← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 63

Sashe 60

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana isa ya daki k'ofar da hannunsa yaji zafi.... Cikin sauri KB da Alonso suka jawo k'arfe suka bugama k'ofar nan ta bud'e... Hango Hisham da sukayi kwance a k'asa yayi mugun d'aga masu hankali, cikin sauri suka k'arasa kansa suna k'ok'arin ceto rayuwar sa...

AT kuwa yana k'arasowa ya finciko Hisham ya kai masa wata wawan naushi a hanci wanda saida yasa sa bud'e idanu babu shiri tamkar d'an maye.. Alonso da KB gefe suka matsa suna kallon ikon Allah, yau Dr AT ne da Dr Hisham a wannan yanyi..

Dukansa AT yake da iya k'arfinsa hawaye na bin k'uncinsa yake fad'in "You Animal I'll kill you, you're despicable wllhi Hisham sai na kashe ka..."

Da k'yar su KB suka janye AT ganin na shirin aika Hisham lahira...

Hisham ya tsuguna saman gwiwoyinsa yana tarin azaba... AT yaci gaba da fad'in "You're unbelievable, Hisham bansan kai meye a gareni ba, duk shekarun nan ashe kanada shirin da kake yi akaina, you're not Human Hisham kai ba d'an adam bane.... You'll rot behind bars and pay for what you did..." Ya k'arashe yana kuma yunk'ura zai capko Hisham...

Mik'ewa Hisham yayi yana layi yana nuna AT da yatsa yake fad'in "You're a coward AT, baka san su waye masu sonka ba bakasan su waye masu k'inka ba, abunda zan fad'a maka sai yafi komai d'aga maka hankali..." yasa hannu ya share jinin da ya gangaro daga bakinsa kafin yace "Aysha ba a had'arin mota ta mutu ba.... She was killed by your wife Shema'u, her very own sister..."

Girgiza kai AT yake yana duban Hisham yake fad'in "You gone insane, baka san me kake fad'a ba, hatred ya cika maka zuciya shiyasa kake magana marassa kan gado...."

Hisham ya fashe da dariya kafin yace "Shema'u ba iyaka abinda tayiba kenan, ta kashe Maama Juu sannan ita ke yunk'urin gurb'ata tarbiyan Sajida and lastly k'anan yaranka rayuwar su na cikin had'ari domin maganar da nake maka a yanzu zata kaisu..... Za'ayi masu fyad'e gaba d'ayansu daga Ni'ima har Jamal, so if I were you I won't waste time here zan tafi ceto rayuwar yarana..."

Bai kai aya ba AT ya kuma kai masa wata wawan naushi yana fad'in "You imbecile I'll kill you...."

Alonso ya dubi KB yace "Buddy let's call the cops let's go..." KB ya gyad'a masa kai suka fice a tamanin...

Hankad'e AT Hisham yayi yana dariya kafin yace "You miserable Coward na fad'a maka sai na karb'i land d'in mahaifina, it's mine... Snann idan kana ganin abinda nake fad'a maka k'arya ne nasan idan ka gani bazaka k'aryata ba...." Daga haka ya zaro wayarsa a aljihu yayi playing videon da Shema'u take k'ok'arin kashe Aysha...

Tamkar gunki haka AT ke bin Video d'in da kallo..... Momma da ahigowar ta wajen kenan itama daskarewa tayi had'i da k'unshe bakinta da duka hannayen ta biyu...

*Saminah Aliyu Mrs💖*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*49*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Sosai hankalin Maryama ya tashi sanda ta isa makarantar su Jamal aka sanar da ita cewa Aunt d'insu tazo ta d'aukesu, idanunta sukayi rau-rau lokaci guda bugun zuciyarta ya k'aru... Innalillahi kawai bakinta ke furtawa, gaba d'aya ta birkice ta rasa wanne zatayi.... Wayarta dake hannunta ne yayi k'ara wanda hakan saida ya firgita ta, tana ganin Ashfaq ne tayi saurin d'agawa lokaci guda ta fashe da kuka tana fad'in "Ya Ashfaq basu nan Aunty Shema'u ta d'auke su... Wllhi ta d'aukesu..."

Haidar ya dubi commissioner of police kafin ya girgiza kai yace "Sir sun baro makarantar na tabbata wajen Daddy na suka nufa...." commissioner ya gyad'a kansa kafin ya dubi ASP yayi masa alama da hannu... Sara masa ASP yayi domin tuni ya gane me yake nufi kafin ya wuce cikin sauri..

Wayar Maryama Haidar ya kuma dannawa kafin yace ta jira shi a wajen yana zuwa yanzu.... Commissioner ta wagan sa kuwa tuni sun d'auki hanyar guest house d'in VP..

*********

D'an napep gaba d'aya ya cika Hajiya da surutu ga traffic ya raba tsakanin su dasu Buzu.... Hajiya bata san sanda ta shiga sille sa ba, ita gaba d'aya tama rasa wani hanya suka nufa ga gari ya canza ko ina flyover.... Kaman ance ta kalli gefen hagu nan ta hangi Buzu na shiga wani guest in....

Talle k'eyar mai Napep tayi ta shiga nuna masa motar tana fad'in "Kaga mu shiga gidan karuwan can da ya shiga, maza muje nace idan bakayi sauri ba kuma ka bani..."

Mai napep ya shiga sosa k'eyarsa yanda Hajiya ta talla masa mari yana fad'in "Baaba bafa gidan karuwai bane Hotel ne...."

A harzuk'e Hajiya tace "Uwar otel ne ma, yo me ake a ciki banda bad'ala da b'arna ko kaga masu kamun kai a wajen ne inyi...." ta k'arashe tana huci...

Mai napep dai bai kuma cewa komai ba domin kuwa Hajiya ta zarce tunanin sa, duk son surutun sa dole yayi shiru....

********

Girgiza kai AT yake yana naman zubewa k'asa.... Murya na rawa yake furta "No... no, wannan ba gaskiya bane, No no no.... This can't be happening......" ya k'arashe yana dafe k'irjinsa dake barazanar rabewa.....

Momma kuwa tuni ta zube a k'asa sumammiya.....

AT yayi kan Hisham zai kai masa duka Hisham ya ciro bindiga a bayan wandon sa yayi pointing AT dashi, kan kace me ya harba masa a kafad'anshi yana wata irin kafiran dariya yake nuna AT da bindiga d'in yake fad'in "I've always known you to be a coward, be a man for once AT, ka kalle ka bazaka iya komai ba saidai kallo da ido....." ya kuma fashewa da dariya yana kallon AT dake durk'ushe rik'e da wajen da ya harbesa jini na zuba yana cije baki.. Da k'yar yake fad'in "You're an Animal Hisham.... Wllhi sai ka girbe abinda ka shuka....."

Hisham ya kuma fashewa da dariya ya k'araso yanda AT yake ya kai masa naushi a hanci nan AT ya fad'i k'asa ga zafin bullet ga jini na kan zuba.... Dariya Hisham keyi yana nuna sa da bakin bindiga yake fad'in "Tashi ka rama.... Da zafi koh nasan da ciwo, zan maka kisan gilla bayan na wulak'anta k...... Bai kai aya ba yaji sauk'ar katako a gadon bayansa..... A tare shida AT suka juyo suna dubanta ba kowa bace illa Momma, hawaye na bin k'uncinta tana rik'e da katakon da gani zaka gane k'arfin hali kawai tayi amma tana jin jiki..

Ganin Hisham ya nufi Momma yasa AT yayi ta maza ya mik'e ya kai mai naushi wanda saida yasa Hisham ya fad'i akan fuskar sa.... Duka AT yake masa irin dukan huce takaicin nan.... Bai ko kula da jini dake bin hannunsa ba sai dukan Hisham da yake tamkar an aiko sa, baka ko ganin fuskan Hisham jini ya rufe gaba d'aya... A haka su KB suka iso da polisawa suka taddasu, da k'yar aka k'waci Hisham hannun AT domin kuwa ya kusan aikasa lahira.... Take akayi arresting Hisham 'yansanda

AT bai daina fimcika yana so a barshi ya k'arasa Hisham ba....

KB na rik'e AT yana fad'in "Dr you're bleeding pls ka bari ayi treating naka..."

Girgiza kai kurum AT yayi yana nunawa KB Momma dake durk'ushe a wajen rik'e da k'irjinta sannan yace "KB just take care of her... My children need me... I've to go... Kar ka damu I'll be fine, bazan iya tsayuwa a nan ba alhali rayuwan yarana na cikin had'ari..."

Da k'yar ya k'arasa gaban Momma dake dafe da k'irjinta idanu rufe, jin ta ambato sunansa a hankali..

Momma taci gaba da fad'in "Tahir jikokina don Allah, Tahir kar ka bari Shema'u ta masu abinda tayi wa mahaifiyarsu, Tahir ka kula dasu don Allah, sannan ka rok'a mun su yafiya domin nice silan komai, kaima ka yafe min, ku yafe ni gaba d'aya hak'ik'a ban kasance uwa ta gari ba, sannan ban zamto Kaka abin alfahari ma jikokin ta ba.... Tahir kar ka bar Shema'u ta kuma kusantar jikokina na rok'i arzikin ka....." Momma ta kasa ci gaba da magana sai tattamke idanu da take tana dafe k'irjinta...

AT dake zuban hawaye yana damk'e da wajen harbinsa saurin ficewa yayi a guje cikin tsantsan tashin hankali....

Gudu yake a tsakiyan kwalta cikin tsananin tashin hankali.

*********

Haidar na isowa ya hangeta tsaye bakin kwalta, da sauri ya bud'e mata bayan taxi yace shiga muje... Cikin sauri Maryama ta shige tana fad'in "Ya Ashfaq naga wulk'awan motar ta mubi bayanta...."

Haidar ya gyad'a kai kafin ya dubi mai taxi yace "Malam mubi direction d'in da take nuna mana...."

Shema'u daketa faman kwasan gudu a kwalta tsawa ta kuma daka ma yaran tace "Zaku mutu yau zaku bi uwarku yanda ta tafi, shegu annoba kun hanani sakat...."

Jamal dake faman huci da d'an k'aramin hancin sa jawo Ni'ima yayi yana lallashinta kafin ya bud'e murya yace "Aunty pls kar ki kashe k'anwata kill me instead kinji....." Dariya Shema'u ta fashe dashi sanda ta waigo ta dubi yaran kafin ta kwaikwayi maganar Jamal ta maimaita abinda yace... Kunnensa ta jawo had'i da buga kansa jikin seat kana tace "All of you must die, no one should survive among you, makiri mai halin kakar sa....."

Jamal ya zuciya ya soma k'ok'arin bud'e lock Shema'u ta ciro takalmin k'afarta ta rik'e steering da hannu guda ta shiga tura d'aya hannun baya tana jibgan yaran da k'afar takalminta mai tsini.... Allah sarki sai kuka suke sun tak'ure waje guda...

Kan kace me tuni Mr President ya turo jet guda na soji garin Kano suna hanya basu sami isowa ba, IG kuwa da kansa suke communicating da Commissioner.... Sanda suka isa gidan already masu lek'en asiri masu tsaro daga main gate sun hango abinda ke wakana cikin unguwar ta hanyar amfani da cameras d'insu, take suka sanar da mai girma VP ... Ransa idan yayi dubu ya b'aci domin tuni 'yansanda sunyima unguwar zobe...
Chapter 60 · 0% Book details