← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 63

Sashe 10

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai faman satan kallon sa take da wutsiyar idanu, shikam kullum k'uriciyar sa dad'a fitowa take ta rufe tsufar sa, sam bazakace ya aifi d'iya kaman Sajida ba. Yana sanye da Jampa ruwan k'asa kansa babu hula, sajen nan nasa a kwace luf, ta kai dubanta ga hannayen sa dake rik'e da steering kaman ka tab'a jini ya fito, so fresh, ga agogon Rolex dake d'aure a hannun nasa, kai gaskiya Uncle d'an gayun k'arshe ne, shi k'anshin sa ma daban ne, ko yaushe cikin k'anshi da gayu yake, duk yanda ya zauna toh k'amshin sa yakan rinjaye wajen, tabbas shida Aunty Aysha sun dace da juna, dukansu 'yan gayun k'arshe ne, Allah sarki mutuwa mai raba tsakani, tausayin sa ya kuma ratsa zuciyarta..... Gabanta ne yayi mugun fad'uwa, ta shiga tambayar kanta. Anya lafiyanta kuwa , meyasa take jin tana tsintar kanta wani irin yanayin duk sanda suka keb'e da Uncle, sannan meyasa take yawan tunanin sa har tayi k'ok'arin wuce gona da iri..? Tabbas ita kanta zuciyarta da take faman shek'o mata wad'annan tambayoyi bata da amsar su, abu guda da tasani shine SHAK'UWA CE sosai a tsakanin su ..... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar sa yana fad'in "Wani exam zakuyi yau.?"

A d'an tak'aice ta amsa masa da "Chemistry practical."

Jinjina kai yayi kafin yace "Har yanzu baku gama practicals d'in ba.?"

"Eh ni idan nayi yau ahikenan su Sajida ne masu yin Food and nutrition su kuma sai Thursday." ta kuma yin maganar duk ba'a sake ba, sam bata saba da wannan canzawar da yayi ba, ta sani tuntuni miskili ne dukda SHAK'UWAR dake tsakanin su amma yanzu abin ya kuma yawa, k'ila rashin matar sa ne.

AT ya kuma jinjina kai kafin yace "Meyasa ke bakiyin Food and Nut d'in, ko Hajiya ta koya maki girkin ne?" Yayi tambayar teasingly.

D'an murmushi tayi tana mai kallon 'yan yatsun ta kafin tace "Ai Hajiya bata barina nayi girki."

D'an karkato da fuskar sa yayi ya dubeta kafin yayi murmushi ya maida fuskar sa ga kwalta sannan yace "Ai kinyi k'arama ma yin girki ne shiyasa, saidai irin ta makaranta banda na gida."

D'an ware idanunta tayi kafin tace "Laa Uncle fah masu shekaruna ma suna girki."

Ya juyo ya dubeta yanda tayi maganar cike da yarinta kafin yace "Nawa ne ma shekarun naki.?" Still idanunsa naga kwalta yayi tambayar.

"18 fah zan cika Decembern nan."

Murmusawa kurum AT yayi yarintar ta na burge sa kafin yace "Au ashema kin d'an fi Sajida, toh ke kin kusa fara gwada girkin amma sai kin cika 18 d'in."

Bata kuma cewa komai ba sai murmushin da tayi kanta a k'asa lokaci guda kuma taji wani iri, don harga Allah sosai yanzu take jin nauyin sa.

K'arfe 8:45am daidai suka iso makarantar. Ta bud'e marfin mota tana fad'in "Na gode Uncle."

Kallon ta Ya d'an yi kafin yace "I hope babu dukan latti."

Murmushi tayi kafin ta girgiza masa kai tace "No ba'a tare 'yan SS3."

Gyad'a kai yayi kafin yace "Allah bada sa'a koh." Ta amsa da ameen kafin ta shige. Saida yaga shigewar ta kafin yaja motar ya bar wajen.

***********

"That imbecile is always bossing me around. Nunawa yake kaman yafi kowa iya aiki da son taimaka ma mutane, I'm sick of him already, kaman na shak'esa na huta haka nake ji." Hisham ya fad'i sanda yake had'a boturan rigar sa.

'Yan kunnayen ta take sakawa kafin tace "You watch your mouth Hisham, ina gargad'in ka don't mess with my AT...." ta k'arashe tana yawo da d'an yatsar ta saman fuskar sa.

Murmushi Hisham yayi kafin yasa hannu ya kamo k'ugunta ya had'e da nasa waje guda, dab da fuskarta yake magana cikin sigan rad'a "Kiyi a hankali my Ally dukda nasan baki fed'e min sirrinki gaba d'aya ba amma ki sani Hisham ya wuce tunanin ki."

Murmushi ta d'anyi kafin ta sauk'e masa light kiss a lips d'insa tace "Dangantakar wancan bak'ar yarinyar da AT zaka fad'a min, dukda nasan AT ya ninka ajin wannan yarinyar sau babu adadi I still need to take precautions, don irin wad'annan munafukan yaran sunfi manya iya makirci."

Hisham ya murmusa kafin yace "Next time zan fad'a maki, kinga yanzu fita zanyi.

D'aukar handbag d'inta tayi had'i da gyara mayafinta kafin suka fito a jere.. Cikin zuciyarta tsantsan tsanar Maryama da uwarta ne zalla, tun yanzu gwara ta soma tunanin ways d'in da zatabi ta rabu dasu, musamman data tuna yanda yaran AT ke son uwar yarinyar, sannan ita kanta Sajida tana tsananin son yarinyar.... Kai dole ma yau taje d'aukan su makaranta don ta kuma ganin yarinyar sosai, tabbas ta ganta lokacin rasuwar Aysha amma sam tama mance kamannin ta, ko banza she feels at ease, don dai wannan yarinyar ne ai batada mastala, ta zaci wata babbar mace ce mai aji irinta Hisham ya gansu da AT d'inta... Da wannan tunanin ta isa jikin motar ta k'irar Accord...

****************

Da gudu Sajida ta k'araso ta rungume ta tana dariya take fad'in "Maryama don Allah kiyi hak'uri, wllhi Aunty Shemah ce ta kawo mu, sai surutu muke a motar shaff na mance da ke, sorry pls."

Harara Maryama ta galla mata kafin tace "Da nayi missing exams ai bakida damuwa."

Dariya Sajida tayi had'i da janyo kafad'an Maryama suka nufi bakin hall d'in tana fad'in "Ai da bakizo ba ma bazan shiga ba nima saidai nayi missing.." Da haka suka k'arasa don already an soma shiga.

*************

Zaune take cikin motar ta sai faman hangen ta ina su Sajida zasu fito take, burinta bai wuce taga Maryama ba.

Can ta hangesu suna tahowa itada Sajida, sai yanzu ta samu ta k'are ma yarinyar kallo. Chocolate ne in colour, don kai tsaye baza'a kirata bak'a ba sannan sam bata a layin farare. Shakka babu dukda uniform ne a jikinta zaka fahimci Allah Ya mata diri mai kyau, bata faye tsawo ba sannan ita ba gajeriya bace, irin mutanen nan ne da bature ke kira average, batada wani tsananin kyau sai manyan idanu da d'an k'aramin lips d'inta, sannan koda murmushi tayi kumatun ta suka d'an lotsa, wannan shine iyaka qualities d'in da Shema'u ta hango tattare da ita.... Wani murmushi ta saki don kuwa wannan ai ko makaho ya shafa yasan bata dace da AT ba, aima ruwa ba sa'an kwando bane, Babban goro sai magogin k'arfe, bayan k'aracin shekaru akwai rashin wayewa a tattare da ita, AT da ita ya dace, yanda yasha boko ya k'oshi ma bazai tsaya soyayya da k'aramar yarinya 'yar cikin sa irin wannan yarinyar ba. Dama bata tsaya damun kanta ba idan dai don wannan yarinyar ce. Abu guda da zatayi kawai shine ta dasa ma Sajida tsanar ta cikin ranta..... Muryar Sajida ce ya katse ta sanda suka k'araso tana fad'in "Oyoyo Sweet Aunt, ashe har kin iso."

Shema'u ta bud'e marfin mota ta tafi tayi hugging Sajida tana gogge mata fuska da hanki kafin tace "Na iso tunkan ku tashi My Sajee, kinsan I don't wanna keep you waiting, sabida banso ki wahala, yaya exams, me kike son ci..?" Ta k'arashe tana wani ware idanu tana sakar ma Sajida sassanyar murmushi.

Maryama dai jinin jikinta tasha, don harga Allah itakam sosai Aunty Shema'u ke bata tsoro, bata san dalilin hakan ba..... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar Sajida tana fad'in "Maryama ga Aunty Shemah baku gaisa ba."

D'an murmushi Maryama tayi kafin ta rusuna ta gaida Shema'u. Da sakin fuska Shema'u ta amsa mata hannun ta still rik'e cikin na Sajida kafin tace "Okay girls mujen ku koh.." A sanyaye Maryama dai ta nufi backseat yayinda Sajida ta nufi front seat sai faman murna take tana fad'in "Wllhi Aunty don kece da tada Daddy ne sam sai ya mance damu, ina sonki Aunty yanda kike son mu...

Shema'u murmushi kawai take tana driving kafin tace "Sweetheart anything for you, you and your siblings are my top priority... Faranta maku ya fiye min komai.." ta k'arashe maganar tana satan kallon Maryama datayi jigum a bayan mota ta cikin mirror.

Kashe AC d'in motar Shema'u tayi tana tara miyau a baki kafin tace "Baby ya sunan k'awar taki ma.?"

Sajida tace "Maryama Aunty. Baki ganeta bane, gidan Hajiya fah take."

Shema'u ta zubar da yawun bakinta kafin tace "Oh na ganeta, itace d'iyar Nannyn su Jamal koh, sannu Maryama, amma dai kina sure da body spray koh, kinsan fah kun zama 'yammata, idan baku kiyayewa wari zaku keyi duk yanda kuka shiga. Nasan My Sajee bata wasa da kayan k'amshi, kike k'ok'ari kina amfani da kayan k'amshi kinji Maryama, yanzu kiji yanda gaba d'aya motar nan ta hamame sabida shigowar ki... So nake ki gyara shiyasa na fad'a maki kinji."

Ba Maryama kawai ba harta Sajida saida taji babu dad'i abinda Aunty Shemah tayi, ta yaya zatace Maryama tana wari, bayan tsafta irinta Maryama, kai duk yayen d'alibai ma da akeyi ita take karb'an wacce tafi kowa tsafta... Kuma itakam sam bata tab'a jin wari a jikin Maryama ba tsawon shekarun da sukayi a tare.

Iya k'uluwa Maryama ta k'ulu, tsanar matan ya kuma shiga ranta, itace mai wari... A duniya babu abinda ta tsana irin wari, amma shine yau har ita akece ma me wari, tana son mutum d'an gaye, amma Sam banda Aunty Shema'u dukda gayu da take ji dashi..... Sajida ta d'an lek'o tana duban ta zatayi magana Shema'u tayi saurin fad'in "Me kuke son ci, ko a biya daku eatery ne, Maryama ko bakujin yunwa ne..?" Ta d'an juyo tana duban Maryama datayi zaune kurum cikin motar kafin tace "I hope dai ba abinda na fad'i bane ya b'ata ranki, kiyi hak'uri ni na d'auke ki ne kaman Sajida, duk abinda na gani na gyara zan maku both ke and Sajida tunda ku d'in tamkar sisters kuke, right my Sajee.?" ta k'arashe tana duban Sajida. Haba nan fah Sajida ta kuma jin dad'i ta kuma yarda lallai Aunty Shemah tana son su da gaske, tunda gashi soyayyar ta shafi har mutanen da suke so.

Murmushin yak'e kawai Maryama tayi wanda hausawa ke cema tafi kuka ciwo, Alla Alla take ta isa gida ta tambayi Hajiyar ta ko da gaske tana wari.
Chapter 10 · 0% Book details