Sashe 21
Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh d'in na sanin, kunfi kusa keda ita, nikam ba k'yaleta zanyi ba kin sani." Cewar Fadila.
Fitowar ta kenan tana faman share hawayen ta taji ta bangaji mutum, saurin d'agowa tayi da niyan masifa don dama a wuya take. Fuskar da tayi tozali dashine ya hanata furta koda kalma, Cak ta tsaya tana bunsa da kallo.
Durk'usawa yayi ya d'ago mata hanki d'inta da ya fad'i k'asa ya karkad'e kafin ya mik'a mata yana murmushi mai kashe 'yan mata da manyan mata yace "Sorry pls, kiyi hak'uri it wasn't intentional..."
Bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, cikin sauri ta shiga girgiza kai tana fad'in "Kar ka damu babu komai."
Buzu ya murmusa kafin yace "Are you sure.?"
Bata sami zarafin amsa masa ba sabida tsaban k'warjinin sa da ya cika idanunta sai gyad'a masa kai tayi alamun eh.
"Kaman na gane fuskar ki." ya fad'i yana k'ura mata idanu.
D'an murmushi tayi kafin tace "A gidan Hajiya koh."
"Exactly." ya fad'i yana mai fad'ad'a murmushin sa had'i da shafa kwantaceccen bak'in sumar sa.
"Congratulations, ashe kema harda ke cikin d'aliban da ake yayewan."
D'an murmushi tayi wanda yafi kama da yak'e kafin tace "Na gode, ka k'arasa ciki, Maryama na ciki, inace wajenta ka zo."
D'an jim yayi kafin yace "No ai banma san tana candy yau ba, don ba ita ta gayyace ni ba, wata cousin d'ita ce nazo mata, kuma mun had'u har munyi pics.... Amma ya na ganki haka, yau ranar farin cikin ki ne kina looking sad, lafiya dai koh..? "
Kasa ce masa komai tayi, sai kallon sa a fuzge da tayi.
D'an gyara tsayuwar sa yayi ya shafi sajen sa kafin yace "Kiyi hak'uri idan na maki tambayan da baki so bane, or maybe na shiga hurumin da ba nawa ba, I'm only concerned about you ne, a beautiful girl like you fushi bai kamace ta ba.." Cikin siga mai cike da jan hankali yayi maganar.
D'ago kai Sajida tayi tana mai tambayan kanta _Did I hear him right, ya kirani Beautiful._..... Ganin tayi sakare tana kallonsa yasa shi sakin wata murmushi kafin yace "Miss Beauriful idan bazaki damu ba mu k'arasa k'asan bishiyar can, inada muhimmiyar magana da nakeso muyi. "
Daga yanda take zaune ta hangesu d'aga masa babban yatsa tayi alamun jinjina, ganin Sajida tabi bayansa kaman rak'umi da akala.
Saurin mik'ewa Shema'u tayi ta lab'e a wani k'ofa don tasan idan su AT basu ganta ba zasuyi tunanin tana tareda Sajida don Karma su nemeta, dad'in da taji AT manyan mutanen nan sun hanasa barin wajen su, Hajiya kuwa tana tareda jikokin ta, Maryama kuwa su Fadila bazasu barta ta fita neman Sajida ba tunda sunsan da gangan ta taho ta bar Maryaman.
"Kinyi shiru Miss Beauriful, nifa friendship kawai na tambayeki nothing more, ko shid'in bazan samu ba." cike da yaudara yake kalaman nasa.
D'an murmushi tayi had'i da rufe fuska da tafukan hannu kafin tace "A'a ba haka bane, kawai dai I'm not comfortable ne tsayuwata da kai a nan don ban saba ba, kuma Daddy na na cikin hall yana iya fitowa any moment, idan ya ganni da kai a nan, he might be thinking otherwise. "
Gyad'a kai yayi kafin yace "Na fahimce ki Miss Beauriful, yanzu bara na baki lambata tunda kince min bakida waya, idan kin sami hali sai ki kirani." yayi maganar had'i da bud'e backseat d'in sabuwar motarsa da Shema'u ta basa ya d'auko takarda da pen ya rubuta mata lambar ya mik'a mata.
Karba tayi tana kallon takardan da murmushi a saman fuskar ta, ta d'ago ta dubeshi kafin tace "Wani suna zan saka maka, ko Buzu zan saka maka.?" ta k'arashe teasingly.
Dariyar shima yayi kafin yace "Duk sunan da kika saka min is okay by me Miss Beauriful."
Ganin AT ya mik'e yana masabaha da mutanen alamun sallama yake masu yasa Shema'u saurin ciro waya ta shiga neman layin Buzu.
Ganin Shema'u ce mai kira yasa bai d'aga ba, sai duban Sajida yayi kana yace "Miss Beauriful Mumsy ta tana kira, ni zan wuce, sai naji daga gareki."
Nan sukayi sallama cike da farin ciki, Sajida ji take kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha sabida murna, kai gaba d'aya ta nemi bak'in cikin da take ciki ta rasa.
Ganin ta tunk'aro k'ofa yasa Shema'u saurin fitowa ta nufi Sajida don ta jiyo AT na tambayan su Hajiya.
"Sajee where have you been, munata neman ki a ciki daga ficewa freshing up.?" ta tambaya cike da nuna damuwa.
Hannunta Sajida ta rik'e cike da farin ciki take fad'in "Aunty zan fad'a maki idan munje gida."
Shema'u ta wani juya idanu kafin tace "Daughter da gani dai kina cikin farin ciki, oya mu k'arasa."
A tare suka k'arasa cikin hall d'in, sai sann Sajida ta k'arasa ta gaida AT da Hajiya, Mai hoton da Shema'u ta kirane ya soma d'aukan su, Sajida ta rik'o hannun Shema'u tace "Aunty Family pic."
Murmushin yak'e Shema'u tayi ta k'arasa gefen AT ta tsaya had'i da dafa kan Jamal, Sajida na d'aya gefen yayinda Ni'ima ke hannun AT.
Koda akazo tafiya Hajiya cewa tayi su tafi abunsu zasu shiga tasi, don dama motar ba isan su zaiyi ba. Fir AT yak'i tafiya ya dage saidai ya kai su Hajiya da Maryama, Hajiya ma k'in aminta tayi tace "Ko don Ni'ima ai gwara ya kaisu, don dai ita da Maryama ne zasu shiga tasi.
AT ya d'anyi Jim, rashin driver d'in nan ya soma damunsa, kai dole ma ya canza driver ya sama ma Hajiya standard.
Wayar sa ya ciro a aljihu ya shiga neman layin Ashfaq. Yako yi sa'a Ashfaq na kusa da makarantar.
Suna gama waya da Ashfaq ya k'araso rumfar dasu Hajiya da Maryama suke kafin ya sanar dasu, abokin aikin sa zaizo har nan ya d'auke su, yanzu zai k'araso. Hajiya ta amsa masa kafin tai masu a sauk'a lafiya. Suna wucewa ta tab'e baki, ina itama ina had'a hanya da wannan mai roba-robar fuskar, fuska uwa anyi b'arin hoda. Tsaki tayi had'i da kauda fuska.
Maryama ta bita da kallo tana mamaki da dariyar halin Hajiya.
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*17*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*On Your Birthday, Today, I Wish You a Year With Loads Of Fun, Excitement and Beautiful Memories......🎉🎉🎊🎊 Happy Birthday K'awata Aysha Sada Machika..... This one's yours my commander ontop 💃🏻💘😜*
Wasu 'yan mata biyu Ashfaq ya tambaya ko sun san Maryama, akayi sa'a juniors d'insu ne masu shirin shiga aji shida nan sukayi directing Ashfaq har rumfar dasu Maryama suke.
Mutuwar tsaye Ashfaq yayi yana duban Maryama dake k'ok'arin bubbud'e kyautukan ta Hajiya na hanata, tana fad'in ta bari sai sunje gida.
Baisan dalili ba amma ganin wannan budurwa yasa shi tsananin fad'uwar gaba, gani yake tamkar ya tab'a ganin fuskar a wani wajen.... Saida Hajiya ta dubesa tsegeg ganin yanda yake bin Maryama da kallon k'urilla kafin tace "Malam lafiya dai koh, inji kai ba Maye bane don yanzu duniya babu yarda." Nan Hankalin Maryama ya dawo ga mutumin da Hajiya ke masa magana.
Saurin saita kansa yayi kafin ya soma gaida Hajiya ya sanar da ita, shine wanda Dr Tahir ya turo don ya tafi dasu..
Hajiya dai dubansa kawai take, don taji Attahiru yace abokin aikinsa zai turo, toh wannan baiyi kama da likita ba sam, ya tara k'asumbi sannan da alama ba'a taje k'asumbin, duk sun dunk'ule waje guda, domin kuwa duk wanda zai bar k'asunbi yana gyarawa ba k'aramin kyau yake k'ara masa ba amma na wannan sam babu gyara,.. Tasan dai likitoci da tsafta da son gayu, wannan kam ba haka yake ba..... Jiyo muryar Maryama tayi suna gaisawa da mutumin... Cikin sauri Hajiya ta kaste su da fad'in "Kai wannan kai ba likita bane, yo likita ne zamu gansa haka babu gayu... Kai ko bature nan yaga likita ya bari wajen gayu..." Maryama sai tamke hannun Hajiya take tana mata magana k'asa-k'asa cewa tayi shiru amma Hajiya ta kasa, sai zuba take.
"Kai wannan kai d'an yankan kai ne da ganin ka, ko kuma masu garkuwa da mutane kinafas (Kidnappers)...."
"Hajiya don girman Allah kiyi shiru." Maryama ta fad'i cikeda b'acin rai.
Shek'ek'e Hajiya ta dubeta kafin tayi magana Ashfaq yayi saurin fad'in "Em babu damuwa barin kira Dr d'in sai ya maku bayani...." Ya k'arashe maganar yana ciro waya a aljihun sa, Maryama kuwa takaicin Hajiya ya cikata fam.
AT na d'aga wayar Ashfaq ya mik'a ma Maryama yace "Ga Dr d'in nan."
Hajiya kuwa fad'i take "Ya daifi da mu shiga motan d'an yankan kai."
Maryama kam mik'a ma Ashfaq wayar sa tayi bayan sun gama magana da AT, ta dubi Hajiya baki a ture kafin tace "Muje Hajiya, kar mu b'ata masa lokaci k'ila nada wurin zuwa."
"Yo shi Attahirun yasan yanada wajen zuwa ya kira mana shi, ke nifa wannan sam bayada zubin likitoci..."
Cike da takaici Maryama ta soma tafiya don tuni Ashfaq ya nufi yanda ya paka 'yar Henacy d'insa.
Har suka iso gida Hajiya bata daina zuba ba.
Maryama kam saida ta bari Hajiya ta shige ciki kafin ta dubi Ashfaq tace " Uncle Dr don Allah kayi hak'uri, wllhi haka Hajiya take, don Allah kayi hak'uri. And mun gode sosai."
D'an murmushi yayi kafin yace "Haba dai ki daina bani hak'uri pls, ai Hajiya tayi gaskiya domin yanzu duniya babu yarda... Ganin tunanin ganin k'ok'on Kan Nabila da yayi a d'akin Daddyn sa na neman fad'o masa yasa sa saurin kauda zancen da fad'in "Kinga sunana ba uncle Dr ba, sunan Ashfaq, just call me Ashfaq."
K'walalo ido waje Maryama tayi kafin tace "Toh ai kai abokin Uncle d'ina ne, kaga kaima ka zama Uncle d'ina."
Murmushi ya kuma yi kafin yace "Ai Uncle d'inki Ya fini tsufa, amma tunda kince haka, ki kirani da Yaya Ashfaq."
Murmushi itama tayi kafin tace "Shikenan, Yaya Ashfaq."
Murmushi yayi kafin yayi congratulating d'inta, bata tsaya biyema surutun sa ba ta shige ciki don tasan yanzu Hajiya sai ta kawo wani zancen.
Ashfaq kuwa kallo ya bita dashi har ta shige kafin ya shige cikin motar sa ya tada ya tafi.
*************