Sashe 24
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsaye suka samu ya usman da yarinyar akan yayantan doctor kuma yana dubashi shima kanshi yaro ne matashi da be wuce shekara 19 ba fari kyakyawa suna kama sosai da kanwar tashi yana kwance yana baccin wahala zama sukayi akan kujerun dakin kallon yarinyar doctor yayi yace " Yan mata ki kwantar da hankalinki yayanki ze samu sauki da izinin Allah kinji" murmushin yaqe tayi shikuma ya fita , mama ce tace " zo nan yata " ita se yanzu ma ta lura dasu dan dazun da tashiga tsaban hankalinta baya jikinta bata wani lura dasu ba jiki asanyaye taje wajan mama ta tsuguna har kasa da siririyar muryanta tace " mama gani" wani irin dadi mama taji jin yarinyar ta kirata da mama lokaci daya taji hankalinta ya kwanta da yarinyar gyara murya mama tayi tace " meye sunanki ? Su waye ku?Kuma sannan ina iyayenku?" Share kwalla yarinyar tayi tace " sunana hairah ! Yayana kuma sunanshi hafiz mu yan garin gombe ne iyayenmu sun rasu wata 9 dasuka wuce, kuma tunkafin su rasu dama bamuda kowa tom dama babanmu ne yakeyin sanaar dako yake siya mana abinda muke sawa cikinmu se yazo yarasu bayan ya rasu da sati daya mamanmu ma tarasu , tundaga lokacin komai ya canza mana bama samun abinda zamuci se nayi mana bara tukun wata rana mu samu wata rana kuma mu kwana haka shine yayana yashiga kasuwa shima yafara yin dakon inya samu kudi se ya siya mana waina ko kuma rogo ko garin kwaki shine yazo yafara ciwo wani mutum dayake hayan will bairon agurinshi ya kawo shi asibiti tunda yazo sau daya be sake dawuwa ba babu kudin dazaa dubashi shisa likitocin babu wanda yakebin ta kanmu " ta gama magana tana kuka me tsuma zuciya sun matukar tausayawa rayuwarsu domin yaran sunga rayuwa ba uwa ba uba dole su wulakanta tunda babu dangin iyayen , ga ta mace kuma karamar yarinya riko hannunta mama tayi ta zaunar da ita a gefenta tana lallashinta fanan dake gefensu ta zubawa hairah ido tana kallon tsantsan kamarsu da khairaty amma tayi murna da faruwan hakan , ya usman de ya kame akan kujera se faraa yakeyi kamar wanda aka mishi kyauta da kujeran makka yanata kallon hairah ,Mr azaad shi abun ya usman ma dariya yaso bashi ganin irin murmushin dayake sakewa tsaban abinda yake nema yasamu.
Baba ne yace" mamansu kuje gida mazan zasu zauna da shi ku dauketa kaima usman tashi ka bisu tunda kaji lafiyar dole ja'iri kawai " tunkafin yagama magana ya usman ya mike riko hannunta suhaima tayi duk suka fito dasu ummin sukayi gidansu fanan din a falo suka yada zango fanan kuma takai kanta dakinta tana yar dingisa kafa binta da kallo mama tayi dan tun zuwansu ta lura da tafiyarta murmushi ta sake kawai , nunawa hairah bathroom suhaima tayi ta shiga tayi wanka sosai, tafito sanye da dogon kodadden hijab dinta na roba ,masha Allah itama ba laifi dukda yanzu ta fara tasowa amma tana da sura me kyau, riga da skirt din atamfa suhaima ta bata sabo dal dan tunda ta karbosu agun dinki kala biyar taga duk sun mata kadan ta ajiyesu shine yanzu ta bawa hairah daya ta ajiye mata sauran , das kayan suka zauna mata ajiki be kamata ba tayi kyau sosai shafa mai tayi kawai ta zauna can nesa dasu duk a takure take se dar_dar take ganin haka yasa fanan ce mata " hairah ki saki jikinki damu kinji kidauke mu kamar yan uwanki na jini karki dinga dar dar daga yanzu kinzama yar gidan nan saboda haka feel free " godiya tayiwa fanan sosai harda kwalla , shigowa dakin zeenat tayi hannunta rike da plate din abinci tuwon shinkafa da miyar kubewa bushashshe yaji kifi banda hade da nama se kamshin man shanu yake, lokaci daya fanan taji yawonta ya tsinke mikawa hairah plate din zeenat tayi da ruwa , tana kokarin zama fanan tace " yau naga wariyar launin fata zee nizakiwa haka ?" Cike da mamaki suke kallonta musamman ma zeenat duk tunaninta tayi mata wani laifin ne tace " anty fanan mena miki?" Bata fuska fanan tayi tace" ni shine bazaki dibo min abincin ba ko " kallon juna suhaima da zeenat sukayi kafin suka fashe da dariya harda tafawa hada baki sukayi wajan fadin " kice mun samu karuwa " dalla musu harara fanan tayi da dara_daran idanunta tace " banason iskanci kun fara ko ?" Haka sukata tsokanata tayi banza dasu kiran layin Amira tayi ta tambayeta ko tana gida , daka tsalle amira tayi tace " besty kinzo gida kenan ?" eh kawai fanan tace mata ta kashe wayar aikuwa kafin kiftawa kawai sukaji yo sallamar amira shigowa tayi tazauna tana kallon besty nata da suka kwana biyu basu hadu ba tun rasuwan mansoor dasuka je musu taaziya " ohhh besty kina nan abun ki gaskiya bakida kirki " cewar fanan " sorry besty kinsan yanda abu suka hade min se a hankali ga school ga asibiti abin ba sauki" bude baki tayi zatayi magana wayarta yafara ringing miko mata wayar hairah tayi se anan ne amira ta ganta tace " woww suhaima aina kuka samo wannan beautyn ko de su zeenat ne suka zo da ita?" tayi maganar tana sake kallon hairah da kanta akasa ta gaisheta takoma ta zauna suhaima ce tace " bakisanta bane itama kanwar muce" kin daga kiran fanan tayi ganin bakuwar special number batasan nawaye ba , five 5 digit din last number ya kare da 99999 seda aka kira kusan sau uku kafin ta daga tasa akunne tayi shuru daddadar muryanshi me tafiya da Kuma ratsa mata jijiyoyin jikine taji ya sauka mata akunne yana " hello " nauyayyar ajiyar zuciya tasauke wanda yasa suka dago suka kalleta tace " assalamualaikum habiby " suhaima, zeenat,amira tsaban shakiyanci har suna hada baki wajen cewa " awwwwwwwwn ! Habiby" hade da shewa pillow fanan ta wurga musu hade da harara sannan tayi kwafa shagwabewa tayi tace " habiby ka gansu suna tsokanata ko ?" Jan numfashi yayi kamar wanda yaci yaji lokaci daya yaji ta tayar mishi da hankali idan tana mishi wannan shagwabar kawai daurewa yakeyi dan shi kadai yasan yanda yakeji katse kiran yayi , tabe baki tayi tace " Allah zanyi maganinku kafin in tafi " kiran hairah tayi ta zauna akusa da ita tadinga janta da labari dan tasamu tasaki jiki ,
Bayan 30mint har lokacin basu fito ba suna dakin suna hira gani sukayi an yaye labuyen bedroom din , Mr azaad ne tsaye ajikin kofa fuskan nan adaure tamau duk seda sukasha jinin jikinsu lokaci daya suka nutsu suka shiga taitayinsu hatta ita fanan din .
" Wato matar tawace kuke tsokana ko?" Kamar zasuyi kuka suka girgiza kai alamar ah ah watsa musu harara yayi kafin yayi kwafa inda fanan take yaje yasa hannu yadauketa cak yayi hanyar fita falo mutsu_mutsu tafara ganin abinda yake shirin aikatawa tasan akwai mutane a falon yazataji in suka gansu haka ahankali tace " habiby kayi hakuri ka saukeni kasa zan iya tafiya da kaina" ko sauraranta beyi ba suka fito falo babu kowa afalon duk sun watse mama da ummi suna daki suna hira, gauron numfashi ta sauke tana godewa Allah .
Be sauketa ako ina ba se a motar yaja suka hau kan titi , cikin nutsuwa yake driving zubawa kyawawan fuskanshi ido tayi tana kallonshi cike da so da kauna, batare da ya kalleta ba yace " baby wannan kallo haka ?" tace " to ai bana gajiya da kallon kane " cize libs dinshi nakasa yayi jiyayi magana ma kadai idan tayi kara ingizashi take bece mata komai ba ya nufi migration office barinta yayi a motar yashiga ciki after some few minutes yafito hannunshi dauke da envelope daura mata yayi akan cinya ya tada motar suka dau hanya bata ko dauki envelope din ba saboda bece mata komai ba yanda yadaurashi hakan tabarshi kallonta yayi yace " open it" sa zara_zara chocolate color yatsunta tayi ta bude passport da visa ta gani nata daduk wani abu da mutum yake bukata inzashi abroad duk akwai jujjuyasu tayi a hannunta kafin ta kalleshi tace " habiby to sukuma wannan fah tafiya zamuyi ?" driving dinshi kawai yakeyi be kalli direction dinta ba ya gyada mata kai, bata sake cewa komai ba ta maidasu ta rufe , cikin makay shawarma suka shiga yayi packing motar fita yazoyi tarike hannunshi tace " habiby nide bazaka barni nidaya anan ba " matso da kanshi yayi ya manna mata kiss a libs dinta yace " bazaki iya tafiya ba kibari inje in fito" kwabe fuska tayi tana kokarin yi mishi kuka bayanson ta tayar mishi da rigima yasa yafito yazo yabude mata itama tafito duk idon jamaa yadawo kansu se kallon akeyi saboda sun burge jamaa sosai musamman ma wayanda suka ganesu , rikota sosai yayi ajikinshi yanda bazataji zafi sosai ba intana tafiya dukda tanajin zafin ba sosai ba haka ta sake daurewa tana hada tafiyanta. makay shawarma babban joint ne a gombe yana da girma dakuma kyau sosai babu abinda babu a ciki , rike hannunta yayi suka fara tafiya har ciki wajan shopping tsayawa yayi yace ta dauki abubuwan da take bukata side din su perfumes taje ta diba masu kamshi da dadi hade da lotion's se shower gel, body spray, mouthwash, sannan takoma kan kayan kwalama ta dibe chocolate sosai da ice cream security wajan ne yariko keken kayan yatura har wajan yin bills ATM ya bada suka cire kudinsu suka hada musu komai a leda karba security yayi akasa a bayan motar suka shiga suka tafi duk tunaninta daga nan gida zasuyi setaga ya sakeyin packing a yahuza suya yafita ya karbo nama da yogurt dinsu masu matukar dadi .