← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 63

Sashe 20

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shema'u dake tsaye dasu Jamal a parking lot baki ta sake kawai tana hangosa. Tun daga nesa ya bud'e masu security lock amma Shema'u bata san ya bud'e ba, tayi nisa cikin duniyar kallon sa.

Saida ya k'araso ya bud'e masu Jamal k'ofar motar kafin hankalin ta Ya dawo jikinta, cike da kissa ta bud'e front seat ta shige tana binsa da mayen kallo, shi kuwa AT sam baison yama kalle ta. Sai biye ta yaransa yake.

Suna tafe suna hira da yaransa Shema'u tana tsomo baki, a dai-dai kwanan shiga makarantar wayarsa ta soma ringing, Hajiya ce mai kira.

Da fad'a ta soma masa don ko zsrafin gaisheta bai samu ba, nan ta sanar dashi Maryama tana gida bata je ba, yauma su Sajidan basu biyo mata ba.

"Subhanallah Ya akayi haka?!" ya furta sanda yake karyan kwanar, Shema'u kuwa k'uri ta masa tana son jin menene ya d'aga masa hankali haka..... Muryarsa ta kuma jiyowa yana fad'in.

"Okay, gani nan zuwa yanzun nan, barin ajiye su Jamal."

Koda ya gama wayan kallo Shema'u ta kuma binsa dashi tana son tambayar sa wa ya kirasa amma babu fuska, iyaka abinda ta fahimta kiran nada mahimmaci a gurinsa.

Sanda ya gama parking a farfajiyan makarantar, ya dubi su Jamal yace "You guys should behave okay, zan dawo bada jimawa ba, just stay with your Aunt okay." Jamal yace "Daddy ina zakaje, Adda Sajida bazataji dad'i ba idan taganmu babu kai.

D'an turo kansa yayi ta k'ofar motar kafin ya shafi kan Jamal yace "Champ, zanje d'auko Addan ku Maryam ce, she supposed to be here by now, tunda harda ita akema yayen. Ku zauna da Aunty ku, yanzu zan dawo..

Kad'an ya rage Shema'u bata saki fitsari a wandonta ba jin yanda AT zaije sabida tsananin tashin hankali...... Tayi nisa duniyar tunani ta tsinkayo muryar AT yana fad'in Ta kula dasu da Allah.

Murmushin yak'e tayi kafin tace "You don't have worry Dr, mu jenku ko babys d'ina, ta rik'o hannayen su suka shige. K'irjinta sai tafarfasa yake.

Cikin sauri AT ya tada motar sa ya bar wajen.

Tana tsaye jikin glass d'in window dashike irin mai kaman madubin nan ne tana gyara d'aurin kwalinta ya hangi bayanta. Kasa ci gaba da tafiya yayi sai mutuwar tsaye da yayi a wajen. Da sauri da sauri zuciyar sa ke bugawa.

Ta cikin mirrorn ta hangesa yayi tsaye yana kallon ta wanda hakan ya sauk'ar mata da fad'uwan gaba.

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*16*

*©Sameena Aleeyou....✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*Fatan Alkhairi k'awayen k'warai Sweetheart Rally Garba 😘 and Shawty 💕 Darling.... Love you guys from the bottom of my heart 😍*

Sajida tana hangosu ta tafi da sauri tana welcoming nasu had'i da basu wajen zama. Su Jamal tuni sun d'ale kan seats sun zazzauna. Shema'u ta wani juya idanu had'i da mik'ewa kafin ta shiga gyara ma Sajida zaman hular nata, with that fake smile on her face, fad'i take "Sweetheart I'm proud of you, kinyi kyau."

Sajida ta murmusa kafin tace "Aunty naji dad'i kinzo,.... Amma ina kuka baro Daddy.?"

Saida Shema'u ta d'an saci kallon su Jamal da hankulansu yafi karkata wajen d'alibai masu Cultural Dance sunyi shiga k'abila daban-daban kana tace "Baby you know your Dad when it comes that social climber,.... Uhm sorry nasan dai k'awarki ce kin d'auketa 'yar uwa, I just couldn't stand her ne, haba Daddyn ku fah har mun iso nan dashi kawai Hajiya ta masa waya ta ringa salle shi da masifa wai Maryama bata taho ba, babu yanda Daddyn ku baiyi ba ta hawo ko adaidaita ne ko taxi ta taho shi zai biya kud'in amma fir tak'i wai saidai shi yaje ya kawota, hmm Sweetheart I'm afraid she's stealing your Dad away from you... Amma kar ki damu kinada ni, bazan tab'a barinta tayi succeeding ba."

Tuni idanu Sajida ya soma kawo ruwa domin kuwa ana iya kiranta karb'an kyauta a koda yaushe, gashi tasha burin mahaifinta ya gani ya rakata su karb'a tare. Ganin haka yasa Shema'u saurin rungumota kafin tace "Oh no My Sajee, kinsan bana son ganin ki cikin damuwa, this is your Day, don't let anything ruin it for you, besides mu munzo ai, gani ga Siblings d'inki, we're all here for you sweetheart."

Gyad'a kai Sajida tayi kafin tace "Aunty what if aka kirani karb'an kyauta babu Daddy, Aunty babu Mummy na sannan shima baya nan, wa zai raka ni amsar kyautan.?"

Hannayen ta Shema'u ta rik'e cike da kissa kafin tace "My Sajee ni zan raka ki karb'a kar ki damu, I'm here, I'm here for you sweetheart, karma ki b'ata ranki kinji, oya koma seat d'inki, nida su Jamal zamu raka ki gaba d'aya da zaran an kiraki." Haka Shema'u ta ringa calming Sajida da makirci har ta yarda ta koma wajen zamanta, amma zuciyarta fam yake da haushin Mahaifin ta da Maryama.

*****************

Kasa ci gaba da abinda take tayi, gaba d'aya sai ta tsinci kanta da jin nauyin sa. A hankali ta juyo idanunta naga k'asa take fad'in "Sannu da zuwa Uncle."

Har lokacin murmushi bai gushe saman kyakkyawan fuskar sa ba, d'an takowa yayi yana mai karantar yanayin ta kafin ya amsa mata gaisuwar ta Ya k'arada "Congratulations, Allah Ya sanya Albarka."

D'an murmushi ta kuma yi kafin tace "Ameen, na gode Uncle." Kasa cewa komai sukayi daga ita har shi kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar sa.

Ita dai Maryama nauyinsa take ji, yayinda AT ya rasa meke faruwa dashi a Al'amarin Maryama.... Hajiya ce ta k'araso cikin cancatewar ta leshi mai jida kyau da tsada, abinka da farar fata sai tayi kyau sosai, yanyin jikinta AT ya d'auko sam jikinsu bai nuna tsufa. Takowa take tana fad'in "A'a Attahiru har ka iso d'in ne, ai sai muyi mu tafi kar mu kuma lattti ko." ta k'arashe tana gyara d'aurin kwalinta jikin madubin window.... Ba Maryama kawai ba harta AT saida Hajiya ta basa dariya yanda take karkata d'aurin kwali.

D'an durk'usawa yayi kafin ya gaidata, Hajiya kam hankalinta fa sam naga cancad'a d'auri take amsa ma AT gaisuwar sa.

"Hajiya kema zaki bukin yayen ne." Ya tambaya sanda ya mik'e tsaye.

Karkatowa tayi ta dubesa da kyau kafin tace " Attahiru wuce mu tafi babu lokaci, bana son dogon zance, yo kaima kaje balle ni."

Maryama kam tuni ta shige ta d'auko graduation gown d'inta da d'an hulan.

AT da Hajiya suka k'arasa yanda ya paka motar sa. Daga can yake hangota yanda tayi kyau sosai, ta d'an nad'e wuyar ta da farin Vail, sosai rigar bukin yayen nasu ya mata kyau. Tana shiga AT ya tada mota suka wuce.

***************

Shema'u dai sam hankalinta baya jikinta, burinta kawai taga b'ullowan AT da wannan tsinanniyar yarinyar.

Nan aka soma kiran d'alibai ana basu kyaututtuka da kuma testimonial d'insu na kammala sakandare. Anata kiran d'alibai d'aya bayan d'aya har aka iso kan Sajida.

Shema'u ta rik'o hannun su Jamal da Ni'ima suka nufi Stage gaba d'aya harda Sajidar daketa faman kallon k'ofar hall d'in ko Daddyn ta zai shigo shiru. Haka ta karb'i takardan shaidan k'arasa karatun ta na sakandare da kuma kyaututtukan ta babu Daddyn ta, k'walla da takaici tab suka taru mata, Shema'u sai karantar ta take tana jin dad'i.

Sanda su AT suka shigo Hall d'in dai-dai lokacin aka soma kiran Maryama ta karb'i nata ktaututtukan a matsayin ta na d'alibar da tafi ko wani d'alibi k'wazo....

Ana kiranta daga can baya ta d'aga hannu ta amsa, gaba d'aya Hall aka juyo ana duban su daga can yanda suke tsaye a bakin k'ofa.

Babu abinda yafi k'ona ran Shema'u kaman yanda taga hulan Maryama a hannun AT, wato ma shi ya rik'e mata. Sajida kuwa babu abinda yafi k'ona ranta kaman yanda taga Daddynta da Hajiya sun d'unguma sun raka Maryama karb'an kyaututtukan ta, sai hotuna ake masu don babu shakka ta amshi kyaututtuka masu yawa, Jamal ma ya rik'o hannun Ni'ima suka kutsa anayin hotunan dasu, AT ya kasa rufe baki, nan ya d'auki Ni'ima ya rik'e a kafad'an sa yayinda Maryama ta kamo hannun Jamal aka masu hoton, Hajiya na gefe ta cakare... Lol.

Su Fadila kuwa sai fad'i suke sunyi kyau, banda hararansu babu abinda Sajida take, Shema'u kuwa sai karantar ta take, a hankali ta sid'ad'e ta fice ta wani k'ofar dake gefe da ita kad'an.

Wayar ta ta ciro ta latsa bugu biyu ya d'aga.

"Hello kana jina, yanzu zata fito, kayi duk yanda zakayi ku bangaji juna, ka gane ai, I don't have to remind you." daga haka katse wayar tayi kafin ta dawo cikin hall d'in ta k'arasa yanda Sajida ke zaune can baya tana hawaye. Ta zauna had'i da dafata kafin ta kai dubanta ga AT dake faman gaisawa da manyan mutane irinsu Deputy Governor su Speaker State House of Assembly.

Sajida ta d'ago tana dubanta kafin tace "Aunty ki gani fah ko nemata basuyi ba, wllhi na tsane su."

Shema'u ta dafi kafad'unta cike kissa kafin tace "Kar ki tsane su, wancan makiran zaki tsana, ita ta rabaki da kakar ki sannan tana k'ok'arin rabaki da Baban ki, amma ta Allah ba tata ba, Allah yaga zuciyarki baki rik'eta da komai ba sai alkhairi ita kuma ta maki halin 'yan adam butulu. Yanzu abinda nake so dake, kar ki nuna ma Daddyn ki komai, ki tashi kije waje kiyi refreshing don karma su gane kuka kikayi, they might be thinking you're jealous of Maryama tunda ta fiki yawan kyauta , especially Hajiya. Sannan da yamma I've a surprise for you." ta k'arashe tana wani murmushi.

Gyad'a mata kai tayi kafin ta mik'e ta fice.

Hajiya tana zaune tareda su Jamal sai raba masu snacks da drinks ake.

Maryama kuwa sai tambayan su Fadila take ina suka gano Sajida. Fadila ta tab'e baki tace "Ask me again, ni ina ruwana nasan yanda taje, k'ila tana wajen wannan Antin nata mai k'irar aljanai." sauran k'awayen sai dariya suke, Maryama kuwa b'ata fuska tayi. Fadila ta tab'e baki tace "Na you Sabi, ta dubi camera man tace "Ci gaba da d'aukar mu. Maryama ta sauk'e mata dundun wasa tace "Zaki sani ne."
Chapter 20 · 0% Book details