Sashe 45
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sati guda Hajiya da Maryama suka tattara suka koma Janbulo, babu yanda AT baiyi ba su zauna Hajiya tak'i hakan a cewarta idan don yaransa ne akwai mai kula dasu tunda yanada Mata sannan 'yaruwa ga mahaifiyar su.
AT kuwa daga asibiti kusan kullum a gidan Hajiya yake yini.
Maryama ta shige d'akin Umminta tana kallon kayayyakin ta da wasu abubuwan ta, tanayi tana hawaye, gaba d'aya ta zama abin tausayi. Idanunta suka sauk'a kan wani d'an k'aramin akwati wanda Marigayiya ta haneta da tab'a akwatin tun tana k'arama.
Gaban Maryama ya yanke ya fad'i, cikin sauri ta shiga goge hawayen ta kana ta nufi yanda k'aramar chase d'in take cikin wardrobe. D'aukowa tayi ta dawo saman gado ta zauna. K'irjinta na bugawa da sauri da sauri ta soma bud'ewa.
Wata sark'a ta gani wanda ba sai ance maka na zallan Diamond bane, tasha mamakin ganin wannan sark'a cikin 'yar akwatin dukda batasan yanayin tsadarta ba tanada kyau sosai.
Murmushi tayi ta rungume sark'an cikin k'irjinta kafin ta furta "Ummi ina sonki, na tabbata wanda ya d'auke min ke ya fini k'aunarki, Allah Ya gafarta maki ya had'a fuskokin mu a darussalam, yanda zamu dawwama muna rayuwa babu mutuwa." Samun kanta tayi tana mai jin nutsuwa cikin zuciyarta bayan ta k'arashe karanto addu'o'i ma Ummin nata. A hankali ta soma saka sark'an a wuyarta tana mai murmushi bushesshen hawaye saman fuskar ta, tabbas itada wannan sark'a mutu ka raba ne, babu abinda zai sakata cirewa sai mutuwa.
Bata kuma bincike akwatin ba ta rufe dukda akwai kaya a k'asa an rufe da wani zani, sam Maryama bata lura da hakan ba, hankalinta yafi karkata kan wannan sark'an.
Ciccib'an akwatin tayi ta maidasa wajen zaman sa.
*********
Sosai Ahsfaq ya shiga matsanancin tashin hankali da mutuwar mahaifiyar Maryama, kullum ya kwanta sai yayi mafarki da matan tana kiransa da asalin sunansa tana fad'in _Haidar ka kula min da d'iyata Maryam, kar ka bari rayuwarta ta salwanta, ka kasance miji kuma garkuwa a gareta ta haka ne kurum zaka iya bata kariya._ amma bai iya tantance fuskar ta sannan muryar yana masa kama da ya tab'a ji wani wajen, Sosai abin ya damesa. Duk ya had'a zufa sharkaf ya zauna saman gado, a hankali ya karanto addu'ar tashi a bacci.
Toh idan matar da yake mafarki da ita mahaifiyar Maryama ce kenan tasan sa kenan, meyasa muryar ke kiransa da Haidar. Ya ja numfashi sannan ya fuzar, kai kodai tsaban son Maryama da yake yi ne ya sakata cikin ransa har yake irin wad'an nan mafarkai...? Toh amma ba sau d'aya ba sau biyu ba yayi, kai gaskiya yana son Maryama sannan zai nemi aurenta koda hakan ka iya jawo fallasan asalin sa...... Da wannan ttunani ya mik'e yana k'are ma asalin kamannin sa kallo jikin mirror.
A b'angaren Buzu kuwa gaba d'aya yayi la'asar, duk barikancinsa bazai iya kashe rai ba, hasalima shi ko yanka ne baiyi ma Hajiyar sa Malam Sallau mai gadinsu keyi, gaba d'aya jinsa yake wani iri, duk wani d'abi'un sa na banza ya watsar dasu. K'arewa ma canza sim d'insa yayi sabida Sajida da Shema'u, shi a halin yanzu tausayin Maryama da soyayyar ta yafi cika zuciyar sa, son gaskiya da aure yake mata. Ya k'udiri niyyan zai nemi aurenta ya zame mata garkuwa daga Shema'u koda hakan na nufin rasa numfashin sa, tunda shi yasan waye Shema'u sannan muddin Maryama ba aure tayi ba Shema'u bazata k'yaleta ba, data salwantar mata da rayuwa gwara ya aureta ko Yemen ne wajen dangin iyayen sa gwara su koma..... Yini zubur tunanin da Buzu yake kenan, yana neman mafita ta yanda zai rabu da Sajida cikin sauk'i.
*******
Sosai abin ya soma damun AT ganin Ashfaq da Buzu basuda wajen yini da ya wuce gidan Hajiya, shima gashi nan rabin yininsa bayan tashi daga wajen aiki a gidan yake, watarana ma tareda Ashfaq suke isowa gidan. Sannan kowa nuna damuwar sa sosai yake akan Maryama, kowa so yake ya burgeta ya mantar da ita halin k'unci da take ciki.
Koda Hajiya taga Maryama da sark'an sam bata hanata sakawa ba, sosai taji dad'i ganin Maryama ta soma sakewa, sannan Sajida ma ta rage hantaran Maryama da take a baya. Har wuni AT ke kawosu gidan Hajiya gaba d'aya yaran don suma su rage kewar da suke ciki....
**********
Tunda ta kwanta take wasu irin mugayen mafarkai, wasu halittu na binta basuda kai balle ta gane kamannin su... Firgita take sosai, idan ta farka tayita gumi kenan kaman an jefata cikin wuta. Ga wani irin zafi da jikinta keyi muddin tayi mafarkin...
*********
Bayan wasu satattuka su Jamal sun koma makaranta, Maryama da Sajida sun shiga computer school, rayuwa ta soma koma masu kaman ta baya, musamman dukan su biyu idan suka tuna sun rasa iyayen su, daga Maryamar har Sajidar, wani sabon SHAK'UWA CE ta soma shiga tsakanin su, Sajida a kullum da tunanin Buzu take kwana take tashi, gaba d'aya ta rasa ta yanda zata sameshi nan ta yanke shawarin sanar da Maryama ko zata taimaka mata.
************
Wani irin muguwar fad'uwar gaba ne ya sauk'o masa jin Mummyn sa na kuka da hawayenta sabida shi.
_Haidar don Allah ka dawo gareni kafin ka rasani..._
Kalman dake kan faman yawo a kunnensa kenan wayar da sukayi da Mahaifiyar sa a daren jiya. Wata b'angare na zuciyar sa kuwa muryar mahaifiyar Maryama ya kasa b'ace masa.
_Haidar kai kad'aine zaka iya zama garkuwa a gareta, ka auri d'iyata domin ka zame mata kariya.._
Runtse idanunsa yayi bugun zuciyarsa na k'aruwa da sauri da sauri, ga kansa da yayi masa nauyi yana neman mafita.
********
Sajida ta gyara zamanta ta kuma rik'o hannun Maryama cikin nata kafin ta soma fad'in "Ki yafe min duk wasu abubuwan da na maki, kinsan zuciya batada k'ashi, all I was thinking shine Daddy sonki yake amma yanzu na aminta SHAK'UWA CE kawai a tsakanin ku da Daddy sannan yana maki irin son da yake mana ne a matsayin d'iya. Maryama pls ki yafe min kinji." ta k'arashw tana k'ak'aro murmushi
Murmushi Maryama ma tayi tausayin kanta ya lullub'e ta, da ace Sajida tasan yanda Allah Ya jarabceta da soyayyan mahaifinta da bata soma fad'in haka ba, but this shows itada Uncle can't never be together, dole ma ta cusa ma ranta ta tursasa ma ranta cireshi daga cikin zuciyarta.... Dole ta amince SHAK'UWA CE kawai a tsakanin su. Kaicon zuciya irin tata wanda bai hasasho abu dai-dai.
K'ak'aro murmushi Maryama tayi had'i da hugging Sajida cikin rawar murya take fad'in "Sajida ban rik'eki da komai ba, nima ki yafe min don Allah kinji..."
Sajida tasa hannu ta shiga share ma Maryama hawayen ta.
Hajiya dake zaune cikin parlor tana hangosu daga veranda ta sa hannu ta goge k'wallan da suka zubo mata tausayin yaran ya cika zuciyarta.
Kaman daga sama suka jiyo sallaman Buzu.... Gabansa ya yanke ya fad'i ganin Maryama da Sajida a tare...
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*38*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Gaisuwa da babban murya gareku masoya wannan labari, Sameena na k'aunarku a duk yanda kuke ❤👌🏾*
_Masu k'orafin na bud'e shafi a wattpad sabida labarin ya ringa isa maku cikin sauk'i naga sak'onku, banyi alk'awarin bud'e shafi a wattpad amma insha Allah zan duba na gani idan da hali zan bud'e, na gode k'warai da nuna k'aunarku 🤝_
Shafa kansa Buzu ya d'anyi kafin ya isa k'ofar parlorn Hajiya yana sallama.
Hajiya ta masa iso ya shiga ya soma gaida ta, gaba d'aya hankalinsa naga waje yanda su Maryama da Sajida ke zaune, sam bai samu sakewa a gidan ba.
Koda ya fito Maryama ce kawai ta sami zarafin gaidashi Sajida kam k'uri ta masa tana jira taji ko zai mata magana shiru..... Bai sami zarafin jimawa a gidan ba, sauri-sauri yayima Hajiya sallama ya fice.
Sam Maryama bata lura da yanayin k'awar tata ba, sai bayan sun k'ule a uwar d'akin Hajiya Maryama ta lura da canzawan Sajida. Dole Maryama ta tasa Sajida a gaba ta fad'a mata abinda ke damunta.
Sosai Maryama ta tausaya ma Sajida, tabbas ta sani tana tsananin son Haris sannan ta sanadiyan Sajida suka saba da shi, wannan karan kam ta d'au alwashin zatayi iya k'ok'arinta wajen ganin Haris ya sauk'e idanunsa kan 'yaruwarta kuma k'awarta, sam bata k'aunan abunda zai kuma kawo masu sab'ani musamman yanzu da Sajida da k'annenta suka tareda zama gidan Hajiya, idan kaga sun tafi gidansu toh weekend ne, hakan yasa attention d'in AT kacaukam ya koma gidan Hajiya, sam Shema'u bata gabansa, wani sa'in har fad'a yakema kansa kar Allah Ya hukunta sa da hakkin Shema'u.
Daga Ashfaq har Buzu yanzu AT ya d'an d'aga masu k'afa ba kaman da ba, ko yayi niyyan fatattakan su ma Hajiya ke hanasa.
***********
Hankalinta duk ya gaza kwanciya, Buzu yayi disappointing d'inta, ga wayan da Alh Aminu ya matsa mata dashi yana so yazo wajenta, nan ta soma tunanin ai gwara yazo ma ta samu kud'i tasan ta yanda zata soma b'ullo ma Al'amarin Haris Buzu da kuma Ashfaq, babban abinda yafi d'aga mata hankali shine yanda yaran gaba d'aya suka gujeta lokaci guda suka koma gidan Hajiya, kai dolema tasan abinyi if not k'ura babba na neman b'arke mata....
**********
Bayan kwana biyu Maryama na faman zullumin maganan da Buzu ya fad'a mata, ta kasa aminta wai shi tuntuni k'aunarta yake, sam bata tab'a kawo soyayya yake mata ba, a iya tunaninta SHAK'UWA CE kawai a tsakanin su. Tirk'ashi lallai Haris yana neman ya jangwalo mata wani aikin.
Tunda wannan magana ta shiga tsakanin Maryama da Buzu ya rage zuwa gidan, domin kuwa cikeda fad'a ta sanar dashi sam babu d'igon soyayyar sa a zuciyarta, sannan ita ba aure zatayi yanzu ba, sai ta cika ma Uncle burinsa na ganin cewa tayi karatu sosai....
Wani sa'in harejajensa Hajiya keyi.
Kwana biyu da faruwan haka Ashfaq ma yazo da nasa batun, sosai hankalin Maryama ya tashi, me suka maidata? Dama duk wannan kulawa da suke bata sunada wata manufa akanta, lokaci guda ta canza masu gaba d'aya ba kaman da ba, idan suna waje ma bata zama. Tamkar me juju haka ta koma, wani irin tasanar su take ji.