← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 66

Sashe 62

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tanzarzar yazo da mugayen aljanun dakarun shi haka shima shubumbum yazo da nashi dakarun masu yawan gaske , yaƙi aka fara yi baji ba gani kowa burinsa yaga yayi nasara yakashe makiyinshi , anyi kashe_kashen da bazasu san adadin su ba , inka duba bangaren sarauniya kisa kawai takeyi idonta yarufe burinta kawai takawo bayan wa'yannan azzaluman dasuka addafi ƙasa, jikinta duk yayi gaja_gaja da jini duk wanda ya shiga hannunta kisan wulakanci takeyi musu ga drygon dinta dake feso musu aman wuta , haka abangaren gimbiya afroza itama kisa takeyi bana wasa ba , harta khairaty ba'a barta abaya ba duk da ankashe musu mutane dayawan gaske amma hakan besa sun sare ba acikin faɗane aka kashe yaron jakadiya abashiyya wato shufan, sannan ankashe galadima abdud Shakur sauran kuma anji musu mugun raunin da bazasu iyayin yaƙi ba duk sun jigata musamman abashiyya da khairaty sunji rauni sosai, sarauniya ganin haka ne yasa ta kara kaimi , isowa gabanta tanzarzar yayi yana fadin " sarauniya karkiyi zaton keda mutanen ki zaku bar nan araye , kiduba munci galaba akanku , dake da jaaazana duk nawane hhhhhhhhhhh" yakarasa maganar nashi yana muguwar dariya ,dirowa shubumbum yayi gabansu ya ce " karya kuke yi nine kadai zan mallaki jaaazana dan haka inkun isa mu gwabza mugani " yafada yana zaro sharɓebiyar wuka, duk su biyun sun mata kewaye ga ta yar karama agaban su , gwabzawa suka farayi suna kaiwa junansu hari cikin zafin nama sarauniya tafito da wa'yannan wukaken da aka bata , tayi wani irin tsalle da seda tayi sama tana ihu me karfin sannan tadawo ƙasa tana caka musu dukkansu biyu lokaci daya nan take shubumbum yazube awajan babu rai duk wasu mutanen shi nan suka fara marmashewa izuwa toka suna mutuwa , karfin hali tanzarzar yayi yazaro wukar acikinshi kafin sarauniya ta ankara ya caka mata acikin ta ya ce " dole sede dukkanmu mu mutu , tunda kikayi nasarar ka war dani abangon duniya dole kema ki mutu " yana karishe maganarsa yazube ƙasa jikinshi yakama da wuta ya marmashe yazama toka yabi iska , haka duk wasu mutanen shi haka suka dinga marmashewa suna komawa toka duk seda suka mutu yayi saura iya yan masarautar nasminaya kadai afilin dagan , ganin halin da sarauniyarsu take cikine yasa yarima ahil da gimbiya afroza da sauran dakaru suka nufota da gudu kamin su iso tafadi aƙasa babu rai atattare da ita zare mata wukar cikinta yarima ahil yayi kafin yadauketa yasabata a kafadarshi suka ɓace , duk wa'yanda suka jigata suma ɓacewa sukayi zuwa masarauta , duk wanda suka gansu sunsan cewa sunyi matukar shan gwagwarmaya a yaƙin da akayi suna shigowa aka fara buga kararrawar nasara nan take kuma lokaci daya masarautar nasminaya ta tashi da labarai guda biyu daya na farin ciki daya na bakin ciki, wato na kashe musu mutane da akayi gakuma sarauniyarsu da aka dawo da ita itama babu rai sekuma na nasarar dasuka samu .

AFTER THREE YEARS ( bayan shekara uku)

Misalin ƙarfe 6:30am na safiya
_____ " twinkle ki tsaya kidena wannan gudun zaki fadi Please kitsaya " suhaima ce tayi maganar dake bin twinkle abaya itakuma tana gudu tana dariya , ashe ba iya suhaima ce take binta ba harda Fawwaz da Hafiz duk iya yinsu sunkasa samun nasarar kamata dan taki tsayawa gudu kawai takeyi , karasawa tsakiyar falon nayi dan nide sunan twinkle kadai naji suna kira amma ban gantaba seda nadawo cikin falon sannan nasamu ganin ta , yarinya ce yar kimanin shekara uku fara tas kamar baturiya yar duma_duma da ita jikinta tsabar yanda hutu yazauna ajikinta ko alamar ƙashi babu tana sanye da kayan baccin pjmas orange color kafarta sanye da takalmi slippers irin nasu na yara gashin kanta brown color ne an raba mata shi gida biyu an yi fakin dinsu idonta brown color fuskanta na dauke da manyan ido ga dogon hancinta tanada zara_zara eyelash , dan mitsintsilin baƙinta nadauke da red libs , babu inda twinkle tabaro fanan akama kamar fanan sanda take karama sede ita fanan gashinta baƙi ne sannan idonta ba brown bane , juyowa tayi tanayi musu gwalo da muryanta irin na yara ta ce " you can't catch me bazaku iyabaaaaa" tafada tana jan maganar kokarin cafke ta Fawwaz yayi ta zille ta bugi Center table dake dauke da glass flower nan take kwalbar flowers din yafado ƙasa ya fashe ganin tayi ɓarna ne yasa tazaro idanunta waje tasa hannu ta rufe baƙinta aikuwa da gudu tashige cikin kitchen tasamu abu na shirya mata breakfast dinta abu tana ganin shigowarta ta ce " tunkwal bazakije school yau bane ?" Cike da iyayi tarike kugu harda gyara tsayuwa kamar wata babbar mace ta ce " well anty Abu kinsan next week is my birthday so teachers dinmu sunbani hutun wata biyar " sa ke baƙi Abu tayi tana kallon twinkle jin abinda ta fada tana kokarin yin magana Hafiz yashigo yana haki ya ce " haba my baby twinkle kiyi hakuri ki tsaya kinga time fa na tafiya zakiyi letting a school" make mishi kafada tayi ta ce " am not going anywhere se bayan birthday party dina" dafe goshi Hafiz yayi sannan yayi kokarin kamota garin guduwa ta tunkude bowl din dake dauke da sauran fulawar da aka mata sandwich dashi yazube aƙasa sannan bowl dinma yafashe , tafi ce da gudu haka suka dinga wasan tsere_tsere da twinkle amma sun gagara kamata.
Bacci yakeyi akan makeken gadonshi jin ƙarar fashewar glass dakuma hayaniya yasa shi gane da waye ake rikici bude sexy eyes dinshi yayi yazauna ya ce " my sturbon baby twinkle ta tashi kenan , wifey your daughter is very stubborn as you , kidawo kiganta yanda ta girma ga surutu kamar wata yar shekara biyar " yasan yanzu duk rigimar da akeyi da ita be wuce akan zuwa school ba , dan kusan kullum haka ake fama da ita akan maganar makaranta duk da batafi wata uku da akasata ba tana nursery one ,amma kwata_kwata twinkle batason zuwa makaranta tafiso tazauna agida tayi ta wasa da kannenta minal yarinyar suhaima se yaron zeenat ashraff da yake gidan wajan ummi . Tashi yayi fuskanshi ahade yasauko downstairs sanye da jallabiya hango twinkle yayi zaune akan kujera sukuma masu bin nata sunyi saronda suna zaune akan kujeran suna maida numfashi, tana ganin shi ta tashi da gudu tana " daddy ! daddy" daukanta yayi sama yanayi mata cakulkuli tana dariya juyawa yayi da ita zuwa part dinsu suna shiga ya ce " meyasa twinkle din daddy tafiye rigima ne? " cuno baƙi tayi ta ce " sorry daddy" toilet yashiga da ita yayi mata wanka yashafa mata lotion dinta sannan ya gyara mata gashinta yashiryata cikin uniform dinta ya sa mata sandal sannan yadauki school bag dinta ya ce " wow twinkle din mom and dad, yanzu se muje kiyi breakfast" ta ce " okay daddy " fitowa sukayi falo yana rike da hannunta tayi kyau gwanin sha'awa tsayawa sukayi agaban hoton fanan yaɗago ta sama kan kafadarshi ya ce " oya talk to mommy before leaving " hoton fanan ta mannawa kiss dede kumatunta da muryanta da maganarta be gama ƙwari ba ta ce" good morning mommy , i missed you , nida daddy muna jiranki bye zantafi school wish me all the best " ta fada tana kara mannawa hoton kiss murmushi kawai Mr azaad yakeyi , shima kiss din ya mannawa hoton sannan ya ce " wifey Ina matukar kewarki sosai ban cire rai da zaki dawo gareni ba muna jiranki nida little fanan " twinkle dake dauke akan kafadarshi da karfi ta ce " yessssssss daddy mommy takusa dawuwa daga tafiya , daddy kafada mata birthday party dina next week ne ?" Barin falon sukayi suka sauko upstairs nan ne ya bata amsa " twinkle shiiii surutunki is too much darling, mommynki tasan birthday dinki yazo , ta ce bazata samu zuwa ba se next month" Jin abinda yafada ne yasa ta ɓare ba'ki zatayi kuka jin wai mommynta bazata zo birthday party dinta ba , ummi da tasauko downstairs ne taji maganar dasukeyi yasa ta girgiza kai ta ce " my twinkle waye yafada miki mommynki bazata zo ba , zatazo kinji don't cry kinji kishiyata" da gudu taje ta rungume ummi tana dariya ta ce " Yes i know mommy na zatazo kuma sannan bazan yanka cake ba harse tazo zamu yanka tare " murmushin yaƙe ummi kawai tayi dan tafadawa twinkle hakane ɗan ta kwantar mata da hankali daukanta ummi tayi suka zauna akan kujera ta kira Abu takawo mata breakfast din twinkle anan tayi feeding dinta sandwich dinta da tea ga lunchbox dinta da aka shirya mata ɗan ita bata cin abinci makarantar da ake bawa student shisa akeyi mata nata kullum inzata tafi , tagama ummi tagoge mata bakinta da tissue, ta ce" grandma Ina my grandpa ?" dariya ummi tayi ta ce" grandpa yayi tafiya amma zedawo before birthday dinki " suhaima ce tafito hannunta rike da minal ta ce " ummi yau kinsan irin exercise din data samu sekinji tausayinmu , gashi yarinya nan narasa ya akayi ta iya gudu kamar wata yar tsere" tazauna tana magana hade da murmushi tana kallon twinkle dake kan cinyar ummi ga Mr azaad agefensu, dariya ummi tayi dan tanajinsu ta ce " to bagashi yanzu tasaku kunyi exercise ba " dariya ummi da suhaima sukayi gaishe da Mr azaad suhaima tayi ya amsa da " lafiya " daukanta yayi ya ce " muntafi " harsuka fita tanayi musu bye-bye suma sunayi mata fuskokinsu dauke da murmushi.

Dropping dinta yayi a school har cikin class dinsu yakaita sannan ya koma gida yakoma bacci .

Karfe 11:30 Faisal yakirashi yasanar dashi ankawo order furniture na company da sukayi a London" okay " kawai yace yakashe wayarsa yatashi yayi wanka yashirya cikin suit yafita zuwa Company dan ganin kayan da aka kawo.
Chapter 62 · 0% Book details