Sashe 12
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Auho inji cewa kikayi naji maki ko kina wari, nidai banji warin bane sai k'amshi shiyasa kika ga ina kawo hanci na, kuma banda iyayi da felek'e duk zamana dake, yo ai idan kina warin kinsan zan fad'i tunda kinsanni banida b'oyo."
"Toh fah, yau kuma ta sami Maudu'i" ta fad'i a hankali kafin taci gaba da fad'in "Nifa kurum tambayar ki nayi Hajiya..."
"Fad'a min uban waye yace kina wari.?" Hajiya ta fad'i tana gyaran d'aurin kallabin ta.
Maryama ta kalleta kafin tace "A bar zancen tunda kince banayi."
"Auw bazaki fad'i min ba ko, naji ko a gidan uban sa ake k'eran man k'anshi da yafi naki tsada da kyau, yo ko agwagwa nan ya ganki ya barki wajen wanka, dukda wankan bak'i asaran ruwa ne, amma ke naki ba asaran bane, ki fad'i min wa yace kina wari...?" Cike da masifa take maganar.
Kaman bazata fad'a ba, tasan ma idan bata fad'a ba wllhi maganar bazai tab'a mutuwa wajen Hajiya ba. Baki a ture tace "Aunty Shema'un nan bane tace wai bana shuwa da body spray, kuma wllhi kullum sai na saka, Hajiya ai ke shaida ce."
Sakare Hajiya tayi tana dubanta kafin tace "Au dama wancan mai suffan aljanai da mayun ne tace kina wari, Meye kuma Shuwa d'in ince man hammatan nane,... Ki sha kurumin ki Allah kai mu gobe suzo d'aukar ki tsaf zan rama maki, Karma ki b'ata ranki."
"Hajiya don Allah kar kice mata komai, dama dai kawai ina son sanin ko da gasken warin nake shiyasa na tambaye ki... "
Ko tankata Hajiya batayi ba ta nufi uwar d'aki tana tunanin kalan rashin mutuncin da zatayi ma Shema'u tunda ta tab'a mata Maryaman ta.
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*09*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
Misalin k'arfe takwas da wasu 'yan dak'ik'ai su Sajida suka iso gidan Hajiya d'aukan Maryama.
Shema'u sai kareraya ake mayafi rufe saman kanta sai ka rantse wata mutuniyar aziki ce. Sajida ce akan gaba sai faman rangad'a kira ma Hajiya take.
Hajiya na Kitchen tana taya Atine karin kumallo ta kafe Shema'u da idanu tana karantar ta, murmushi tayi a hankali kafin ta wanke hannunta ta fito daga Kitchen d'in.
"Hajiyar mu kinaji inata rattaba maki kira kikak'i amsawa koh." Sajida ta fad'i baki a ture daidai lokacin da Maryama ta fito tana saka hijabin ta.
Hajiya ta kalli Sajida ta watsar don daga ita har Shema'un haushi suka bata. Saida ta isa saman farin kujera dake barandar ta zauna kafin tace "Yo wannan kira da kike min sekace makahon da ya rasa d'an jagora."
Dariya Sajida tayi kafin suka soma gaisawa don wannan dama halin Hajiya ne tsaf ta saba da hakan... Kaman daga sama sai jiyo muryar Shema'u sukayi tana gaida Hajiya daga nan yanda take a tsaye.
Musamman Hajiya ta kaikaito tana duban Shema'u kafin tace "Lafiya, Almiski sarkin k'amshi.."
Ganin Hajiya zata Saki layi yasa Maryama saurin d'aukar jakkan ta kafin tace "Aunty Shema'u ina kwana."
Shema'u ta amsa da sakin fuska, cikin sauri Maryama ta soma fad'in "Hajiya mun tafi kar muyi latti.."
Hajiya bata sami zarafin amsa Maryama ba sai k'are ma Shema'u kallo da take, tun daga sama har k'asa wanda hakan yasa Shema'u shan jinin jikinta sosai ta tsargu da wannan kallo da Hajiya ke mata..... Jiyo muryar Hajiya sukayi tana fad'in "Yo ashema warin man Bilica (Bleaching) kike." Tayi maganar baki a tab'e..
Sajida sam bata gane ina Hajiya ta dosa ba hankalinta yafi karkata kan Solution d'in wani equation da Maryama ke nuna mata, Maryama kuwa tuni ta d'ago Hajiya, kai wato dai Hajiya bata barin kota kwana. Sai faman k'yafta idanu take ma Hajiya sam tak'i kallonta balle tayi shiru.
Hajiya ta jawo sandar dake gefenta ta shiga d'aga k'asan skirt d'in Shema'u dashi tana fad'in "Haba haba, duba sawayen ki ki gani, duk sun k'one sun dauje, yo dama wannan farin naki uwa toka ai nasan na man kanti ne, tun daga shigowar ki gidan nan Ya hamame da warin arna, da kika ce Maryama tana wari yo ai ga wari nan jikin ki .. Kina shiga rana ta soya wannan roba robar fuskar taki wari ne zai kuma tashi...."
Baki sake kawai Shema'u da Sajida suke duban Hajiya... Maryama kuwa janye Sajida ta shiga tana fad'in "Aunty Shema'u don Allah kiyi hak'uri muje , kar ki saurari Hajiya.
"Rufewa mutane baki ke kuma, wato kar ta saurare ni sabida ga mahaukaciya ko, ince 'yancin ki nake karb'a maki, gobe bazata sake duban ki tace kina wari ba.. " Sai lokacin Sajida ta gane meke faruwa, wato maganar da Aunty Shemah tayi ma Maryama jiya a mota shine har tazo ta beza wa Hajiya... Sosai abin ya bawa Sajida haushi, itakam sam bataga laifin Aunty Shemah ba don tana son gyara su, kuma ai tayi apologizing ma Maryama tun a jiyan.
A kufule Sajida ta soma fad'in "Haba Hajiya, haba Hajiya, gaskiya ki daina irin haka..." bata kai aya ba Hajiya ta watsa mata mugun kallo kafin tace "Rufe min baki ke kuma kafin na hamb'are bakin."
Kan kace me hawaye sun ciko idanun Maryama. Shema'u kuwa cikin kissa ta soma bawa Hajiya hak'uri tana fad'in "Kiyi hak'uri Hajiya wllhi ni bada cin zarafi na fad'i hakan ma Maryam ba, pls kiyi hak'uri Hajiya..."
Sam basuji sallaman AT ba dake shigowa cikin shirin tafiya aiki.... Tsaye yayi kurum yana kallon yanda Shema'u ke durk'ushe gaban Hajiya tana bata hak'uri ga Maryama rakub'e gefe tana hawaye. Ita kuwa Sajida ita ta kula da shigowar sa. Cikin sauri ta k'arasa ta rik'o hannun sa tana fad'in "Daddy please kazo ka bawa Aunty hak'uri wllhi Hajiya tayi addressing nata sosai, it's unfair, it is totally unfair..." Jin haka yasa Shema'u fashewa da kuka sosai tana nan durk'ushe gaban Hajiya, haba nan fah hankalin Sajida ya kuma tashi, ta shiga jan hannun AT da yayi tsaye kurum yana kallon yanda Maryama ke hawaye, haka kurum yaji k'irjinsa na bugawa da sauri da sauri ganin hawayen Maryam na zuba.
Kasa cewa komai yayi har lokacin idanunsa naga Maryama, Sajida kuwa banda watsa wa Maryama mugun kallo bata komai,...
Kan yayi magana Hajiya ta soma karanto masa abinda ya faru tsaf, sannan ta k'ara da "Wllhi ko gobe ta kuma b'ata ran Maryama ta, nata ran itama sai ya b'aci, banda naci da bak'in iyayi su tattara mana su koma garin su tunda yara sunada masu kula dasu..." Kuka Sajida ta fashe dashi tana fad'in "Wllhi wllhi babu yanda zasu tafi, wllhi idan Aunty Shemah ta tafi nima binta zanyi, wllhi barin gidan zanyi..."
AT ya saba da fad'an Hajiya amma sam bai saba da tashin hankali irin haka ba, yama rasa da waye zai soma cikin su... "
Cikin kissa murya irinta mai kuka Shema'u ta soma fad'in "Sajee kiyi hak'uri, ina sonku keda k'annen ki, but I have no choice dole na tafi, I can't stay here and be causing problems with your family.... Baby ko bana nan nasan you'll always be good girl.. Ki... " bata kai aya ba Sajida dake girgiza kai tana kuka ta fincike hannayen ta daga rik'on da Shema'u ta mata ta fita waje da gudun gaske tana fad'in "Wllhi saidai ni na rigaki tafiya, ko kuma mota ta markad'e ni... "
Ai gaba d'aya cikin tashin hankali suka bi bayanta, AT yana fad'i ma Ilu kar ya bari Sajida ta wuce gate, inaaa , tuni Sajida ta nufi waje har ta kusan isa babban titi... Hajiya ma zani a hannu ta fito, haka Maryama dake kuka shar shar da hawaye..
Shema'u kuwa itace kan gaba, kan kace me tayi kan Sajida dake shirin tsallake babban kwalta ga babbar mota ta tink'aro... Hankalin AT sosai yayi mugun tashi, mutuwar matarshi bai gama fita daga jikin sa ba, kansa tuni ya soma juyawa yana tuno sanda yaga Aysha cikin jini, gaba d'aya bai gane meke faruwa... Kaman daga sama sai ganin Shema'u sukayi tayi ta maza ta rik'o Sajida sun zube gefen kwalta... Hajiya kuwa isarta wajen ta d'auke Sajida da mari mai ji da lafiya... Shema'u ta tare ta tana fad'in "Hajiya kiyi hak'uri don Allah yarinya ce,.." Hajiya huci kawai take tana turiri take fad'in "Don ubanta kashe kanta zatayi ne ko kuma kashe mun nawa d'an zatayi inyi, b'acin rai hauka ne, Allah yasa jaririya ce ita ba yarinya ba... " Kuka kawai Maryama keyi sai karkarwa da jikinta keyi.
Sajida na rungume cikin jikin Shema'u, a hankali AT ya k'araso kafin ya mik'a ma Sajida hannu yace "Come here Baby, mak'e masa kafad'a tayi still tana hawaye.
Shema'u dake rungume da Sajidar ta d'ago tana duban AT kafin ta dubi Sajida tace "Sajee kije wajen Daddyn ki kinji sweetheart. Ta k'arashe cikin tsananin damuwa.
Mak'e kafad'a Sajida tayi a karo na biyu kafin tace "Aunty don Allah kar ki tafi ki barni kinji."
AT ya dubi Shema'u ya dubi Sajida yanda suke rik'e da juna k'am, saida Shema'u tayi da gaske kafin Sajida ta mik'a hannu ma AT, kai tsaye motar sa ya nufa da ita..
Hajiya wangale baki tayi tana kallon ikon Allah, da k'yar ta iya furta "Yo naga bariki da k'afafun ta.." tab'e baki tayi kafin ta nufi Maryama dake tsaye gefe tana hawaye ta janye hannun ta tace "Shige muje, su suka sani, kuma daga yau idan babu me kaiki makaranta sai wannan aljanar ni zan wanke k'afafuna na kaiki tunda Allah yasa da K'arfi na rass.." Ta fige hannun Maryama suka wuce ciki..
Suna shigewa Shema'u tayi wata kafiran murmushi kafin tace "This is just the beginning Shemah, kiji dad'in ki da sannu zaki sami abinda kika jima kina buri. Karkad'e jikinta tayi ta tashi ta nufi motar ta, zuciyar ta fari k'al.
*********
Duk maganar duniyar nan tayi Maryama tak'i amsa mata, sai faman shan zuciya kurum take alamun taci kuka.
Hajiya duk sai taji babu dad'i don kuwa bata jure fushin Maryama. D'an matsowa tayi kafin tace "Tashi muje na kaiki kar kiyi latti."
Baki a ture tace "Na fasa zuwa."
"Jarabawar fah, inyi.?"
"Bamuda yau, dama karatu zamuje." tayi maganar tana mai mik'ewa had'i da shigewa d'aki....
**********
"Hello kana ina ne.?" ta fad'i tana saka trafficator.