← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 66

Sashe 35

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

fanan ta dade dayin bacci while Mr azaad idonshi biyu beyi bacci ba dan so yakeyi adaren nan yayi clearing issues din dasuke faruwa acikin gidan sulalewa yayi yafice adakin yasauko ya bude kofar part din gaba daya yaje garden din shikadai kamar wani maye ko ina yayi tsit se kananun maganganun dayakeji kasa_kasa which is yasan nasu wayene haka yazauna yana girgiza kafa.

Mommy na kwance akan makeken gadonta fatalwar mansoor yabayyana atsaye agefen gadonta, murya da dan karfi yafara kiran " mommy! mommy! mommy! Ki tashi kina bacci wato kin barni inata garari Koh?" adan firgice mommy ta tashi daga bacci tana mustsuka idonta rass ta waresu akan Mansoor dake tsaye yana sanye da fararen kaya tashi tayi tazauna dakyau tana kiran " Mansoor dina kaine? dana nayi kewarka" daka mata tsawa yayi ya ce " karki sake kirana da danki muguwa azzaluma, ke ba uwa ta gari bace annamimiya kawai . hankalinki yakwanta dakikayi sanadiyar barina duniya?" ya daka mata wani gigitacciyar tsawa " nace hankalinki yakwanta yanzu? bazan taba samun salama ba harse asirinki ya tono senayi hanyar dazan fadawa kowa ke matsafiyace yar kungiyar BAPHOMET masu shan jini da shirka , yanzu wato babban burinki shine ki kashesu ko ?" hawayene yake zuba akan kumatun mommy taduqa akasa ta ce " my son kayafemin yanda nakesonka bazan taba barin komai yasameka ba bare har inyi sanadiyar rayuwarka sannan magana akan daukan fansana dole sena kashesu kaf dinsu Koda shugaba tanzarzar be amince min ba sena aiwatar da hakan , daga zaran munyi nasarar gamawa da shafin sarauniyar nasminaya sesune target dina " girgiza kai kawai fatalwar mansoor kafin lokaci daya yabace bat .

Inbanda tsuma da jijjiga babu abinda jikin Mr azaad yakeyi tsabar bacin rai da bakin ciki idon nan yajuya yazama mugun jajir da karfi yake cizan libs dinshi na kasa da har gurin yayi ja sosai yafara tsastsafo da jini . yau bayajin ze iya barin mommy ta kwana daranta seya kasheta dan daga inda yake zaune a garden yana yana jiyo duk wani maganar dasukayi da ita da fatalwar mansoor tabbas mommy ta cucesu ta ha'incesu yanzu dama all this while suna tare da munafuka matsafiya agida daya basu saniba tom tabbas shi zedau mumunar mataki akanta tunkafin abba yadawo daga marley sede yadawo yaji labarin kawai ya kasheta. yana cikin wannan mugun bacin ran fatalwar mansoor yabayyana agabanshi fuskanshi dauke da murmushi ya ce " yayana yanzu nayi farin ciki dakasan gaskiya akan mommy zansamu salama yanzu bazaku kara ganina ba se adarul salam nabarka lafiya " yafada yana me bacewa yanawa Mr azaad bye-bye shima bye-bye din ya mishi duk da yana cikin matsanancin bacin rai, hakan be hanashi maida mishi da martanin murmushin daya mishi ba, domin yafayyace musu komai dangane da mommy.

Tofa ana wata ga wata yaude alhamdulillah asirin mommy yatonu shikenan.

Ina jiran ruwan comments dinku duk wanda yasan ina binshi bashin comment yafito yamin abuna tam.

Se munhadu ranar laraba jibi kenan inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏.
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

Gargadi
ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin.

Three pages in one .
Page 5️⃣8️⃣

Yana barin garden din part din mommy yanufa kofofin part din arufe knocking yayi , mommy dake kuka taji ana knocking yasata goge fuskanta tazo ta bude kofar ganin Mr azaad ne yasa tadaure fuska tamau ta ce " kai lafiya zakazo kana bugamin kofa da wannar uwar Daren?" miskilin murmushi Mr azaad yayi yadan hadiye bacin ranshi ya ce " ehhh to lafiya ba lafiya ba zan iya shigowa ?" shima yajefa mata tambaya ganin taki motsawa daga inda take tsaye ne yasa ya kutsa kai cikin part din nata direct kan kujera yaje yazauna yana ciro wayarsa yakira layin abba, " hello abba sorry natasheka abacci banason kadawo ka ji labarin na kashe maka mata shisa nace bari in sanar dakai tukun" tunda abba yaji abinda Mr azaad yafada yagane kancewa yagano komai hamdala yayi dominshi yasan komai akanta amma shi sun rufe mishi baki Koda yayi kokarin sanar da wasu seya gagara , gyara murya abba yayi ya ce " karka mata komai tukun 4:00am zan biyo flight din safe just make sure bata gudu ba " jinjina kai Mr azaad yayi ya datse kiran.
ganin ya shige mata falo ne yabarta tsaye acan bakin kofa , shigowa falon itama tayi taga ya zauna be da niyar tafiya kuma shi be fada mata abinda yakawoshi wajanta ba ya sa ta ce " katashi ka fita kabani guri " afusace yatashi dan dama haushinta yakeji kamar yakasheta lokaci daya kowa ya huta , ya mata mugun shaqa fiffitowa idon mommy yayi waje taji damkar maza kakari tafarayi idonta yajuya jaa tana kokarin shekewa domin shaqar da Mr azaad yamata bana wasa bane ya daka mata tsawa lokaci da ya yacanza fuskan nan tayi ja tsaban bacin rai " kimin shuru ko kuma kiyi dana sani" mit mommy tayi ganin ya hayayyako gashi yaki sakinta cillar da ita yayi ta kifu akasa tana rike wuyanta hade da nishin wahala ga idonta yayi ja , dakyar ta rarrafa tazauna akan kujera tana tunani iri_iri shi meyasa Mr azaad zeyi mata haka yaron da ma zata iya kirga sau nawa magana yataba hadasu tunda aka haifeshi be taba shiga part dinta ba sede in yanason hira da anty zainab da anty shayida ya kirasu suzo part din ummi ko a garden.

Tanzarzar na kallon abinda yake faruwa ta mudubin tsafi nan yagane asirin mommy yatonu kuma inde taji bakar azaba zata iya tonawa sauran yan kungiya asiri hakan yasa yamata magana ta cikin madubin " hafsat kisan hanyar dazakiyi ki tsere musu domin yarigada yasan komai akanki " jin abinda tanzarzar yafada mata yasa taji wani irin fargaba yakamata bawai dan na asirinta yatonu ba sedan tasan muddin ta fadi wata kalma dangane da yan kungiya to tabbas nata yakare, dago kai mommy tayi ta kalli Mr azaad dashima firgitattun idonshi na kanta , wuff tamike zata da ki kasa domin ta bace kenan , sarauniya ta damki dantsen hannunta ta baya , wurgi da ita kasa sarauniya tayi tana binta da muguwar kallo da idanunta masu firgita abokan gaba fuskan nan babu alamun sassauci ko rangwama atare da ita. Mamaki ne yakama Mr azaad ya akayi fanan tasan da yana nan Kuma ga abinda yakawoshi, laakari da irin shigar dake jikinta dayayine yagane ba fanan bace sarauniya fadima ce , sarauniyar nasminaya, hakan yasa yamike yatsaya yana kallonta ganin ko inda yake tsaye bata kallaba bare yasa ran zatamai magana. abinda yayi laakari dashi shine duk sanda ta bayyana a asalin sarauniyarta tofa wasu dabi'un ta kamar bata sansu ba wata zuciyar ta ce mai " karfin jaaazana ne yasa hakan domin inta bayyana, sarauniya ce bawai fanan ba " gabanshi ne yatsinke lokaci daya, da ya tuna kenan fanan intabar nasu duniyar mantawa zatayi dasu gabaki daya kenan bazama tasan da zamansu ba balle tayi tunanin dawuwa wajan ahalinta, dafe kai yayi dayaji yana juyawa.
daga inda sarauniya take tsaye ta daga hannunta tayi pointing mommy dake yashe akasa , kyasta yatsunta guda biyu tayi nan take igiyoyi suka fara daure mommy dauri bana wasa ba suka mata tamau yanda ko numfashi dakyar take iya fitarwa. tana gama daure mommy kuwa ta bace tabarshi tsaye awajan.
Chapter 35 · 0% Book details