa amsa kai tsaye ka mance bazaura fah ka aura ba budurwa ba, koma yaya ne zata jira ya soma zuwa gareta.... Muryar ta Ya jiyo tanai masa sannu da gajjiyan hanya...

A d'an tak'aice ya amsa ba tareda ya k'ara da komai ba, kaman tasan tunanin da yake nan ta soma fad'in "Wllhi su Inna Larai ne wai zasu kwana a d'akin nawa, gaba d'aya sun cike d'akin shiyasa nazo nan, I hope bazan tak'ura ka ba..

Murmushi ya sakar mata kafin yace "Ko kad'an this your house ai..." Wayyo dad'i kaman ya kar Shema'u..

Akan idanunsa ta yaye hijabin jikinta, AT yayi saurin d'auke idanunsa domin kuwa wata kafiran rigar bacci ne a jikin Shema'u.. Ta nufi k'ofan bathroom tana satan kallon sa, nan ta d'ebi jiki ta zube a k'asa da gangan, cikin sauri ya nufeta yanai mata sannu yana tambayarta bataji ciwo ba, k'in tashi tayi sai d'an kama kunkuminta da take yi cikeda k'issa. Ya d'an rank'wafo yana k'ok'arin d'agota kaman wacce take jira nan ta shige cikin jikinsa.....

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*28*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*Anmunah*
*Aysher cool*
*Fatima Tasi'u*
*Maman Ikram*
*Mum Izaddeen*
*Ummu Jawad*
*Xee Mako*
*Suwaiba*
*Miss k'anwar AT*
*Mum Hisham*
*Mum Mus'ab*

*Da sauran members na MUSHAA KARATU wannan shafi damarku ce ina k'aunarku da zuciya guda ❤ A ringa ragar ma amaryar AT 😹*

Gaba d'aya ta cukwikuyesa ta shige cikin k'irjinsa sai kukan shagwab'a take tana kuma narke masa, da k'yar AT ya samu ya masu masauk'i saman _chaise lounge_ irin kujeran Aina'un nan dake can gefe a wani angle cikin d'akin. Sannu yake kan faman mata don a zatonshi ciwo wajen ke mata, ya yunk'ura zai tashi yana fad'in bari ya d'auko man zafi..... Tana ganin ya mik'e ta kauda kai gefe tana murna harda wani karkashe idanu tsaban nishad'i da take ji...

Fairst aid d'insa ya bud'e ya ciro man zafi kafin ya dawo gareta, k'ank'amesa ta kuma yi tana fad'in kujeran ya matse ta ya kaita gado...

AT ya d'anyi jim kafin ya kamota yayi mata masauk'i saman gado, mik'a mata man zafin yayi yace ta shafa a wajen.... Kuka ta fashe masa dashi tana fad'in bazata iya ba...
Chapter 34 · 0% Book details