← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 63

Sashe 15

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ma tambayar ta bawa Maryama kafin tace "This is ridiculous, haba Sajida kar kiyi magana haka, wllhi ni Maryam banga namiji da zai shiga tsakanina dake ba, babu shi.... Kawai dai ina so ayi abubuwa ne the right way, abinda kike son yi ba haram bane amma baki biyo ta hanyar da ya dace ba... Kiyi tunani akan maganar da na fad'a maki.

Sai yanzu ta yarda da maganar Aunty Shemah, Maryama is just keeping Buzu for her self ne. Kallon Maryama tayi kafin tace " Shikenan with or without you Haris zai soni, he's mine, ni kad'ai... Idan ma kin fad'a ma soyayyar sa ce ina mai gargad'inki da ki ciresa a ranki... " Daga haka fuuu ta wuce ta nufi mota.

Sauk'e ajiyan zuciya Maryama tayi cike da mamakin canzawan da Sajida tayi a 'yan kwanakin nan, girgiza kai kurum tayi kafin ta wuce mota.

************

Hisham ya kalle sa a karo na biyu kafin yace "Dr wai meke damunka ne kam, kana looking dull tun shigowar ka, idan tunanin Aisha ne, hak'uri zakayi Tahir, Allah shi ya tsara hakan sannan yafika sonta tunda shi ya hallice ta, Tahir don Allah kake rage ma kanka tunain nan, you are perfectly aware of the consequences, yanzu sai ciwo ya rafke ka, kaga ba'ayi riba ba."

Fuzar da iska AT yayi had'i da zuba hannayen sa gaba d'aya saman table d'insa kafin yace "Hisham, no matter how hard I try not to think of it...... I just couldn't.. Amma haka ne yanda kace ne, Allahn da ya d'auketa ya fini sonta sannan Allah yana tareda masu hak'uri da tawakkali, what worries me the most , Hajiya ce."

Hisham ya k'araso ya zauna a kujera mai kallon na AT kafin yace "Hajiya kuma, me Hajiya tayi.?"

AT ya d'an girgiza Kai kafin yace "Could you just imagine, wai ta fara min maganar aure, na sani sooner or later zata kuma yin batun tunda ta fara, abin ya dameni sosai. Sannan she's asking me na sallami su Shema'u daga gidan, kasan bazan iya ba, aside from that yaran sosai suke son Shema'u, tana d'ebe masu kewar mahaifiyar su, I was even thinking of asking her to stay a bit longer har sai yaran sun k'ara recovering, amma kaji abinda Hajiya take fad'i.

Shiru Hisham yayi kaman bazaice komai ba sai kuma yace "Toh kai baka son auren ne.?"

Galala AT ya kallesa kafin yace "Aure kuma ni yanzu, ai babu batun aure yanzu kam a gaba na, mace guda nake so kuma ta tafi, kai kasan da hakan."

Hisham ya jinjina kai kafin yace "Haka ne, amma kasan kaman yanda Hajiya tace bazaka tabbata a haka babu mata ba, for the sake of your children, tunda Shema'u ba tabbata zatayi a gidanka ba .....you've to keep this in mind."

AT dai baice masa komai ba sai mik'ewa da yayi ya nufi k'aramar fridge d'in dake a cikin office d'in.

Hisham kuwa wani irin dad'i ne ya ziyarce sa, burinsa ya kusa cika, Sajmal ya kusa zama mallakin sa, all he needs to do now shine yayi updating Shema'u wannan daddad'an labarin. Daga nan store suka nufa don duba magaungunan da basu dashi a asibitin.

**************

"Hello, kina jina.." cewar Hisham bayan Shema'u ta d'aga wayan.

Yamutsa fuska tayi kafin tace "Ina jinka mana, meke faruwa, what's on the ground.?"

Murmushi Hisham yayi kafin ya labarta mata duk zancen da sukayi da AT.

Mik'ewa tayi tamkar wata zautacciya, ta k'arasa tasa key ma k'ofarta kafin ta soma fad'in "I'm sick of that old woman, she's getting on freaking nerves, wllhi wllhi if she keeps on getting on my way zan b'atar da ita..." Sai huci take tana maganar tana zazzare idanu.

Hisham ya murmusa kafin yace "Kwantar da hankalin ki and don't think of doing anything stupid, idan kika ci gaba da saye zukatan yaran AT ina mai tabbatar maki kece zaki zama matar sa, tunda shid'in bashida wacce yake so a halin yanzu, duk macen da zai so tabbas tayi grabbing affection d'in yaran sa ne. Don haka kar ki b'ata shirin ki by hurting Hajiya, just keep on killing her with kindness na tabbata itama eventually zata soki, koda kanta da k'aho ne."

D'an dafe kanta tayi had'i da zama saman couch kafin tace "Hisham baka san wannan uwar tasa bane, she's insane wllhi batada hankali, ba abu mai wahala bane ta zab'o masa mata a k'auye... Amma nasan yanda zanyi, Shema'u nake, da kanta zata soni ta zab'a ma d'anta da jikokinta zama dani.." Daga haka katse wayar tayi tana wani irin huci... Wata wayar ce ta kuma shigo mata.

Ganin ogan ta ne a wajen aiki yasata d'agawa da k'yar sai faman yatsina fuska take.

Daga d'aya b'angaren Alh Aminu yace "Rankishidad'e kin mance dani, sai kewarki nake."

D'an murmushin yak'e tayi kafin tace "Haba my Alhaji kasan ai bazan mance da kai ba, wllhi yaran ne sam basu saba da kowa ba sai ni, mussaman k'aramar cikin su, wllhi my Alhaji idan ka gansu sai ka zubda k'walla sabida tausayi." Ta k'arashe maganar kaman me shirin yin kuka.

Sauk'e ajiyan zuciya Alh Aminu yayi kafin yace "Shema'u magana ta gaskiya kinsan dai kinyi neglecting aikin ki, sannan albashi bai yanke maki ba tunda ni ne babba a waje, amma ki sani duk randa Governor ya kawo ziyara ministry d'inmu akwai babban matsala, sannan nima ina buk'atan ki tunda kinsan idan ban jiki a jikina ba sam banida kwanciyar hankali, Shema'u don Allah ki bari muyi auren nan na huta..."

Dumm! Haka taji maganar Alh Aminu, cike da masifa ta soma fad'in "Lallaima Alhaji, waye zai aureka yaje cikin wad'an nan locals wives d'in naka, kaga na maka kama da zama cikin su ne, sannan da kake min maganar aure yanzu yaran 'yar uwatan ma waye zan barsu, idan gorin abubuwan da kake min zakayi fine sai mu rabu it's not a big deal ai, kaima kasan duk yanda na shiga bazan rasa masoya ba."

A daburce Alh Aminu ya soma bata hak'uri "Shema'u kiyi hak'uri sam ba haka nake nufi ba, sannan maganar matana kinsan bazan tab'a had'aki gida guda dasu ba, yaran 'yar uwanki kuma kina iya rik'esu koda a gidana ne, amma don Allah kar kice zaki rabu dani."

Murmushin cin nasara tayi kafin tayi k'asa da murya kaman mai shirin kuka ta soma fad'in "My Alhaji kasan bazan tab'a rabuwa da kai ba, kasan ina sonka sosai, sannan naso zuwa Jalingo dubaka amma motata ta tawarwatse kasan da ita mukayi had'arin, wllhi shi ya hanani zuwa, kuma banida enough cash da na biyo jirgi.."

Alh Aminu yayi wata murmushin jin dad'i kafin yace "Yauwa sanyin rayuwa ta, shiyasa a kullum nike k'ara sonki, ai bansan da motarki akayi had'arin ba da tuni an aiko maki sabo, ki kwantar da hankalin ki, mota da kud'u suna nan tafe cikin satin nan."

"Allah my Alhaji, wayyo shiyasa nake k'ara sonka.." Tayi maganar full of excitement.

Nan suka b'uge da hiran soyayya, tana gama wayar dogon tsaki taja kafin tace "Banza kawai, ina ni ina kai, babban baho." tana gama fad'in haka ta mik'e ta nufi d'akin Sajida.

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*12*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Zaune take saman gadon ta tayi tagumi da hannayen ta biyu saman pillow. Saida Shema'u ta gama karantar ta tsaf kafin ta shigo cikin d'akin, da alama Sajida tayi nisa duniyar tunani. Saida Shema'u ta lellek'a corridor ta tabbatar babu mai zuwa kafin ta maida k'ofar ta rufe ta k'araso cike kissa fuska fal damuwa ta zauna gefen Sajida ta dafata tana fad'in "Sweetheart lafiya na ganki haka, kinsan I hate to see you cikin damuwa, com'on Sajida kinyi k'arama ma shiga damuwa, kar ki manta you have me, kinadani pls ko me kike so ki sameni ki fad'a min Sajida bawai ki dinga shiga damuwa ba." Ta k'arashe maganar tamkar zatayi kuka.

Da sauri Sajida ta rungume ta kafin ta soma fad'in "Aunty meyasa abubuwa suke faruwa haka, Aunty ina son Maryama bana so wani abu ya raba mu, but it seems SHAK'UWAR mu da ita yana gab da yankewa, Aunty you were right da kika ce Maryama ba sona da Haris take ba, sam bata son alak'ata dashi, I was stupid da na yarda da ita a baya, gaskiyar ki ne Aunty yanzu ne zan gane masu sona tsakani da Allah tunda yanzu ne na soma girma na soma sanin ciwon kai na."

Shema'u tamkar ta zuba ruwa a k'asa tasha sabida farin ciki, tuggun data shirya ya tafi yanda take so, perfect inji bature .

"Ohhh Sweery come here..." ta fad'i sanda take rungumo Sajida kafin tace "My Sajee har raina naji dad'i da idanuwan ki suka bud'e kika gane wannan Maryama she's nothing but a Social climber, k'ok'ari take ta sace soyayyar kowa naki daga gareki, tana kai kanta yanda Allah bai kaita ba , ki duba yanda Hajiya kakar ki take sonta, ko ku jikokin ta Albarka, har marinki Hajiya tayi amma na tabbata ko zungurin Maryama bata tab'ayi ba, Daddyn ki yakanje da kansa ya kaita school, har wani nunawa take ta fiki son karatu sabida tsaban makirci irin nata, wllhi nan gaba ina mai tabbatar maki Daddyn ki sai yafi sauraren ta fiye dake, uwa uba kin aminta da ita kin had'ata da saurayin da kike so ta zaga tana cin amanar ki, kuma zakiga ko cikin k'awayen ku zasufi sonta sabida ta k'ure a makirci da munafunci, amma dai ni banaso ki rabu da ita tunda kina sonta sannan tare kuka taso, abinda zance maki dai shine you should be careful with her. From now on ba komai zakina sharing da ita ba tunda true color d'inta ya fito fili kin gane ko wacece ita. Maganar Haris kuma ni nai maki alk'awari duk iya makircinta sai Haris yaso ki ke kad'ai, you've my word, kinji sweetheart, so kima daina saka ma ranki damuwa tunda kinadani." ta k'arashe tana sakar ma Sajida sassanyar murmushi.

Murmushi Sajidar ma tayi kafin tace "Aunty, thank you for always been here."
Chapter 15 · 0% Book details