← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 63

Sashe 18

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matseta jikin garu Hisham ya kuma yi yana wata mayaudariyan murmushi ya d'ago hab'arta suna kallon juna cikin ido kafin yace "Da ace kinga shed'an da bansan yaya zaki zama ba, kai ni duk iya tsawon ratuwata da yawon da nayi a duniya ban tab'a gamuwa da shed'aniya irinki ba, duk abinda kike so sai kin samu da k'arfin gaske."

Murmushi Shema'u keyi kafin ta shiga zagaye fuskar sa da fingertips d'inta tana fad'in "Rantsuwa nayi sai na tarwatsa iyalan Aysha and keep AT for myself."

Dariyan rainin hankali Hisham yayi kafin yace "Idan kina sonshi ai zaki so 'ya'yan shi, sannan barikiji na fad'a maki wacce sai tafi zama illa ma rayuwar ki fiye da yaran AT. I'm afraid tana iya zama matar AT ke baki zama ba."

K'walalo idanu waje Shema'u ta shigayi tana girgiza kai tana kalle-kalle tamkar mai tab'in hankali kafin ta soma fad'in "No no no, wllhi ba'a haifeta ba, ince wancan shegiyar Nurse d'in kake nufi mai suffan karan rake. B'atar da ita mai sauk'i ne."

Dariya Hisham ya kumayi kafin yace "Dad'ina dake bakida imani wajen kisa, kina manta cewa akwai mutanen da idan kin kashe su bazakiyi succeeding abinda kike buri ba, bari kiji na fad'a maki akwai certain people da dole kiyi hak'uri dasu don rashin su ka iya kawo nak'asu ma abinda kike nema. Sannan ni ba Huda nake nufi ba, idan ita ce ai da sauk'i tunda kinsan irinsu AT dole 'yanmata nurses suyita rushing akansu, ko a TH ma akwai masu mutuwar sonsa, amma kinsan basa gaban sa, wacce nake nufi ba kowa bace illa MARYAMA, AT da mahaifiyar sa Kai harma da yaransa suna son yarinyar nan da uwarta tamkar sun had'a jini.... So ina mai baki shawari kiyi taka tsan-tsan dasu SHAK'UWA CE mai tsanani tsakaninsu da Family d'in... Kar ki ganta k'arama kiyi tunanin he can't fall for her, k'aramin gashin ido yakan shiga ido ya hanaka zaune ya hanaka kwance."

Jikin Shema'u yayi sanyi da maganganun Hisham, saurin d'ago idanu tayi tana dubansa yana k'ok'arin had'e boturan rigarsa kafin tace "Hisham wllhi yau babu yanda zakaje sai ka gaya min WACECE MARYAMA, who is she to AT and his family.. I need to know who she really is..???"

Murmusawa yayi yana kallonta da wutsiyar idanu kafin yace "You are unbelievable, how comes baki sansu ba bayan k'anwarki tana auren AT."

Hannayenta biyu ta d'aura a duka kafad'unsa kafin tace "Don't be such an ass, tunda Aysha tayi aure zuwana gidanta baifi a k'irga ba, nasan sau biyu ne zuwa na tun bayan aurenta sabida bazan iya jure ganinta a gidan AT ba, zuwata na farko lokacin data haifi Sajida ce nazo bikin suna, daga nan ban kuma zuwa ba sai sunan Ni'ima, toh tun daga wannan lokacin da na kuma yin arba da AT na k'udiri niyyan next zuwa da zanyi, salwantar da Aysha da iyalanta zanyi na mallaki AT, ka fahimta..." ta k'arashe tana tale masa fuska kaman wani toy.

Hisham ya jinjina kai kafin yace "I see, okay zauna na fad'a maki wacece ita."

Zama tayi saman gado ta zubawa Hisham dake zaune saman stool idanu.

"Kaman yanda kika sani, washe garin auren AT, Allah Ya karb'i ran mahaifin sa Alh Muhammad Shattima. Babu yanda AT baiyiba Hajiya ta koma gidansa da zama bayan ta gama takaba fir tak'i tace ita a nan gidanta zata zauna har itama tata ta sameta. Hajiya tanada fad'a sosai hakan yasa duk mai aikin da aka samata ko 'yar tayin zama sai sun gagara zama da Hajiya sun gudu, ke k'arewarta har Rano asalin garin mahaifan AT. ... AT da Aisha sunje sun d'auko 'yar uwa ta zauna da Hajiya amma abu yaci tura, babu mai hak'urin zama da Hajiya sabida tsananin fad'anta, ada fad'an Hajiya ya ninninka wanda takeyi a yanzu, ai yanzu tayi sanyi sosai babu ma had'i da da....." cikin sauri Shema'u ta katse sa da fad'in "Au yanzu matar nan da tafi haka fad'a..? Kace anyi annoba jarabebbiya. "

Hisham ya murmusa kafin yace "Ai saura kika samu, Ayshan kanta sosai tayi hak'uri da Hajiya kafin daga baya Hajiya ta sota sosai, me yake hana Momman ki zaman bayan haihuwa ma Aysha, masifar Hajiya ce kurum ke korarta sabida halinsu baizo d'aya ba, ba sai na fad'i ba kinsan keda mahifiyarku halinku yayi shige, Aysha ta fita zakka cikin ku, kinga ko ai bazasu jitu da Hajiya ba.... " Ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Mu dawo cikin labari.... Ana nan a haka kowa ya kasa zama da Hajiya sabida fad'anta, ranan da Aisha ta tashi da nak'udan babbar 'yarta Fatima Sajida, sosai hankalin AT ya tashi driving ma da k'yar yakeyi, yanayi yana juyawa baya yana kallon Aisha yanda take mark'usoso Hajiya na rik'e da ita. Kaman daga sama suka hangi Mace Kwance tsakiyar titi.... Horn AT ya ringayi mata tak'i matsawa, a zaton sa mahaukaciya ce, ga tashin hankalin da yake ciki.... Da k'arfin gaske yabi ta gefen matar ya wuce. Nan suka hangi jaririya 'yar shekara d'aya tana zaune gefen matan ashe, matar kuma tamkar ta mutu, yarinyar sai tsalla kuka take ga duhu na dare ga Aysha na murk'usoson nak'uda, gaba d'aya ya rasa da wanne zaiji ga Hajiya sai salle sa take tana fad'in yazo su tafi asibiti.

AT ya tsaya cirko-cirko a tsakiyan titi kafin ya d'aga hannayen sa sama yace "Ya Allah kaga zuciyata, bansan wanne zanyi ba wanne zan bari, k'aramar yarinya tana kuka a tsakiyan titi da duhu na dare, Mace mai tsananin buk'atan taimako tana kwance tamkar gawa a tsakiyan kwalta, ya Allah ka kawo mun d'auki, matata bazata iya haihuwa da kanta ba saidai a cire abinda ke cikin, idan na barta a haka zan iya rasata ya Allah nasan duk abinda kayi there must be a reason, Allah ka kawo min mafita.. AT bai sauk'e hannunsa k'asa ba yaji kukan sabuwar jaririya na fitowa daga cikin mota, ma'ana Allah Ya sauk'i Aisha lafia.... Hawayen farin ciki ne ya shiga keto masa, k'arasawa yayi ya sungumi yarinyar dake zaune saman kwalta ya rungumeta kafin ya nufi mota tareda yanda ya tarar Hajiya sai murna take don bata tab'a ganin haihuwa mai sauk'in na Aisha ba. Kallon yarinyar dake rik'e hannunsa yayi yana mai murmushi had'i da hawaye kaman daga sama ya jiyo muryar Hajiya tana fad'in Attahiru tabbas kayi tunani da baka bari mun tafi mun bar bayin Allahn nan a nan ba, Allah yaga niyarka na taimako kuma ya yassare maka damuwar ka. Attahiru daga yau bazan k'ara hanaka taimako ba, kuma insha Allahu ni zan zauna da wad'an nan bayin Allah cikin aminci da k'aunar juna......"

Shiru Haisham ya d'anyi don baisan yaya akayi zuciyarsa ta shiga jero labarin nan yana mai jin rauni na ratsa sa ba, tabbas bazai iya k'arya zai fad'a ma Shema'u iyaka abinda ya sani, don bayan shi baya jin akwai wanda AT ya basa wannan exact labarin tunda shine aminin sa..... Kaman daga sama ya jiyo muryar Shema'u tana fad'in "Kar kace min wai imani ne ya soma shigar ka don kana labari mai tab'a zuciya, k'arasa labarta min nasan ta yanda zan b'ullo masu."

Dariya Hisham ya fashe dashi kafin yace "Zan tuba amma sai na amshe asibitina daga hannun AT. Daga nan yaci gaba da fad'in "Koda mahaifiyar Maryama ta farfad'o a firgice ta farfad'o ta ringa masu wasu irin sunbatu tamkar na tab'in k'wak'walwa, ta jima tana asibiti Hajiya ita ke kula da Maryama, bacci tare komai tare, kinji yanda SHAK'UWAR Maryama da Hajiya ta samo asali, sannan AT tun daga wannan lokacin idan yaje gidan Hajiya yana tare da Maryama yanai mata wasa don dama shi Allah yayisa mai son yara, Sannan shi ya fara ambatan ta da MARYAM sabida son suratu Maryam mahaifiyar annabi Isah da yake a cikin Alk'ur'ani, tunda mahaifiyarta babu lafiya balle ta fad'i masu sunanta, Jaririyar d'iyarsa kuwa taci sunan mahaifiyar sa Fatima. idan ya koma gida ga Sajida, Idan yaje gidan Hajiya ga Maryama. Kinji dalilin da yasa nace maki SHAK'UWA CE mai k'arfi a tsakanin su....." Shema'u ta kafesa da idanu kafin tace "Nifa banji kace min ga asalinsu ba, ita Maryaman da Uwarta, ko kan street shine asalin su.?"

Hisham ya murmusa kafin yace "Ana baki kina rok'o, ai ce maki nayi mahaifiyarta ta kwana biyu a asibiti, tayi kusan watanni biyu kafin ta dawo dai-dai. Sanda ta dawo hayyacinta nan ta sanar dasu cewa Su d'in asalin su 'yan Jihar Katsina ne, Zaizayan K'asa da akayi a wancan lokacin shi ya kashe masu kowa nasu, daga ita sai d'iyarta sukayi saura. Koda ta farka taji suna ambatonta da Maryama tasha mamaki sosai domin kuwa Maryam shine sunanta na asali. Toh fah tun daga wannan lokaci mahaifiyar Maryama ita ta raini yaran AT gaba d'ayansu shiyasa suke tsananin sonta kinji yanda SHAK'UWAR su ta samo asalin " Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye kafin yace "Toh kina iya barina na fita, ko akwai sauran abinda kike son ji.?"

Jinjina kai tayi kafin tace "Now that I learned more about them yanzu ne zan tattaro makaman yak'ina, I'll destroy them one after the other."

D'ago face d'inta Hisham yayi kafin yace "Ke meyasa bazaki bi bikaye da malamai ba don cikan burinki cikin gaggawa kaman yanda matan zamani suke. Huh...?"

Bursting tayi cikin dariya kafin tace "Ai ni nan nafi ko wani shegen boka da Malam iya tuugu da makirci, da zasu zo wajena ma da na basu tips d'in da zasuke bawa masu zuwa wajen su suyi su sami biyan buk'ata..." Ta k'arashe tana d'aga masa gira sama.

Hisham na fita itama ta fice, bata zarce ko ina ba sai shagon saida waya. Android mai kyau ta saya kafin ta nufi gida.

******************

"Ummi yanzu yauma ba kwana zakiyi ba duk kun tare gidan Uncle, gasu Aunty Shema'u da Momma duk basu isa ba kema sai kin koma." ta k'arashe maganar baki a ture.

"Haba Maryama ai ganin mutane haka yana d'ebe masu kewa, kuma Momma satin nan da zamu shiga zata tafi."

D'an jim Maryama tayi cikin zuciyarta addu'a take Allah yasa harda Aunty Shema'u zasu tafi don Allah Ya gani sam tak'i jinin matar.

***************
Chapter 18 · 0% Book details