Sashe 29
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai kuwa sosai tayi murna da kyautar, Hajiya ma sosai taji dad'in kyautar AT d'in, nan kuma yake sanar da Hajiya zai saka su a makarantar koyon computer ita Maryam d'in da Sajidar kafin jarabawar su ta fito, Hajiya tayi na'am da hakan. Maryama ma taji dad'i sosai tai masa godiya, cikeda zumud'i ta kinkimi laptop d'in ta wuce sashen Maama Juu don ta nuna mata..
Tahir ya bita da kallo har ta shige yanda taketa murna, sosai zuciyarsa tayi sanyin ganinta cikin farin ciki, gyara zamansa yayi da kyau ya dubi Hajiya kafin yace
"Hajiya dama akwai maganar da nake so muyi gameda maganar aure da kika min jiya."
Hajiya ta washe baki tace "Kai Masha Allah, yau dai Attahiru ka faranta min rai, kai naji dad'i sosai, asirin Kulu da d'iyarta Allah Ya warware maka, toh wacece surkan tawa kuma a ina take..?"
Dummm! K'irjin AT ya buga yana tunanin yanda zasu kwashe da Hajiya..
Daurewa yayi ya soma magana domin kuwa bashida zab'in da ya wuce ya sanar da Hajiya dukda baiji ta bakin ita kanta Shema'un ba...
"Kai nake saurare Attahiru." muryar Hajiya ya katse sa.
"Dama... Dama Shema'u ce nake tunanin ko zan nemi aurenta tunda naga yaran suna k'aunar ta kuma....... 'yaruwan mahaifiyar....... "
Bai kai aya ba Hajiya dake faman huci tana jin zancen nasa kaman sauk'an aradu ta dakatar dashi da fad'in "Rufe min baki shanyayye kawai, yo ko mata sun k'are a duniya zan barka ka auri wannan zabon ce, kod'add'iyar da ta gama gantalinta a titi, Attahiru anya basu juya maka kwanya ba..." Ta shiga tafe hannaye tana sallallami...
Maryama da ke tsaye k'ofa k'arasowarta kenan batasan lokacin da hawaye suka shiga zarya a kumatunta ba..
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*23*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
Ta yanda take shiga bata nan take fita ba, sai faman huci kurum take tana salle AT.
"Inyin, don ka rasa mafad'i a doron k'asa sai na zuba maka idanu ka auri sauran titi, wannan da k'yar idan aka aunata ba'a sameta da cutan zamani ba, banda jaraba irinta d'anamiji har uwan me ka hanga a jikinta kaji ta maye gurbin Aysha, inyi. ...."
AT ya d'ago idanu cikeda mamaki yana dubanta, harga Allah halin Hajiya ya soma isan sa, yaya tana mahaifiyar sa zatake fad'an maganganu haka, shi ko nauyin 'ya'yan fari da manya keyi da yaransu sam Hajiya batayi dashi, k'ila don bashida k'anne ne shiyasa take yin hakan... Muryarta ya kuma dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi..
"Tashi, tashi ka fice min daga gida nace, shanyeyye kawai, idan da batun da zaka zo min kenan kar na kuma ganin sawayenka a gida na..." ta k'arashe tana sauk'e labulen k'ofa da k'arfin gaske.
Daga yanda take tsaye hawaye sharkaf a k'uncinta, tausayin sa ya cikata ganin ya fito jikinsa babu laka.... Saurin juyawa tayi a tunaninta AT bai ganta ba... Shi d'inma bai iya tab'uka komai ba sai kallo da ya bi bayanta dashi har ta shige... Da k'yar yaci gaba da d'aga k'afafunsa har ya isa yanda motar sa take...
Driving kawai yake amma harga Allah baijin yanada buk'atar wata mace bayan Shema'u baisan dalilin ko don ita 'yar uwar Aysha bace yake jin wannan feelings d'in a game da ita ba oho, all he knows shi ne yana tsananin buk'atar Shema'u abin har mamaki yake basa... Da haka ya isa gida ana kiraye-kirayen sallan La'asar...
A can wajen swing ya hangesu gaba d'aya suna zazzaune su Momma dasu Shema'u da Sajida suna saman grass carpet suna hiran tafiyar Momma da zatayi a gobe, yayinda Jamal da Ni'ima ke saman lilon.. Idanunsa k'yam akan Shema'u, take ya soma karanto addu'o'in tsari daga shed'an ya nufi cikin gida, gaba d'ayansu babu wanda ya kula da dawowar sa don ko k'aran bud'e gate basuji ba dashike ana tonon borehole a mak'otansu.
Tunanin abubuwa da dama suke yawo a kwanyar sa, hawayen da ya gani kwance fuskar Maryam shi ya hanasa kwanciyar hankali, yana son tambayarta meke damunta, yana son sanin halin da take ciki, toh waima me yasata kuka..? Wata zuciya ta basa amsa da _Fad'an da Hajiya tayi maka ne.._ A hankali ya lumshe idanunsa abubuwa da dama suka cigaba da yawo a kwanyar sa...
Kotakan sabon laptop d'in nata bata bi ba, itakam sam bataso Uncle ya auri Aunty Shema'u, idan ya aureta shikenan bazata daina ganinta ba har abada, sam zuciyarta bata son Aunty Shema'u da Momma ta tabbata Aunty Shema'u is playing innocent ne, jikinta na bata she's wicked ba son yaran Uncle take ba, meyasa Uncle zaice yana son aurenta.... Wani sabon hawaye ya kuma wanke mata fuska, jin Hajiya ta bud'e labule ta shigo tana mai ci gaba da sababi don har lokacin bata daina sababi ba, tuni Maryama ta lumshe idanunta tamkar mai barci..
*****************
*Abuja, birnin tarayya*
Misalin k'arfe 3:00am Vice president ya shigo gidan, idan da sabo Hajiya Maryam ta saba wani sa'in mijin nata a wajen meeting yake kwana.
Yasha mamakin ganinta yau idanunta biyu batayi bacci ba, da murmushi saman fuskar sa ya k'araso ya zauna gefenta had'i da kwab'e babbar rigar sa... Ganin bata kulasa ba yasa shi kamo 'yan yastun hannunta yace "Ayimin hak'uri Maryama kinsan yanayin aikin nawa da kuma hidima da jama'a ga election na k'aratowa bama so mu rasa muk'anman mu.."
Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta soma fad'in "Ni jimawanka a waje sam baya damuna tunda idan da sabo na saba tun ina damuwa ina tunanin ko zaka daina tun kana deputy governor baka daina ba balle yanzu da kake a matsayin mataimakin shugaban k'asa, ni abinda ke damuna kawai shine yanda ka fifita muk'aminka a gwabnati fiye da iyalanka, fisabilillahi yanzu haka zamu ci gaba da zama babu Haidar.."
Bata kai aya ba ya mik'e yana cire links d'in hannun rigar sa... Hajiya Maryam ta mik'e tana dubansa kafin tace "Your excellency magana nake maka, na gaji da zama babu d'ana don Allah ka janye k'udirinka na aura masa Fairuzah k'ila ya dawo garemu..." ta k'arashe cikin rawar murya..
Kallonta yayi yana huci don shi kad'ai yasan irin hukuncin da ya tanadar ma Haidar, murya a dake ya soma fad'in "Maryama, a yau idan ina so a zak'ulo min Haidar a fad'in k'asar nan za'a zak'ulo min shi amma bata nasa nake ba tunda rayuwar da ya zab'a ma kansa kenan yaga yafi masa sauk'i fine yaje yayi tayi amma nidai kam bazan bisa ina lallashinsa ya dawo gareni ba, yaron da na masa rana a rayuwa, yaron da na fifita sa fiyeda......" Shiru yayi bai k'arasa maganar nasa sannan ya fuzar da iska yace "Maryam kiyi wa Allah ki cire damuwar Haidar a ranki, abu guda tak na tambayesa bayan duk halaccin da na masa Ya kasa min ya watsa min k'asa a idanun duniya bayan na gama tara jama'a, ya nuna min shid'in ba d'an halak bane, ko kinsan har yau mahaifin Fairuzah na kallona da abin, sannan ba lallai ya amince ya kawo mana k'uri'un da muke samu na manyan 'yan kasuwa daga garesa ba, Haidar failed me yayi niyan yayi ruining d'ina ne if not meyasa tuntuni baik'i amince ma auren Fairuzah ba sai ranar d'aurin auren a wayi gari baya nan, ko kinsan zafin ka tara manyan mutane daga k'asashe daban-daban ai maka irin wannan cin fuska... Koda shike ba laifinsa bane dama dole yayi irin hakan.... " Da sauri Hajiya Maryam tasa hannu ta toshe masa baki tana girgiza masa kai take fad'in "Dan Allah kar ka tab'a fad'a mishi, Haidar d'anmu ne wllhi d'anmu ne,..." ta k'arashe cikin kuka..
Saurin rungumota yayi yana mai jin zafin kukan da take, tabbas yana tsananin son Maryama soyayyar da bazai tab'a bari tasan babban laifin da ya tapka ba.....
*****************
*Kano*
Tsaye yayi gaban doguwar mirror dake manne cikin closet d'insa yana k'are ma kansa kallo, kana ganin fuskar sa ba sai ance maka yanada damuwa ba, babban abinda yafi d'aga masa hankali shine a daren jiya har mafarki da Shema'u yayi wanda dama baccin satansa tayi, wannan wani irin masifa yake k'ok'arin aukawa ciki, tabbas Allah Ya jarabce sa, bashida mafita da ya wuce ya auri Shema'un idan har zata yarda dashi..... Yana tsaye yana wannan tunani kunnensa ke jiyo masa kaman hayaniya daga k'asa, kuma muryar tamkar ta Hajiya, gabansa ya yanke ya fad'i.
Cikin sauri ya nufi downstairs k'irjinsa na ci gaba da bugawa, saida ya sauk'o parlor yaga ashe hayaniyar ma daga waje take shigowa... Cikin sauri ya nufi k'ofa..
Nan ya hangi kayan Momma jikin trunk d'in motar SShema'u na gefe ta rik'e Sajida dake zuban hawaye yayinda Hajiya da Momma aka rasa mai bama wani hak'uri, ko wacce gaya ma 'yaruwarta magana take...
"Wllhi Kulu duk tsiddabarun da kuka zuba wa d'ana sai Allah Ya maidashi kanku, bacin haka har yaushe Attahiru zai soma maganar auren wannan mai suffar agwagwan..." ta k'arashe tana nuni da Shema'u...
Daga Shema'u har Momma a sama suka tari zancen, kenan AT yana son auren Shema'u, dad'i ya lullub'e Shema'u ta kuma rik'o hannun Sajida tace "Muje ciki sweetheart kinji.... " Ai kan tayi wani yunk'uri Hajiya ta fizgo wuyar ta baya tana fad'in "Ki shiga ina, ai yanda kikaga uwarki ta fito toh kuwa binta zakiyi, annoba kawai, tunda kuka zo gidan nan hankula basu kwanta ba, munafuka ni tunda naga kina nan-nan da yaran nan nasan da biyu kikeyi, kin lik'e ma mijin k'anwa banda asara, gadon jaraba gadon Kulu..."
Har wuya AT yazo ganin a gaban Sajida Hajiya take wad'an nan maganganun, cikin sauri ya juya ya koma cikin gidan... Shema'u ta bisa da kallo kaman ta zuba ruwa a k'asa ta sha, cikeda makirci take bawa Hajiya hak'uri tana rok'onta tayi shiru ko don Sajida.... Gaba d'aya Hajiya ta had'e su gaba d'aya taci gaba da sille su...
Momma kuwa tunda Shema'u ta kwab'eta ta had'iye bak'incikinta don kuwa tabbas ta yarda da shawarin Shema'u ta ringa hak'uri da Hajiya har su sami biyar buk'atar su...