Sashe 51
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AT ya shafi goshinsa a karo na biyu kafin yace "Toh Hisham wai ya zanyi ne, ya zanyi ne fisabilillahi.... Ni kaina ba son auren Maryam nake ba but banida choice...."
Hisham ya jinjina kai kana yace "AT don't say I didn't warn you, domin kai kanka kasan abinda kayi is a big mess...."
"Enough pls Hisham! Kar ka k'ara min more headache pls......." bai kai aya ba waya daga asibitin da aka kai Sajida ya shigo masa.... A zabure ya mik'e yana amsa wayar...
Cikeda tashin hankali ya dubi Hisham yace "Sajida tana asibiti, I've to go....." daga haka k'ofa ya nufa Hisham ya mik'e cikin sauri yabi bayansa.
********************
Tsaye suke cirko-cirko cikin parlorn Haidar wanda yake a Penthouse d'insa.....
Mari ya kuma watsa ma Haidar a karo na biyu, kafin ya d'ago hab'arsa yace "Ka sani there's a good and wrong way of doing things....."
Mummy dake gefe tana sharan kuka cikin sauri ta k'araso ta janye Haidar tana kallon yanda fuskar sa tayi jajazir abinka da farin fata... Fad'i take "Fu'ad kayiwa Allah ka k'yale yaron nan haka, kowa yana kuskure, ko so kake ka illata min shi...." Kallonta VP Fua'ad Mainasara yayi kafin yace "Duk laifinki ne, ke kika sangarta sa gaba d'aya shiyasa yake ganin yayi girman da zaici gashin kansa. Kuma na gama magana Haidar k'ofa bazai kuma ficewa ba har sai lokacin da ya nustu yayi hankali....."
Daga haka kallon Chief security na kula da al'amaran cikin gida yayi kafin yace "Make sure you locked him up..." daga haka ficewa yayi ya nufi sashen sa cikin sauri....
Mugun kallo ya rakasa dashi zuciyar sa na masa zafi, ji yake tamkar ya shak'esa ko zai huce takaici. Ba don health condition na mahaifiyar sa ba wllhi da ya sanar da ita Daddy shi ya kashe Nabila... Sanar da hukuma is pointless sannan sanar da Mummyn sa na nufin rasa rayuwarta.....
*Sameena Aliyu Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*42*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
Hankali tashe AT suka isa asibitin, kai tsaye Dr d'in da ya amshi case d'in Sajida suka samu, daga shi har Hisham d'in Dr baiji wani d'ar d'in sanar dasu komai ba sabida yasan su duka likitoci ne.... Daga office d'in Dr ward d'in da Sajida take suka nufa...
Shema'u na zaune saman faran plastic chair ta cika tayi fam, kana ganinta kasan hankalinta baya jikinta gaba d'aya a birkice take, Sajida na kwance saman gado drip mak'ale a hannunta na hagu...
Kallo d'aya Shema'u ta watsa masu had'i da kauda kai gefe zuciyarta na mata wani irin zogi da rad'ad'i.... Kallo Hisham ya bita dashi yana karantar yanayinta yayinda AT yayi kan Sajida a tamanin ko takan Shema'u bai bi ba..
Bandage d'aure a goshinta da hannunta maras cannula.. Tausayinta ya cika zuciyar AT, shafa goshinta yake a hankali yana furta "I'm here sweetheart, meyasa zakiyi haka ma kanki, why Sajida....?"
A hankali ta soma bud'e idanunta don kaman a mafarki take jiyo muryar mahaifin nata, aiko suna had'a idanu ta fashe da wani irin kuka ta fincika zata tashi AT yayi saurin rik'eta...
Kuka take sosai tana fad'in "I don't want to see you ever again, just get out of here.... Ka tafi Daddy banson ganinka.... Bana sonka, I hate you....."
Da sauri Shema'u ta matso ta rik'e Sajida sosai daga fincikan da take, rungume Shema'u tayi tana ci gaba da kuka take fad'in "Aunty I want to die, I don't wanna live anymore..... Aunty ina so nima na tafi na sami Mummy zaifi mun wannan rayuwa mai k'unci da zanyi...." kuka yaci k'arfinta.
Shema'u ta k'ak'aro hawaye tana girgiza kai take fad'i ma Sajida "Ki daina fad'in haka Sajee, kiyi hak'uri kinji sweetheart.... I'm here kinji koh, ki daina fad'in mutuwa yafi maki kar Allah yayi fushi dake...."
Hisham ya janye AT suka fice daga d'akin, kana ganin AT kasan a birkice yake gaba d'aya, idanunsa sun kad'a sunyi jazir...
Fuzar da iska ya kuma a karo na babu adadi kafin ya dubi Hisham yace "Hisham she's not normal, she need a therapist, muyi transferring nata to hospital d'inmu tunda kana....." Hisham ne ya katse sa da fad'in "Karma ka soma wannan tunanin AT idan akwai mai buk'atan therapist toh kaine, ai dama kasan dole irin haka ta kasance.... Kaima kasan definitely dole reaction d'inta ya zama haka, implications d'in da nake jiye maka kenan, sannan ita kanta Maryamar bakasan yaya zaka kwashe da ita ba...."
Mugun kallo AT ya watsa masa kafin yace "Shut the hell up Hisham! don't give me more headaches here.... Just pls give me a breathing space, you are not helping at all .... Gajeren tsaki yayi sannan yayi ficewarsa daga asibitin gaba d'aya... Hisham ya bisa da mugun kallo kafin ya tab'e baki.... Tunani ya somayi, tabbas yanzu Shema'u bata gaban AT gwara tun wuri yasan me yake ciki, wllhi yanda ya taimaka mata ta mallaki AT dole ta taimaka masa ya mallaki abinda ya jima yana buri, dole su k'arasa abinda suka riga suka soma.... Yana cikin wannan tunanin Shema'u ta fito ta riske sa. Murmushi ya sakar mata kana yace "Kin fito a dai-dai ina muka kwana, kinsan gwara nasan matsayi na tunda ga dukkan alamu kin kusa zama stohuwar yayi...."
Saida ta waiga gefe da gefe taga babu mai zuwa kafin ta janyo Hisham suka d'an fice wani k'ofa.
"Meye kika kawo mu nan.?" ya tambaya yana dubanta...
Gajeren tsaki tayi kafin tace "Muna tsaye a can wani zai iya jiyo mu, ina Tahir...?"
Hisham ya dafe hannunsa da garu kafin yace "Ya tafi wajen sweet 18 d'insa...."
Murmushin yak'e Shema'u tayi wanda hausawa ke cema kafi kuka ciwo kana tace "Kutumar uwar 18 d'in, wllhi yarinyar nan sai tasan ta aurin mijin wata, sai na maidata abin kwantance, dukkansu sai na shayar dasu mamaki har shi mai budurwar zuciyar...."
Hisham yayi tak'aitaccen dariya kafin yace "Ni dai damuwata ki tabbata na mallaki takardun filin nan tun kinada sauran amfani kafin ki k'arasa komawa k'arfan 'yan gwan-gwan..."
Shema'u ta kuma murmusawa kafin tace "My Ally kenan, kasan without me bazaka cimma burinka ba, sannan nima idan babu kai burina bazai kammala cika ba, yanzu mu d'au next step, zamuyi utilizing wannan opportunity d'in na rashin lafiyan Sajida, kasan AT yaransa sune rayuwar sa...."
Tuni Hisham ya d'ago me Shema'u ke nufi, Murmushi ya sakar mata kafin yace "Allah rabamu da kaidin ki..."
Itama murmushin tayi kafin tace "Kaga na samu hanyar rabashi da shegiyar yarinyar kafin na bijiro mata da wani bala'in da hankalinta bazai d'auka ba..." ta k'arashe tana wani kafiran murmushi...
************
Gidansa ya wuce kai tsaye domin ko zarafin zuwa gidan Hajiya bai samu ba, gaba d'aya abun ya d'aure masa kai, Aysha ce ta fad'o zuciyarsa. A hankali ya lumshe idanun sa, sam Sajida da ba haka take ba, quite alright yasan batada wayo but baisan wautan nata har ya kai haka ba, sau biyu kenan tana attempting abu makamancin haka.... Dafe kansa yayi da duka hannayen sa biyu lamarin ya hanasa sukuni gaba d'aya.
Sallah kurum AT yake tashi yayi don ko fita ya kasa...
Yana nan zaune a parlorn har wajajen k'arfe 9:30pm kaman daga sama yaji ana tab'a k'ofa.
D'ago idanu yayi yana dubansu cikeda mamaki don bai zaci za'ayi discharging nata yau ba idan da tashine da an barta a asibiti ta k'ara recovering, sannan ko sallaman ta akayi bai zaci zata yarda ta dawo gida cikin lumana ba, yasan wannan aikin Shema'u ne, akan yaransa zata iya yin komai sabida k'aunar da take masu..
Shema'u na rik'e da Sajidar suka k'arasa shigowa.... Ko darajan gaisuwa bai samu daga Sajida ba tayi wucewarta upstairs, Shema'u ta dubeta tace "Sajee are you sure zaki iya haye matakalan ko na rik'e ki....?"
Girgiza kai Sajida tayi murya can k'asa tace "Zan iya Aunty..." daga haka ci gaba da d'ingisawa tayi har ta haye bene..
Ko kallo AT bai ishi Shema'u ba tasa kai zata shige.... Saurin mik'ewa tsaye yayi ya sha gabanta, k'warjininsa ya hanata kasa furta komai sanda idanunsu ya had'e waje guda.
A hankali ya furta "Thank you, thanks for everything..."
Idanun Shema'u yayi rau-rau amma ta dake tace "I only did what I had to do...." Daga haka bata jira amsar sa ba tayi wucewarta upstairs tana matsan hawaye... AT yabi bayanta da kallo jikinsa duk a Mace, gani yake sam bai kyauta ma Shema'u ba...
Kaman daga sama ya jiyo knocking cikin sauri ya k'arasa ya bud'e, ganin Hisham ne yasa sa basa hanya ya shigo. AT bai ce masa komai ba don har yanzu a shak'e yake dashi, ya k'arasa saman couch ya zauna, Hisham d'inma zama yayi cikin d'aya daga cikin kujerun ya k'urawa abokin nasa idanu.
AT ya d'an dubesa kaman bazaice komai ba sai kuma yace "So kai ka kawo su kenan.?"
Hisham ya jinjina kai kana yace "Nayi magana da Sajida da taimakon Aunt d'inta Shema'u. From what I observed she's quite devastated, and nothing is wrong with her sanity, kawai dai tana buk'atan space domin kuwa abun da ya faru yayi matuk'ar b'ata mata rai, just put your self in her place zaka gane me nake nufi.... Sannan magana ta gaba da nake tsoron sanar da kai shine...." shiru yayi baici gaba ba sai dunk'ule hannayensa da yayi ya d'aura hab'arsa akai.
AT ya gyara zama kafin yace "umhum go ahead, me tace..?"
Hisham ya fuzar da iska kafin yace "Cewa tayi the moment aka kawo Maryama cikin gidan nan a matsayin matar ka zata sha poising ko kuma ta shiga duniya, don bazata iya zama gida guda da aminyarta a matsayin matar Babanta ba...." Daga haka mik'ewa tsaye yayi hannayen sa cikin aljihu..
Mik'ewa AT d'ima yayi zuciyarsa cikeda shakkun abinda abokin nasa ya gama sanar dashi... Har farfajiyan gidan AT ya raka Hisham kafin ya komo cikin gidan.
Ya jima yana kallon k'ofar d'akin Sajida kafin ya nufi d'akin Shema'u, tana zaune bakin gado tana shafe jikinta lotion ya shigo....
Sarai taji shigowar sa tayi masa banza.
Cikin takunsa na k'asaita ya k'araso har gabanta, da sauri ta mik'e zata shige bathroom AT yayi saurin rik'ota yace "Shema'u pls we've to talk..."