Sashe 48
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yana fada shida sarki azaad suna hira da sauran kawunan shi , kiran sunanshi yaji anyi hakan yasa yaɗago saboda yayi tsammanin daya daga cikinsu ne ya kirashi din , kallon fuskokinsu yayi yaga hirama sukeyi babu wanda yakirashi daga cikinsu karajin kiran yayi ana fadin " azaaad kafito ina waje " mikewa yayi yace musu yana ɗan zuwa tafiya yakeyi bega ko alamun wanda ke kiran nashi ba acikin masarautar hakan yasa yanufi gate fadawan dasuke wajan suka bude mishi gate suna kokarin yi mishi rakiya ya ɗaga musu hannu alamar baya bukata yayi waje , titin masarautar shuru babu kowa tafiya yakeyi har lokacin bega kowa ba wani dattijo yagani yana zaune aƙasa kayan jikinshi duk ya koɗe yarufe jikinshi da yar bargo ga kwanon baranshi agabanshi wuce shi Mr azaad yayi, sekuma zuciyarshi ta raya mishi wani abu dawuwa yayi wajan wannan dattijon yazauna kusa dashi bedamu da ya jikinshi zeyi datti kokuma wani abu ba ya ce " kaine ka ƙirani ?" batare da dattijon yaɗago kai ya kalleshi ba yabashi amsa da " nine nayi ƙira agareka " kallonshi dakyau Mr azaad yayi kafin ya ce " shin ko zan iya sanin dalilin wannan kiran " gyara bargon da yarufe jikinshi dashi dattijon yayi yafara magana " nasan kanata tambayar kanka menene abinda yake shirin faruwa dakai abisa sabon al'amarin daka tsinci kanka a ciki na jiye_jiyen maganar mutane harta da wa'yanda ba mutane ba , abinda bakasani ba shine kaidin ɗan baiwane , kana dauke da baiwar jin magana duk nisar dakuwa akayi ta zaka iyaji . Awannan ƙarnin ku uku ne kaɗai masu irin wannan baiwa kune akewa laƙabi da ' majiya ' azaad kaiɗin majiyine yau na amsa maka wannan tambayar taka" cike da zallar mamaki Mr azaad yake kallon wannan dattijon dayake mishi wa'yannan bayanan domin tabbas wani sabon al'amarin daya tsinci kanshi aciki yana damunshi sannan kullum cikin tambayar kansa yake yi menene dalilin faruwar hakan, tambayar dattijon yayi ya ce " to kaiɗin wanene? " yaye bargon daya rufe jikinshi dashi dattijon yayi fuskanshi ya bayyana fara ni ƙal ga gashi ne ajikinshi kwantacce tako ina hatta fuskantar shi akwai suma kallon cikin idon Mr azaad yayi da idonshi da ya kasance kwayar idon jane da fari ba kalar na bil adama bane ya ce " sunana tsuntsu arnass me baku bayanai akan wasu lamuranku dasukeson sarƙe muku, yanzu babban abinda yakawoni wajan ka shine magana akan sarauniyar nasminaya, wato cikekkiyar yar baiwa me dauke da karfin ikon jaaazana atare da ita. ta kasance yar baiwa ce me bada abubuwa guda biyu a rayuwar dan adam , tana dauke da baiwar taimako dakuma baiwar yaɗa farin ciki a duk inda ta zauna wannan dalilin yasa setafi kowa iya sarrafa karfin ikon jaaazana ajikinta saboda shi jaaazana baya bayan mugunta hakan ne ya sanya ya zabeta a domin baiwar da Allah yayi mata atare da ita , sarauniya fadima inharde tana waje farin ciki yana bayyana awannan waje sannan tana taimako da iya iyawarta.
Abu nagaba da baka sani ba shine kungiyar BAPHOMET sun shirya ganin bayanta adoron ƙasa domin cikar muradinsu hakan yasa suka nemo wanda yakasance dan baiwa domin suyi amfani dashi wajan tarwatsata sannan su mallaki jaaazana , daga zaran sun mallaki jaaazana kuwa komai ze dagule babu me iya ceton al'ummar duniya fa ce Allah SAW, shin kokasan dawa zasuyi amfani domin cikar muradinsu?" Ya wurgawa Mr azaad tambaya idonshi cikin nasa , jikin Mr azaad yayi sanyi sosai dakyar ya iya furta kalmar" ah ah bansaniba "
Murmushi arnass yayi ya ce " kaine nan " arazane Mr azaad yake kallonshi ya nuna kanshi da yatsarshi ya ce " arnass nikuma ? Me dalilin hakan ? " Cigaba da magana arnass yayi " tabbas dakai zasuyi amfani ko kana so , ko bakaso dole dakai zasuyi amfani suna nan suna shirya yanda zasu jefa maka wutar kiyayyar sarauniya acikin zuciyarka wanda hakan ne zesa duk wani sirrin abinda yake wakanan zaka dinga sanar dasu , sukuma zasu shirya yanda zasubi su sameta harsu cire narƙekken jaaazana ajikinta wanda anacireshi ta karfin tsiya dole sarauniya zata mutu su kuma zasu samu abinda suke nema bayan bukatar su ta biya zasu kashe duk yan masarautar nasminaya kasan da sa hannun waye za'a kashe sarauniya? da sa hannunka za'a kashe ta . daga bayan bukatar su ta biya zasu tarwatsa kungiyar SATANIC sekuma abu nagaba zasu kashe ka domin ka gama musu amfani sesu dawo kan al'ummar duniya su fara yaɗa zalunci su . Wannan abun da nake fada maka du ka nanda yan watanni nan zasu faruwa kuma yanzu kaine sa ransu kaine makaminsu azaaad majiyi " idon Mr azaad ya rine yakoma jaa jin irin wannan tashin hankalin dake tunkarosu babban abinda yafi daga mishi hankali shine jin dasa hannunshi za'a tarwatsa sarauniya sannan akasheta shikuma yayi alƙawarin baze taba basu wannan dama hakan yasa riko dukka hannayen arnass dasuke kamar ƙankara tsabar sanyi ya ce" arnass shin babu wani hanya da zaabi domin ganin wannan mummunar ƙudirin nasu be faru ba ? Wallahi da inbada wannan gudunmawan ganin bayan wacce nake so gwara in rasa raina " jinjina kai arnass yayi yana kara girmama wannan girman soyayyar tasu domin sudin an haifesu ne saboda junansu hakan yasa daya ze iya bada ranshi ga dan uwanshi , shafa kan Mr azaad arnass yayi ya ce" akwai hanya daya dazaabi amma hakan ze iya sawa ka rasa naka baiwar jin , se bayan shekara hudu zedawo gareka " a gaggauce Mr azaad ya ce" na amince koma miye inhar hakan zesa bazasuyi amfani da ni ba" " hakan yayi kyau azaaad inkayi hakan shine Kacika babban masoyi, yanzu anan wajan zan zare maka baiwar jinka dakake dauke dashi zantafi dashi inje in ɓoye , zaka koma yanda kake ɗa , zaka dena jin wa'yannan maganganun , hakan ze ɓata musu nasu shirin zasu dena bibiyarka domin abinda kake dauke dashi din babu. Wannan kadai ze hana faruwar wannan lamarin, amma kasani nan da yan watanni za'a tabka babban zaluncin da ze farkar da jaaazana dake jikin sarauniya awannan ranar kuma zata tafi tafiya kuma kusan na har abada " tunda Mr azaad yake arayuwarshi betaba shiga irin wannan tashin hankalin ba seyau yanayin yanda kirjinshi yake bugawa kadai mutum yaji yasan akwai babban tashin hankalin dake damunshi wasu irin zafafan hawayene suke saukowa daga idonshi , tabbas abinda zesaka jajirtacce kuma jarumin namiji kamar azaad zubar da hawaye tabbas ba karamin abu bane . Dafa kafadarshi arnass yayi ya ce " kayi hakuri azaaad kasani koda ace tafiyarta bata rabaku ba to tabbas mutuwa dake kan kowa ze rabaku " yafada mishi yana sa hannunshi atafin hannun Mr azaad ya fara magana , wani irin kananun taurarine suke fitowa daga jikin Mr azaad suna shiga cikin kwanon baran arnass , har suka shige gabaki daya cikin kwanon sake mishi hannu yayi yarufe kwanon yamike tsaye , mikewa Mr azaad yayi shima arnass ya ce mishi " daga rana irin nayau bazaka sake jin wani magana dake nesa ba nafitar da majiyi ajikinka se nan da shekaru hudu zasu dawo gareka ni zan tafi ka isarmin da sakon gaisuwana awajan jaruma , sadaukiya sarauniya, duk sanda kakeson ganina kawai ka kira sunana da izinin Allah zan bayyana nabarka lafiya " kallonshi Mr azaad kawai yakeyi saboda baya cikin yanayi najin ze iyayin magana da kowa ba , murmushi arnass yayi mishi sannan yakoma wani irin tsuntsu me ban sha'awa yafire sama.