Sashe 23
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
" auta zoki kaiwa yayanku abincinshi daki nasan yana nan yana bacci be tashi ba " cewar mama da ta gama zubawa kowa abinci tunda akayi wannar case din na tsakanin ya usman da khairaty yadena shiga cikin mutane ko kasuwa ba wani zuwa yakeyi ba yarame yayi baki kamar ba ya usman ba babu yanda basuyi dan ya sake amma abu yaci tura harsuka gaji suka zuba mishi ido koda ya al ameen yaje dan yamishi hira haka zeyi shuru ya barshi harya gaji yayi shuru haka suka zubamai ido kawai kuma tundaga wannan ranar be sake ganin koda me kama da khairaty ba , shigowa dakin auta tayi hannunta na rike da kulan abincin shi wata razananniyar kara tasa da gudun gaske suka shigo dakin nashi cikin tashin hankali dan karan da auta tayi ta firgitasu kwance suka samu ya usman acikin aman jinin da yayi asume innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai suke iya furtawa daukanshi ya al ameen yayi yasashi a mota shida suhaima da auta baba kuma shida mama basu tsaya ako ina ba se a medical center na cikin garin gombe admitting dinshi sukayi a emergency , taimakon gaggawa suka fara bashi kusan bayan 1 hour suka fito suna goge zufa tasowa sukayi suna tambayarsu ya jikin nashi kallon baba da ya al ameen doctor yayi yace " ku biyoni office" yayi gaba suka bi bayanshi duk sun matsu suji me ze fada zama sukayi doctor yacire glass din idonshi yafara magana " am ranka yadade kuyi hakuri da abinda zan fada muku! dan ku gaskiya yana cikin wani halin rayuwa ko mutuwa duk da ranshi baa hannunmu yake ba amma a halin dayake ciki yanzu tabbas inbe samu abinda yakeso ba zaa iya rasa shi domin yakamu da ciwon zuciya kuma saura kadan ya buga , a shawarce kafin nan da awa 2 ku gaggawar samo mishi abinda yakeso saboda inya tashi yayi arba dashi ko hakan ze taimaka amma in ba haka ba yana cikin danger" tunda doctor yafara magana baba da ya al ameen suke zufa kamar wanda aka watsawa ruwa sun jike tashin hankali da baa sa mishi rana yanzu tayaya zasu fara wannan kwamachalan hada aljan da mutum .
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
🧑⚕️🧑⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺
Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹
🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚
( J. W. A 📚📚📚)
PAGE 5️⃣1️⃣ & 5️⃣2️⃣
Damuwa iya damuwa su baba sun shiga fadawa su mama yayi suma hankalinsu inyayi million seda yatashi duk sun shiga tashin hankali sun kasa tsaye sun kasa zaune yanzu me sukasan zasuyiwa ya usman ko giyar wake suka sha de babu yanda zaa hada aljan da bil adama, matsawa suhaima tayi awajansu ta kira layin fanan , fanan na manne ajikin mijinta suna bacci kadan kadan takejin kamar ringing din wayarta idonta arufe ta dauka tasa akunne tace " assalamualaikum" amsawa suhaima tayi tana " fanan ya usman ba lafiya yanzu muka kawo shi asibiti yana aman jini" duk baccin dake idonta lokaci daya ya kaurace mata ta zauna cikin damuwa tace " innalillahi wainna ilaijiraji unnn! suhaima meyake damun ya Usman din ?" Abangaren suhaima ta bata amsa da " doctor's sunce yanada ciwon zuciya kuma daf yake da bugawa inde baa samo mishi abinda yakeso ba " da karfin gaske kirjin fanan yake bugawa taya sukasan zasu fara wannan kwamachalan , jin maganar ta ne yatashi Mr azaad daga bacci kallo daya yamata ya gane akwai abinda yake faruwa sa hannu yayi ya karbi wayar yasa akunne yaji muryan suhaima tambayar ta yayi meyake faruwa suhaima kamar wata yar jarida ko hadiye yawo batayi se jero mishi jawabi takeyi , sosai lamarin ya girgiza shi jin usman harda aman jini katse Kiran yayi yatashi yasa jallabiya yadau car key dinshi kallonshi fanan tayi kafin tace " habiby ina zakaje da wannan tsohon daren?" dawuwa yayi inda take ya manna mata kiss a kumatu yace " asibitin zanje zanturo miki zeenat ta tayaki bacci" langwabe kai tayi tace " ayyah habiby am zan bika" girgiza mata kai yayi kawai yafice adakin part din ummi yaje ya ma zeenat knocking tasowa tayi tabude dakin tana mustsuka idonta, waro ido tayi ganin mr azaad a bakin bedroom dinta a irin wannan lokacin 12:58am nadare " kije ki taya antynki kwana zanje asibiti " abinda yace mata kenan yafice securities biyu ne suka rakashi har asibitin a zaune yasamesu duk sunyi cirko_cirko suna neman mafita gaishesu yayi ya zauna akusa da baba sukaci gaba da maganar lallai gaskiya lamarin usman akwai rudarwa yanzu mafita kawai suke nema haka suka kwana bakin ward din auta ce kawai tayi bacci sukam sun gagarayin bacci sakamakon jikin ya usman daya tashi numfashinshi yana sama yana kasa idonshi ya sauya kala duk sunyi tsammanin fitan rai ne dan abinda yakeyi kamar wanda zewuce lokaci dayane duk suna waje suna ta mishi adduah likitoci kusan shida sun hadu akanshi domin ceto rayuwarshi , family mainasara ne suka shigo asibitin securities na rike da basket na abinci, ciki kuwa harda fanan da ta nace se ta bisu taga jikin dan uwanta dan yanda take tafiya ma mutum ya lura yasan something is fishy haka de anty amina ce take rike da ita kuma ta daure sosai tana tafiya dede dakyar saboda batason kowa ya fahimci wani abu, anty amina tana rike da ita suka shigo zaunar da ita anty amina tayi suka gaisa da mama da mutanen wajen , Mr azaad beji dadin zuwan da akayi da itaba dan yasan wahala kawai takesha daurewa takeyi saboda irin karfin halinta , ummi na tare da maman tana kwantar mata da hankali, fitowa likitocin sukayi dukansu sukayo kansu suna tambayarsu ko anyi dace daya daga cikin likitocin ne yace " a yanzu de munyi nasarar dedeta numfashinsa da bugun zuciyarshi amma zuwa anjuma kuma duk abinda ya biyo baya muqaddarine daga Allah"jikinsu yayi sanyi sosai babu abinda sukeyi se adduah samun sauki dasuke yiwa ya usman, fanan tayi tagumi tana cikin tsaka me wuya yanzu bata da wani solution inde tayi sanya akan al amarin zata iya rasa dan uwanta na jini mafi soyuwa agareta , wani tunani tayi na meze hana ta mantar dashi komai wata zuciyar tace mata" hakan bazeyuba inde ya manta komai zezama yamanta da kowa dake cikin rayuwarshi hatta shikanshi se yamanta dashi wanene" kallon su mama tayi taga yanda duk suka shiga cikin damuwa aranta tace" yah Allah kadubi wannan bawan naka ka sassauta mishi abinda yake damunshi ka kawo mishi mafita kabashi lafiya" wayar Mr azaad ne yayi ringing yaduba yaga abba ne picking yayi yace " hello abba" abangaren abba ne yake tambayarshi ya jikin usman din yabashi amsa dasauki mikawa baba wayar Mr azaad yayi suka fara magana .
Suna ahaka aka fito da ya usman dake kwance rai a hannun Allah akan gadon marasa lafiya nurse's suna turawa zuwa resting room, wani ward babba shi kadai aka kaishi sannan nurse tace musu " zaku iya shiga " duk shiga sukayi, sukayi shuru , ahankali yabude bakinshi yafara magana jini na fitowa abakinshi yace " khairat karki barni kinji wallahi inasonki" sa tissue ya al ameen yayi ya goge jinin dake fita abakinshi, duk tagumi sukayi sun rasa abinyi , ware idonshi yayi yafara bin yan dakin da kallo kokarin tashi yafara dasauri ya al ameen ya gyara mishi pillow ya zaunar dashi , duk se ya jiki suke mai baya iya ce musu uhmmm balle uhmm uhmmm , se kawai kallonsu yakeyi kamar be sansu din suwaye ba doctor ne yadawo yana mishi preking din drip din .
Dukan kofar dakin ward din akeyi kamar zaa fasa shi dan tsaki doctor yayi yace" ko su waye haka oho kilama wasu daga cikin yan sakatiri ne " mikewa fawwaz yayi ya bude kofar wata matashiyar budurwa ce wacce bazata wuce shekara 16 ba a duniya kayan jikinta duk ya kode yafita a hayyacin sa kodadden hijab dinta har kasa tasa hannu da hijab dinta ta kare fuskarta tana kuka tashigo dakin duk juyowa sukayi suna kallonta , cikin siririyar muryanta tace " doctor dan Allah kazo ka dubamin Yayana karya mutu ya barni " ji yayi kirjinshi na bugawa da mugun karfi muryanta seda yaratsa dukkan wani sassar jikinsa zabura ya usman yayi jin muryan da be taba tunanin jiba ganin ya zabura ne yasa suka rirriko shi sunyi tunanin wani abunne yasa meshi ko kuma ciwon ne , dirkowa yayi daga kan gadon ya tsaya agaban yarinyar hannunshi yasa ya cire hijab din da ta rufe fuskanta dashi ja baya yayi yana furta "khairatyyy" da karfi , kallonsu suka maida kan ita yarinyar bakaramin girgiza sukayi ba ganin sak me kama da khairaty babu abinda ya rabasu sede ita komai nata normal ne saboda ita bil adama ce itakuma khairatyyy komai nata over mikewa sukayi tsaye suna al ajabin wannan iKon Allah , bata ko kalle ya usman da yake mata magana ba taje ta zube guiwanta akasa ta kama kafar doctor tana " doctor dan Allah ! dan annabi kamar yanda Allah yarufa maka asiri ka taimakemu mudin narayu ne, ka cece rayuwan yayana ze mutu wallahi duk duniya shi kadai ne gata na bamuda kowa kayi hakuri kaje ka dubashi" ta gama magana tana sheshekar kuka sude kawai ido suka zuba mata tausayinta ya darsu aransu ganin yar karamar yarinya da ita me kananun shekaru tana irin wannan rokon tabbas suna cikin mawuyacin hali, without thinking twice ya usman ya dagota yana kallon cikin manyan idonta da suka kasance brown masu daukan hankali yace " fadamin meya sami yayan naki ?" Share hawayen fuskanta tayi tace" bashida lafiya ne yanzu kuma dakyar yake numfashi dan Allah ku taimakamin kucewa likitocin nan su dubashi, in yayana ya mutu nima mutuwa zanyi " girgiza kai ya usman yayi yace " my girl bazaki mutu ba babu abinda ze sameki da shidin ! In kika mutu nima mutuwa zanyi" gyada mishi kai kawai yarinyar tayi dan bata gane inda zancen nashi ya dosaba , riko hannunta yayi suka fita a dakin shida ita sukayi dakin da yayan nata yake.
Duk zuru sukayi suna kallon ikon god daga su har doctor bin bayansu sukayi da kallo ganin lokaci daya ya usman ya watsake kamar bashine bashi da lafiya ba yana kwance harda su aman jini amma lokaci daya yakoma rass dashi harda jan hannunta sukayi waje , kallonsu doctor yayi yace " dama itace abinda yakeso kenan ?" Yar dariya sukayi suka amsa mishi da "ehh " kawai dan basusan amsar da zasu bashi ba , dariya yayi yace " soyayya kenan to Allah yabasu zaman lafiya" Ameen suka amsa shikuma yafita yabi bayan ya usman da yarinyar, sude ganin abun sukeyi kamar almara duk da ance dama kowa yanada me kama dashi guda bakwai amma ai khairaty ba mutum bace taya akayi sukayi kama da wannar yarinyar to basuda me basu amsa yasa suma sukayi dakin da yayan nata yake kwance, tunda wanda suke jinyar yayi waje ya barsu suma suka fito, suhaima ce tace " ohhh su ya usman abin nema yasamu " dariya zeenat da fanan sukayi harara fawwaz yamusu na wasa yace " kude Allah yashiryeku ! ke Kuma baby danyi maganinki tunda kowa tsokanan shi kikeyi " nanma dariya su fanan sukayi dan dama sudin ne suka rage abaya su ummi da mama,baba Mr azaad,anty amina,duk sunyi gaba sun barsu abaya. Ya al ameen ne yace " nikam bazan iya shirmenku ba nayi nan kaide da zaka iya sekata fama " yafada yana nuna fawwaz sannan ya shige ciki suma rufa mishi baya sukayi wannan karon zeenat ce take rike da fanan kuma sosai ta daure tana takawa .