← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 63

Sashe 54

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AT murmushin jin dad'i yake yana dubansu gaba d'aya kafin Ya bud'e hannayen sa yayi hugging d'insu su duka biyu, cikin kunnen Shema'u ya rad'a mata "Thank you my Shemah"

Shema'u cikeda jin dad'i ta kuma lafewa cikin jikinsa....

**********

Washe gari Sajida ta shirya tsaf ta tafi gidan Hajiya, saida tayi timing lokacin da Hajiya ke islamiya kafin ta tafi gidan...

Maryama na kwance a parlor ta gama karance sak'on da Uncle ya turo mata ta jiyo sallamar Sajida... Gabanta ya yanke ya fad'i, cikin sauri ta mik'e zunbur ta zauna tana rarraba idanu...

To her greatest surprise murmushi Sajidar ta sakar mata kafin ta k'arasa shigowa ta zauna a gefenta...

Maryama ta rasa me zatace mata sai sadda kanta k'asa da tayi..

Murmushi Sajida ta kuma yi kafin ta kamo hannayen Maryama ta soma fad'in "Kar ki damu nasan ba laifinki bane, Maryama ki sani har abada ke 'yaruwa ce agareni, Daddy Ya aureki sabida ya raba alak'ar dake tsakanin mu, amma nasan nida ke bazamu tab'a rabuwa ba, nasan idan damuwa ya sami d'aya daga cikin mu toh babu shakka ya sami d'aya haka ne ko ba haka ba...?" ta k'arashe kaman zatayi kuka..

Maryam da hawaye ke gangaro mata cikin sauri ta shiga gyad'a mata kai alamun haka ne...

Sajida tasa bayan hannu ta goge hawayenta kafin tace "idan har hakane alk'awari d'aya nake so ki min..."

Maryama cikin muryar kuka take fad'in "Ki fad'a Sajida zan maki ko menene insha Allah..."

"Ki min alk'awari har abada auratayya bazai tab'a shiga tsakanin ku da Daddy na ba, idan kin min haka kin gama min komai, sannan idan kika sab'a alk'awarin wllhi wllhi nida ke har abada...."

Kaman an buga guduma haka k'irjin Maryama ya buga...

*Sameena Aliyu Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*44*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*Assalamu alaikum makaranta wannan littafi ina mai baku hak'urin jina da kukayi shiru na tsawon kwanaki biyu hakan ya faru ne sakamakon dakatar da rubutu da nayi sabida wasu uzururruka nawa da suka sha gaba na..... Amma duba da k'orafe-k'orafen ku zanyi k'ok'ari duk lokacin da na sami dama nai maku typing koda ba akai-akai kaman yanda aka saba ba.... Na gode k'warai da nuna k'aunarku a gareni.....🤝*

_Haly Mom Farhan_
_Sholingaye_
_Sadnaf_
_Maman Aysha_
_Halima MK_
_Mrs Mansoor_

*Ina mik'a gaisuwata a gareku ❤🤝*

Girgiza kai Maryama keyi tana duban Sajida cikeda mamaki, ta kasa yarda wad'annan kalaman daga bakin Sajida suke fitowa.... Kai tasan halin Sajida tasan kalan sangartar ta da kuma wautanta wannan tunani ya girmi tunanin Sajida duk yanda akayi akwai wata a k'asa, akwai mai neman gurb'ata mata tunani.... Likaci guda Aunty Shema'u ta fad'o zuciyarta, tabbas zuciyarta ba kowa take zargi ba illa Aunty Shema'u..... Muryar Sajida ne ya katse mata tunanin nata....

"Sanda ta mik'e tsaye tana gyara zaman Vail d'in abayarta take fad'in "Ni zan tafi, Maryama this should be between us, babu wanda zaisan abunda muka tattauna koda Hajiya ne, na barki lafiya...."

Daga haka tasa kai ta fice... Maryama ta kuma binta da kallon mamaki, yini guda na wannan rana haka Maryama tayishi sukuku gaba d'aya maganganun Sajida sun d'aure mata kai, haka kurum taji tana son sanin meke faruwa a gidan Uncle tsakanin iyalansa da Aunty Shema'u, lokaci guda maganar Ni'ima ya kuma tsaya mata a rai cewa Aunty Shema'u tace duk wanda ya mutu spirit d'insa ne yake dawowa monster.... Tana nan zaune tana tunanin, Hajiya ta tasa ta gaba tanata mata fad'an tak'i shan magani gashi yau da ciwon k'irjinta tashi da shike watan ta ya zagayo... Nan suka jiyo sallaman sa cikin dadd'an sautin sa...

Gaban Maryama ya yanke ya fad'i, kaman wata munafuka tayi saurin jawo hijabin dake gefenta ta rufa a kanta....

Kallo ya bita dashi kafin suka soma gaisawa shida Hajiya....

Hajiya ta mik'e tana k'ok'arin linke sallayan ta casbaha a hannu take fad'in "Toh ai tunda kazo sai ka sata tasha maganin...."

AT yayi saurin karb'an abin sallan ya linke mata ya d'aura hannun kujera sai wani sanne kai yake yana satan kallon Maryama.

Hajiya tana shigewa d'aki ya jiyo yana dubanta sosai...

Da k'yar ta bud'e baki ta gaishesa, ya amsa yana mai k'arasowa yanda take.

Zama yayi kusan k'afafunta da shike saman 3seater take kwance, a hankali ta janye k'afafun nata...

Kallo d'aya AT ya mata ya gane cikin kwanakin ta take.... Bai kuma cewa komai ba sai mik'ewa da yayi ya k'arasa saman d'an wani stool dake gefen parlorn yanda Hajiya ke ajiye magunguna, k'ullin goro da wasu 'yan k'ulle-k'ullen ta na tsofi da ba'a rabasu...

Maryama sai satan kallonsa take yanda yake gudanar da Al'amran sa, yana sanye cikin gray shirt da bak'ar Jeans ba k'aramin kyau da haske k'ananan kaya ke k'ara masa ba sam bakace ya haifi Sajida ba.... Tayi saurin sadda idanunta k'asa ganin ya k'araso ya zauna saman carpet saitin kujeran da take kwance bisa.

Irin zaman cin abinci yayi kafin ya b'ula ledar ruwa ya tsiyaya a cup, ya shiga b'alle magungunan... Ganin tayi rau-rau da idanu yasa shi cin mur sosai murya a dake yace "Sauk'o kisha magani...."

Dad'a marairaice fuska tayi kaman zatayi kuka, ganin sam babu wasa a tattare dashi sannan cikeda umarni yayi maganar ya sanya Maryama silalowa saman carpet d'in bakinta a ture, dama naturally idan tana period toh ranta a b'ace yake, uwa uba idan ta tuna maganganun da Sajida ta fad'a mata, gaba d'aya haushin Uncle d'in takeji ya rufeta...

Ganin sam babu walwala a tattare da ita ya sanyasa yin wata murmushi a hankali kafin ya sassauta murya yace "Oya irin logic d'in da na koya maki jiya shi zakiyi, just close your eyes kiyi imagining sweet kike sha kinji koh..." ya k'arashe yana mik'a mata maganin..

Itakam idan yana shagwab'ata haka abin har dariya yake kusan sakata, saikace wata Ni'ima, wai za'a mata wayo ace tayi imagining magani sweet ne... Wani ikon Allah kuma sai ta sami kanta da biye masa tana shagwab'ewa yana riritata.... Ya k'arashe bata maganin kafin yace "Yaya jikin naki...?"

Da k'yar ta amsa masa murya a ciki...

AT ya tsareta da idanu kafin yace " Kirjin fah suna maki ciwo...?"

Gabanta ya yanke ya fad'i, toh ya akayi ya sani.. Bata sami zarafin amsa masa ba sai sadda kanta k'asa da tayi cikeda kunya...

Ya d'an gyara zama kafin yace "Zo na gani sai na maki prescribing magani...."

Maryama ta d'ago ta dubesa a razane, nan taga da gaske yake maganar bada wasa ba... Ta d'an sunkuyar da kanta cikeda kunyarsa kaman k'asa ta tsage ta shige ciki, murya can k'asa tace "Na warke...." kana jin yanda tayi maganar zaka fahimci a birkice take...

AT ya kuma d'aure fuska tamau kafin yace "The earlier the better, gwara a duba tun yanzu asan wani irin ciwo ke damun ki ko kina so akai peak d'in da za'ace sai an yankesu gaba d'aya...." yanda yayi maganar sam babu alamun wasa a tattare dashi..

Maryama kuwa tsoro ya cikata, hawaye suka ciko idanunta, cikin rawar murya take fad'in "Uncle mutuwa zanyi koh...."

Ganin yanda ta tsorata sosai abun yaso bawa AT dariya amma ya gimtse ya jawota cikin jikinsa murya can k'asa yace "BABY bazaki mutu ba shiyasa zan duba ki yanzu..."

Maryama ta rintse idanunta tana jin yanda AT ya yaye hijabin data rufa yana k'ok'arin rabata da suturan dake jikinta, k'irjinta sai lugude yake, ita sam bata ko kula da sabon sunan da AT ya kirata dashi ba...

A hankali ya mik'e ya lek'a Hajiya yaga tayi nisa a bacci, ya saki labulen a hankali had'i da jawo k'ofa, har lokacin idanun Maryama suna nan a runtse, bata san me likitan nata keyi ba sai hanneyensa data jiyo cikin jikinta.....

**********

Shema'u kaman wacce aka bugama guduma haka taji k'irjijta ya buga sanda ta kuma duban agogon bangon dake mak'ale a d'akin ya nuna k'arfe goma saura, ta shiga zagaye d'akin cikin tsananin tashin hankali tana tunanin kardai AT wajen Maryama ya tafi... Tamkar wata zararriya, cikin sauri ta rarumo wayarta ta shiga neman layin Hisham..

Hisham yana d'agawa ya soma fad'in "Da fatan labari mai dad'i zaki sanar dani, don wllhi sati biyun da na d'ibar maki suka cika baki mallaka min takardun asibitin nan ba wllhi wllhi zan k'ona asibitin harma da majiyantan dake ciki sannan na d'aura blame d'in akan Tahir kinsan dole kowa ya yarda muddin akaji zancen daga bakina ya fito, kinga finally zan mallaki abinda na jima ina buk'ata shi kuma he'll rot in jail domin babu mai yarda dashi, mutum d'aya ne dama zai kawo min cikas, that counterfeit Ashfaq toh shima I got rid of him kinga cikan burina bazaimin wahala ba a yanzu, so idan kinason Attahiru bakiso ya tafi jail ki dank'a min takardun nan In two weeks time..."

Shema'u ta shiga muzurai tana zare idanu take fad'in "No, no no Hisham bazaka min haka ba, AT bazai tafi jail ba he's my whole life, wllhi wllhi bazan tab'a k'yaleka kayi abu makamancin haka ba, kasanno kasan halina akan AT zan iya yin komai....."

Dariya Hisham ya fashe dashi kafin yace "Nasanki farin sani ma kuwa, you're smart but such an idiot, har yau bakisan me nake shirya maki ba, amma duk ranar da kikace zaki takala fad'a dani rannan ne zaki san ko wanene Hisham, na baki sati biyu idan baki cika min alk'awarina ba I won't think twice....." Daga haka katse wayar yayi yana wata irin kafiran dariya....

Shema'u tamkar tab'ebb'iya haka ta shiga cisge gashin kanta tana wani irin k'ara tana buge-buge tana wargaza kayan d'akin...

*******

Wani irin yanayi ne ya ziyarce su su duka biyun, tunowa da kalaman Sajida ya sata saurin ture AT daga jikinta tana mai ci gaba da hawaye...

Ya d'ago idanunsa a galabaice kafin yace "Baby mammography nake maki just calm down babu abinda zan maki kinji..."

Baki a ture tace "Nidai ciwo suke min kuma ni bacci zanyi...."
Chapter 54 · 0% Book details