← Book details Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 63

Sashe 41

Shakuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashfaq ya shafi goshinsa, da gaske mahaifiyar sa har gado aka bata a asibiti, shi wai yaya zaiyi ne, tabbas ya koma ma Daddy babu mata zai aura masa Fairuzah yarinyar da ta gama barikancinta a VICTORIA UNIVERSITY OF MANCHESTER, ENGLAND. Aside from wannan ma sam bai yi shirin confronting mahaifin nasa ba, toh wai ya zaiyi ne..... Baffah Yawale ne kawai ya fad'o masa a rai, shi kad'aine yasan Haidar na living wata rayuwa, shi kad'aine yasan Haidar na b'oye kansa saidai shi a iya saninsa Haidar na b'oye kansa ne sabida 'yanmata masu son shi da muk'amin mahaifin sa ko kuma da kyaun halittan sa, amma bayaga wannan baisan akwai wata dalilin ba.

Sauk'e nannauyan aniyan zuciya Ashfaq yayi, tabbas Baffah Yawale zai tsaya masa a neman aurensa ba tareda sanin mabaifin sa ba, zasu fita da Mummy zuwa k'asar Germany in a couple of weeks, yanaso da zaran sun dawo yaje ya duba mabaifiyar sa sannan a lokacin da matar sa zaije yasan idan Fairuzah taga yayi aure ta hak'ura dashi kenan har abada sabida yasan zafin kishi irin na Fairuzah, koda suke school tasha attempting hallak'a 'yanmata masu kawo masa hari. Da wannan tunani Ashfaq ya kwanta, ya jima yana tunanin ta shi kad'ai yake murmushi yana tuna yanda AT yake son hanasu alak'a ta k'arfin tsiya, tunowa yayi yanada Hajiya. Take ya saki wata sassanyar murmushi had'i "Keenafas" mik'ewa yayi ya shiga manna gashin bakinsa ya shafa wata irin hoda da yake amfani da ita mai b'atar da asalin kalan fatan mutum kafin yayi shirinsa cikin k'anan kaya mai dogon hannu kana ya fice ya nufi gidan Hajiya.

Sosai Hajiya taji dad'in zuwan nasa, tabbas Allah Ya had'a just jinin Hajiya da Keenafas. Maryama da wuni guda tayi kusan yinsa a d'aki sosai take dariyan hiran nasu, saida ta jiyo muryar Ashfaq na tambayar ta kafin ta mik'e ta fito parlorn, kallo ya bita dashi don kaman ya lura wani abu na damunta. Hajiya sai satan kallon sa take, cikin zuciyarta take fad'in _Zama ka fad'i ne da bakinka Keenafas, son d'iyata kake kaman Pep alop (five alive)_.

Dabara Hajiya tayi t mik'e ta barsu a parlorn, tunda ta gaishesa bata kuma cewa komai ba, shi kuwa sai jefo mata tmbayoyi yake uwa d'an jarida..

****************

Gidan Dr Ahmad Tahir Shattima dai haka kowa ya wuni babu walwala, idan ka d'auke Shema'u dake faman k'ulle-k'ullen step d'inta na gaba, Maama Juu dai an bata da tunanin abubuwan da suke kan faman faruwa, ita kuwa Sajida wuni tayi d'akinta a kulle tak'i magana ma kowa tak'i bud'e k'ofa. Shi kuwa AT tunda ya kad'e k'afafunsa ya tafi _Sajmal_ bai waiwayo gidan ba.

Uwar d'aki ta k'ule ta shiga waya da Buzu tana sanar dashi Dama ta samu, babu haufi yanzu Sajida zata bisa duk yanda yake so... Daga nan waya tayi dasu Jarka su Spider ta sanar dasu su cika aikin su yau, dama jiya data fita saida suka had'u a wani uncompleted building ta basu kud'in su cash.

Ita kad'ai sai annashuwa take, abubuwa suna tafiya mata yanda ta shirya ta kuma tsara.

***********

Yau dai sosai Ashfaq yaja Hajiya da Maryama da hira, har dinner saida yaci a gidan. Dr Bilyamin abokin aikinsa ne ya masa waya zai basa wasu takardu gobe ya shiga dasu TH da sassafe akwai wani taron likitoci da zasuyi, Dr Shattima (AT) ya sanar dashi yanada ziyartan asibitin koyarwa na Bauchi a gobe, so ba lallai ya halarci taron ba.. Ashfaq ya kwatanta masa yanda yake Dr Bilya ya tsaya ya basa har yana masa tsiya ya tare gidansu Dr Shattima kodai kamuwa yayi.

Ashfaq dai sai dariya kawai yake sukayi sallama da Dr Bilya, komowa cikin gidan Hajiya yayi suka d'an kuma tab'a hira kafin ya masu saida safe, ba don Maryama taso ba Hajiya ta sakata dole ta raka Keenafas har wajen motar sa.

*********

Jin knocking d'in Daddynta a k'ofa yasa gabanta ya yanke ya fad'i, tayi saurin katse wayar da suke da Buzu ta cilla wayar k'asar gado kafin ta k'araso ta bud'e masa k'ofan bakinta a ture...

Shi d'inma babu walwala a fuskad sa ya shigo.

Zama tayi bisa gado kafin ta gaida shi.

Kaman bazai amsa ba sai kuma ya amsa ta a tak'aice. Hard'e hannayen sa yayi a k'irji yasha mur sosai kafin ya soma fad'in "Bazan lamunci rashin kunya daga wajen ki ba , sarai na sani kina kan gab'ar ne har yanzu, toh ki sani I'm your father not your brother, don na baki room ina sharing abu daku yarana doesn't mean zakiyi duk abinda kike so, be careful . Ki shiga hankalin ki, bansan yanda kika samo wancan idea d'inba amma ki sani duk abinda zanyi ku nake fara tunowa first my family, sai na duba yin abin wani implications zai haifar sai nasan matsayin abun kafin nayi. Kwanan nan na auri 'yaruwar mahaifiyar ku sabida ku sabida na inganta maku rayuwar ku, sabida na faranta maku, ashe ke kina babba bazaki kula da hakan ba har kina bud'an baki kina fad'an magana akaina Sajida!! Mahaifin ki, toh wllhi ki shiga hankalinki bazanyi tolerating rashin kunya koda wasa, kina jina..." ya k'arashe cikin daka tsawa.

Jinjina kai tayi hawaye na k'ok'arin zubo mata don tunda take da mahaifinta bai tab'a yin fushi irin haka da ita ba, da k'yar ta iya furta "Daddy I'm sorry." Still yayi bai amsata ba... Tana jin sanda ya fita daga d'akin still ransa a b'ace... Wayarta ta kuma lalumowa ta kulle k'ofarta ta shiga neman layin masoyinta Buzu domin shi kad'aine zaiyi calming nata taji sanyi.

Tsaye yake cikin closet d'insa yana sanye da inner white da lallausar wando na bacci, bayan ya gama feshe jikinsa da body spray na AXE ya k'araso cikin d'akin, nan ya samu Shema'u har ta kwanta, kaman daga sama sai jiyo sautin kukanta a hankali yake.

Gaba d'aya jikinsa yayi sanyi, d'an zama yayi gefenta yama rasa me zai soma fad'i mata, hannu ya mik'a ya d'agota nan yaga hawaye kwance saman fuskar ta sai faman k'ok'arin b'oye fuskar take..

AT ya k'ura mata idanu kafin yasa hannunsa ya shiga goge mata hawayen yana fad'in "Kiyi hak'uri nasan matsalar kukan ki bazai wuce nawa matsalan ba, I'm sorry kinji believe me nima abun ya dameni sosai sannan ina research akai kullum kinji koh, I promise you komai zai zama normal insha Allah kinji...."

Bursting ta kuma yi cikin kuka ta shige cikin jikinsa cikeda salo na makirci.. Matse ta yayi cikin jikinsa his heart's beating so fast, yana tsoro kar Allah Ya kamasa tunda ya kasa sauk'e nauyin da ya d'aura masa.

A hankali ya soma furta, "Shema'u banso na zama azzalumi a gareki, ina so muyi magana na fahimta nida ke, idan auratayya bazai yuwu a tsakanin mu ba, zan sawwak'e maki sabida ko kad'an banson shiga hakkin ki...."

D'ago watery eyes d'inta tayi tana dubansa yanda yayi maganar, k'irjinta ya buga uwa an sauk'e mata guduma, girgiza kai ta soma tamkar tab'ebb'iya tana kuma cukwikuye masa riga take fad'in "No, no my AT I love you, I can't do without you, zan jira har lokacin da zaka sami lafiya, pls kar kace zamu rabu kaji...."

Cikeda mamaki yake kallonta kaman ba ita bace tace sabida yaran 'yaruwarta zata aure sa ba... Ya shiga yin wasu irin tunani sarara, jin tak'i daina kuka yasa sa hugging d'inta still tunanin maganar nata yak'i barinsa.

Shaf ya mance takardun da Dr Bilya ya basa a gidan Hajiya, gashi gobe da sassafe ake buk'ata gashi go slow d'in da ake samu da safe a titin unguwar Hajiya zuwa TH ka iya jawo masa ya rasa meeting d'in kuma takardun are very important..

Agogon hannunsa ya duba yaga har goma ta wuce amma gwara yaje, domin zuwan nasa yau zaifi, idan ya kai gobe komai ka iya faruwa.

*Sameena Aleeyou Mrs*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*34*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*Jinjina, Fatan Alkhairi tareda gaisuwa a gareki gwanata Biebee Isa, ina matuk'ar jin dad'in yanda kike biye da wannan labari nawa.... Rabbi ya kareki da kariyar sa, Ubangiji ya bar k'auna❤*

Saidai ya shigo layin ya kuma duba agogon jikin motar sa, k'arfe goma da kusan rabi harta gauta, d'an jim yayi kafin ya soma tunanin ta yaya zai soma masu sallama a wannan daren, wannan ma ai sai yasa suji tsoro, gaskiya sam hakan baiyi tsari ba.

Ashfaq ya karya kan motar sa ya fito daga close d'in gidan Hajiya, dama gidan nata shine yanda kwalta ya k'are shine a k'arshen layi.

Clash Ashfaq yayi da wata bak'ar mota sai faman danna masa full light suke suna kashe masa idanu, d'an tsaki yayi kafin ya basu hanya suka wuce... Sannan shima yayi wucewar sa..

Bacci suke dukansu biyu hankali kwance, jin ana buga masu k'ofa yasa Hajiya ta mik'e zunbur bakinta d'auke da salati tana k'ok'arin lalumo tocilanta, nan Maryama ma ta bud'e idanu tana k'ok'arin mutstsuka su. Hajiya ta haska tocilan ta tana tafe take fad'in "Ilu sam bakada saiti, yo ko uwar me kake nema talatainin daren nan oho....." muryarta ne ya carke ganin tik'a-tik'an k'arti kusan guda uku dukansu da bak'ak'en kaya sannan fuskokinsu a rufe....

Salati ta soma tana fad'in "K'alu innalillahi wa inna ilalihirraji'una ku kuke ganin mu bamuke ganin ku ba......" bata kai aya ba Spider ya bud'e murya yace "Shut up! kar ki cika mana kunne..."

Firgit Maryama ta kuma farkawa ta mik'e tana k'ok'arin saka hijabinta...

Oga IK ya kalli Spider yace "Shiga ka zak'ulo mana yarinyar..." Spider ya gyad'a kai kafin ya soma bud'e k'ofofi.... Hajiya tayi wuf ta tare masa hanya tana fad'in "Halan ajiya kayi cikin d'akin??" yanda tayi maganar sam babu tsoro a tattareda ita.. Spider kallo kurum ya tsaya yana binta dashi...

Oga IK ya kalli Jarka da tuntuni yake jiran umarnin sa kafin yace "Ka buge buhun nan ka danna min kan wannan tsohuwar ciki, kai kuma Spider ka shige ka fito min da yarinyar nace maka..."

Ya k'arashe yana karya k'afafu saman kujera yana hura bakin bindiga...

Hajiya tayi masu k'uri tana kallon ikon Allah yanda Jarka ke warware k'aton buhu wai ita za'a danna kanta ciki, jakar uba!
Chapter 41 · 0% Book details